Showing 45001 words to 48000 words out of 163036 words
“Yaya mafita ɗaya muke da ita shine yi mata aure....”
“Aure Yousuf? To da wa? Kasan dai Mawaddat bata kula kowa. Kana dai ganin duk kurari da jan idon Baba (Alhaji Sufi Garko) yayi ya barta akan sanya ranarta da yaron Sulaiman data bijirewa. Har gargaɗin duk randa wani ya sake zuwa garesa domin santa zai aura masa ita koba amincewar ta da mu kammu yay mata amma bata ɗauki hakan da muhimmanci ba saboda bushewar zuciya. Yousuf na rasa da ga ina na kuskure akan Mawaddat. Shin nuna mata soyayya na nufin ba dai-dai ba kenan?”.
“Humm Yaya wannan harda laifinka kaima ka sani, ba'a hana iyaye su nunama ƴaƴansu soyayya ba, sai dai ba ƙazamar soyayya irin wadda kaima Mawaddat ba da har tazama jagoran hanata fahimtar minene addininta. Yaya kofa salla nagartacciya Mawaddat bata iya ba a wannan shekarun nata balle azo ga sauran al'amuran addini, hakan kuma duk kuskurenka ne da kasa barinta ta samu tarbiyya irinta uwa a wajen Aunty Kareema saboda son zuciyarka..... Amma dai mu ajiye abinda ya wuce mu kalla na yanzu. Yanzu dai bayan tabbatar da aure ne mafitarmu akan lamarin Mawaddat bani da wani idea kuma. Amma dai ka bani lokaci nayi nazari tukunna. Sannan dan ALLAH ka kwantar da hankalinka. Dan lamarin Mawaddat an baro shiri ne tun rani. Amma insha ALLAHU tsayayyen miji a gareta zai jagoranceta da sabuwar tarbiyyarsa irin wadda tun farko ya kamata ace ta samu da ga garemu. Addu'a ya kamata mu duƙufa mata musamman ma kai ɗin nan. Sannan mu dage da sadaka ALLAH ya shiryar mana da ita, ya kuma kawo mana mafita cikin sauƙi. Sannan ka ajiye batun su Alh. Baita ni da kaina zanyi bincike a kansu insha ALLAHU zan gano alaƙarta da su”.
“Shike nan Yousuf ALLAH yay maka albarka.”
“Amin yaya”.
Daddy ya sake nisawa a hankali da faɗin, “Sai dai kabi a hankali a duk wani bincikenka dan a wannan gaɓar da gaske inajin ƙanina, tsoro na gaske nakeji wlhy a wannan gaɓar. Miya kawo su Alh. Baita cikin rayuwar Mawaddat?”.
“Bana tunanin wani abu saɓanin wanda zuciyata ke kallo yaya. Kasan dai da yawan wasu manyan ƙasar nan sunata taka wata rawa cikin rayuwar lalacewar yaranmu batare da mun farga ba”.
“Nafika sanin hakan Yousuf. Sai dai al'amarin ya wuce a yanda kai kake kallonsa da hasashensa. Kai dai kamar yanda na faɗa maka inajin tsoro da gaske a yanzu tsoro nake ji irin wanda a baya babu shi a zuciyata.....”
“Yaya na kasa fahimtar mi kake nufi ka ruɗar dani fa, Miye ke baka tsiro ne wai?”.
Murmushi Daddy yayi mai nuna tsantsar damuwa a bayyane. Maimakon amsa sai ya dafa kafaɗar Uncle Yousuf tare da ɗan bubbugawa ya miƙe. “Tashi kaje office auta karka makara”.
Kallo Uncle Yousuf ya bisa da shi mai tsayawa a rai, sai zuciyarsa ke wani irin rawa dan shi kaɗai yasan mi yake iya hangowa game da ɗan uwan nasa, sai kawai shima yaji kamar ya fara jin tsoron. Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari wanda ya kamata ace ya sani amma ta yaya? (Bincike akan alaƙar Mawaddat da su Hon. Babale Nakowa) kansa ya jinjina cikin gamsuwa da shawarar zuciyarsa. Dan haka shima ya miƙa ya fice. Da kallo yabi motar Yayansa dake ƙoƙarin ficewa a gidan. Numfashi ya sauke da ƙyar tare da nufar tashi motar shima.
★★★ ∆ ★★★
Smart kam tattara al'amarin Lulu yay ya wancalakar gefe domin fuskantar tasa mai muhimmanci. Gida ya nufa kai tsaye saboda kiran da Abba yay masa. Ya samu gidan da ƴar hayaniyar kasancewar zuwan Sa'id da wasu kawunansa uku. Cikin girmamawa ya gaishesu batare da ya kalla inda Sa'id ya ke gurfane ba kamar mai kuka. Ya maida hankalinsa ga Abba da Hawwah ke a kusa da ƙafafunsa kamar tana kuka itama.
“Abba gani”.
Ya faɗa cikin dakewarsa. Nisawa Abba yay da nuna Hawwah ya ce, “Kaine ka ɗakko Hauwa'u a gidanta?”.
“Eh tabbas nine Abba”.
“Me yasa?”.
Shiru ya ɗan yi kafin ya nisa. “Abba saboda ta kirani akan ga mahaifiyar mijinta na neman ƙonata da mangyaɗa. Banje gidan da nufin ɗakkota ba sai jin ba'asi na kuma sasanta kamar na baya da akai batare da kun sani ba. Sai dai na samu abin ya wuce yanda nake zatonsa shiyyasa na ɗakkota kafin a cutar da ita tunda mu bawai mun daina sonta bane ba. Ba kuma mun bashi bane dan mun gaji da ita a gidan nan kota gundiremu. Abba abubuwa da yawa sun faru akan auren Hawwah amma ina sasantawa a iya can batare da kai ko Ammah kun taɓa sani ba. Bama ku ba hatta da Aunty Bilkisu ban taɓa sanarmawa ba, kuma na gargaɗi Hawwah sanar ma kowa. Shiyyasa wannan karon na ɗakkota kuma bazata sake koma musu gida ba. Yaje ya auri wadda mahaifiyarsa ke son zama da ita haka nan dan ALLAH kowa ya huta.”........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣7️⃣
........Cikin ɓacin rai ƙanin mahaifin Sa'id ya ce, “Ai ba ita kaɗai ce keda iko da shi ba. Sannan kuma ni banga laifinka anan ba yaro. Hasalima abinda kai sai ka birgeni dan kayi abinda ya kamata ace ƴan uwa na ƙwarai suyi akan ƙannensu. Wannan shine girman kuma shine darajtawar.”
“Tabbas abinda yay yayi dai-dai. Kuma tunda hakane muma kan zamu fidda kammu a wannan zancen ku ɗauki duk matakin da kuke gani shine dai-dai dan halin Rafi'a sam bashi da burgewa. Narasa mitake son maida kanta a rayuwa ita ba ƙaramar yarinya ba amma kullum aita abu guda kamar cin ƙwan makauniya, yanzu da tsautsayi yasa ta samu yarinyar nan da mangyaɗan yaya kenan? Wace amsa take da shi na kare kanta. Dama tausayin yaron nan ya samu tasowa mu biyosa da wuri kafin abin yay zurfi. Amma tunda hakane zamuje muma har sai kun yanke hukunci kafin sannan shima Yaya Ibrahim ɗin ya dawo da ga tafiyar da yayi”.
Kuka mai tsuma rai Sa'id ya saki, dan harga ALLAH yana matuƙar ƙaunar matarsa Hauwa'u da ƴar ɗiyarsu Nasreen da taci sunan mahaifiyar tasa. Amma hukuncin da iyayen nasa suka yanke yasa bazai iya jayayya da su ba. Babu yanda zai yi ya bisu yana kallon Hawwah da kanta ke ƙasa tun shigiwarta batako kalla sashen da yake ba ma......
Ajiyar zuciya Abba ya saki a hankali, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. A taƙaice ya ce, “Kuje ciki zamuyi maganar a nutse”. Daga Hawwah har Smart miƙewa sukai suka fice. Babu kowa a tsakar gidan sai Umma da ke kai kawon girkin rana. Yanda bata tanka musu ba suma basu tanka mata ba. Sai dai murmushin data saki akan idon Smart. Shi ba ma'abocin maida hankali bane akan irin waɗan nan abubuwan dan haka yay shigewarsa, sai dai murmushin ya sosa masa zuciya da tsaya masa a rai. Ammah dake zaune a falo Nasreen a cinyarta tana shan kunu kallo ɗaya tai musu ta maida hankalinta ga Nasreen ɗin. Zama yay kamar yanda Hawwah da ke sharar hawaye itama ta zauna. Idanu ya ɗan zuba mata tare da furzar da huci kaɗan. “Shi wannan kukan babu amfanin da zai miki, bakuma zai gyara abinda yake faruwar ba. Kisama ranki haƙuri da nutsuwa, dan bazaki koma wannan gidan ba har sai tasan darajarki. Idan kuma kina ganin ba'ai miki gata ba a hakan dan naga k da mijin naki duk shashashu ne ga hanya nan zaki iya binsu” Daga haka ya miƙe.
“Kayi haƙuri Yaya ni banga laifinka ba, kuma nagode da ƙoƙarinka a kaina”.
Komai baice mata ba, sai duban Ammah da tai kamar bata ɗakin da yay. “Ammah ni zan koma”.
“ALLAH ya tsare ya bada sa'a”. Tace masa batare data ɗago ba. Da Amin ya amsa yana ɗan lakatar kumatun Nasreen da itama tai masa a dawo lafiyar. Da ga haka ya fice abinsa badan yasan ina ya kamata ya dosa ba tunda boss ɗin tasa ta korosa yau.
Sai da ya fito gaba ɗaya da ga layin nasu zuciyarsa ta kwaɗaita masa zuwa ma ya duba trainers ɗinsu. Dan kwana biyu basuga juna ba. Waya ya ciro tare da ɗan ƙura mata ido kamar mai tunani, sai kuma ya ɗan ɗage kafaɗa tare da kai wayar kunnensa bayan yay dailing number daya lalubo. Bugu uku aka ɗaga, yay ƙaramin murmushi da faɗin, “Barka da hantsi sir”. Amsar da aka bashi da ga can ta sakashi sakin murmushi. Sai kuma ya ɗan shafo kansa alamar jin kunya tamkar yana gabansa. “Am sorry Sir na ɗauka laifina. Yanzu ma ina son zuwa gaishekanne shiyyasa nace bara naji inda kake”. Ya ɗan yi shiru alamar saurare. Sai kuma ya amsa da “Okay gani nan zuwa in sha ALLAHU”.
Tafiyar mintuna ƙalilan da bai wuce ashirin ba ta kaisa babban stadium ɗin da coach ɗin nasa yace masa yana acan. Wajen ya ƙayatu matuƙa. Babu yawan hayaniyar mutane sai isu-isu ƴan wasa da ke ta tsalle-tsalle alamar training sukeyi saboda wasan sada zumunci da suke shirin zuwa kudancin ƙasar. Tunda ya shigo wajen ɗaya da ga cikinsu da ya fara ganinsa ya saki wani irin fito daya jawo hankalin sauran suma. *_“Capten!! Carpten!!”_* suka shiga faɗa cikin ihun da ke nuna tsantsar farin cikin ganinsa. Murmushin Smart ne ya sake faɗaɗa, shima ya shiga ɗaga musu hannayensa duka biyu har ya ƙarasa gaban Trainers ɗin nasu da ke kallonsa shima da murmushi. Har cikin rai yana matuƙar son yaron, ya kuma ci buri a kansa dan Smart ya iya gara ƙwallo mai suna ƙwallo ta gaske, dan ma mun kasance a ƙasa irin ta Nigeria da mai alfarma yafi ma'iyi da tuni wani labarin ake akansa ba wannan ba. Amma duk da haka shima ya damu wasu dama na barin ƙasar ƙaddara ta toshe su. Sai dai ALLAH mai hikima duk da tarin damammakin da yaron ya samu tun yana da shekara goma sha takwas komai yaƙi motsa kansa a inda yake. Hannunsa ya kamo da ga hanashi risininawar da yay niyyar yi, “Yarona irin wannan ƙiba haka anya kuwa kana motsa jiki?”.
A yanda coach ɗin yay maganar ya saka Smart yin ƙaramar dariya da shafa kai yana ɗan dudduƙar da kansa da faɗin. “Sir ina nan a yanda ka sanni girman rigane kawai”.
“Bari nace to. Amma badan na yarda ba. Ykk to ya kwana biyu? Tunda ka samu aikin nan ka ɓuya gaba ɗaya ko?”. Ya ƙare maganar yana jan hanunsa suka ƙarasa kan wasu kujeru da ke gefe kaɗan. Smart da har yanzu bai bar murmushi ba ya ce, “Sir aikinne bai barin motsin kirki. Amma kuna raina sosai”.
“To Alhamdullah babu dai wata matsala kuma ko?”.
“Da sauƙi dai Sir”.
“A cigaba da haƙuri, komai yay farko zaiyi ƙarshe. Fatanmu dai ALLAH ya warware mana abinda bamu da ilimin sani akansa”.
“Amin Sir”. Ya faɗa cikin damuwa idanunsa akan teammate ɗinsa da ke ta tsalle-tsalle su har yanzu. Hira suka cigaba da yi da oga wani kaso na hankalinsa na ga teammate ɗin nasa dai. Kiran wayar coach da akai ta sakashi miƙewa ya ɗan matsa a wajen. Dai-dai nan ɗaya daga cikin ball ɗin da suke training ɗin da ita ta gangaro wajen filin har inda Smart ke zaune. Kamar wanda aka tsikara ya miƙe da alamar tsumin ya motsa. Cikin wani irin salo da iya ƙwarewa a harkar ya buga ball ɗin tamkar abin almara bata sauka ko ina ba sai cikin raga. A take wajen ya ruɗe da ihunsa, kamar waɗanda ake juyawa da remote suka raba kansu yanda ƴan ƙwallo kanyi a cikin fili yayin wasa. Ƙarasa shigewa cikin filin yay shima cikin zafin nama da jin shauƙi a ransa, dan da gaske ball itace hubby na Smart. Tana sakashi karsashi da nishaɗi maƙurar ƙurewa.
Juyowar coach da ya kammala waya ya sashi waro idanunsa waje sosai na ganin abinda ke faruwa. Sosai ya rikice dan yasan da wahala a wanye lafiya... Ilai kuwa kafin ya kai ƙarshen tunaninsa da yay dai-dai da sake saka ƙwallo ta biyu a raga da Smart yayi ya wani ƙwalla ƙara hannayensa duka biyu dafe da kansa. Kafin su isa kansa ya zube ƙasa a sassanƙame. Hankalin coach idan yay dubu ya tashi, haka ma sauran teammate ɗin nasa duk sun rikice. Babu ɓata lokaci suka fiddashi a filin coach na musu faɗan miyasa suka barshi ya shiga tunda sun san matsalarsa. Su dai basu da tacewa dan mai afkuwa ta riga da ta afku kuma. Sai fatan a kiyaye na gaba dai.
Duk wani kalan taimakon da sukan masa idan matsalar ta samesa ita Hameed yay masa, sai dai kamar yanda aka saba babu alamar za'a samu kansa a yau ɗin. Sosai ya sake shiga damuwa, ina daɗi da ga zuwansa gaishesa a rarraɓesa a kaima iyayensa shi a haka. Dole yay kiran ƙaninsa Ahmad aboki ga Smart ɗin kenan akan yazo suje gidan su Smart ɗin. Da mamaki Ahmad ke tambayar yayan nasa ko wani abu ne ya faru? Bai wani tsaya kwana-kwana ba ta sanar masa. Hankalin Ahmad ya tashi, babu shiri ya baro office ya nufo stadium ɗin.
Yana ajiye wayar kiran babban amininsa Yousuf Ibrahim Jiƙamshi na shigo masa a waya (Uncle Yousuf) kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga ɗin dan sunyi da shi zasu haɗu shi shaf ma ya manta sai da yaga kiran. Furucin Uncle Yousuf da ke faɗin, “To baban ƴan tamaula ALLAH yasa dai ka gama da yaran naka dan bana son zuwa nai zaman jiranka zan koma office saboda baƙi da nake tsumaye bayan azhar”.
Cikin damuwa coach ya ce, “Wlhy ni nama manta da da batun zuwan naka ina nan a rikice”.
“A rikice kuma a kan mi?” Uncle Yousuf ta faɗa cikin mamakin aminin nasa.
Shima amsa ya bashi da faɗin, “Wlhy Aliyu ne yazo mu gaisa fa na ɗan tashi amsa waya ban san yaya akai ba ya shiga cikin fili ka gansa nan sharɓan babu alamar rai tare da shi”.
“Ya Arrahaman! Aliyu dai Aliyu nawa Smart Mawashi?”.
Sai yanzu ma shi coach ya tuna ashe Aliyu a ƙarƙashin abokin nasa yake a yanzu. Dan haka ya bashi amsa da cewar, “Yess! Yes! Shifa wlhy”.
“Ya Salam gani nan a hanya”.
Kusan a tare Uncle Yousuf da Ahmad suka iso wajen. Kowanne ya fito a motarsa da sassarfa zuwa inda suke zagaye da Smart da ke kwance a ƙasa kansa bisa jikin coach da ke faman shafa masa ruwa yana fatan ya farfaɗo, dan bai son su kai shi gida a wannan yanayin musamman daya tuno irin tashin hankalin da Ammah ta shiga last da abin ya faru da shi. Har rige-rige ake tsakanin Uncle Yousuf da Ahmad, sai dai kowanne ya samu nasarar kai hannunsa jikinsa. Ganin yanda aketa faman saka masa ruwa babu alamar zai farfaɗo Uncle Yousuf ya cema coach “Hameed muje asibiti kawai dan banga alamar zai farfaɗo ba a hakan nan”.
Cikin damuwa coach ya dubesa shima da bashi amsa da “Yousuf zuwa asibitin nan babu abinda zai canja. Dan mun gwada yin hakan a baya sai dai mu gama zaman banza dan su amsa ɗaya ma suke bamu zuciyarsa ta tsaya da aiki. Al'amarin nasa ne fa kamar abin sihiri gashi nan dai. Gida kawai ya kamata mu kaisa duk da gaskiya hakan na sakani fargaba dan tayarwa iyayensa hankali kawai zamuyi”.
“Gaskiya kar a kaishi can Brother” Ahmad ya faɗa cikin damuwa. Bai jira cewar kowa ba ya cigaba da faɗin, “Mizai hana muje wajen mutumin nan da ya taɓa bashi magani sanda abun ya takura masa”.
“Shawara mai ƙyau Ahmad, da ni duk nama rikice wlhy hakan bai zo min a rai ba. Kunga ku kamashi kusa a mota”.
A bayan motar Uncle Yousuf aka saka shi kamar yanda ya buƙata, shi da coach suka shiga gaba Ahmad a baya ya riƙe Smart. Kai tsaye ƙofar ruwa suka nufa, gudun da coach keyi ya sakasu isa cikin ƙanƙanin lokaci. Gidane irin na talaka mai ƙaramin ƙarfi, sai dai da ga waje shafe yake da siminti tsaf da shi da milk ɗin fenti. Da ga gaban gidan kaɗan islamiyya ce ta ƙanan yara da keta karatu kasancewar akwai ta safe zuwa ƙarfe ɗaya. Tsaiwar motar ta saka wani saurayi da ke tsaye da ga jikin barandar Islamiyyar matsowa garesu yana musu sannu. Basu wani tsaya jan maganar ba suka buƙaci ganin Malam. Kafin ya basu amsa sai ga malam ɗin ya fito da ga gida..........✍️
_Yau dai Smart ɗin ku ya ɗan bani tausayi🥲_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣8️⃣
_Ya rabbi ka gafartama *Sheikh Abubakar Giro Arugungun*. Ka yafe masa kurakuransa, alkairan da