Showing 63001 words to 66000 words out of 163036 words
Dan a jiya mahaifinsa a gabanmu ya sake gabatar da zancen ku ga Baba. Nasan kuma baki manta da alwashi Baba ba na cewar duk wanda yazo neman aurenki ko da amincewarki ko babu ko da tamu ko babu zai aura masa ke. Kinga hakan na nufin a cikin biyun nan dole ne ki zaɓi ɗaya”.
“Wlhy Uncle You bana son kowa a cikinsu. Kuma shi tsinanne Haruna ɗin nan ni ban taɓa magana da shi ba ma balle maganar aure na rantse maka Uncle”.
“Ni wannan ba matsalata bace Mawaddat. Dan a yanzu haka ma Baba nacan na zaman jiranmu ni da ke da Yaya akan wannan maganar dan haka ma na dakatar da ke daga fita. Idan kuma kina da wanda kike so sai ki faɗa mana yanzu mu nemosa aje da shi gaban Baba ki kuɓutar da kanki, dan hakanne kawai zai hana Baba bama ɗaya da ga cikin waɗan can ɗin aurenki kamar yanda kika san shi baya magana biyu”.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣6️⃣
........“Na shiga uku Uncle, ni ban shirya yin aure ba wlhy. Dan ALLAH ka faɗa mini ya zanyi?”.
“To ni Mawaddat taya zan san ya zakiyi. Yanzun ma na faɗa miki ne dan bana son a miki abinda nasan baki so. Dan Baba bazai taɓa canja ra'ayinsa ba a wannan karon kin sani na sani. Ga kuma Yaya wajen ƙoƙarin ganin ya kare ki sai ya sake wata ɓaranɓaramar wai kina da wanda kike so”.
Fuska ta kuma kwaɓewa idanunta na cika da ƙwalla. “Uncle You wlhy guduwa zanyi”.
“Guduwa kuma? A ganinki itace mafita Mawaddat?. To ai ina ganin dan kin gudu kinyi a banza, dan in dai Baba ne zai aurar da ke ɗin babu fashi ya kuma saka mijin taddaki har inda kika je ɗin ko shi yaje da kansa ya dawo da ke ya danƙama mijin. Kinga anyi ba'aiba kenan ko. Ni dai ina ganin kawai mu ɗauki kariyar da Yaya ya baki muyi amfani da ita dan ki kuɓuta gaba ɗaya”.
“Uncle wacce kenan?”.
“Samo wani matsayin wanda kike so kuma zaki aura. Sai dai ni da ke ne kawai muka san ba haka bane, bayan ƙura ta lafa shike nan sai ki cigaba da sabgarki, idan Baba yayi magana muce iyayen yaron muke jira dan sunce a ɗan jinkirta musu zai ƙarasa gininsa ko dai mu samo wani abu da zai ɗauke hankalin Baba da ga kanki gaba ɗaya”
“Hakan yayi, to amma Uncle kasan fa baba da shegen bin ƙwaƙwƙwafin abu idan kuma ya gano fa?. Sannan ma wa zamu iya samu ya mana wannan aikin batare da an samu wata matsala ba?”.
“Eh kuma fa kema kinzo da maganar dubawa gaskiya. Dan Baba kam zai ma iya sawa ai masa bincike. To amma ina ganin mizai hana shi wanda zamu samar ɗin kawai ki yarda kuyi auren contract da shi, komai mune zamu tsara masa ayi auren amma bayan wata ɗaya ya rabu da ke, sai dai da sharaɗin kada kowa ma yasan ya sake ki har sai bayan wasu shekaru.”
Shiru Lulu tai tana auna zancen Uncle ɗin nata. Sai dai da ace tana da ilimin addini da ya kamata tai hasashen yin hakan fa zai iya zama kamar ta zurma kanta ne. Amma a maimakon hakan ita wani tunani take da ban, dan tana ƙiyasta faruwar al'amarin ne cikin sauƙi kasancewar a inda ta girma cikin turawa wannan ba komai bane yin auren yarjejeniya.. ganin yanda tai nisa Uncle Yousuf ya katseta da faɗin, “Mawaddat bamu da wani isashen lokacin dogon tunani a yanzun fa”. Firgigit ta dawo hankalinta, sai kuma ta langaɓe kai cikin shagwaɓa. “Uncle You ni gaba ɗaya ma kaina ya kulle ne, dan ban san inda zan samo wanda zamuyi hakan ba”.
“To mizai hana ki yarda da batun Tajuddeen kawai, yaron nan yanada hankali da nutsuwa ga ilimi. Yana aikinsa sannan yana matuƙar sonki”.
“Uncle wlhy ni bana son sa, na tabbatar kuma bazan taɓa son shi ba. ALLAH idan aka matsamin kan na auresa zan iya halakash....”
“No! no! Kar na sake jin haka. Tunda har baki sonshi shike nan kawai abar maganarsa. Mu koma kan maganar mu kawai ta nemo wanda zai zame mana makamin kuɓuta da ga Baba.”
“Uncle bazan ɓoye maka ba wlhy na tsani duk wani abinda zai haɗa mu'mulata da wani namiji bayan ku, balle ma ace mu kasance wai ma'aurata. Impossible hakan ya kasance dan bazan taɓa aure ba.”
Har cikin rai kalmar (Bazan taɓa aure ba) ta daki Uncle Yousuf, dan a karo na farko zuciyarsa ta fara hasaso masa wani al'amari mai girma dangane da Mawaddat ɗin. Dolene akwai abinda ya kamata su sani da ke ɓoye a ƙasan zuciyarta, sanin kuma na nufin haƙurin bin matakan daya dace. Wannan tunanin ya sashi cigaba da faɗin, “Mizai hana muyi amfani da Aliyu, dan yaron nada nutsuwar da bazai taɓa iya bamu ciwon kai ba koda anan gaba”.
“Aliyu kuma? Waye shi?”.
*_“DRIVERN KI”_*
Fitar kalmar da ga bakinsa da zaburowar zuciyarta tamkar ragabzane a tsakanin jirgi da jirgi a sararin samaniya. Badan Uncle You bane, da bayan zaburar da tai abinda zai biyo baya shine lailayo masa zagi mai kawuna bakwai ta dire masa shi a tsaye sannan ta tisa da wanke fuskarsa da marin da sai ya hango yanda yaƙin duniya na uku zai kasance tun kafin lokacin faruwarsa. Sai dai kash furucin ya fito da ga bakin da ko harara bazata iya binsa da ita ba balle ɗaukar mataki. Uncle Yousuf da ya zuba mata idanu, sai dai a ƙasan ransa dariya ce ke cinsa yana dannewa da ƙyar yay mata nuni da kujera, tare da faɗin, “Sit mana kika wani zabura kamar wadda na faɗama mummunar magana. Nifa ba nace dole bane, shawarace kawai dan neman mafita. Amma idan batai miki ba muje kawai dan lokaci ma ya cika gashi ana jirana a office. Kije ki zama cikin shiri da yin sabon tunani akan wani tunda naga baki aminta da zancen shi Aliyu ba”.
Bakin data tura gaba ta buɗe zatai magana sallamar Daddy ta dakatar da ita. Alamar zip Uncle Yousuf yay mata wai kar Daddy yaji. Daddy da gaba ɗaya ya gama jin tattaunawar tasu dan tun ɗazun a laɓe yake dama sai ya sake fuskewa cikin pretending ya ce, “Wai mi ake tattaunawa ne kuka shige haka shiru?”.
Cikin ɗan ɗage kafaɗa Uncle Yousuf ya bashi amsa da “Sirri ne tsakanin baba da ƴarsa yaya”.
Dariya Daddy yayi, sai kuma ya juya hanyar fita yana faɗin, “Oh to bari nayi nan tunda ba'a buƙatar naji”.
A karan farko Lulu tai dariya tana mai kamo hannun Daddyn nata cike da shagwaɓa. A haka suka fito suna ƴar dariya.....
Fitowarsu tayi dai-dai da shigowarsa gidan. Kamar ko yaushe sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsar jikinsa. Ƴar ramar da yay ta ciwo ta sashi zama wani fayau da shi a idon mai kallo. Cikin girmama juna ya gaisa da su baba maigadi sannan ya ƙaraso inda suke tsaye. Anan ɗin ma da girmamawa ya gaisa da Daddy da Uncle Yousuf. Lulu da ke gefensu tana danna waya tai jiran jin ya gaisheta amma sai taji shiru. Karo na farko ta ɗago idanunta ta kallesa tana mai sake tsuke fuska. Ƙoƙarin barin ma wajen yake alamar ita bazai gaisheta ba kenan. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne da takaici ya shaƙure mata wuya har taji tama kasa yin magana, sai dai yanda take binsa da wani mugun kallo ya sa Daddy farga da ita. Ya kuma fahimci miya fusatata ɗin.
“Aliyu!”.
Yay kiran sunan Smart da ke ƙoƙarin komawa inda su baba maigadi suke. Cikin girmamawa ya amsa yana mai juyowa garesu. Uncle Yousuf da ya sha jinjin jikinsa da tunanin ɓaranɓaramar da Yayan nasa ke shirin yine yay saurin faɗin “Am yaya inaga muje na ajiyekan tunda malam Zaidun bai dawo ba, in yaso daga can sai ya sameka Office ɗin. Aliyu zuwa 1:30 ku samemu a Nasarawa G.R.A please karku makara”.
“In sha ALLAH Alhaji”.
Smart ya faɗa cikin gyaɗa kai abubuwa da yawa na masa kai kawo a rai musamman da Uncle Yousuf ɗin ya ambaci Nasarawa G.R.A. Huci ya ɗan furzar kaɗan, a yanzun ma dai bai kalla inda taken ba ya nufi motar da mai wanki keta faman gogewa alamar ita zasu shiga. Baya ya buɗe mata, batare da ya jira tazo ta shiga ba ya koma mazaunin driver ya shiga yana karanto addu'ar shiga abin hawa. Harta ƙudiri aniyar ƙin shiga, sai kuma mita tuna oho mata ta tako cike da yauƙin nan nata da yanga ta shiga. Mai wanki ya maida motar ya rufe yana jera mata addu'ar dawowa lafiya. Motar yaja suka fice, zuciyarsa cike taf da abubuwan da suka faru jiya a waya tsakaninsa da Uncle Yousuf....
A daren jiya bayan ajiye motar Mawaddat da ya kai sakatariyarta Zainab gida shima gida ya koma abinsa. Kai tsaye wajen Abba ya nufa suka gaisa, sun ɗan taɓa hira da Abban sai dai hirar batai masa daɗi ba sosai kasancewar da ga maganar Hawwah ta juye maganar aurensa. Sosai Abba ya dinga zuba masa faɗa akan infa har bai nemo matar aure ba a cikin watannan tofa shi zai nemo masa da kansa duk da ba aƙidarsa bace yima ƴaƴansa auren dole. Haƙuri shi dai yayta bashi da tabbatar masa cewa in sha ALLAHU zai kawo matar auren nan kusa. Kamar Abba ya gamsu da hakan sai kuma shigowar Umma ta sake saka Abban hayewa sama. Dan kamar wadda dama take a laɓe tana saurarensu tana shigowa sai kawai ta shiga assasa wutar kan cewar shi dai baiyi niyyar yin auren bane kawai. Inba haka ba baga yarinyar maƙwaftansu ba nan Nazifa yarinyar na matuƙar sonshi amma yaƙi saurarenta. Kallonta yay da mamaki, dan kowa dai yasan wacece Nazifa a anguwar. Yarinya ce mara jin magana dan tsabar bleaching fuskarta har yellow takeyi. Tabbas Nazifa ta jima tana nuna masa soyayya, sai dai shi bai taɓa nuna yasan mi takeyi ba. Kai shi ko magana tai masa ma da ga gaisuwa bai sake kulata. Wannan halin watsar da ita ɗin da yake yi yasa tun tana juriyar bibiyarsa har tai fushi ta daina kulashi. Amma da har abubuwa take saye ta aikoma Ammah ko ta bama su Asma'u. Nan ɗin ma dai bata samu nasarar ba dan Ammah tace ita babu ruwanta, idan yaga zai aureta bazata hana ba, za kuma ta bisu da addu'a dan koba komai yayi jihadin raba Nazifa da rayuwar banza da kowa ya shaida tanayi. Yanajin Ammah ta bada goyon baya ya samu Nazifa yay mata gargaɗi na ƙarshen ƙarni ya kuma yima Yayanta magana akan ta fita sabgarsa, shi kuma Yayan yaji haushi ya gaggaya masa magana bai kulashi ba shi dai dan ya yanke magana. Da ga ranar bai san miya faru ba bai sake ganin Nazifa ba. Amma shine dan tsabar sharri Umma ke tisa zancen a yanzu bayan shekara kusan uku kenan da ajiyesa gefe. Tuni Abba ya ƙara tujaresa da faɗa amma baice komai ba akan Nazifa, hasalima ya fahimci kamar faɗan nasa na son zama zargi ne ko minene bai dai fahimta ba. Jiki a sanyaye ya baro wajen Abba, ɗakinsa ya nufa dan bai buƙatar zuwama Amma a wannan yanayin. Ya gama cire kayansa kenan zai shiga wanka kira ya shigo masa. Yayi mamakin ganin Uncle Yousuf, sai da ya kalli agogo ƙarfe kusan sha ɗaya da rabi fa. Haka dai ya daure ya ɗaga cikin taraddadi.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣7️⃣
........“Alhaji badai wata matsala bace ba ko?”. Ya faɗa maimakon sallama da Uncle Yousuf ɗin yay masa. Murmushi da ga can Uncle Yousuf ya saki tare da gyara zamansa a kujerar falon da ya fito. “Babu komai sai alkairi Aliyu. Wata magana ce mai muhimmanci tasa na kiraka. Ina dai fatan baka kwanta ba na tasheka ko?”.
“Ina dai shirin kwanciyar ne Alhaji. Amma dai lafiya?”.
“Eh lafiya kamar yanda na sanar makan”.
“To Alhamdullahi Alhaji, ina saurarenka”.
Ɗan jimmm Uncle Yousuf yay kafin ya furzar da huci kaɗan. “Aliyu shawara nake nema a wajen ka”. Cike da mamaki ya amsa da, “Alhaji shawara? Sannan kuma ma a wajena?”.
“Eh Aliyu. Kuma ina fatan zaka bani wadda zata fiddani da ga ruɗanin da nake ciki” bai jira cewarsaba ba ya cigaba da faɗin. “Kasan na faɗa maka an taɓa sakama Mawaddat rana da Tajuddeen ai. Amma ALLAH baiyi auren nasu ba wasu matsaloli suka gitta, mafi yawansu da ga Mawaddat ne sai dai kuma akwai ɓoyayyen sirrin saɓani a tsakanin Yaya da mahaifin Tajuddeen da shima ya taka rawar gani. So an share maganar aure kowa ya haƙura, sai dai kakanta na ɓangaren mahaifiyarta Alhaji Sufi Ado Garko ya ɗauki alwashin duk randa wani yazo domin neman aurenta koda yardarta ko babu zai amince masa ya aurar da ita. Wauta ya sata amincewa. Bayan nan magana bata ƙara tashi ba sai a yau ɗin nan a gaban Alhaji Sufi ɗin, shi Alhaji Sulaiman ya sake kawo maganar, amma Yaya yayi saurin cewar ai Mawaddat nada wanda take so.........” Tsaf ya kwashe komai ya sanar masa har zancen su Hon. HD Nakowa da Daddy ya sanar masa suma sunje bayan barowarsu. Hakan ya matuƙar bashi mamaki dan tuna abinda ya faru a tsakanin Mawaddat ɗin da su Hon. HD Nakowa. Cikin kasa daure abinda ke bakinsa ya ce, “To amma Alhaji naga kamar ita da shi Honorable ɗin sam basa shan inuwa ɗaya. Taya zaije yace yana sonta da aure?”.
“Muma shine abinda ya ɗaure mana kai Aliyu. Shiyyasa muka kasa zaune muka kasa tsaye akan al'amurin, dan Hon. Nakowa nada ƙarfi sosai a wajen Baba, saboda yaronsa ne, hasalima shine ya zame masa kamar wani ƙashin baya a harkar siyasa.”
“To amma Alhaji mizai hana ku sasanta shi Alhaji Babba da mahaifin shi Tajuddeen ku aura musu juna kawai a wuce wajen”.
“Hakan bazai yiwuba Aliyu. Dan ita Mawaddat sam bata son Tajuddeen, ta tabbatar min idan aka aura mata shi komai zai iya faruwa. Sannan abinda ke tsakanin yaya da mahaifin Tajuddeen abune babba bawai yanda kake zaton zai sasantu cikin sauƙi bane. Kaga ko maganin ayi zumunci ya wargatse ai Gara kar a fara ko”.
“Hakane kuma Alhaji”.
“To Miye mafita Aliyu? Dan Baba fa sam baya magana biyu. In har gobe idan ALLAH ya kaimu Mawaddat bataje da wanda take son aura ba babu fashi cikin biyu dole ayi ɗaya. Shiyyasa ma na kiraka domin neman taimako. Ina son idan ban shiga huruminka ba dan ALLAH Mawaddat ta nunaka a matsayin kai ne zaɓinta, da zaran Baba ya yarda a wajen shikenan. Ni kuma zanyi ƙoƙarin ganin ta fidda miji kafin Baba ya sake magana”.
“Ni kuma Alhaji?!!”.
“Eh dan ALLAH Aliyu ka taimakemu. A yanda rayuwar Mawaddat take yanzu muna buƙatar nutsuwa kafin sama mata mijin da zai saita mata rayuwa. Ni kaina bazan so ta auri Tajuddeen ba duk da nasan mutumin kirki ne amma bazai iya control ɗin ta yanda yake so ko ya kamata ba. Sannan Hon. HD Nakowa, kai ne shedar a inda ka gansu tare, maimakon gyaruwar Mawaddat aurenta da shi sai dai ya ƙarasa lalata ta kawai, shi kuma Baba duk bai san waɗan nan halayyar ba. Amma kaga idan muka kuɓutar da ita a wannan gaɓar sannu a hankali sai irin mijin da muke fata ya samu, kai kawai ta nunakan a gobe shine kawai dan Baba ya aminta ya bar waɗan can ɗin. Amma na baka damar kayi tunani, sai dai bamu da isashen lokaci daren yau ne kawai......
“Wai kai malam ba magana nake da kai ba! Tsabar baka san muhimmancin rayuwa ba kana driving kana ma mutane tunaninka na iska!!”.
Firgigit ya dawo hayyacinsa tamkar wanda aka tada a barci. Sam bai san tunanin nasa har yayi zurfi irin haka ba. Gefen titi ya gangara a hankali tare da kai hannunsa saman goshi ya dafe yana mai furzar da iska. Gaba ɗaya ma ba hanyar da ya kamata yabi da su yabi ɗin ba tsabar hankalinsa bama a tuƙin yake ba gaba ɗaya. Karan farko a rayuwarsa da tunda ya fara aiki matsayin driver ɗinta ya furta mata “Am sorry”. Cikin tausasa harshe kuma. Cak numfashin Lulu ya nema tsayawa a ƙirjinta. Haka ma maganar bakinta kasa ƙarasa fita tai tsabar kalmar ban haƙurin tazo mata a matuƙar bazatar da bata taɓa tunanin hakan da ga bakinsa ba kasancewar kallon da take masa mai shegen girman kai. Har ya sake tada motar da juyawa bata iya sake yin ko tari ba kamar wadda aka ɗinke ma lips. A nashi ɓangaren bai kawo komai game da shirun nata ba, a tunaninsa maganar Uncle Yousuf ce ta jiya ke