Showing 129001 words to 132000 words out of 163036 words
Jiƙamshi. Kasan bazaka iya ƙarasa wasan ba miyasa ka fara? Common ƙyaleni bana buƙatar hayaniya, ba kace da ni zaka buga game ba? Muje zuwa”.
(Tana mun magana kamar wata lady boss) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam kansa kawai ya dafe. Abu tamkar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa har 12 tayi Lulu bata da niyyar bama Smart key ɗin nan, zuciyarsa na raya masa ya turmuzeta ya amsa amma yana gargaɗin kansa karta tada masa aljanu, dan yasan mata da iya aljanu. Sha biyu da kusan kwata kiran Uncle Yousuf ya shigo masa. Ya ɗaga ya gaida shi da mutuntawa kamar yanda ya saba. Da ga can Uncle Yousuf ya ce, “Aliyu yaya dai? Kai muke jira na ga har 12:15?”.
Ɗan kallon Lulu da ke ta aikinta a laptop tana zuba murmushin mugunta yayi, a can ƙasan maƙoshi ya ce, “Uncle ta kwashe keys ɗin ne fa, wai tunda na hanata fita nima babu inda zanje”.
“What! Mawaddat ɗin? Kaga bata wayar Please bana son shiririta”
Maimakon bata sai ya saka a hansfree yanda zataji, kiran sunanta da Uncle Yousuf ɗin yay ya sata ɗagowa ta kalla wayar, sai kuma ta amsa da “Yes Papa good afternoon”.
“Afternoon Dear. Miya faru kika hana Aliyu fitowa ga shi munata jiransa?”. Murmushin muguntar da take ta faman yi tun ɗazun alamar duniya ta mata daɗi ta sake saki da faɗin, “Uncle You shi ya zaɓi hakan ai, dan haka ka manta da shi kawai, dan yanda ya hanani fita sai dai mu yini tare a gidan.”
“Mawaddat Please!!”
“Uncle please”.
Ta faɗa itama kamar yanda yayin tana tura baki. Kai kawai Uncle Yousuf ya dafe da ga can, yayinda Coach ke kwasar dariya dan Smart ɗin kawai ya ke hangowa, kai mace daban ce, yo inba mace daban take ba Smart ɗinsa ne da ya sani mai tsaurin nan da rashin son magana za'a kullema ƙofa a hanashi fita. Aure aunre yayi. A ɓangaren Uncle Yousuf kam iyakar lallaɓa yay ma Lulu tafa ce ba gudu babu ja da baya, har ya koma faɗa amma tai biris, ba komai ke tunzurata ba kuma sai ganin yanda fuskar Smart ta fara canjawa da dauriyar da yake zuwa ɓacin rai. “Uncle bye”. Ta ce cikin siririyar dariya tana miƙewa tare da laptop ɗinta da wayoyinta tabar falon ma tana ɗagawa Smart yatsu biyu na ƙularwa ta ce, “2-1 ka shirya yin game over gaba kaɗan”.
Wani irin bahagon iska ya furzar da ga bakinsa yana mai dafe kansa. Da ga can cikin tunzura shima Uncle Yousuf ya ce, “Aliyu wai yarinyar nan tafi ƙarfinka ne da karɓar key a wajenta ya gagareka. Be a man mana Son”.
“Uncle bazaka gane bane wlhy, yarinyar nan azababbiya ce, tafa saka key ɗinne.....”
Sai kuma yay shiru fahimtar ɓaranɓaramar da yake neman yi. Uncle Yousuf zai sake magana coach ya katsesa da faɗin, “Kaga ƙyaleta muje mu samesa a can kawai nikam, dan amarya dai bata laifi koda ta kashe ɗan masu gida. Zakina jiramu karka damu”.
Kafin Smart ya ce wani abu an yanke wayar, sai kawai ya girgiza kai. Wannan ma sauƙin kan na Coach ya sa yake sake jin ƙaunarsa a ransa. Mutumin nan shi na musamman ne a garesa, dan ya taka rawa kala-kala a cikin rayuwarsa da har abada bazai manta ba........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣2️⃣
.........Cikin mintuna da basu wuce ashirin ba sai gasu sun iso, jin horn ɗin su da kiran da Coach yay masa ya ce gasu sun iso ya saka shi miƙewa ya nufi bedroom da ta shige. Fuskarsa babu walwala da ga bakin ƙofar ya tsaya yana kallonta da faɗin, “Sun iso Please ki kawo naje na buɗe musu”.
Ɗagowa tai ta ɗan hararesa da maida kanta tana taɓe baki, “Oh wai har yanzu kana tunanin amsa cikin sauƙi ko min wayo? To anƙi a bada ɗin na ƙarfi ne”.
Kaɗan ya cije lips ɗinsa da jin jina kai yana wani ɗan murmushi, dan ya fahimci sai yayi abinda tun ɗazun yake hana kansa yi sannan. Takowa yay zuwa gaban gadon tare da kaiwa zaune cikin lallashi ya ce, “Mawaddat su Uncle Yousuf ne fa, kuma na faɗa miki magana mai muhimmanci zamuyi....”
“Nima ai aiki da zan fita yi mai muhimmanci ne ka sani. Gara ma ka bar wani sauke murya ba badawa zanyi ba ehe”. Ta juya ta cigaba da aikinta.
Lips ɗinsa ya sake cijewa da faɗin, “Amma kin san zan iya amsar key ɗin a duk ta yanda naso ko?”.
A gatsine ta ce, “To ƙarɓi ɗin mana”.
“Haka kika ce?”.
Shiru ta masa kamar bata ji ba, sai ma faman murmushin ta take tana sarrafa system ɗin gabanta cike da ƙwarewa dan charting take yi da wata friend ɗinta ƴar ƙasar Hong kong da sukayi karatu a America tare. Laptop ɗin gaban nata ya janye gefe tare da birkitota, zabura tayi dan batai zaton zai yi yunƙurin amsar ba, sai dai kafin tayi wani yunƙuri ya danneta da rabin jikinsa ya riƙe hannayenta duk biyu a cikin nasa. Rawa jikin nata ya fara yi saboda yanayin na neman maimaita kansa ne da abinda ya shuɗe, amma cikin ƙoƙarin dakewa ta ballara masa harara. duk da shima ya fahimci hakan bai bi takanta ba sai ma baki da ya taɓe da sakin murmushin nan nasa data raɗa ma suna na rainin hankali cikin kashe ido ɗaya ya ce, “Zaki bayar da arziƙi kona ɗauka?”.
Sosai ta waro idamunta da suka cika da ɓacin rai ta ce, “Saboda kai ɗan is.....”
Baki ya taɓe da faɗin, “Oh ɗan iska ko?” sai ya ƙara ƙasa da murya yana kai bakinsa jikin kunnenta ya raɗa mata, “Dole ne ma nayi iskancin nan dan banzan amsa sunan nan a banza ba”.
“Aliyu!!”
Ta faɗa tana zaburowa gaba ɗayanta sai dai har ya riga ya tura hannunsa a rigarta ya ciro key ɗin. “3-1 Madam” ya faɗa yana sakin mata hannu da ɗagata murmushin mugunta fal fuskarsa ya nufi ƙofa ya fice harda mata gwalo.. Rumtse idanunta kawai tai da masifar ƙarfi tana ƙoƙarin dai-daita numfashinta dake rawa a maƙoshi......
Koda ya fito cikin girmamawa ya tarbi su Uncle Yousuf ɗin, basu shiga ciki ba kamar yanda ya buƙata, sai suka zauna a ƙarƙashin rumfar bunu da ke a harabar gidan domin hutawa. Ya gaishesu cikin mutuntawa, yayin da Coach ya tasashi a gaba da tsokana, murmushi kawai yake yi amma ya kasa cewa komai. Uncle Yousuf ya harari Coach da faɗin, “ALLAH kai dai anyi Yayan kwabo, ka ƙyale min yaro ya huta”.
Cikin dariya Coach ya ce, “Oh ashe fa kai yanzu ka tashi da ga Yaya ka koma suruki. No wander bakin Zaki na ya sake zama rumus yau. Bara to na tausaya masa sai ka matsa na ɗora da ga inda na tsaya dan ba barinsa zanyi ba fa”. Murmushi kawai Smart ke yi dan in dai Coach ne ya riga ya saba da wannan barkwancin nasa. Dama kuma can bai iya maidawa balle yanzu da yake ganin Uncle Yousuf da ya ƙara girma a idonsa na wajen. Sake gaisawa sukayi kafin su fara tattauna abinda ya tarasun. “Aliyu nasan ka ɗokantu da son jin dalilin wannan zama namu, kamar yanda muma muke a ɗokancen”.
“Haka ne Sir, dan da har na fara tunanin ko nayi wani laifi ne ma”.
Murmushi Uncle Yousuf da Coach sukayi a tare, kafin Coach ya cigaba da faɗin, “Aliyu kai na daban ne ai, duk da dai ɗan adam tara yake bai cika goma ba. Bakai laifin komai ba abinda muketa fatane da buri ya kasance. Yousuf abokina ne koma nace maka ɗan uwana dan ina jinsa tamkar matsayin twins brother, kamar yanda ka sani ya sanni da kai tun kana ƙaraminka, sannan masoyine naka dan yana ɗaya daga cikin wanda suka dinga goyon bayanka matuƙa, sannan ya taka rawar gani matuƙa a baya na son ganin ka ƙetare ƙasar nan amma ƙaddara ta hana hakan. Bai haƙura ba ya cigaba da shigi da fici na ganin abubuwa sun dai-dai har kawo yanzun nan bai huta ba. A yanzu dai a matakin ƙwallo shekarunka sunja Aliyu, sai dai Alhmdllh yanayin jikinka da kula da motsashi yasa kai tsaye baza'a iya cewa ka kai shekarun da kake ɗin ba a yanzu. Dan haka mataki na farko shine mun zabge maka shekaru a rubuce, mataki na biyu yanzu zaka daidaita cin abubuwan da duk suke saka jiki nauyi domin samun daidaito, sannan zaka sake jajircewa da training. Inata kai ka ban faɗa maka dalilin zancen ba. A karo na babu adadi Yousuf ya sake maidaka duniyar ƙwallon ƙafa a yanzu, a kuma matsayin manager ɗin ka. Duk wani abu da zamu iya kallo a matsala yayi iya bakin ƙoƙarin sa na shiga da fita wajen gyarashi da alkintashi cikin nasara kasancewar sa mutum mai kutsa-kutsa da huɗɗa da mutane a ƙasashen ƙetare. A yanzu haka ka samu team a ƙasar London in sha ALLAH signing da abinda baza'a rasa a kawai ya rage”.
Shiru kawai Smart yay yana saurarensu, har sai da Coach ya kai ayar bayaninsa sannan ya dubesa ya dubi Uncle Yousuf ɗin ƙwalla na cika masa ido. Kai Uncle Yousuf ya girgiza masa da masa alamar zip a baki baya son yace komai kenan. Wani irin al'amari mai girma Smart ya haɗiye tare da duƙar da kansa yay shiru ba tsawon mintina. Ba komai yake ba face kwararoma waɗan nan mutane biyu addu'oi kala da iri, sai da ya kammala sannan ya ɗago cikin ƴar damuwa. “Kun hana nace komai duk da inada abubuwan faɗa masu yawa. Ku na dabanne a garen....”
“Shiiii!!” Uncle Yousuf ya faɗa cikin dakatar da shi. Dole ya haɗiye tarin yabo da godiyar dake gumtse a zuciyarsa zuwa baki, ya tsira musu idanu kawai, sai kuma ya nisa a hankali “Amma Sir bakwa gudun a sake samun makamanciyar irin waccan matsalar?, bana son ku sake shiga matsala a dalilina”.
“In sha ALLAHU bama fatan hakan Aliyu. Kuma ai mu fatanmu wannan dabarar ta zama mafita. Ball hubby na ka ne, na sanka komai akace kayi ba ita ba zaka iya yin amma badan hakan na maka daɗi a rai ba. To a rayuwa duk abinda bawa zaiyi badan yana son abin nan ba zakaga yana tafiya ne babu wani armashi. A wannan karon bawai kai tsaye muke son ayi hakan ba, sai da muka duƙufa addu'a mu da su Ammah gaba ɗaya kafin ma duk wannan kai kawon na Yousuf, dan na tabbatar addu'oi nasu ne suka shiga kan gaban komai ya tafi mana yanda mukai fata ƴan matsalolin da suka faffaru ba wasu masu yawa bane gaskiya”.
“Su Ammah?!...”
Smart ya faɗa da ɗan mamaki, kai Coach ya gyaɗa masa da faɗin, “Yes da ga ita har Abba sun san komai akan wannan, kuma Alhmdllh bamu sha wahala wajen amincewar tasu ba kamar farkon magana da su akan barinka fara ƙwallo”.
A hankali ya ɗan furzar da iska yana jin jina kai shima, sai dai a ƙasan ransa yana jin wata nutsuwa mai tarin yawa, dan da gaske ƙwallo abar sonsa ce, burinsa ce tun yana ƙanƙaninsa fiye da kowanne abu da zai iya yi ciki harda zaman office. Takardun da Coach ya fara bashi a farko ya buɗe, ɗan duddubawa yay sai kuma ya ɗago yana kallon Coach ɗin, “Ammah Sir taya kuka samu irin wannan damar haka cikin sauƙi, bayan nasan mutanen kudancin nan namu da iya babbake komai sai su. Su kuma turawan nan da tsantsani akan komai?”.
“Addu'a ne kawai Aliyu, sannan bawai da sauƙin aka samuba ma, an jima ana yaƙin, amma mutuminka dai ne wannan karon ma ya sake shiga ya fita da tsayawar ALLAH data Yousuf muka samu sunan naka ya zama gaba-gaba. Sai su kuma wasanninka da suka ɗan gaggani na baya ya sake ɗaukar hankalinsu matuƙa. Kaga kenan Addu'ar su Ammah tafi gaban komai”.
“Hakane Sir” ya faɗa cikin rauni, sai kuma yay murmushi da kallon Uncle Yousuf da shima ke kallonsa da murmushin. “Uncle kayi haƙuri ka barni na faɗa, wlhy ku na dabbanne a gareni a cikin daban. Har abada harshena bazai gushe wajen muku addu'a ba ku da zuri'arku. Uncle......”
“No no no Aliyu it's ok! Ya Isa haka ba sai ka cigaba da cewa komai ba, addu'ar nan daka ambata a garemu ita kaɗai ta wadatar, muma bayin kammu bane, ALLAH kaɗai yasan alkairin da ke cikin al'amarin shiyyasa nasarori da yawa suka samu cikin sauƙi. Abinda kawai na sani shine Aliyu kai yaron kirki ne nagartacce da bai kamata ai sakacin da samuwar wata dama irin haka gareku ba, dan arewacin Nigeria na matuƙar buƙatar irinku koma nace Nigeria ko African gaba ɗaya, in sha ALLAHU nan da lokaci ƙalilan sunan Smart Mawashi da ya fara bayyana ƙaddara ta binne sa zai yi zaburar da zata girgiza duniyar ƙwallon ƙafa. Wannan basirar taka bazata wuce a banza ba kamar yanda muke sakaci da ire-iren ku ta hanyar dakushesu a dalilin rashin kulawarmu. Wannan plan ne na shekara kusan biyu da rabi, koda wasa bana son ka kallesa a matsayin dan kana auren ɗiyata ne”.
Murmushi mai faɗi Smart yayi har wasu ƴan ƙwalla na sake tarar masa a ido kaɗan, sai yaji yama kasa cewa komai kawai. Dai-dai nan Lulu ta iso wajen, maganar Uncle Yousuf ta fargar da shi hakan.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣3️⃣
.......Juyawa yay ya kalleta, sai akai sa'a itama ta kallesan suka haɗa ido. Harararsa tai ta ɗauke kanta. Shima sai ya maida nasa gefe kaɗan yana ɗan murmushi. Bata saka hijjab ba amma ta ɗaura Abaya a saman kayan jikinta tare da yane kanta da ɗankwalinta. Tray ɗin hannunta ta ajiye musu fuskarta da murmushi da shagwaɓa bayan ta gaida su ta dubi Uncle Yousuf da faɗin, “Papa i miss you ALLAH”. Dariya Uncle Yousuf yayi da jin daɗin ganinta yanda yake fata tunkan aje ko'ina. Sai da ya karɓi kofin ruwa data zuba masa sannan ya furta, “Mu kewarki ma bamu san yanda zamu misalta ta ba ai Mawaddatan'warahmah. Na gaban goshinki na can yau da ƙyar ya yarda zaije makaranta”.
Murmushi tayi da faɗin “Uncle Please a kawo min shi to mana”.
Shima sai yay ɗan murmushin da faɗin, “Tom ki ƙara hutawa, in dai waɗan nan ne sai kin gaji da su a gidan nan. Dan yanzu haka ma su Auntynki na zuwa”.
Sosai taji farin cikin hakan, duk sai zumuɗi ma ya hanata zama ta juya ciki wai bari yaje ta shirya kafin su iso. Shi da Uncle Yousuf da kallo duk suka bita, yayinda Coach hankalinsa ke kan takardun nan. “Ina fata dai babu wata damuwa ko?”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin katse tunanin Smart. Kansa ya jinjina masa cikin sauke numfashi ya ce, “Da sauƙi dai kam. Dan na fahimci wani lokacin tana da sauƙin kai musamman akan lagon mahaifiyarta da ka bani, dan in har zan jingina mata sunanta akan abu zatayi sa babu musu”.
“To Alhamdullah, naji daɗi sosai dan hakan ma ci gaba ne. Ka ƙara haƙuri na haɗaka da aiki, amma nasan nan gaba kaɗan zaka gode min kaima. Dan Mawaddat nada wasu ɓoyayyun al'amura musamman halayen masu ƙyau, a yanda ta tashi taga kanta ne kawai babbar matsalar, sai dai duk da haka tsiwa da jin kanta sama sosai a jininta yake, dan mahaifiyarta tamkar tayi kaki ne ta ajiye, itama haka take kamar wata jinin sarauta wajen izza. Bambanci su kawai ita ta samu tarbiyya fiye data Lulu ne, da kuma kasancewar ita da girmanta ta haura wata ƙasa karatu ba kamar Mawaddat ba. Sai dai fa Aliyu yanzu yaƙin bana Mawaddat bane kawai, sannan ba ita kaɗai bace a filin dagar. Na farko sai munyi haƙuri da Yaya, na biyu Alhaji Sulaiman da ɗansa, dan nasan duk da baya ƙasar nan hankalinsa na nan, kuma gab yake da dawowa tunda jikin Tajuddeen ɗin da sauƙi.”
“Karka damu Uncle Yousuf ku dai ku cigaba da mana addu'a. Daddy kuma insha ALLAH babu komai a tsakanina da shi sai girmamawa, na kuma fahimci son da yake mata ne mai tsanani da tausayinta ke rinjayarsa”.
“To Alhamdullah nagode daka fahimci haka. Yanzu sai ka fara shirin nan da kwanaki zakaje Legos ɗin kamar yanda suka buƙata”.
“ALLAH ya kaimu”.
Da Amin suka amsa su biyun. Da ga haka suka ɗan sake tattaunawa shi da Coach akan abinda ya shafesu na harkar ball ɗin dan yanzu kam zai koma filin daga saboda training, sunja lokaci sosai dan har aka kira sallar azhar kafin su bar gidan su uku suna tsokanarsa da dariya wai yanzu ya koma ɗan 23years. Uncle Yousuf harda faɗin yanzu