Showing 123001 words to 126000 words out of 163036 words
Afrah ke mata. Sosai ta baza ƙamshi aka toshe ido da glass bayan ta yana ƙaramin veil a kanta ta naɗesa a kafaɗunta. Dan ƙyau kam tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. Cikin takun nan nata na yanga da gayu ta fito ɗauke da tarkacenta, sai key ɗin motarta da aka kawota da ita kaɗaice a nan ɗin sauran ba'a kawo mata ba. Kanta tsaye ta doshi hanyar fita, sai dai me tana taɓa ƙofar ta jita a rufe. Ƙaramin tsaki taja da duban agogon dake a tsintsiyar hanunta. Sam bata son makara, dan haka ta nufi kitchen da nufi fita ta ƙofar baya, sai dai nan ɗin ma ɓam. Cikin ɗan jin takaici ta rumtse idonta da komawa falon, kayan hanunta ta zube a saman kujera ta nufi ɗakin Smart. Yana tsaka da barcinsa ya ji ana bubbuga masa gefen filon daya tada kai, da ƙyar ya buɗe idanunsa da ke jingim da nauyin barci ya sauke a kanta. Kauda natan tayi da ga kansa a gadarance ta ce, “Malam bani key zan wuce. Ka wani bi ka rurrufe ƙofofi kamar a prison”.
Kallonta yake shi dai da ga sama har ƙasa har takai ƙarshen maganarta. Ƙoƙarin tashi yay zaune ya jingina da gadon ya harɗe hannayensa a ƙirji rabin ƙafafunsa zuwa ƙugu lulluɓe cikin bargo.”
“Malam ka tsaya kana kallona kamar wata hoto, bayan kuma kaji na faɗa maka bana son na makara ko? Inada important abubuwa a office”.
Wani ɗan jan idanunsa yay kamar zai lumshe sai dai kafin ya rufe ɗin ya sake buɗesu a kanta. Cikin yanayin muryar wanda barci bai isa ba da ɗan taɓe fuska ya ce, “Ban fahimceki ba, sake maimaitawa”.
Kallon takaici ta watsa masa. Dan ta fara hasala. Amma sai ta danne da ƙyar a ɗan zafafen dai ta ce, “Wai kai miyasa komai a wajenka abin wasa ne. Kasan ko mi kake yi? Ka bani key ni ba neman jidali nake ba”.
“Humm ke idan ance miki ki fita a yau a kuma haka yanda kiken nan sai ki fitan?”.
Harara ta watsa masa cikin gatsali da faɗin, “Sai ka hanani fitar idan na tashi”.
“Okay haka kika ce? To ko zan tabbatar miki ko ƙofar gate bazaki fita ba, idan kema kin shiga duniyar mafarkinne sai ki farka, dan idan har kinga kin fita a gidan nan da sunan aiki sai next week ma. Sannan bada wannan shigar ba idan har kina son aikin naki kenan. Dan bazan hanaki yi ba saboda wasu dalilai na, amma ba'a yanda ranki ya raya miki ba. Yanzu a ƙarƙashin ikon Aliyu Mika'il Idris Mawashi kike ba su Daddy ba. Abinda ya tsara a gidansa dole shi za'ayi ko ana so ko ba'a so. Garama ki nufi kitchen haɗa mana break fast”. Da ga haka ya juya yay kwanciyarsa. Wani irin ƙarajin kiran sunansa ta ƙwala a matuƙar zafafe. Sai kawai yaja filo ya ɗaurama kansa ya toshe kunnuwansa ma ya maida idanunsa ya lumshe. Masifa ta fara zazzaga masa zuciyarta na raɗaɗi kamar zata fito ta baki, amma bawan ALLAHn nan yay biris da ita, da ya ga ma filon bazai masa ba sai ya ɗauki bluetooth ɗin sa da ke a bed side drawer ya manna a kunne ya saka ƙira'a abinsa. Fita tayi a ɗakin dan ta fahimci sai ta haɗashi da Daddy. Wayarta ta cira a handbag ta shiga dannama Daddy kira. Bugu biyu kuwa ya ɗaga dan fitowarsa a wanka kenan shima zai yi shirin office. Kafin ma yace wani abu ta sakar masa kuka da faɗin, “Daddy kaga mutumin nan ko? ALLAH ina raga masa ne saboda abinda Baba da Uncle You suka cemin, amma idan ya ce muyi ta inda ya ɓullo zan hargitsa masa rayuwa, nifa babu lallai babu dole zan dawo gida Daddy, garama komi Baban zaiyi yayi....”
Duk da abinda Daddy keji na yunƙuro masa shima sai ya danne da ƙyar, cikin tausasa harshe ya ce, “Baby kinga relax mi yake faruwa? Mi yay miki?”.
“Daddy Office fa zanje yabi ya kulle ƙofofin, naje ya bani key amma yay min banza yama saka bluetooth a kunne wai babu inda zanje sai next week, irin like kamar wata baiwarsa da ya saya a kasuwar bayi”.
Ƙololuwar ɓaci ran Daddy ya kai, a taƙaice ya ce “Ina zuwa”. Ya yanke kiran, number Smart ya lalubo a karo na farko ya danna masa kira. Kasancewar bluetooth a kunnensa ya sashi jin shigowar kiran a bazata, hannu ya kai ya zare guda ɗaya yana kai hannu kan wayar tasa ya ɗauka dan ganin wanene mai kiransa haka. Bai san number ɗin ba, dan baida Number Daddy, kamar zai share sai kuma dai ya ɗaga gudun kar yay mistake.
“To sannu isashshe”.
Kalmar data fara dukan kunnensa kenan a maimakon sallama.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣9️⃣
........Cikin sa'a kuma ya gane muryar Daddy. Amma sai ya danne bai nuna ba, cikin dai nutsuwarsa ya ce, “Assalamu alaikum”.
“Da sallamar nake da buƙata da ita zan maka ai. Miye dalilinka na hana Mawaddat fita office ka kuma kulleta?”.
Shiru Smart yayi kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya furzar da numfashi kaɗan yana gyara kwanciyarsa. Sake tausasa muryarsa yay fiye da ɗazun ya ce, “Kayi haƙuri Daddy sallama wajibi ne ga musulmi, haka ma amsata ga wanda akaimawa. Kai ya kamata ka tunatar da ni hakan a matsayinka na mahaifi. Dan haka kayi haƙuri ka amsa min sallamata kafin muyi maganar da kake son. Assalamu'alaikum!”.
A cinkushe Daddyn ya amsa masa, Smart ya ɗan girgiza kansa sannan ya tashi zaune sosai. Cikin sake tsantsan da kai na girmamawa ya ce, “Daddy ina kwana”. Bai amsa masa ba nan kam. Shima sai bai damuba ya ɗora da faɗin, “Zan sake baka haƙuri a karo na biyu Daddy, dan ALLAH karka saka baki a wannan zancen dan a yanzu Mawaddat tana ƙarƙashin na ne. Inada damar zartar mata da hukunci akan abinda ya dace da kuma banbance mata wanda bai dace ba. Kai mana fatan alkairi kawai shi mukafi buƙata da sanya albarkar ku, na riga na gama yanke hukunci akan hakan babu kuma tunanin canjawa a tattare dani amin afuwa. Na Barka lafiya”. Daga haka ya yanke wayar tare da kasheta gaba ɗaya ya koma yay kwanciyarsa ransa fal mamakin halin surukin nasa.
Ƙaramin hauka ne ya kusan samun Daddy da ga can jin Smart ya yanke wayar bayan ya gama datsa masa zafafan magana kamar yanda zuciyarsa ta fassara masa. Ƙoƙarin sake kira yayi amma sai wayar switch up. Kaɗan ya rage ya maka wayar da ƙasa. Amma sai ya fasa ya maida akalar kiran kan Uncle Yousuf. Suna zaune shi da yara da akaima shirin makaranta suna breakfast kiran Daddyn ya samesa. Bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga, sai dai kiran sunansa da Daddy yay a tsawace ya sashi rumtse idonsa. Sai kuma ya miƙe yabar daining ɗin ya nufi bedroom ɗinsa. Cikin tausasawa ya ce, “Yaya lafiya dai kuwa?”.
“Yousuf yanzun nan ka kira ɗan iskan yaron can ka faɗa masa ya sakar min yarinya tunda ba ubansa ya haifa min ita ba, har ni yake da bakin gayama Mawaddat ta koma ƙarƙashin ikonsa ya kuma yanke hukunci a kanta bazai canja ba kamar shine ya haifa min ita.”
“Ya Salam. Yaya Please calm down dan ALLAH muyi magana mana. Wlhy sam ban fahimci mi kake son faɗa min ba. Mi Aliyun yay maka ne?”.
“Miye ma bai mun ba, babu abinda ya manta na rashin kunya bai faɗa min ba. Shiyyasa tun farko na faɗa maka yaron nan ɗan zafin kai ne zai iya bamu matsa ta duk inda bamuyi zato ba. To gashi ya fara, ya kulle gida ya hanata fita aiki, ta masa magana ya ce sai next week babu inda zataje, ta kirani nai kiransa nai masa magana amma ya daddatsamin magana son ransa tsabar shi ya cika cikakken ɗan iska.”
Girgiza kai Uncle Yousuf yayi, kafin ya ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, ka dai san mi ɓacin rai ke haifar maka a yanzu. Zan kira shi na masa magana sai naji dalilinsa. Sai dai ma yaya banda abunka ai bai kamata ka biye mata kai kiransa ba, karfa ka manta yau kwana biyu kawai da tarewarsu, ai bai dace ba ta fita aiki sai mutane suyi magana kadai san yanda al'amarin yake yanzu mutane sun bar damuwa da al'amarin su sun koma hango na wasu”.
“Yousuf bana buƙatar jin komai, sannan ni babu ruwana da wasu mutane ko abinda zasu faɗa, farin cikin yarinyata kawai na sani. Shi wanene da zai tauyeta bayan da aikinta ya ganta, sannan waya faɗa masa shi ɗin har ma yanada wani ƙarfin iko a hannunsa a kanta da zaima mutane wani gadara koda ace auren nasu mai muhimmanci ne. Wannan shine na guda tun farko amma ka kasa fahimtata, shiyyasa kuma nace ayi komai a rubuce amma nan ma ka wani kakkaresa gashi nan tun kan aje ko ina ya fara nuna halinsa, a haka kwanakin da kace ɗin zai cika yay abinda ake so? an faɗa masa akan ƴata zai nuna gargajiyancinsa ne”.
“Naji duk na ɗauka kayi haƙuri zanyi magana da shi yanzun.” daga haka Uncle Yousuf ya yanke wayar batare da ya jira cewar Daddy ɗin ba. Hannunsa ya kai ya dafe kansa, sai kuma ya girgiza a hankali ya ɗago yana murmushi mai sanyi. A fili ya furta, “Yaya yaya kenan, kai da gaske jiran cikar lokacin kake kenan? Humm aiki ya sameka. Aliyun dama shine ai dai-dai da kai game da lamarin Mawaddat duka kai da itan. Ashe babu daɗi lokacin da ka dakatar da Aunty Kareema fita aiki a dalilin Marigayiya, duk da hakan ya mata ciwo kuma ta haƙura iyakarta kuka ta share hawayenta, ashe ita daga sama ta faɗo? Kai gashi hana fitar kwanaki kawai da akai ma taka ɗiyar ya zafafaka har haka. ALLAH na gode maka da ka kaini da rai da lafiyar ganin irin wannan ranar, shiyyasa akace yanzu ma tun a duniya ake fara hisabi basai an mutu ba. Muje zuwa yanzu aka fara wasan ai. Mai ƙarfi sai yaci kofin”. Ya ƙara sakin murmushi. Ƙoƙarin kiran Smart yayi sai ya samu wayar switch up. Ya sake sakin murmushi da faɗin, “Kaga mazan ƙwarai”. Da ga haka ya miƙe ya fito abinsa. Ya samu yara har sun wuce, sai Aunty Saliha da ke zaune tana tsumayen fitowarsa dan ya sakata a ruɗani.
“Abban Ra'is lafiya dai ko?”.
Ajiyar zuciya ya saki yana kaiwa zaune, ta turo masa kunun data sake zuba masa dan wanda ya bari ya huce. Sai da yasha kusan sau uku sannan ya dubeta. “Yaushe zakuje gidan Mawaddat ɗinne?”.
“Sai zuwa anjima kaɗan dan muje mu dawo da wuri ko”.
“Inaga ku kuyi zamanku, su Hussain suje sukai mata, motocin ta kuma a barsu ba yanzu ba.”
“Amma wani abu ya faru ne?”.
“Zai dai faru Saliha.......” nan ya zayyane mata komai daya faru. Cikin damuwa ta ce, “Amma Yaya da bai kirashi ba ai. Dan Aliyun ya fishi gaskiya, yaza'ai amaryar da aka kai gidan miji shekaran jiya kuma a ganta a office yau dole zai iya zama abin magana. Inda waɗan nan ƙananun matsalolin zai dinga sawa iyaye na neman sakin ƴaƴansu ai da kowama ya zama babu aure kenan. Ni sai nake ganin kamar maganar Aunty Kareema zata iya zama gaskiya....”
“Hummm ku mata kullum tunaninku iri ɗaya ne, miyasa komai a rayuwa idan yazo mana a yanayin da ba haka muke tunanin ganinsa ba sai mu dinga ɗaukarsa asiri. Nasan asiri yana ɗaya daga cikin abinda al'ummar mu suke kallon babbar mafita ga al'amuransu a halin yanzu, sai dai bai kamata muna tsuke dukkanin zukatanmu waje guda ba akan kowanne bigire muyi masa kallon asirin. Amma dai bari nai miki wata tambaya, shin ku minene dalilinku na kallon al'amarin Yaya matsayin asiri?”.
Duk da maganganunsa na farko sun shigeta sai bata gaza wajen faɗa masa hujjojin da suke kallonba su. Ta ce, “Na yarda da zancenka nima, sai dai ka kalla wani abu Abban Ra'is. Kafin auren marigayiya kai da kanka ka bani labarin ba haka Yaya yake ba sam, sannan Yaya nada ilimin addini mai zurfi da yasan minene aure da ƙaddara. Amma kaga yanda idanunsa suke rufewa ta yanda idan wani aka faɗamawa da bai gani ba zai iya ma ƙaryatawa. Dolene muyi tunanin akwai sammu tattare da shi”.
Murmushi yay da cewa “Hummm! Saliha kenan. Duk ilimin mutum bakwa tunanin son zuciya zai iya sakashi ajiye ilimin gefe ya aikata abinda baida alaƙa dana masu ilimin. A al'amarin Yaya babu wani asiri, akwai ɓoyayyen al'amarin da yake ɓoyewa dai tun kafin auren Mawaddat ɗin, sai da ya auretanne ya fara fitowa, wanda tamkar ALLAH ya jarabcesa da sanya masa tsoron faruwar irinsa akan Mawaddat ne, ba komai ya kawo hakan ba kuma sai dan itace mafi soyuwa a ransa ko kuma ana masa barazana da ita, shiyyasa ma tun farko ya gagara yarda da kowa game da kula da al'amarin ta, a tunaninsa shi zai iya kareta akan komai, sai kuma akai rashin sa'a ƙaddarorinta ba'a fatar jiki suke ba ko mahallin zamanta balle yay tunanin kuɓutar da ita a yanda yaso da kuma ƙarfinsa da wayonsa. Dan haka kuma bar damuwa da al'amarin sa ana gab da zuwa gaɓar da zai fallasa kansa da kansa batare da ya sani ba. Yanzu Mawaddat itace mafi ƙololuwar abar tausayi, dan ina matuƙar jin tausayin rayuwar yarinyar a dalilin halin data tsinta kanta a ciki.”
Yanda ya ƙare maganar cikin matuƙar damuwa da ɓacin rai yasa Aunty Saliha tasowa ta dawo kusa da shi tare da dafa kafaɗarsa. “Kayi haƙuri Abban Ra'is, tabbas tausayin Mawaddat dolene ga duk wanda ya fahimci muhimmancin rayuwa. Sai dai namu addu'a ce a yanzu tsakaninmu da ita, mu kuma cigaba da bama Aliyu goyon baya akan abinda ya fara, dan a yau na sake gamsuwa da fahimtar hikimarka ta haɗa wannan auren. Inaga kuma lokaci yayi da shima zaka fara aiwatar da shirinka na taimakonsa da tun farko shine dalilin jawosa jikinka da kayi, dan namiji bazai yiwu ya rayu babu abinyi ba yakan ja masa ƙasƙanci tsakaninsa da mace, musamman irin Mawaddat da tunda ta tashi bata san minene babu ba”.
“Hakane kam, insha ALLAHU kuma a yanzu haka ina kan shirye-shirye ni da Hameed, dan kin san al'amarin nasa sai anbi ta bayan fage yazo a bazata tamkar yanda maganar auren nan tazo a bazata. Dan bayyanawa na nuna zaburar da mai ƙullin ne”.
“Tabbas hakane, ALLAH ya bada nasara yasa shima iyakar wahalar tasa ce tazo. Ku kuma da kuke ƙoƙarin ALLAH ya saka muku da alkairi ya hana bayanku kuka”.
“Amin ya rabbi. Bara na kirata idan naga da yiwuwar kuje ɗin to”.
“To ba damuwa”.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣0️⃣
.......Zaune take a falo dafe da kanta dake matuƙar sara mata saboda ɓacin rai, a yanda take jinta zata iya aikata komai akan mutumin nan, amma ta zauna tsumayen kiran Daddy ne da yace ta dakacesa, sai dai an shafe kusan mintuna ashirin kenan shiru, hannunta ta janye tare da kallon wayarta da idanunta da sukai wani irin jazur. Wayar ta ɗauke da tunanin sake kiran Daddy ɗin kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Wayar ta tsaya tana kallo kawai, sai da ta kusa tsinkewa ta iya ɗagawa ta kai kunne, sai dai tayi shiru dan in har tai magana kuka ma zai iya ƙwace mata. Ƙaramin murmushi Uncle Yousuf yay da ga can da bazata iya jiyo sautinsa ba, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “My Daughter yau babu gaisuwa ne?”.
Nan ma shiru ta kasa magana. Tofa yasan an kai ƙololuwar ɓacin rai kenan, dan haka ya sake tausasa harshe cikin komawa serious ya ce, “Mawaddat miya faru? Ko baki da lafiya ne?”.
Hawayen da take riƙewa ne tun ɗazun suka kufce mata, da rawar murya irin ta mai kuka ta ce, “Papa bazan iya ba, bana son damuwa gida zan dawo. Wannan ba rayuwan da zan iya yi bane...”
“Kwantar da hankalinki sanarmin mike faruwa?” ya faɗa like bai san komai akai ba. Da ƙyar ta iya masa bayanin abinda ya farun kamar yanda Daddy ya sanar masa. Anan ɗin ma murmushi ya sake yi ɓoyayye. Kafin ya ce, “Mawaddat rayuwar aure haka take, a komai ita mace ƙarƙashin ikon mijinta ta ke, wajib ne kuma yimasa biyayya in har shima bai keta dokar UBANGIJI ba ko jagorantar ta saɓa masa. Anan kam ba'a yarda ta masa biyayya ba sam, dan ba'ama wani biyayya ko tarayya wajen saɓama ALLAH......”
“Bazai yiwu ba Uncle You, domin ni da kai da shi duk mun san matsayin wannan zaman ba sunansa aure ba, Please Uncle kace masa ya sakeni idan