Showing 144001 words to 147000 words out of 163036 words

Chapter 49 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

471

sai da takai inda take so har tai shiru sannan Lulu ta taɓe baki. “To wai ni kuwa Dada dan ALLAH miye na damuwa anan, shiga napep ɗin shi minene a cikinsa. Kinbi kin saka ma kanki damuwa”.

“Ya bazan sakama kaina damuwa ba Mawaddat. Kamarki ace kina hawa Napep. To ai ko uwarki datai irin wannan ƙaddararren auren naki bai kai naki watsewa da lalacewa ba. Shi wai cikakken ɗan iska ma, an bashi abinda zai riƙeki har yace baya buƙata. Ke anya kuwa yaron nan ba asiri yay miki ba kuwa?”.

Dariya Lulu ta kwashe da shi a karo na farko, ta ce, “Ho Dada tamu, Aliyun ne zai min asiri. To wlhy bara na faɗa miki ma shi ustazu ne. Dama cakikai girman kai ya hanashi amsa sai na yarda. Amma ba asiri ba. Yo ni koma asirin ne ina ruwana ma, iyakaci lokaci na cika zan ƙara gaba babu abinda asirinsa zaimun ballema ni nasan ba asirin bane. Kuma nidai ki daina zagar min miji dan nima ƴan uwansa basu zagan ba sai ma girmamani da mutuntani da nuna min soyayya sukeyi”.

Dada data saki baki tana kallonta ta ce, “Iyyeee a lallai Mawaddat kinyi baki, harni kike gayama wannan zantukan. To inba asiri ba ubanmi zai kaiki auren yaron dake matsayin driver ɗinki. Ko ƙyan nasa ne ya ruɗeki da waɗan nan shegun idanun nasa kamar na ƴan maye. Dubeki fa wai kece da saka hijjabi yau kamar wata tsohuwa. Yo koni dana haifi uwarki na ninkaki shekaru bazan saka wannan abun har ƙasa na fita ba”.

Baki Lulu ta taɓe tana miƙawa, “Dada bazaki gane ba ke dai. Ya kike so nayi? ya rantse in ban saka ba bazan fito ba gashi inada shari'a mai muhimmanci. Wlhy taurin kan Aliyun nan ya wuce duk yanda kike tsammani. Bar ganinsa yana wani sissine kan nan shegen kansa ne.”

“A to lallai na sake yarda yaron nan asiri yay miki wlhy, ke yanzu duk yanda na sankin nan da rashin ɗaukar raini har kece taurin kan wani ɗa namiji zai girgiza ki ko ya baki tsoro da saki laushi haka a cikin sati ɗaya kacal. Dolene na miƙe tsaye dan wlhy koma miza'ai sai na rabaki da shegen yaron nan dan baza'a sake maimaita abinda ya faru akan uwarki ba. ALLAH dai yasa baki miƙa masa kanki ba ya lalube shegen”.

Dariya Lulu tai harda kwanciya, sai kuma ta ɗago cikin dariyar dai ta ce, “Ke kam Dada inda ace a zamanin baya kikazo irinku ne bakwa musulinta da wuri ga riƙe gaba har ƙarshen numfashi. Indai aurena ne ki kwantar da hankalinki bamai daɗewa bane, sati biyu ya rage ana uku na koma free. Sannan kina damuna da habaici akan Daddy na da Mamana, idan na tambayeki kuma kiƙi faɗa min, kin kuma hana kowa gayamin. Mi Daddyna yay miki ne kike jin haushinsa haka, idan dan yaƙi baki riƙona ne ba gashi yanzu na dawo kina ganina ba”.

“Ke ni ƙyaleni shashasha ba ganewa zakiyi ba. Ni ina tambayarki wani abu ya shiga tsakaninku ne? Sannan kince nanda sati biyu, kin fa sani a duhu”.........✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣0️⃣

 

........Shiru kamar Lulu bazatace komai ba, sai kuma taɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa. Cikin rashin damuwa da kallon abinda zatayi ɗin a wani abu ta kwashe komai dangane da auren contract da Uncle Yousuf ya sanar mata saboda kar Baba yay mata auren dole ta sanarma Dada. Ta kuma faɗa mata ita babu abinda Aliyu yama taɓa nuna yana so a gareta, shiyyasa ma take ɗan ganin girmansa”.

Salati Dada keyi a zuciya tana tsinema Uncle Yousuf, wato sunyi hakanne dan kar Lulu ta auri jikanta dake gadon asibiti. To lallai idan sun san wata ai basu san wataba kuwa. A zahiri kam bata nunama Lulu komai ba, tunda dama dai bugar cikinta take. Abinka da tsohuwar mace gashi taji abinda batai zato ba, Lulu kuwa har yanzu yarinya ce fa, dan ma ALLAH ya bata ilimi da kaifin basira, sannan ga yanayin rainon data tashi irin waɗan nan makirce-makircen na tsoffin matan ƙasar hausa ba gane kansu take ba. Sun cigaba da hira da Dada data ajiye maganar Smart har sai da Baba ya farka suka fito, Lulu taje ta dubashi. Ta jima a wajensa kafin ta tafi dan tana son komawa office. Mai Napep ɗin nan da yay zaman jiranta dan Uncle Yousuf ya bashi napep ɗin ne domin kawai bibiyar Lulun. Smart ya kirashi har sau biyu amma yana sanar masa tana a ciki bata fito ba. Da ta fito kuma yay kiransa ya gaya masa. Hakama da suka koma office. Ta sake zaman kusan awa biyu a office kafin ta fito Zainab biye da ita d kayayyakinta. Bayan ta saka mata ta sanar da ita gobe ta fito da wuri dan akwai wasu baƙin da take saran zasu zo nemanta. Da girmamawa Zainab ɗin ta amsa mata, ita kuma ta shiga mota sai gida. Sai dai ta tsaya wajen wani mai bread ta saya. Koda mai napep ya sanarma Smart bai kawo komai a ransa ba game da sayen bread.

(Ni dai nace Humm lulun mu fa ta wuce da saninka Smarty 😂😜).

★★★......

Tun shigowarsu cikin Saloon ɗin nata tai kamar wadda ta suma. Ba ita kaɗai ba hatta matan dake wajen ana musu ayyuka mabanbanta kallon mamaki suke musu dan kowa dai yasan anan mata kawai akema aiki banda maza. MM Atik Kumo ya katsema Nadiya tunani da faɗin, “Hello girl”.

Nannauyan nufashi ta kawo da dubansa, cikin ƙarfin hali da in ina ta ce, “Ranka ya daɗe lafiya dai?”.

“Ita ta kawomu. Ko zamu iya ganinki a waje?”. Asim ya bata amsa kai tsaye. Ƴan shagon ta duba, ganin duk sun zuba musu idanu yasata cewa, “Okay muje”. Su suka fara fita sannan tabi bayansu tana jan ƙaramin tsaki da gargaɗar yaranta su cigaba da ayyukan gabansu. A cikin motar su ta samesu, MM Atik dake zaune mazaunin driver yay mata nuni da ta shiga ciki itama. Batai musu ba ya buɗe ta shiga, bayan ta rufe ta gaishesu. Asim ne kawai ya amsa mata MM Atik kam tambaya ya jeho mata na cewar “Yaya ƙawarki?”

Numfashi ta ɗan furzar da gimtse fuska, a taƙaice ta ce, “Ban san yaya take ba dan bama tare yanzu. Tun a waccan ranar bamu sake kasancewa tare ba”.

“Saboda mi?”.

Cewar MM Atik ɗin yana jiyowa gaba ɗayansa gareta. “Hummm saboda naje da su Alhaji Baita wannan get together ɗin fa. Kasan na faɗa maka Lulu ta tsani maza, shiyyasa nake kallon kamar aljani ya aureta ne shiyyasa. Yanzu haka ma zancen bikinta sai gani nai an ɗaura mata aure wai da driver ɗin nan nata a tv, hakama dinner ɗin ta gani kawai nayi ana nunawa duk da kuwa na bata haƙuri ta waya da duk hanyar data dace amma taƙi saurarena”.

Murmushi MM Atik yayi damin hango irin ruwan bala'in datai masa a randa ya fara ganinta. Nadiyar ya kalla da faɗin, “Ai masifa bata mata wahala. Bar batun auren driver dan kuwa muna ganin da manufa tayisa, sakamakon son gujema auren Hon. Nakowa da wannan ɗan uwan nata Tajuddeen Sulaiman Garko. Ba ita kawai ba nima naji haushin ganinku da tsoffin nan a wancan ranar, kawai dai na miki shiru ne”. Shiru Nadiya batace komai ba akan hakan, shima sai ya cigaba da faɗin, “Manta abinda ya faru ya faru ya wuce, yanzu sabon dil nake son mu ƙulla”.

“Nami kuma kenan?”.

“Akan ƙawar taki dai, dan bazan iya haƙura ba.”

“Abu mai wahala kenan, dan ta yanke alaƙarmu, tare da gargaɗin nisantar ta. Nasan halinta kuma sarai idan ta faɗi abu har cikin ranta ne. Abu ne mai matuƙar wahala Lulu ta sake kallona balle har na shiga jikinta”.

“Zamu iya amfani da wata ai, amma ya zama ke zakina controlling nata”. Cewar Asim.

Kai Nadiya ta jinjina da faɗin, “Wai babbar magana. Na fahimci bakusan wacece Lulu ba. Kubar ganinta haka batajin magana tasan mitakeyi. Sannan koni kaina nasha wahala kafin mu fara abota gaskiya, dan bata da saurin sakewa da mutane, sannan ba kowa ke iya haƙuri da halin Lulu ba”.

“Karki damu inhar aka jajirce wannan ba komai bane ba. Sannan kema fa akan aikin nan zakija manda. Dan a yanzu haka zamu sauke miki miliyan ɗaya kafin ma aikin ya fara”.

Sosai Nadiya ta zaro ido waje, ranta fal farin ciki ta ce, “Yanzu yaya kuke so ayi?”.

Kallon juna sukai da murmushi, kafin Asim ya miƙa mata card da faɗin, “Ki samemu a wannan address ɗin zuwa anjima”.

“Wannan yafi komai sauƙi”.

Ta faɗa tana amsar card ɗin........

_______________★

Kwanaki uku kenan da fara fitar Lulu aiki, kullum kuma Smart ke kaita office da safe sannan shima ya koma gidan yay shirin tashi fitar a Napep. Idan ko fita ta kamata a yinin mai Napep ɗin nan da bata san da shi ba na biye da ita. Duk kuma inda ta saka ƙafa ana sanar masa. A lissafinsa dai babu wani abu dake faruwa, dan ranar farko ta sayi bread wanda bai san a tsakkiyarsa aka saka mata kayan shaye-shayen ta ba, kamar yanda takeyi sai zata kwanta tasha hakan tayi, shiyyasa bai gane komai ba sai ya ɗauka kawai gajiyar aikin data koma ce tunda tayi ƴar zirga-zirga. Washe gari dai yaga ta tashi a tsayenta bakamar kwana biyu datai wani sukuku ba. Rana ta biyu ma sai da tai amfani da dabarun nasu ta amsa, hakama jiya. Yau cikon kwana na uku yaso ya ɗan fara tsarguwa, amma dai baice komai ba. Yana son mata tambaya akan zuwa gidan su Sa'id sai kuma dai yay shiru. Sai kuma gashi a yau yana tare da Coach kira ya sameshi da ga Ammah wai yazo da sauri idan yana kusa. Ya Isa gidan da tunani kala-kala sai ya ɓige da samun mahaifiyar Sa'id da wasu ƴan uwanta maza uku dan dangin mahaifinsa sun rantse bazasu zo ba, ita data ɓata taje ta gyara sun dai zo na farko. Ba Smart kaɗai ba kowa ma na gidan nan yau mamakin jin maman Sa'id wai sunzo bada haƙuri ne da neman afuwar Hawwah dan ALLAH tai haƙuri ta koma yake. Smart yace shifa ƴar uwarsa bazata koma wannan gida ba, anyi kenan takardar saki kawai yake buƙata Sa'id ya kawo, dan suna sonta baza'a kashe musu yarinya ba. Sosai Maman Sa'id ke faman magiya akan wancan ma daya faru tsautsayi ne da munafuncin munafukai, amma yanzu ta gane gaskiya. Ankai ruwa rana matuƙa kafin Smart ya haƙura zata koman amma ba wannan gidan ba. Da sauri Mama tace ta yarda, Hawwah ta zaɓi duk inda take so a gidajensu a gyara mata. Wannan abu yaba kowa mamaki, Umma na son magana tana tsoron ta tanka Maman Sa'id tai mata bankaɗa tunda taji tana shaguɓe akan munafukai, ba kowa kuma ne mai zuwa ɓata Ammah da Hawwah a wajenta ba sai ita dama. Bayan wucewarsu kowa ya shiga mamaki, Abba ya tsare Smart akan miya ma maman Sa'id ɗin har tai irin wannan sakkowar lokaci ɗaya. Ya tabbatar musu bashi bane, dan shi target ɗinsa akan jiran dawowar mahaifin Sa'id ne ai. Yana son kawo Lulu a ransa wani gefe na zuciyarsa na musa masa. Amma dai duk da haka bayan ya koma gida da daddare sai da ya kasa haƙuri yay mata tambaya. Dariya kawai tayi taƙi faɗa masa komai, hakan ya tabbatar masa itace kenan tayi koma miye. Sai kawai ya zuba mata ido yana jin wani abu mai girma na ƙara ratsashi a kanta. Jin kaifin idanunsa a kanta ya sata dakatawa da ga abinda take a system ta ɗago, harararsa tai da faɗin, “Malam wannan kallon fa? Ni fa bana son kallo”. Ta ƙare maganar da murguɗa baki. Murmushi ya saki mai sanyi batare da ya janye idanun ba, sai ya samu kansa da furta, “Kullum sake mamaye komai da komai kike yi”. Bata fahimci ina ya dosa ba, sai dai yanda yay maganar a ƙasan maƙoshi da tausasa fitar sautin matuƙa ya sata tsayawa kallonsa, “Lafiya kake kuwa? Kodai kaima ka fara ban sani ba?”.

“Na fara mi?”.

“A hawa network mana”.

Ƙaramar dariya yay yana girgiza kansa. “Tom maybe na fara amma nawa ba irin naki bane gaskiya. Kema fata nake ki daina wannan ai ki dawo wannan irin nawan”.

Nan ɗin ma dai ba fahimtar tai ba, dan haka ma ta taɓe baki da miƙewa tana faɗin, “Ai kai kam wani lokacin kamar mai aljanu. Dolene na sanarma Ammah ta fara maka addu'ar su ko ka kwaso a drivern cin ba'a sani ba”. Daga haka ta wuce bedroom ta barshi yana murmushi.........✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣1️⃣



.........Washe gari gidansu ya wuce bayan ya sauketa, anan ne yake samun Abba da Ammah da batun shifa yana zargin Mawaddat ce tayi koma miye. Dan an sanar masa taje gidan a ranar monday. Mamaki sukaitayi suma da tunanin to mita faɗa ma maman Sa'id da har ta risina haka da sauri. A gefe kuma ƙaunar yarinyar na sake shigar musu zukata. Kamar yanda akace sati ɗaya cikin satin Hawwah ta fara shirin komawa sabon gidanta danƙarere. Hankalin Umma ya sake tashi, da bin ƙwanƙwanto ta gano Lulu ce tamayi koma miye har komai ya dai-daita. Hankali a tashe ta nufi gidan Hajiya Naqiba ƙawarta. Acan suka baje faifain zagin Ammah da bata san sunayi ba da Ƴaƴanta suna neman mafita dan abubuwa fa nata faman kufce musu a hannu, sai dai gaba ɗaya hankalinsu da mugayen ƙudirinsu sun tattara ne ga Lulu yanzu. Dan sun fahimci shigowarta gidan abubuwa da yawa ke neman taɓarɓarewa. Duk da su basu fahimci cewar asirin jikin Smart ma ya gama warwarewa gaba ɗaya ba. Ga aikin Malam na-zuru yaƙi yiwuwa, dan kayan Lulu da Smart dai sun gagara ɗakkuwa. Hajiya Naqiba ce cikin dogon tunani ta ce, “Aminiya anya bazamu canja taku ba?”.

“Kamarya? Fito kimun dalla-dalla, kin san bana son kwana-kwana fa”.

“Ina nufin ba asiri bane kaɗai yanzu ya kamata musa gaba dole mu haɗa da makirci da kissa. Kamar dai yanda nai akan shegun yaran can na baƙar dagar tawa.”

“In dai wannan ne ai mun jima munayi Aminiya, yanzu ko ita akan wannan shegiyar da zata koma Hawwah ai kinga sai da muka haɗa da makirci waccan shegiyar da bamu san mitaje tayi ba ta ɓata mana komai.”

“Kwantar da hankalinki karki damu, murnarsu zata koma ciki ne. Yanzu mu fara kai wannan baƙuwar hauren ƙasa tukunna dai. Dan wannan ƴar iskar amaryar da aka jajubo muku na fahimci da ƙarfinta tazo, gashi yarinyar nada ilimi fiye da tunaninki kuma goyon turai, ga kuɗi a gida, kuɗi a mota, kuɗi a Office, kuɗi a banki. Idan mukai sake fa komai zai koma wanwarne, ni ko da kishiya da yaƴanta su ji daɗin duniya ko komawa sama dani gara ace kowa ya mutu a ƙasar, ke ama busa ƙaho”.

Dariya Umma tayi da faɗin, “Hajjaju ke bala'i ce ai, shiyyasa nake sake tausayin Matar gidan nan naki. Yanzu ke miye shawararki?”.

“Dole ne muyi bincike akan yarinyar mu samo wanda zamu shiga jikinsa nata mu mata rugu-rugu”.

“Tab babbar magana ta yaya kenan? Bayan kin san daga wane gida ta fito, gate ɗin gidan su ma taɓa shi ba masifa bane balle shiga gidan”.

“Kwantar min da hankalinki. Akwai matar nan mai min ƙunshi ranar ana labarin dukiyar da aka zubar a auren ita yarinyar da aka kai gidanku take cewa ai ita taga zahiri dan itace kema matar Alhaji Garko ƙunshi shekaru kusan shidda kenan, shiyyasa tasan abubuwa da yawa a gidan nan ko shagalin bikin nan duk akan idonsu akai komai. Ita kanta taci rabonta dan tayi ƙunshi sosai a gidan, sai dai ta fahimci kamar matar Alhaji Garko bata son auren fin ƙarfinta akayi, yarinyar da ɗan uwanta aka saka mata biki lokaci guda ta birkice wai sai yaron gidanku”.

“Kai haba da gaske wai? Anya ba asiri suka mata ba ma kuwa”.

“Wlhy haka tace, babu abinda Hafsatu bazata iyaba wlhy, wama ya sani. Shiyyasa nake ganin ya kamata muje gidan Alhaji Garko mu kunnowa Hafsatu wutar da zata ƙoneta ƙurmus har ƴaƴan nata a wannan karon. Ba suna murna sun samu ɗiyar biloniya ba. Zasuci ubansu ne”.

Dariya suka kwashe da ita suna tafawa......

_____________★★

Kwanaki sun ƙara shiɗawa, dan a lissafin Lulu dai next week ne rabuwarsu da Smart. A week ɗin daya wuce ya kaita gidansu da gidan Uncle Yousuf, daga nan ta samu ƙafar zuwa duk bayan kwana biyu haka idan ta fita aiki takan leƙasu duk da dai daga Daddy har Uncle Yousuf ɗin ma dai sunyi tafiya basa ƙasar ma. A ranta a duk sanda ta ƙiyasta tana jin farin cikin komawarta free dan ta fara jin ƙosawa da tsakurarsa musamman ta saka hijjabi da tafi cimata zuciya da rai fiye da komai. Sai dai wani sashe na zuciyar tata na mata kamar babu daɗi musamman idan ta tuna Ammah da ƴan uwansa. Takan faɗa dogon nazari akan hakan, amma idan taje duba jikin kakanta Alhaji Garko da har yanzu dai babu lafiya suna ma shirin fita da shi ƙasar ne duk da yana turjewa sai da Dada taita mata fanfo da zugeta. Wani lokacin Lulun kan nutsu ta saurareta, wani lokacin kuma tace “Kai Dada dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login