Showing 93001 words to 96000 words out of 163036 words
ne Ammah ke masa bayanin shawarar da ta yanke akan inda zasu zauna. Sun gama shawara da ƙanwarta Sa'adah zasuyi magana da Abba a gyara masa gidan da suka gada kasancewar su biyu ne dama ke da shi ta ɓangarensu dan suma sunada ƴan uba. Sai yay zamansa, za'a tashi ƴan hayar gidan.
“A'a Ammah kar ayi haka. In dama ace babu kowa a gidan ne, amma bazan so saboda ni a tashi mutanen da ke a gida tsahon shekaru ba kuma a ƙurarren lokaci irin wannan. Kudai bani lokaci ina kan nazari in sha ALLAHU za'a sami mafita. Dan dama zance kodai a musu magana su kai tarewan zuwa sati biyu haka ko wata ɗaya”.
Ammah ce ta katsesa da faɗin, “A'a Hydar kar ai haka. Tunda mutanen nan sukace sati ɗayan kawai mu amsa ayi a wuce wajen. ALLAH shine zai rufama kowa asiri. Dan kaga dai a ɓangaren lefe Alhmdllh matsalarsa kamar ta ƙare zance. Ga dai Hawwah nan da Bilkisu zasu shiga kasuwa da kuɗin da ke hannunsu tun da sunyi alƙawarin dai sune zasu haɗa lefen nan. Ko a yanzu ma suturar da suka tara ɗin fa tafi arba'in tunda kowa na saye ta ɓangarensa. Gashi Alhamdullah duk manya ne kamar sun san inda auren naka zai faɗa dama. Kaga yanzu kam kokawarmu ai ta wajen da za'a zauna ne kawai sai kuma kai ɗan ɗinkunan da zakai amfani da shi na angwanci”.
“Kai Ammah ni sai nayi wani sabon ɗinki?”.
Hararar sa ta ɗan yi da faɗin, “Oh da haka kake son shiga angwancin. Haba Babangida, ai lokacin abu ayisa kaji. Kasan kuwa a irin farin cikin da nake ciki tsakanin jiya da yau. Ko auren su Maryam bai damuna kamar yanda zamanka babu mace ke cimun rai. Na gaji da jin gori da habaici akan zaman nan naka babu mace har ma da sheri. Amma Alhamdullah ga iyaka ALLAH ya kawo a gaɓar da bamuyi zato ba sai kuma muƙi nuna godiyarmu garesa.”
“Hakane Ammah. Amma ai inata sakaku wahala. Sam ba haka naso al'amarin nan yazo ba. Ban so ɗaura nauyin aurena a kanku ba, domin nine ya kamata nai muku hidima bawai ku kucigaba da min ba bayan tun ina ciki kuke min har zuwa yau ɗin nan”. Yanda yake maganar cikin damuwa ya sa Ammah sakin murmushi da miƙewa tana faɗin, “Shi komai lokaci ne da shi. Haƙuri akan jarabawa kuma cikar kamala da imanin ɗan Adam ne. Idan aka cigaba da jurewa duk komai zai cigaba da zama labari tamkar bai faru ba, ko a yanda auren nan ma yazo ai babbar aya ce. Fatana ni dai ka kasance da iyalinka fiye da yanda nake zatonka da tsammani. Ka kuma riƙe mutuncinka dan kar zuciyarka ta ɗora maka cewar dan su masu shi ne shikenan zaka zauna su zame maka rijiyar tatsar abin duniya. Babu ruwanka da dukiyarsu ka tashi ka nema na kanka ka ciyar da ƴarsu ka tufatar da ita da kare mata dukkan wani hakkinta da ke a kanka. Kar ka yarda ka bada wata ƙofa ta amsa da ga garesu da sunan wai kana auren ƴarsu. Duk da dai bana kokwanto a kanka Aliyu. Ina dai sake tunatar da kai ne dan dukiya shu'umar abuce mai shiga rai da jinin ɗan adam harma da ɓargo.”
Sosai nasihar mahaifiyar tasa ke ratsashi matuƙa. Tana ƙara masa ƙwarin gwiwa akan nasa ra'ayin kuma da ƙyakykyawar manufa.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣2️⃣
......Shirye-shiryen biki kam ya kankama ta kowanne ɓangare. Yayinda shima Abba ya goce batun tada mutane da ga gidan su Ammah a gyarama Smart. Yana ganin hakan zai zama su kuma an cuta musu. Gara dai kawai a kama masa haya na shekara biyu idan zai samu kafin aga abinda ALLAH zaiyi kuma. Ana cikin wannan lissafi sai ga Coach ɗin su Abdull-Hameed yazo da batun Smart ya amsa gidansa da ke anguwar sharaɗa ya zauna har sanda ALLAH zai hore masa nasa. A cewarsa wannan itace tasa gudummawar. Da farko dai Smart ƙin yarda yay, sai dai ya kafe akan zai biya kuɗin hayar gidan, sai da Coach ya nuna masa ɓacin ransa akai sosai harda faɗin ashe shine keta haukansa Smart ɗin bai ɗaukesa matsayin Yaya kamar yanda shi yake masa kallon ƙaninsa Ahmad ba, yay fushi zai tafiyarsa sai da ƙyar Smart ya bashi haƙuri ya tsaya suka tattauna. Da ga ƙarshe dai Abba ya ce an amshi gidan sukai godiya da sanyama Coach ɗin albarka dan ya jima yana ɗawainiya da Smart. Duk wani matakin nasara akan ball shine riƙe da hannun Smart ɗin. Dan tunda ya ga iya ƙwallo na Smart a wani wasan sada zumunta na makaranta da sukai sannan Smart na ss1 ya jashi jikinsa, tun ma suna ɗar-ɗar har suka saki jiki da juna ganin kowanne nada zuciya mai ƙyau. Kusan family ɗin su Ahmad sun san Smart sosai, haka suma family ɗin Smart sun san waye Ahmad da Abdull-Hameed a rayuwar Smart. Babu hanyar da Umma batabi na son ganin ta rabasu ba amma hakan ya gagareta shiyyasa ta tsani Coach matuƙa. Akwai lokacin da har sharri tai masu wai Coach kodai yana ɗabi'ar banza da Smart ne. Sai da Abba ya nuna mata asalin haukarsa a lokacin dan har saki ɗaya yay mata sannan ta dawo hankalinta tana bada haƙuri, da ga nan bata sake maimaitawa ba kuwa.
Smart yaje ya ga gida tare da Ahmad. Gidane madaidaici zaman mace ɗaya flat. Bedrooms uku biyu manya ɗaya ƙarami kowanne da toilet sai falo babba tare da dining, sai kitchen da store. Harabar gidan zai iya cin mota biyu zuwa uku. Ga flowers an zagaye ko'ina da suka ƙara ƙawatashi. Sabon fenti da gyare-gyare duk an masa, dan ana dawowa da ga ɗaurin auren Smart Coach ɗin ya nema masu aikin gidan aka fara. Dama ƴan hayane suka fita kusan watanni huɗu kenan kasancewar ALLAH ya hore musu suma sun gina nasu, shi kuma sai bai sake saka kowa ba a ciki ya ɗan fara masa gyara sai kuma ya watsar ya rufesa kawai. Sai da idanun Smart ya ciko da ƙwalla, dan a rayuwa yakan rasa mizai ma Coach ya iya kwatanta alkairan da yay masa ne koma yake a kan masa, ya jima yana ɗawainiya da shi kashi-kashi da shi kansa bai san adadi ba.
Bayan sun dawo suma su Aunty Bilkisu sukaje suka gano, Abba kuma da Ammah sai washe gari ya kaisu suma. Su Umma dai basu san hidimar da ake ba, summa koma gefe sun zuba ido suga wai yaya wasan zai ƙare ne. Dan ta aiwatar da ƴan abubuwan da malam Na-zuru ya bata yanzu jiran ranar tarewar amarya kawai take ta samu kayan da aka kawota da su da wanda Smart zai saka shima. Alhmdllh lefe ma ya haɗu tsaf, dan bayan ƙoƙarin su Hawwah suma dangin Ammah sun taka rawar gani, dama su mutanene masu haɗin kai matuƙa. Gashi kuma yanzu ne Ammah zata aurar da ɗa namiji kuma shi kaɗai tilo gareta. Hankalin su Umma da ya ɗan fara tashi ganin gudunmawar da keta shigowa mai jijjiga zukata da ga ƴan uwa da abokan arziƙi, dan ko kuɗi Smart ya samesu ba laifi. Ana saura kwanaki uku ya amsa kiran su Uncle Yousuf, dan rabonsa da gidan fa tun kafin a ɗaura aurensa da gimbiya. Aiki bai sake zuwa ba, dan itama dai Lulun Uncle Yousuf ya dakatar da ita fitar bisa wayon Aunty Saliha da ta ɗakko mai mata gyara tun daga Sudan da Marocco. Da farko tayi butsutsun nata na bata so Uncle Yousuf ya zauna ya tsarata tsaf a kwali dole tabi. Suma dai shirye-shirye suke na bikin ƴar gata, musamman ma Uncle Yousuf da Baba da Mommy da Aunty Saliha. Ya samu tarba ta muntunawa ga Mommy matsayin suriki garesu a yanzu. Duk da dama dai ita kam bata taɓa wulaƙantashi ba. Shima ya gaishesu cikin mutuntawa da girmamawa kamar yanda ya saba. Da ga haka suka fara tattauna abinda ya tarasu. Shiru yay yana sauraren Daddy da ke masa bayani akan takardun hannunsa. Ɗaya na gida da ya bashi halak malam ƙaton gaske anan cikin anguwar hotoro G.R.A ɗin upstairs ma, sai key na mota da takardunta itama sabuwa fil a ledarta, da zunzurutun kuɗi har naira miliyan ashirin, ya kuma zaɓi duk aikin da yake so ya nema masa. Tunda Daddy ya fara murmushi kawai Smart yake yi amma baice komai ba. Shima dai Uncle Yousuf da Mommy basu ce komai ba dama.
A hankali Smart ya girgiza ma Daddy da ke miƙo masa takardun da key ɗin motar kai. Cikin tausasa harshe da girmamawa ya ce, “Daddy kayi haƙuri bazan amsa komai da ga gareku ba ni. Na auri Mawaddat ne domin ALLAH da bautarsa. Na kuma muku alƙawarin riƙeta in sha ALLAHU da abinda ALLAH ya azurtani da shi, bazaku taɓa dana sani da ni ba. A yanzu haka inada inda zan ajiyeta, batun neman aiki kuma insha ALLAH shima zan nema abinyi da kaina, hakan zai fi ƙaramin himma da sanin muhimmancin abinda na samu ɗin. Idan nayi ba dai-dai ba a gafarceni dan ALLAH”.
Tsittt falon yay tamkar ruwa ya cinye kowa. Bakaji komai sai sautin ƙarar ac da ke aiki. Murmushi sosai Mommy da Uncle Yousuf keyi ƙasa-ƙasa. Yayinda Daddy yay wani sansarakwai da shi yana kallon Smart cike da mamaki da al'ajab. Kaba mutum irin wannan dukiyar amma ya nuna maka bai buƙata, matashin saurayi kuma da ayanzu yake fafutukar gina rayuwarsa. Da ƙyar ya iya jan numfashi har sannan idanun nasa dai akan Smart. Ya ce, “Aliyu ban baka wannan abubuwan ba dan wataran ka maido min da madadinsu. Na baka ne saboda kaima yanzu matsayin ɗa kake amsawa a garemu, fatanmu kawai ka riƙe mana Mawaddat cikin aminci da amana”.
“In sha ALLAHU Daddy zan cika alkawarin riƙeta, koba komai nima inada ƴan uwa mata, bazan so na tsinci rayuwarsu cikin aƙubar zaman aure ba. Zanyi iya ƙoƙarina kamar yanda MANZON ALLAH (S. A.W) ya koyar da mu murayu a gidajen auren mu”.
Magana Daddy ya ƙara yunƙurowa zai yi cikin ɗan jin haushi-haushi, amma sai Uncle Yousuf yay saurin taresa yana girgiza masa kai da faɗin, “Shike nan Aliyu mun gode da wannan karamcin naka. Dama mu ai hakan muke son ji da ga gareka. Zamu cigaba da muku fatan alkairi dana zama lafiya. ALLAH ya baku ikon sauke hakkin juna. Ga waɗan nan katunan Baba ya ce a baka. Sai dai yace a faɗa maka kayi haƙuri baiyi shawara da kai ba wajen haɗa wannan dinner, yaso yin hakan sai uziri mai girma ya taso masa dan yanzu haka ma yana Abuja. Muma a madadinsa muna sake neman afuwarka da roƙon kayi haƙuri ya haɗa dinner ɗin ne sakamakon yanda ɗaurin auren ya kasance ga kuma mutane da yawa ya cancanci suzo”.
Ɗan murmushi kawai Smart yayi, duk da harga ALLAH shi a tsarinsa babu batun waɗan nan bidi'oin, amma yana jin nauyin Baba da Uncle Yousuf ɗin. Dan haka ya amsa katunan yace ba komai abin ƴan awoyine ai. Da ga haka yay musu sallama ya wuce da sanar musu baƙi na zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Daddy dai bai tanka ba, hasalima ransa a ɓace yake. Taya zai haifi yarinya, ya raineta tsawon shekara ashirin da huɗu. Rana ɗaya tak wani ya nuna masa iko akan al'amuranta. Idan bai amshi waɗan nan abubuwan daya bashi ba taya zai riƙe masa yarinya da daraja kamarr yanda ya raini abarsa. Sosai Mommy ta fahimci yanda Daddy ke cika da batsewa, dan haka ta miƙe tana cema Uncle Yousuf bari taje tai waya da su Hajiya Aysha da su Aunty Saliha suzo a tsara abinda za'a tarbi baƙin da Smart ɗin ya ce zasu zo gobe. Cikin murmushi da barkwanci Uncle Yousuf ya ce, “Umm bafa sabun ba zamu aurar da ƴar farko a gida”. Dariya ta fita tanayi. Shima yana tasa. Tana gama ficewa Daddy ya miƙe a zafafe.
“Kai Yousuf bazai yiwu ba. Shiyyasa tun farko nace maka yaron nan zai iya bamu matsala dan na fahimci gadararre ne shi mai girman kai. Taya zan bashi abinda zai inganta rayuwarsa da ma ta duk zuri'arsa darajar ƴata zata shiga cikinsu amma ya nunamin shi yafi ƙarfin hakan bayan baida komai. To gaskiya ayi komai a rubuce wata ɗayan daka ambata ya sakamin yarinya ta kawai......” Haka ya cigaba da zazzaga masifa ko haɗiyar yawu bayayi. Shi dai Uncle Yousuf na zaune kawai yana kallonsa har yayi ya gama. Baice komai ba, sai ma ya tashi tsam ya fice a falon yay tafiyarsa ya bar Daddy da sakin baki yana kallonsa.........✍️
(Uncle You kaima fa ɗan manni ne wlhy🤣).
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣3️⃣
.......A ɓangaren Smart sosai abinda ya farun ya dinga cimasa rai. Amma haka ya danne bai sanarma kowa ba yama kashe wayarsa dan kar wani tsakanin su Daddy yace zai sake kiransa akan batun. Bayan ya koma gida ya shiga ciki gaida Ammah su Hawwah suka buɗe masa lefe ya gani. Set guda na akwati mai biyar, sai ƙwara biyu daban da Abba ya saya da kaya a ciki suma matsayin kayan sa rana. Kaya kam sunyi sai dai maƙiyi, ga shi kuma duk manyan atamfofi da lasses hakama shaddoji da dogayen riguna dai-dai ƙarfin mai rufin asiri dai. Sosai Aunty Bilkisu da Hawwah suka taka rawar gani, dama sunyi alƙawarin duk randa ɗan uwan nasu tilo ɗaya ya tashi yin aure sai sun nuna bajintar da zata girgiza jama'ar gidan nasu kowa ya tabbatar da shi ɗan gata ne. Aiko sun girgiza ɗin, dan ko gidan su ya girgiza matuƙa da ganin wannan lefe da ba'a taɓa tunanin gani ba, sai su Umma suka shiga yada habaicin wai sai dai in iyayen yarinyar ne suka haɗa lefen, da ga Ammah har ƴaƴanta babu wanda yay ko tari har sukaci suka tsire. Gyalillan ciki kaf ya kwashe yabar guda uku, da mamaki su Aunty Bilkisu ke kallonsa, duk da ya lura da hakan baice komai ba ya dubi Maryam ya ce, “Bani saƙon dana baki ajiya”. Tashi tai tana murmushi ta shiga bedroom ɗinsu. Babu jimawa ta dawo da leda babba ta miƙa masa. Amsa yay ya miƙama aunty Bilkisu da faɗin, “Ku saka waɗan nan a kayan, wannan kubarta har sai tazo na bata da kaina. Aunty Bilkisu zatayi magana Ammah ta katseta da faɗin, “Kumasa yanda yake so ɗin kawai tunda baku san dalilinsa ba”. Su masu biyayyane ga umarnin mahaifiyarsu, dan haka babu wanda ya sake magana aka loda hijjabai da suka sha guga har guda goma ciff cikin akwati....
Washe gari alhamis aka kai lefe, ba wani gayya akai ba. Umma ne da Aunty Amarya, sai Aunty Bilkisu da Inna Mariya. Da wata gwaggon su mai suna Jamila. Sai matan maƙwaftansu su biyu. Ahmad ne ya kaisu da motarsa, sunko samu tarba irin wadda basuyi zato ba. Dan su Mommy da su Aunty Saliha sun nuna karamci mai ban mamaki. Ga gida cike masha ALLAH iyalan gidan Baba suma sun zazzo. Sosai suma kansu su Mommyn sukasha mamakin wannan lefe, dan gaskiya basuyi zato ko tsammani ba. Abu a cikin kwana shida haka. Kai da mamaki. Ga kaya babu na kushewa sai san barka. Harda kuɗin ɗinki, sai dai basu amshi kuɗin ɗinkin ba dai. Su Umma fa sun girgiza matuƙa, dan ganin gidan su Lulun ya ƙara tayar musu da hankali da sake tabbatarwa eh lallai Smart ya shiga inda akafi ƙarfinsa, dan yanda mutanen keda wannan irin dukiya sai dai idan asiri ne yay tasiri, yo inba asiri ba ƴar data tashi a wannan gidan ce zata auri ɗan talakawa kamar Smart. Ammah dai tasan tsiyar data yi ɗan nata ya auri yarinyar nan. Duk wannan abu dake faruwa amarya bata sani ba, tana gidan Aunty Saliha data turketa ana mata gyaran jiki na fitar hankali. Dan ta ƙara wani irin fresh da ita, damuwarta ɗaya kayan shaye-shayen ta da bata samu. Dan a jiya har kuka tayi ita kaɗai a bayi saboda buƙatar son sha da takeyi amma babu dama. Tsoffin nan da aka kawo mata sunbi sun tare ko'ina basa barinta ko motsin kirki. Gasu da ihu da tace zata musu gardama suke rufeta da kwakwazo dole take zama suyi yanda suke so da ita. Sai dai ita kanta tasan ta canja. Dan fatan ta ko daga nesa ka hangota kasan ta ƙara karɓar sunnonin gyara. Ga wani almurin ƙamshi mai ratsa zuciyar mai shaƙa. Ita kanta ƙamshin ne ma ke tafiya da imanin ta shiyyasa wani lokacin take ragama tsoffin ta haƙura su zauna.
Bayan wucewar ƴan kawo lefe da aka cika da sha tara ta arziƙi suma su Aunty Saliha suka nufi gidan da za'a kai Mawaddat ɗin domin raka Company da Uncle Yousuf ya bama kwangilar shirya mata kaya. Su kansu gidan ya birgesu yanda yake cif-cif abinsa. Duk da nasu ya ninka shi sau biyar girma da ƙyau, shima wannan ɗin nada nashi kalar sirrin ƙyau ɗin da yanayin