Showing 141001 words to 144000 words out of 163036 words

Chapter 48 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

467

fa. Ke Mawaddat tashi ku wuce gida.”

Miƙewa Lulu tayi kamar yanda Smart ya miƙe babu alamar komai da zaka iya fahimta a fuskarsa. Sai ma kallon Baban yay cikin girmamawa yay masa sallama tare da sauran jama'ar ɗakin. Wasu sun amsa masa wasu ko nata faman taɓe baki ƙasa-ƙasa yanda Baba bazai gani ba. Koda yayma Dada sallama bata kulashi ba, shima kuma bai nuna ya damu ba yay ficewarsa. Suna fita cikin ƙarfin halin rashin jin daɗin jiki Baba ya balbale Dada da faɗa, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har sai da ta koma bashi hakuri duk da dai fa ta ciki na ciki.....

Lulu tata satar kallon Smart da tunanin zaice wani abu akan abinda Dadar ta masa amma har sukazo gida baida alamar cewa komai. Bayan ya sallami mai napep ya buɗe musu suka shiga, gaba ɗaya kayan na'a hannunsa har handbag ɗinta ma. Har ɗaki yakai mata kayan sannan ya fita zuwa nashi ya barta da binsa da kallo. Harga ALLAH bataji daɗin abinda Dada tai masa ba. Dan koba komai ita ai daga gidansu take. An kuma girmamata an mutuntata kamar a goyata. Kuma fa duk ta bama Dadan labari a taƙaice amma ta aikata masa hakan. ALLAH ya kaimu gobe zataje sai tai mata magana dan bata son haka. Duk da bata son shi bata kuma tunanin zama da shi bayan na wata ɗayan nan bazata so a wulaƙantashi ba dan itama dai da taje gidansu ba'a wulaƙantatan ba ai. Da wannan tunanin ta shiga wanka.

Shima a can wankan ya shiga, sai dai duk da ya danne abinda Dadan ta masa yay masa ciwo sosai. Sai dai ya zaɓi shanyewa dan koba komai taci darajar Baba. Sannan bazai taɓa wulaƙantata ba kasancewarta kaka ga Lulu. Bayan yay wankan ya fito shafa'i da wutri yayi sannan ya fito. Shayi ya haɗa a kofi biyu ya nufi ɗakin Lulu da su. Kwance ya sameta rigingine ta ƙurama fanka ido da alamun damuwa tattare da ita. Dan ko sallamar sa bataji ba sam. Zama yay a bakin gadon da yin gyaran murya sannan ta dawo firgigit, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da tashi zaune. Idanunsa ya janye daga kallon ta yana haɗiyar busashen yawun daya tokare maƙoshinsa dan shi yasan abinda idonsa ya gani kasancewar rigar jikinta ta barci ce mai santsi. Itama sai ta jawo ƴar saman rigar data ajiye gefe ta ɗora akan wadda ke jikinta dan ƙarama ce ma da kaɗan ta wuce mata cinya. Taji kunyar ganin nata a hakan amma dai ta basar. Shayin ya miƙa mata shima cikin basarwar, amsa tai idanunta a kansa, ganin babu dai damuwar da take tunanin gani ya sata jan ajiyar zuciya da faɗin, “Thanks.” kansa kawai ya ɗan jinjina mata. Numfashi ta sauke a hankali sai kuma ta sake dubansa da faɗin, “Kayi haƙuri da abinda Dada tayi, ni ban faɗa mata da wani manufa ba. Ita haka take tana da faɗa ne sosai”.

Murmushi yay a karo na farko, sai kuma ya ɗan kafeta da idanunsa da suka canja launi kaɗan. cikin tsokana ya ce, “Wajenta kika koyi faɗa kenan?“. Hararsa tayi da ɗan murguɗa baki. Ya sake sakin murmushi da kai shayinsa baki. “Karki damu ai nima kakatace. Ni ban ɗauki abinda tai ɗin komai ba. Yanzu ma magana nazo muyi”. Bai bata damar sake cewa komai ba akan Dadan ya shiga bata bayanan daya ɗan tattara mata game da case ɗin yarinyar can dake a asibiti, sai kawai ji yay ta rungumesa a bazata. Wani irin mahaukacin bugawa zuciyar Smart tayi, jinin jikinsa ya shiga yamutsawa tsigar jikinsa duk ta mimmiƙe. Lulu da bata kawo komai da wata manufa ba game da abinda tai ɗin ba ta ɗago tare da lakace masa hanci tana kallonsa da murmushi ta kashe masa ido ɗaya. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana mai lumshe idanunsa.

Komawa tai ta zauna da faɗin, “Ashe kana da kirki wani lokacin”. Shi dariya ma ta bashi, sai dai baice komai ba kan hakan ya sake yin murmushi kawai da ɗakko maganar fitarta aiki gobe idan ALLAH ya kaimu ko zai samu daidaiton abinda ke tsikarinsa. Nasiha ya fara mata cikin kwantar da kai da muryarsa data koma ƙasan maƙoshi, tare da faɗa mata dokokinsa akan yanda yake buƙatar ta dinga fita”. Da farko taso daurewa, sai dai jin dokar fita da hijjab har ƙasa ya sata dubansa cikin tura baki ta ce.

“Hijjab har ƙasa? Ni ce zan saka hijjab har ƙasa, impossible hakan ta kasance, idan mafarki kake ka farka. Wai miyasa kai baka so a zauna lafiya ga son nuna ma mutane gadara akan rayuwarsu? Ka mance wannan auren ba aure bane balle ka dinga tursasani yin abubuwan nan. To ni ko auren gaskiya ace nakeyi bazan zama a ƙarƙashin takalmin namiji ya takani ba, idan zamuyi rayuwa cikin kowa yanada freedom fine, balle wannan auren. Please ka bari kwanakin nan su cika muna masu mutunta juna. Ni harka ma ɓatamin rai na”.

Kallonta kawai yake yi batare daya fahimci mima take nufi ba, sai dai baice komai ba harta gama. (karku manta Smart bai san da tsarin auren yarjejeniya ba, Uncle Yousuf Daddy da Lulu kawai ya shuka a haka). Tashi tai ta bar masa wajen ta shige toilet dan bata buƙatar abinda zai ɓata mata farin cikin data samu yau a wajen ƴan uwansa, shima sai ya mike ya fita a ransa yana faɗin (akwai ƙura kenan kuwa gobe. Dan shikam wannan tsarinsa ne, ko yau ma ya barta ta fitane da gyalen dan kawai tare zasu fitan, ya kuma san daga gida sai gida kawai....

WASHE GARI ta tashi da ɗokin fita aikinta, musamman zancen shiga kotu da zasu fara yau akan case ɗin nan. Tsaf ta gama shirinta, sai uban ƙamshi take zubawa dan ta baza turaren nata. Tana ƙoƙarin ɗaura igiyar takalmanta ya shigo ɗakin. Sanye yake da jallabiya ash da bata kai masa har ƙasa ba sosai, sannan gajeren hannu ne da ita. A jikin ƙofar ya jingina tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu kawai. Ƙin ɗagowa tai duk da taji shigowar tasa har sai da ta kammala. Koda ta ɗago ɗin ma kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tana miƙewa. Da ga sama har ƙasa ya sake ƙare mata kallo. Yayinda ita kuma ta ƙarasa tattare kayanta ta nufo ƙofar kanta tsaye. Kallonsa tai kamar yanda shima yake kallon nata, a dake ta ce, “Ina kwana bani hanya”.

Maimakon amsa mata sai ya ɗan kauda idanun nasa a kanta ka ɗan batare da ya motsa ba ko ya tanka. Ta fahimci so yake su maimaita na waccan ranar, ita kuma ba haka take buƙata ba. Dan haka ta danne abinda ke taso mata da ɗan kwantar da murya ta ce, “Please Hydar 9:30 ne shiga court fa, kuma ka sani”.

Cikin husky voice ya ce, “Idan baƙyason rasa shari'ar ko makarar go and change your dresses. Na faɗa miki duk abinda bakina ya furta shine nake buƙata kuma bana canjawa da ga ra'ayina akan duk abinda na riga na tsara.”

Cikin ɓacin ran da ya fara yunƙuro mata ta ce, “Aliyu!!...”

Hannu ya ɗaga mata babu alamar wasa a tattare da shi. Muryarsa vary deep and vary clear ya ce, “Na yanke kuma na zartar, bi kawai shine masalaha Mawaddat. Ke matata ce, nace bana buƙata to bana buƙatar. Kiyi kawai kodan kuma ki sami yanda kike so mu kuma zauna lafiya”.

Jitai jiri ma na neman kamar ɗibarta. Amma sai batace komai ba tai masa wani irin kallo mai ƙunshe da abubuwa masu yawa ta juya kawai ta ajiye kayan hannunta a saman gadon. Komawa tai wadrobe ta ɗakko hijjab zata saka kawai, amma sai ta tsinkayi muryarsa yana faɗin, “Kayan duk zaki canja zuwa wasu, bana son wannan turaren kuma idan zaki fita, idan zaki saka a gida fine ko zakiyi wanka da shine ba babu damuwa a gareni. Sakawa a fita ne dai bana so dan haramunne ma a gareki ba faɗa ta bace.” bata tanka masa ba, sai kayan data ɗauka ta nufi toilet dan taga baida alamar fita, ita kuma taci alwashin bazata kulashi ba a yanzu saboda abinda ke a gabanta. Tsaf ta sake shiryawa cikin wasu kayan ta saka hijjab ɗin ta fito, sai ya samu kansa da kafeta da ido. Dan tayi ƙyau matuƙa a cikin hijjab ɗin fiye da waccan ranar. Shi da kansa ya ɗibar mata kayan yay gaba tabisa a baya tana taunar lips na danne masifar dake cimata zuciya. Baya ya ajiye mata kayan tare da miƙa mata hannu alamar ta bashi key ɗin motar dake hanunta.

Rai a ɓace ta ce, “Bana buƙata”.

“Kema kin san aikina ne ai hakan”. Ya faɗa babu wasa shima a tattare da shi. “Aina faɗa maka na kore ka”.

“Ban koru ba, dan bake kika ɗauke ni aiki ba ai ko”. Ya sake bata amsa a dake yana zare key ɗin tare da jan hanunta ya tura ta kujerar kusa da driver ya maida ya rufe. Zagayawa yay shima mazaunin drivern. Koda yaje gaban gate sai da ya fita ya buɗe sannan ya zo ya fita da motar ya sake komawa ya rufe gidan sannan. Tunda suka ɗauki hanya babu wanda ya tankama wani, gara shi ma ya miƙa mata ƙaramin flaks da ya haɗa mata tea a ciki. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa tana harararsa. Murmushi kawai yay batare da yace komai ba ya maida hankalinsa ga tuƙinsa. Kai tsaye office ya kaita, inda suka samu abokan aikinta suna tsaiwar jiranta duk da safiya ce sosai. Motar na shigowa suka shiga mata marhabun su Zainab na mata spry da ƙyalkyali mai ƙamshi da ga shi har ita. A take aka shiga musu murnar auren. Kamar yanda ya dake yana amsawa itama sai ta dake tana amsawa. Sunci kusan mintina goma a wajen kafin Zainab ta kwashi kayanta suka wuce office, shi kuma sai ya fito bayan sun ɗan yi magana da security ɗin nan da a yanzu suka saba sosai ya samu napep ya shiga ya koma gida.........✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣9️⃣



.......Alhamdullah yau Lulu zata ce kasancewar abubuwa sun tafi mata yanda take so. Dan duk da zaman shari'ar yau aka fara Alhmdllh tana hango nasara a cikinta. Bayan barin kotu da Hassan yazo ya kaita da kansa office ya sake maidata, ta ɗan taɓa aiki bayan sallar azhar ta fito. Tana jan mota ta fita Security ɗin nan ya dannama Smart waya ya sanar masa. Godiya yay masa sannan shima yay kiran wanda ya saka ya dinga bibiyar masa ita akan yabi bayanta da napep ɗin. Kai tsaye anguwar da mijin Hawwah yake ta nufa, da tambaya ta isa gidansu Sa'id. Mai Napep da ke binta ya kirasa ya sanar masa. Sosai Smart yay mamakin abinda ya kaita, har ya dinga jin son yazo amma dai ya dake da ƙyar dan son ganin iya gudun ruwanta. Sama-sama ta gaishe da maigadin tare da tambayarsa ko hajiyar gidan na nan? Amsa mata yay da eh cikin washe haƙora. Fuska ta yamutse cike da izzarta ta ce, “Sanar mata tana da baƙuwa”. Babu musu ya amsa mata da to yana nufar cikin gidan. Mintinan baifi uku ba sai gashi ya dawo ya ce ance ta shiga.

Kallon gidan ta dingayi side by side tana taɓe baki, a irin dukiya ta gidansu gidan su Sa'id ɗin ba komai bane ba, sai dai ba laifi suma dai da gani akwai kuɗin sai dai ko kama ƙafarsu basu isa yi ba. Ƙofar da take ƙyautata zaton falon gidan kenan ta nufa, cikin sa'a ma sai ta hango wata yarinya tsaye kamar tana kuka da alama mai aiki ce, isowarta kusa da ita ya sata daina kukan ta risina ta gaisheta. Sau ɗaya ta amsa mata ta ɗauke kanta. Yarinyar ce ta mata iso cikin falon, babbane sosai ya kumaji ɗirka-ɗirkan kujeru kamar bana dattijuwa ba. Kallo ɗaya taima matar dake zaune a falon ta fahimci itace mamar mijin Hawwah ɗin, dan ko'a ido ka kalleta kasan za'a zuba da ita kam. Zama tai kanta tsaye tun kan ma ace ta zauna, maman Sa'id dai kallonta take alamar rashin sani, duk da Lulu ta fahimci hakan sai ta basar, cikin ɗaukar kan nan nata na isa da ƙasaita ta ce, “Hajiya barka da rana. Sunana Barrister Mawaddat Isma'il Jiƙamshi.”

Sai da zuciyar maman Sa'id ta motsa jin ƴar waye, sannan sunan kansa na Mawaddat ɗin duk mai bibiyar harkokin mata a fanin fyaɗe dole zai santa, ita kanta dama tunanin ina tasan wannan fuskar takeyi. Lulu data lura da hakan ta cigaba da faɗin, “A yanzu haka matar Aliyu M. Idris Mawashi yayan matar ɗanki dan bana tunanin kin halarci bikin sati ɗaya daya shige”.

Gaba ɗaya Mama duk sai ma taji ta daburce, dan tabbas Sa'id yata roƙarta zuwa bikin amma tace bazataje ba dan ba'a gayyaceta ba, koma an gayyacetan bazataje bikin matsiyata ba dan tasan dai bai wuce tuwo da waina da zoɓo ba. Harga ALLAH bata san ɗiyar wa Aliyun ya aura ba. Da ɗan jimami ta ce, “Da gaske kece matar Aliyun?”.

Lulu dake mata wani kallo a yamutse ta amsa da, “Oh baki yarda bane? Zaki iya tambayar ɗanki ni yanzu ba wannan ne ya kawoni ba. Nazo nan ne game da case ɗinki da Hawwah, kinyi ƙoƙarin zuba mata mai dake saman wuta da nufin ƙonata, ba kuma wannan ne karo na farko ba da hakan ta faru. Kinci arziƙin ɗanki shiyyasa banzo da police ba a yanzu haka domin kamaki. Amma nazo da kalaman gargaɗi a gareki a karo na farko. Su iyayenta sun barki saboda jin nauyin karamcin ɗanki. To ni kuma a matsayina na mai kare hakkin mata kuma matar Yayanta bazan iya barinki ba. Kin haifi Sa'id ba kin haliccesa bane, yana kuma da damar yin aure tunda bake zaki auresa bane, matsayinki daban matsayin uwa matsayin matarsa daban matsayin mata. Nan gidan aurenki ne, shi kuma nan gidan da aka haifesa ne, kina zaune da mijinki lafiya dan haka itama ki barta ta zauna da nata mijin lafiya. Wannan takardar da kike gani na tattara dukan abubuwan da kikai mata ne, tare da bincike mai yawa akanki a wajen ƴan anguwa da ƴan uwanki dana mijinki, kuma sun bani duk wani information a kanki har ma wanda bakiyi zato ba. Haka ma mijinki nayi waya da shi yanzu haka, dan haka kina da zaɓi biyu zaki saka hannu zan saka hannu Sa'id zai saka hannu hakama Hawwah da sharaɗin zaki fita rayuwar aurensu ki zauna a matsayinki na mahaifiyarsa, zakuma subar wannan gidan su koma nasu, sannan kije da kanki gidansu ki bata haƙuri ki bama iyayenta haƙuri. Zaɓi na biyu ƙin amincewa da shawarar farko na shigar da wannan case ɗin kotu mu zuba shari'a wlhy har sai na kaiki jail dan har video ke gareni na randa kika kusa kasheta a dalilin hankaɗota daga saman upstairs gashi”. Ta ɗaga mata wayar tana mai playing video ɗin, jikin maman Sa'id ya fara rawa, Lulu ta sake shiga wani ta ce, “Ga kuma na randa kika watsa mata ruwan shayi harta ƙone a wuya shima”. Sosai Lulu taga ruɗewa a idanun Mama. Tai murmushi da kaɗa kanta cike da isa. “Ba waɗannan kawai ne ba, akwai wasu tari-tari kuma duk Hawwahn ke ajiyesu, bata nuna bane saboda mutuncin ɗanki. Amma ni yanzu na shirya fiddosu a gaban alƙali. Kin san dai mijinki siyasa yake yi har yana shirin fitowa takara a shekara mai zuwa ko, sannan yayanki a yanzu haka ɗan majalissa ne, to a dalilinki duk zan iya tarwatsa wannan damammakin, dan bayan kasancewa jinin Jiƙamshi jinin Alhaji Sufi Ado Garko nake kuma. Sai ki zaɓa na baki nan da kwanaki uku kacal. Na barki lafiya”. Ta faɗa tana miƙewa murmushi ɗauke da fuskarta ta ɗaga mata yatsu biyu tai ficewarta. Sosai jikin maman Sa'id ke rawa da kakkarwa. Dan kuwa Lulu ta daketa ne a inda taji zafi sosai. Videos ɗin nan sun matuƙar tayar mata da hankali, har tana mamakin yaushe Hawwah duk ta ɗaukesu batare da ita ta sani ba. Na biyu matsayin Lulu da hatsabibancinta akan shari'ar duk da ta saka a gaba. Na uku zancen siyasar mijinta da tai matuƙar ƙwallafama rai da buri a yanzu tare da matsayin ɗan uwanta da shima take taƙama da tinƙaho da shi a duk inda ta shiga. Idan wannan damar duk ta kufce musu ai ta shiga uku wlhy, dan za'a mata dariya matuƙa. Itafa dama kishiyar uwar yarinyar nan ce ke sake tunzurata akan tsanarta (Umma), duk da dai dama bata sonta kasancewarta ƴar talakawa, dan taso ace Sa'id yay auren kece raini ne na ƙwarya tabi ƙwarya. Amma ya ƙare da auren ƴar malam shehu......

Lulu data fita da ƙayataccen murmushi a fuska ta shige motar tare da yin reverse tabar angur da gudu dan ita kam akwai wauta da mota. Mai Napep ɗin nan dai na biye da ita. Ganin sun ɗauki hanyar Nasara G.R.A yasa shi kiran Smart ya sanar masa. Koda suka iso gidan na Garko daka ɗan nesa ya tsaya, yayinda ita aka buɗe mata gate ta shige ciki. Yau ma da mutane a gidan, sai dai kusan duk matan kawunan ta ne, suma ɗin dai wanda basa fita aiki ne. Ta samu Baba na barci saboda allura da akai masa, hakan ya bama Dada dake cika na batsewa wa matan ƴaƴan nata jan Lulu suka shige ƙuryar ɗaki. Dan fa ita tun jiya ranta a ɓace yake da batun zuwansu a napep. Balbale lulun tai da masifa, ita kuma ta tsaya tana kallonta da mamaki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login