Showing 114001 words to 117000 words out of 163036 words

Chapter 39 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

463

iya ƙara sawa ba, common Malama ɗakko hijjab ɗinki ki wuce gida, wannan abincin ki tafi da shi a bama wani dan nan dai bacinsa za'ai ba”. Da ga haka yay wucewarsa hanyar bedroom. Sum-sum Asma'u ta nufi kwanikan da suka kammala cin abincin ta tattara zata kai kitchen sannan tazo ta wuce dan tasan shifa baya magana sau biyu. Takaicin wannan nuna isar tasa ya saka Lulu miƙewa a fusace tabi bayansa. Burumm ta shigo ɗakin dai-dai ya zare rigarsa zai cire wandon, amma sai ya dakata ya tsaya kallonta.
      “Malam wai kai miyasa kake son dinga juya mutanene kamar wasu ƴaƴanka?”.
      Kallonta kawai yake yi batare da yace komai ba. Aiko sai ta sake fusata da takaicinsa ta ce, “To babu inda zataje”.
         “Idan kece sama da ni kenan”.
      Ya faɗa yana ƙara tsatstsareta da idanu. Itama a tsiwace ta ce, “Oh da mika ɗauki kanka?”. Karo na biyu ya saki murmushi, dan shi kam ƙarfin halinta tunba yanzu ba dariya ma yake bashi. A hankali ya tako zuwa gabanta daf, ta wani yamutsa fuska tare da matsawa baya tana hararsa, sake matsawa yay shima ta matsa itama, shima ya bitan dai, a masife ta ce, “Miye haka wai?”.
      “Ina son nuna miki abinda na ɗauki kaina ɗin ne Madam” yay maganar dai-dai suna danganewa da bango idanunsa cikin nata. Yanda suke daf-daf ga hannunsa da ya tokare a bangon ya bashi damar dabaibaye ta da ƙyau har tanajin numfashi na neman mata wahalar shaƙa dan in ma ta shaƙa ɗin ƙamshinsa ne iskar da kawai take iya zuƙowa ya sata faɗin, “Aliyu bana son iskanci da raini fa. Dalla matsa min”..
            “Haba Madam! K bakiji kunyar faɗar sunan ba haka gatsal sunan mijinki ne fa”. Yay maganar da sake ranƙwafowa yay mata rumfa ta yanda jikinta ke neman fara rawa. Amma sai ta dake dan bata yarda itafa yaga gazawarta ba. Hannu tasa ta turashi amma ko gezau, sai ma wani lumshe idanun da yay ya sauke akan hannayen nata da ke a saman jikinsa. Da sauri ta janye tana jan tsaki da faɗin, “In ma abinda banzan zuciyarka ke faɗa maka kenan to ka goge, dan tamkar kana mafarki ne a gaɓar da ake gab da tashinka da ruwan sanyi, wannan auren baida maraba da wasan drama ɗan son banza phone store”.
      Idanunsa ya lumshe da buɗewa a lokaci guda yana cafko hanunta dan shirin duƙewa take tabar wajen. “Haba Madam ya kuma zaki wuce ban nuna miki abinda na ɗauki kan nawa ba?”.
          “Aliyu!!”.
     Ta sake faɗa da ƴar tsawar takaicin kiranta Madam da yake yi dana goga jikinsa a nata.
       “Uhmm Madam”.
   Ya amsa mata da wata irin kasalalliyar muryar son sake ƙular da ita yana sake kusanta fuskarsa gab-gab.........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣4️⃣



........Ƙarshen kuma firgita Lulu ta gama kaiwa, sai dai kafin tai wani yunƙuri a matuƙar bazata taji saukar lips ɗinsa masu sanyi akan tausasan nata masu sheƙi da ƙamshin lipgloss ɗin data ɗan saka, cin abinci ma yasa duk ta shanye rabi. Iyakar rikicewa da firgici Lulu ta shiga, gashi ya mata ritsawar da ko iya motsa kanta ta gagara yi balle tace zata iya ƙwacewa. Shi kansa da yayi ne domin kawai tabbatar mata ba drama ɗin data ambata ɗin bane jiyay gaba ɗaya jininsa na yamutsawa, dan karo na farko kenan a rayuwarsa da haka ta faru tsakaninsa da mace. Da ƙyar ya iya juriyar shafe minti guda sannan ya sake mata lips amma bai matsa da ga jikin nata ba, sai ma magana da ya fara cikin kunnenta muryarsa a wani irin sarƙe duk da jarumtar son hana hakan bayyana da yake nunawa. “Waya gaya miki baƙo na kwana gidan sabbin aure ne? Ai sai ya jiyoma kansa abinda zai hanashi barci, bar yarinyar mutane ta tafi gidansu girmanta bai kai ba. Sannan ki rage ɗaukar kanki sama can ƙololuwa, dan a wannan fadar Aliyu Hydar shine ZAKIN KI. Fassara SARKIN KI Mawaddatan'warahmah Isma'il Ibrahim Jiƙamshi”. Ya ƙare maganar da ɗanja baya yana wani kashe mata ido ɗaya ya bar wajen gaba ɗaya.. Suɓul numfashin Lulu ya nema barin jikinta. Takaici ne, baƙin ciki ne. Mamaki ne bata sani ba. Abinda kawai ta sani wannan itace rana mafi abin takaici da koma baya da tazo mata a tarihinta. Bakin illiterate driver ɗinta ne cikin nata, ya zuba mata yawunsa ta sha fa a cikin cikinta. Wayyo ALLAH shike nan tata ta gama ƙarewa....
       Kamar Smart ya san mi take tunani, dai-dai yana hawa gadon ya wani lashi lips ɗinsa da faɗin, “1-0 kenan, amma fa yawunki akwai daɗi Madam. Ina fatan nawa ma akwai ɗanɗano na musamman irin wanda iyali zasu so. Dama na faɗa miki jahilin baƙauyen nan fa ɗan takife ne, ki guji masa gatsali dan bajin magana yake ba. kije ki sallami yarinyar mutane inba haka ba na tashi na ganta a gidan nan ita ranta zai ɓaci, ke kuma zakisha yawun baƙauyenki”.
       Harara ta watso masa da faɗin, “Shash....” bata ƙarasa ba ya yunƙura zai tashi. Da gudu ta fice kuwa tana nunashi da yatsa da faɗin, “Wlhy sai na koya maka hankali. Maye!”.
            Komawa yay ya kwanta yana mai lumshe idanunsa da sakin ƙaramar dariya. A hankali ya furta, “Na samu promotion da ga illiterate velleger zuwa MAYE kenan”. Sai kuma ya kai hannunsa saman lips ɗin nasa ya shafa yana jin wani abu na masa yawo a cikin jini har yanzu. “Ko mima ya kai ni, ni Aliyu Madam ce fa”. Ya sake faɗa yana wani ɓata fuska kamar gaske, sai kuma yaja filo ya ɗaura a saman face ɗin sa da sake faɗin, “ALLAH ya shiryeka Aliyu wannan abun kunyar da ka tafka fa wa ogarka”.

         (😂😂Ɗan manni, amma ka kwana da sanin idan muka tashi ramawa sai ka raina kan ka malam🥱 Tom😏🚴).


_________★


A hankali Mommy ta jinjina kanta tare da sakin ajiyar zuciya na ɗunbin mamakin Daddy a karo na babu adadi. Kallonta ta sake maida wa garesa har yanzu yana a yanda yake zaune da tagumi hannu bibbiyu. Abincin data ajiye masa kusan tsawon awa guda har ya ƙandare shayin ko ya koma kamar ruwan sanyi. A tsakanin shekaranjiya zuwa yinin jiya yanayinsa na nuna kewar barin Lulu gidan ne kamar yanda suma duk sunji hakan a ransu, amma da ga daren jiya zuwa safiyar yau yanayin nasa sai ya ninka ko barcin kirki bata tunanin yayi, da farko tayi tunanin ko baya jin daɗin jikinsa ne. Amma koda ta tambayesa amsar da ya bata sai taji ta girmi kunnenta. Tun cikin daren take tunanin anya kuwa mijin nata kuma ɗan uwanta lafiya lau yake? Dan al'amarin nasa kuma ya fara wuce makaɗi da rawa. Ita bama ta fatan ko Yousuf yaji wannan taɓargazar tasa a wannan gaɓar dan abin kunya ne na gaske. Ajiyar zuciyar ta sake saukewa, sai kuma ta miƙe a nutsenta ta koma gefensa ta zauna. Karo na farko akan al'amurin Lulu ta fuskancesa da son tausasawa da nuna masa goyon baya ɗari bisa ɗari. Hannunsa ta kamo cikin nata tana ɗan murmushi da faɗin, “Yaya kayi haƙuri kaci abincin, ka kuma kwantar da hankalinka bari na shirya sai naje gidan na duba mana Mawaddat ɗin, duk da dai inaji a jikina yaron nan bazaiyi abinda zamuce ALLAH wadarai ba. Amma nima zuwa yanzu zuciyata tafi gamsuwa da naje na dubatan tunda babu waya a hannunta balle mu kira, tura yara kuma bazai bamu abinda muke so ba.”
       A karo na farko shima Daddy ya dubi Mommy ɗin da tausasawa a akan lamarin Lulun. Murya a sanyaye ya ce, “Kina ganin baza'ace munyi ba daidai ba Kareema, kin san fa masifar Yousuf akan yaron nan daban ce, na rasa wane irin so yake masa da bai son ace yayi ba dai-dai ba. Ni kuma wlhy ina tsoron ya illatamin yarinya a banza tunda dai ba taɓa auren nan yay ba balle muce zai kamanta dattako”.
        Shike maganar amma Mommy ita kejin kunyar, amma sai ta danne ta biye masa cikin sake kwantar da murya. “Na fahimceka Yaya, dan samarin nan na yanzu kam rawar kai ya musu yawa, duk da shi dai a fuska kamar nutsatstse amma ba'a yabon ɗan kuturu. Yanzu dai kaci abincin bara na canjo maka sai naje na gano ɗin ko yaya kace?”.
     “Shike nan, in dai kina ganin babu matsalar kije ɗin, dan nima dai hakan zai fi sama min kwanciyar hankali. Sannan dan ALLAH ki lallaɓa Yousuf ya bata wayoyinta dan mu dinga jinta akai-akai”.
          “Karka damu idan yazo anjima zan masa magana. Bari na kawo maka abincin kaci namaje na dawo da wuri kafin yazo gidan”.
    Kai ya gyaɗa mata, ita kuma ta tashi ta fice idanunta na cika da ƙwallar tausayinsa. Yayinda zuciyarta ke faman kai kawon anya kuwa mijin nata yana lafiya? Dan ita dai gaskiya a wannan gaɓar ta fara jin al'amarin nasa da girma, wanan wace irin makauniyar soyayya ce? Haka fa idonsa yay masifar rufewa akan mahaifiyar yarinyar nan a lokacin tamkar wanda baya a hayyacinsa. Anya kuwa basuyi kuskuren nutsuwar fahimtar al'amarin nan ba a bai-bai tun a shekarun baya? Kuɗi kam na iya canja mutum fiye da abinda Daddy yayi a kan Mawaddat, sai dai akan ƴarsa Mawaddat kuma fa? Idan ance soyayyar mahaifiyarta ce ta dawo kanta gaba ɗaya ai abin nasa na neman wuce makaɗi da rawa kuma, sannan ko sanda ya auri Mawaddat yanada abin hannunsa, bayan auren nata ne dai ya sake bunƙasa za'ace, gaskiya tana buƙatar yin dogon nazari a wannan karon fiye da wanda sukeyi a baya game da shi. Koda ta kawo masa abincin ma lallaɓashi tai tayi sai gashi yaci, ta sake lallaɓashi yay wanka ya kwanta dan yau kam babu alamar zaije office ma. Ita kuma ta shirya ta fice a gidan kamar gaske gidan Lulun zataje. Yo ita zata biye masa ne su zama ɗaya miya ja mata wannan abin kunyar. Gidan Uncle Yousuf tai tafiyarta, tai sa'ar samun shima yau ɗin bai fita office ba wai zai ɗan huta a gida.......

      ____________★

           Duk yanda Lulu taso lallaɓa Asma'u ta zauna hakan bai yiwu ba, dan ita dai Asma'u tasan wanene yayan nasu. Haƙuri tai ta bama Lulu akan ai zataje ta dawo kawo musu abincin rana. Amma yanzu idan bataji maganarsa ta tafi ba ya fito zai iya zane ta. Mamakin Lulu sai ya sake ninkuwa, irin wannan tsoronsa da suke ai abin yayi yawa. Amma idan yasan wata ai bai san wata ba. Sai tayi duk yanda zatai Asma'u ta dawo gidan nan da zama kafin cikar sati ukun da zatatai a cikinsa kodan ta tabbatar masa itama ɗin ba kanwar lasa bace. Da ga haka tabarta ta wuce. Kasancewar gidan shiru ita kuma bata son kaɗaici yana tayar mata da hankali ya sata miƙewa ta ɗan zazzagaya, duk da kasancewar gidan ƙarami sosai, dan ko sashen masu aikinsu ya fisa girma bai hana gidan birgeta ba. Balle ma an sake ƙawatashi da kayan da aka zuba mata, wanda har mamakin sakasu tayi ita da zatai zaman sati uku. Sai dai batace komai ba akan hakan. Ta ɗan jima a waje tana shan iska sai kuma ta koma ciki, bedroom ɗin ta, a ranta tana raya gara ta ɗan sha abubuwanta ta kwanta itama tai barci, sai dai me koda ta duba babu ledar maganin ma gaba ɗaya. Shiru tai alamar tunanin ko ta ajiyesu a wani waje ne, kai ina a bedside drawer ta barsu. Da sauri ta buɗe drawer ɗinsa amma babu alamar su, maganganunsa na ɗazun bayan zuwan su Asma'u ne suka shiga dawo mata, to ko ya fahimci abinda tai jiyan. “Wayyo ni” ta faɗa tana dafe kanta. Dama fa tayi matuƙar mamakin jin ya ɗakko topic ɗin nan, sai dai kafin tai masa tambayar da tai niyya ya fita ya barta. “Mutum nan maye ne, ya akai yay saurin ganoni” ta sake faɗa tana faɗawa saman gadon da jan tsaki. Bataso haka ba gaskiya, dan tana ganin ta samu hanya mai sauƙi da zata dinga samun abinda take so cikin sauƙi tana wasa da hankalinsa. “Mugun kai fal gadara da ƙauyanci sai shegen wayo kamar ɗan dila” ta sake faɗa cikin nuna takaici. Da ga haka tai shiru lamo abinda ya farun yanzu babu jimawa a tsakaninsu na sake dawo mata. Tsaki taja mai ƙarfin masifa ta sake juya kwanciyarta dan sam bata son tunawa, dan duk ƙaƙarin aman data dinga yi bayan barowarta ɗakin nasa batai ba, sai ɓigewa tai da yin brush kusan sau huɗu amma hakan bai hanata cigaba da jin saukar lips ɗin nasa a nata ba har yanzu. Tsaki taja tana tunzura bakin gaba. Da ga haka ALLAH ya taimakata barci ya kwasheta mai ƙarfi. Dan koba komai akwai gajiya da ƙarancin barcin na kwana biyu a tattare da ita.........✍️

         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣5️⃣



........Cike da matuƙar ɗoki Asma'u ta isa gida, kusa da Ammah ta zauna da ke kallonta ganin yanda take ta faman washe haƙora. “Auta lafiya kuwa irin wannan washe baki haka ko suruki na samu?”. Adda Sa'adah ta faɗa cike da zolaya. Su Adda Suwaiba da ke ta shirin wucewa gidajensu suma dai duk idanu suka zubawa Asma'un. Dariyar ta sake faɗaɗawa tana ɓoye fuskarta a jikin Ammah da faɗin, “Kai Gwaggo nifa ba haka bane, zan faɗama Ammah albishir ne”.
“A to muma sai a faɗa duk muji ai”. Cewar Gwaggo Sa'adah. Asma'u dai na dariyarta ta ce, “Gwaggo dama fa zan sanarma Ammah ne matar Yaya itace lawyer ɗin da take so ɗin nan mai taimakon mutane musamman akan harkar fyaɗe”.
Kallonta Ammah tai da sauri, dan haka cike da zumuɗi Asma'u ta sake faɗin, “Wlhy Ammah da gaske nakeyi. Barrister Mawaddat Jiƙamshi ce matar Yaya, dama tun shekaran jiya nake ta mamaki dana ga kamanninsu yayi yawa duk da ban taɓa ganin waccan a zahiri ba sai a tv, sai banyi magana ba sai yau dana tabbatar”.
Wani irin abu ne mai sanyi ya shiga ratsa zuciyar Ammah ta shiga sake tsarkake sunan ALLAH maji roƙon bayinsa. Tun a randa ta fara ganin yarinyar nan ana hira da ita a gidan tv akan wani case data cimmawa na fyaɗe har yarinyar ta kamu da cuta mai karwa garkuwar jiki da wanda yay mata fyaɗen ya goga mata a ranta taji inama ace ɗiyarta ce ita, ko kuma Aliyu ya sameta a matsayin mata. A ranar tai addu'a da fatan idan hakan zai iya kasancewa kuma ya zama alkairi ALLAH ya tabbatar, idan kuma har matarsa ce. Amma da ga baya sai ta cire hakan a ranta sakamakon jin yarinyar ɗiyace ga babban hamshaƙin mai arziƙi nan Alhaji Isma'il Ibrahim Jiƙamshi. Ta cigaba da ƙaunarta kawai a ranta da mata fatan alkairi a rayuwa. Tuna wannan al'amari ya sakata jin ratsawar wannan al'amari mai sanyi har zuciyarta na harbawa da sauri-sauri, tabbas wannan shine ɗaya da ga cikin alkairan son mutum domin ALLAH, dan ita kam taso yarinyar nan domin ALLAH ne......


★★....

Tunda Mommy ta fara magana Uncle Yousuf ya zuba mata idanu kawai yana kallonta har sai da takai aya. Ta ƙare da faɗin, “Gaskiya Yousuf zuciyata ta fara raya min wani al'amari mai girma. Anya kuwa babu lauje cikin naɗi a wannan al'amarin. Kasan mu mata munada wani hali na rufewar ido a duk sanda muke son ganin buƙatarmu ta biya akan abinda muke so. Ka tuna randa marigayiya ta fara ganin Yaya kuna tare, kuma kaine da kanka ka sanar min tunda yay mata kallo ɗaya ya watsar da lamarinta har kuka baro gidan a wancan lokacin bai sake kulata ba”.
       “Tabbas anyi haka aunty Kareema, amma miya alaƙanta wannan abin kunyar da yake yi yanzu da wancan?”.
     “Ba zamuce sunada alaƙa ba, ba kuma zamuce basu da shi ba. Amma inaji a jikina wannan soyayyar mai zafi da yakema Mawaddat bata lafiya bace.”
          Murmushi Uncle Yousuf yay da gyara zamansa. Ya ce, “Aunty Kareema ban katseki ba ko ƙin fahimtarki anan, amma ina roƙonki karki sakama zuciyarki komai game da abinda Yaya keyi da tunanin wani. Lafiyarsa lau ya kuma san mi yake yi sarai. Akwai dai abinda yake ɓoyewa shiyyasa yake kaffa-kaffa da Mawaddat, dan ba wai tsantsar soyayyar bace ba kawai. Abu na biyu tausayin rasa mahaifiyarta tana laɓuɓuwa ma ya taka rawar gani a kansa. Kin san mu maza munada wani abu akan ƴaƴan mu musamman idan ya kasance mahaifiyar yaro bama tare da su, sai mu dinga jin wadda ke riƙe da su zata cuta musu ne kawai. Shiyyasa zakiga maza da yawa suna samun saɓani da matansu akan ƴaƴan da uwarsu ta fita a gida, kota rasu ta bari.”
        “To haka ɗinne kuma. Amma inaga ya kamata ace munsan abinda yake ɓoye manan ko hakan zaisa mu fahimcesa”.
     “Karki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login