Showing 3001 words to 6000 words out of 163036 words
∆••••••∆ ★ ∆•••••∆
Tafkeken gida daya amsa sunansa gida a anguwar Nasarawa GRA drivern taxi ɗin yay horn kamar yanda ta umarcesa. Leƙowa maigadin yayi, ganin ba motar gidan bace ya wani yamutse fuska zai farama mai taxi ɗin wulaƙanci idonsa ya sauka a kanta. Wani irin rawa jikinsa ya fara da gudu ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Ko gama parking mai taxi ɗin baiyi da ƙyau ba ta ɓalle murfin motar ta fice cikin takun nan nata da ke motsa duk wata hallitar jikinta kamar tarwaɗa. Abinda zai baka mamaki ko rawa ƙafarta batayi a dalilin matsiyacin takalmin ƙafarta mai shegen tsini. Duk wani ma'aikaci dake gidan da ga kallo ɗaya baya sake mata na biyu zakaga ya nutsu cikin tashin hankalin ganinta. Dan halin masifarta da iya taka kowa a duk lokacin da taso buɗaɗɗen abune ga duk wani ma'aikaci na gidan. Duk tsufarka duk ƙanƙantarka zata iya gogeka tas idan ka kuskure mata koda a ƙanƙanin abu ne, tsiranka gareta kawai kada ka shiga shirginta, idan kuma ta saka ka abu yi ƙoƙarin mata a yanda ta buƙata babu kuskure. A duk lokacin da tai tafiya daɗi kowa keji a gidan, idan kuma ta dawo zakaga hankalin kowa a tashe. Satin ta biyu kenan da tafiya Abuja wajen ƙanin mahaifiyarta domin yin hutun aiki data samu acan, har addu'a suke ALLAH yasa karta dawo da wuri, sai dai kuma da alama addu'ar tasu bata amsu ba😂 dan gata ta dawo ɗin a bazata.
Shigowarta a fusace katafaren falon gidan ya saka duk wanda ke ciki ɗagowa ya zuba mata idanu. A tsakkiyar falon ta tsaya tana harare-harare da cika da batsewa kamar wata kububuwa.
“To aunty masifatu, lafiya kika shigo kina kumbura da ga dawowa kuma?”. Ɗaya da ga cikin wanda ke a falon ya faɗa cikin taɓe baki. Kamar mai jira a taɓata a fusace ta ce, “Shi ɗan uban waye a ƙasar nan da aka aikashi ɗakkoni? Miyake taƙama da shi?...”
Kusan a tare suka shiga kallon-kallo, sai dai kafin wani ya bata amsa Dattijo mutumin dake a kujerar zaman mutum ɗaya da jarida a hannu ya miƙa mata hannu, “Kinga zo ki zauna naji miya faru Baby na?”.
“Daddy babu maganar zama a fara faɗa min uban waye shi?, dan sai na wulaƙanta rayuwarsa a gidan nan wlhy, sai yayi dana sanin shigowa gidan nan yin aiki, idan kuma bazaku faɗamin ba ALLAH duk wani ma'aikaci da ke a gidan nan yau sai ya bar gidan...”.
Sun san zata iya aikatawa, kaɗan daga aikinta kuma babu abinda Daddy ɗin nasu zaiyi saboda makahon son da yake mata a gidan. Ƴar budurwar da zata iya kai shekaru goma sha bakwai ce ta bata amsa da “Aunty Lu! Uncle Yousuf ne ya kawo shi, sabon driver ne ko sati biyu ma bai yiba fa, dan bayan wucewarki Abuja da kwana biyu ya kawo shi. Ni kaina baimin ba saboda naga yana da girman kan tsiya, ƙyawun fuskar tasa ne inaga ke ruɗarsa bayan baida ko sisi matsiyaci Mtsowww!!.....” Ta ƙarasa maganar a hankali cikin ƴar sassarfar harshe saboda hararar da dattijuwar matar dake gefen Dattijon nan ta watso mata. Wanda yay maganar farko ne a shigiwarta ya ce, “Wai miya miki ne? Bai je ya ɗakkokin ba?”.
“Bamunje ba ta masa ihu. Shiko yay tahowarsa. Kuma na faɗa mata Uncle Smart baya san ihu amma tayi” yaron nan da suke tare ya shigo yanzu ya basu amsa yana tuttura baki shi a dole yaji haushin abinda tayi. Duka ta kaima yaron ya ruga da gudu, cikin zafin rai da masifarta tace, “An masa ihun waye shi. Daddy wlhy yau idan banci uban guy ɗin nan ba babu zaman lafiya a gidan nan!”.
Cikin sauri dattijon ya miƙe yana girgiza kansa, cike da damuwa ya iso gareta. Hannunta ya kama murya a tausashe yace “Kinga Baby yi haƙuri zauna kisha ruwa ki huta. Ni da kaina ma zan ɗauki matakin dan bazan taɓa zama da wanda zai saɓa miki ba a gidan nan ko wanene shi. Har mi akai akayi wani driver banza can da zai ɓata miki rai irin haka. Haba dai cool down my heartbeat ɗin Daddynta yanzu zan nema Yousef ɗin ma ya dakatar da shi”.
Yanzu kam babu musu ta yarda ta zauna ɗin, sauran yaran duk sai suka shiga taɓe baki. Hakama mamansu tsaki ta ɗan ja a hankali tama miƙe tabar falon. Shiko Daddy ko'a jikinsa ya shiga lallashinta da kalaman ban haƙuri masu sanyaya zuciya gareta tamkar itace uban shine ƴar. Ruwa ma da aka saka mai aiki kawowa da kansa ya tsiyaya a kofi ya bata a baki. Kaɗan tasha ta kauda kai tana faman huci. Sake matsota yay jikinsa ya kwantar mata da kai a kafaɗarsa yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa kamar wadda ta fito daga tarnaƙin yaƙin duniya, sai kuma zuwa can ta ɗan ɗago. “Daddy kar ka kira Uncle Yousuf ɗin ban san a sallemsa yanzu, sai na rama abinda yay min. Aikin sati biyu zai min ALLAH sai na wajiga rayuwarsa sannan na masa korar da kare ma sai ya fisa daraja”.
“Babyna in dai hakan zai sa ki huce ina tare da ke”.
“Thanks you sweet Papa..”
Ta faɗa tana ɗan rungumesa da sumbatar hannunsa sannan ta miƙe, yatsu biyu ta ɗaya masa alamar bye ta nufi ɗakinta dake acan gefe part guda kamar wata mai aure, sai dai duk a cikin sashen iyayen ne. Murmushi yake da binta da kallo har ta ɓacema ganinsa. Bata zauna a ƙayatacen falonta da ya gama tsaruwa ba ta nufi bedroom kai tsaye. Ɗaki ne haɗaɗɗen gaske kuma ƙato. Dan bayan ƙaton gado da wardrobe kusan rabin bango da mirror akwai set na kujeru da aka shirya tsaf tamkar falo anan ma, sosai ɗakin ya haɗu tare da amsa sunansa ɗaki kamar na macen aure. Cikin yamutse fuska take bin dattijuwar dake ta saka turaren wuta a burners kusan kashi uku da harara, sai kuma cikin faɗa da masifarta ta daka mata tsawa. “Da uwar mi kike a ɗakin da baki gama min ba har na shigo....?”
“A gafarce ni Aunty (Duk da zata iya haifarta ta kafama duk wani ma'aikaci dake gidan dokar kiranta aunty komai tsufarsa). Bayi na tsaya wankewa da ƙyau har jikin bangon da kikace”.
Kakkauran tsaki ta ƙara ja da ƙarasa shiga ɗakin, saman gadon da aka lailaye da bedsheet mai shegen ƙyau fari tas ta jefa wayarta, itama ta faɗa ta kwanta tana mai wargaza fillos ɗin da aka gama wahalar tsara mata yanda take so, har ta lumshe idanu ta buɗe, a gadarance ta ce, “Kimun farfesun kifi mai yaji da kunun tsamiya, biyar nayi ki haɗamin ruwan wanka. Idan kikai min kalar haukan wancan ranar wlhy bazaki gane kanki ba a hannuna fitar min anan banza ƙazamiya sai wani tsamin zufa kike”........✍️
*_Humm nama rasa abin cewa nikam😶😒._*
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇
+22799643131
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣
........Idanun dattijuwar cike da ƙwalla ta amsa mata da girmamawa. A haife ta haifeta, bama ita ba har wadda ta fita, amma sam bata ɗaga ƙafa wajen cimata zarafi. Wai a hakan ma itafa da sauƙi, dan a kaf masu aikin gidan ita kawai ta yarda ta shigo mata ɗaki ta gyara kota dafa mata abinda zata ci, hatta key ɗin ɗakin ita kaɗai ta bamawa amma ko momynsu bata da shi. Rigarta ta kama ta shinshina, babu abinda take sai ƙamshi amma ta ce mata tana warin zufa. “ALLAH ya shiryeki ƴarnan” ta faɗa cikin tausasawa tana ɗauke ƴar ƙwallar da suka cika mata ido. Dan duk da wulaƙancin da Lulu ke mata tana ƙyautata mata, zata iya cewa duk abinda ta samu na cigaba a aikin nan nata sanadin Lulu ne, ba ita kawai ba hatta ƴaƴanta dake ƙauye da ƴan jikokinta suna ci da ga alkairin Lulu, barta dai da shegen rashin mutunci, da2 in har zakai lissafin masifaffun mutane a rayuwa to indai Lulu batazo ta farko ba tazo ana biyu. Bata da kirki sam, kuma bata ragama uban kowa sai Daddy da Uncle Yousuf, wani lokacin ma Uncle Yousuf ɗin ne ya ɗan fi cin nasararta, dan shi har faɗa yakan ɗan mata da nuna mata kuskure idan tayi, amma Daddy shi komai tayi ma dai-dai yake koda kuwa ba dai-dai ɗin bane ba....
Wannan kenan
∆•••••∆ ★ ∆•••••∆
Da ga airport babban kamfanin Jiƙamshi's ya nufa ransa a ɓace. Kai tsaye ofishin Uncle Yousuf yay ma tsinke, sai dai yayi rashin sa'ar samunsa da ga bakin sakatariyarsa. Bayajin zai iya ƙara minti biyar a wajen, dan haka ya ajiye key ɗin motar tare da amsar takarda a wajen sakatariyar yay ɗan rubutu ya haɗa da key ɗin. A takaice yace, “Ki bashi idan ya dawo”. Da ga haka ya juya yay ficewarsa. Da kallo ta bisa tana tsarkake sunan ALLAH. Ga dai namiji har namiji sai dai aljihu babu ko sisi. A hankali taja ajiyar zuciya da ɗan taɓe baki...
Shiko da bai san ma tanai ba tuni ya fice, a ƙofar Companyn ya samu napep. Tsaki ya dinga ja a ƙasan maƙoshi har yanzu zuciyarsa na masa ƙuna da kaikawon abinda ballagazar yarinyar can ta masa. Har abada shi *_Aliyu Haydar Mika'il Idris Mawashi_* baiga talaucin da zai sakashi zama ana ƙasƙantar da rayuwarsa irin haka ba. Zai iya jure kowace irin wahala da ƙarfin ƙwanjinsa amma ba ƙasƙanci ba. Shi ba kowa bane, amma har gaban abadan bazai iya zama a ƙarƙashin takalmin kowa ba. Da'ace wannan yarinyar namiji ce yau wlhy sai ya kakkarya mata ƙasusuwa ya zubar da ita a airport ɗin nan. Amma ta godema ALLAH data kasance ƴa mace.....
“Ɗan uwa wane layi muka nufa?”. Mai napep ya faɗa ganin har sun shigo cikin anguwar ta fage. Sauka kawai yay daga napep ɗin maimakon amsa, ya zaro ɗari biyu a cikin aljihunsa ya miƙa masa. Bai jira mai napep ɗin da ke faɗa masa baida canjin hamsin da zai bashi ba yay gaba abinsa..
*_Aliyu M Idris Mawashi_* kenan da akafi sani da _Smart Mawashi_ yara da matasa na ƙasa da shi kan kirasa Uncle Smart. Abokansa kance Mawashi ko Smart guy, dan sune suka saka masa sunan dama saboda mutum ne mai matuƙar nutsuwa da kuma himma akan komai ga kaifin basira. Ɗa na bakwai a gurin Malam Mika'il Idris Mawashi. Shekararsa talatin da huɗu a duniya. Yayi karatunsa na addini dana zamani har zuwa matakin masters. Bayan nan ma yayi wasu couses har biyu. Sai dai har yanzu aiki ya gagara garesa. Uncle Smart mutum ne mai matuƙar nutsuwa, sannan babban hubby nasa a duniya shine ƙwallon ƙafa. Ya iyata matuƙa dan tun yana a secondary yasha ciwoma makarantar su wassani, bayan kammala sakandire ɗinne ya samu nasarar shiga Kano pillars. Ya buga wasu manyan wassani da suka fara fiddo darajarsa da sunansa wa duniya, sai dai abin mamaki sai komai ya tsaya masa cak, ya zamto in har ya shiga fili domin buga ƙwallo sai ya yanke jiki ya faɗi sai an kamosa an maida gida kamar wanda ya mutu. Da yawan mutane sun fassara al'amarin da asiri, sai dai shi yaƙi ɗaukar hakan da muhimmanci. Daga baya ma sai ya tattara ƙwallon ya ajiye ya koma makaranta bisa shawarar mahaifiyarsa. Duk da haka yakan ɗan gwada yin ƙwallon amma dai ana nan jiya iyau, daya shiga fili sai dai a maidashi gida a sandare. A haka dai ya kammala karatunsa har yay bautar ƙasa ma, ya fara neman aiki amma yaƙi samuwa duk da takardunsa sunyi ƙyau matuƙa, abinda zai baka mamaki ma wani wajen har sai an ɗaukesa daga baya sai suce ba haka ba. Shi mutum ne da ya tsani wulaƙanci dan yanada saurin fushi. Sannan mutum ne da baya ɗaukar raini ga uban kowa duk tsananin wahala. Ya tattara aiki da ƙwallon ƙafa ya ajiye gefe ya shiga ƙoƙarin sana'a, sai dai anan ɗin ma dai komai yaƙi zama. Gashi daya fara sai ALLAH ya sanya masa albarka amma abin mamaki sai komai ya tushe cikin ƙanƙanin lokaci al'amarin nasa dai kamar saka hannu. Yanayin rayuwar gidansu da ake ta kowa nasa ke son ya zama gwani ya sashi bai daina ƙoƙarin kamo can idan nan taƙi ba, a hakanne har takaisa ga samun aikin nan na driver a dalilin wani yayan abokinsa, badan yana so ba ya yarda zaiyi, sai dan tausayama mahaifinsu akan wahala da yay da su game da karatunsu amma a yanzu ƴan uwansa babu mai taimaka masa daga su sai matansu da iyayensu mata. Dan matan Malam Mika'il Idris Mawashi huɗu ne cif, hakama ƴaƴa su talatin da biyu ne maza da mata. A yanzu haka wasunsu sunyi aure a mazan da matan, akwai kuma samari da ƴammata da suka rage musu har ma da Zawrawa biyu.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09018600202
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
Ƴan Niger kuma ga naku. Kuyi magana ta wannan number ɗin👇
+22799643131
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣
_Free pages end_
.........Gidane irin ginin da amma kuma babbane sosai, sannan kuma ko'ina mulmule yake da suminti. BQ ɗin yaran gidan maza itace a farkon shiga, sai daga can ciki iyayensu mata, baya can ƙarshe sashen mahaifinsu Malam Mika'il Idris Mawashi. Sam baya buƙatar shiga cikin gidan balle ya tada hankalin mahaifiyarsa, dan haka ya shige nasu sashen na samari. Da ga can ciki ɗakinsa yake, kasancewarsa tuzurun da duk ya girma sauran ƙanensa da basuyi aure ba yasa shi kadai ke rayuwa a ɗakinsa. Dan a yanzu haka akwaima ƙanan nasa da sunyi auren wasu ma matansu har sun haihu, shiko bama ya kula ƴar kowa balle a saka ran zaiyi. Mahaifinsa yayi faɗan har ya gaji, hakama mahaifiyarsa har ƙwallar ɓacin rai take akan zaman nasa haka babu aure, babu aiki, babu wata ƙwaƙwƙwarar sana'a. Shi ba wani iskanci yake ba, ba shaye-shaye ba, ba ɗaukar magana ba. Amma sun rasa mi yake taɗe rayuwarsa haka. Duk inda ɗa nutsatstse mai nagarta yake Aliyu Hydar yakai har ma ya zarta, gashi mutum mai tausayin iyayensa da son tallafar rayuwarsu. Ga tarin ilimin addini dana zamani ALLAH ya bashi, ga addini. Barshi dai da shegen taurin kai ga saurin fusatar tsiya da shiru-shiru, dan ko'a cikin abokai idan ba yaso ba baya fira.
Ɗakine ɗan babba mai ɗauke da kafet maroon color mai laushi, sai ƙatuwar katifa irin wadda ba'a sakawa a gadon nan. Wadrobe mai biyu sai kanta a gefenta cike da litattafan addini dama na bokon, an ɗan yi teburin karatu da kujerarsa. Ɗakin babu wani tarkace sannan fes yake ga ƙamshi kamar ba ɗakin namiji ba. Uniform ɗin da aka sharɗanta masa sakawa matsayin driver ya cire, a kujerar 2sitter dake ɗakin ƙwara ɗaya ya jefasu ya haye katifarsa da ga shi sai boxer da singlet yay kwanciyarsa yana furzar da tagwayen huci masu zafi da ɗaci, dan abinda yarinyar tai masa sam yaƙi barin ransa. Sai kuma shigar jikinta da tafi komai ƙona masa zuciya. Haka yake shi ya tsani mace haka. Kai koda atamfa ko lass yaga mace tama ɗinkin fidda surar jikinta baƙin ciki yake ji balle wannan da gaba ɗaya ta canja suffarta daga hausawan ta koma kamar wata jinin kafirai. Tsaki yaja mai ƙarfin gaske ya juya kwanciyarsa yana mai ingije tunanin a ransa. Sai dai duk yanda yaso hakan bai yiwu ba. Al'amurin ma yaƙi barinsa yin barcin da yake buƙatar yin ko zai samu sassaucin baƙin cikin dake sukar zuciyarsa.. Da ƙyar ya samu barcin ya ɗaukesa, baima yi na minti talatin ba akai kiran sallar la'asar. tashi yay da ƙyar yana faman yamutse fuska dan a barcin ma harda mafarkinta. siririn tsaki yaja ya miƙe ya shiga toilet ɗin ɗakin nasa, a gurguje yay wanka da alwala ya fito jin har za'a shiga salla. jallabiya kawai ya saka da turare ya fita kasancewar masallacin a kusan ƙofar gidansu yake, dan baifi gida huɗu ba ne tsakaninsu....
Ana idar da salla gidan ya dawo, sai dai maimakon ɗakinsa yanzu ciki ya shiga ɓangaren iyayensu. Gida ne da tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar na zaman mace huɗu ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a ƙalla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform na islamiyya wasu nacin abinci wasu kuma na ɗan kai kawon aiki. Tsit kake ji duk wani ihu da hayaniyar da gidan ya ɗauka ya tsagaita, yaran suka shiga gaidashi. Sau ɗaya ya amsa musu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa kai tsaye. Sun san ba wasa yake da su ba dan haka babu wanda ya damu da yanayin nashi, sai dai sauri-sauri da suka shiga yi na son kowa ya kammala abinda yake ya fice islamiyya kafin ya fito ya sake ganinsu..
Daga ɓangarensa kam da mamaki mahaifiyarsa ke kallonsa daga inda take zaune. A hankali ya kai zaune a ƙasan carpet ɗin da aka saka a gaba ɗaya falon kalar blue. Basu