Showing 36001 words to 39000 words out of 163036 words
★★★ ∆∆ ★★★
Da asuba Uncle Yousuf da kansa ya shiga ɗakin aunty Saliha da ya kai Lulu dan ita a ɗakinsa ta kwana ya tadata yin salla. Sam bata da nauyin barci, damma yau akwai na maye tare da ita, da alama kuma ya bugar da ita da yawa, dan ma tana da jini mai ƙarfi, da ace tana da saurin buguwa ma abubuwan da MM Atik Kumo ya harmutsa mata zata iya ƙara shanye yinin yau bata san inda kanta yake ba. Amma sai gashi Alhamdullah ita da sauƙi ya saketa. Zata fara masa gardama ya daka mata tsawa. A firgice ta tashi zaune zumbur jin Muryar Uncle Yousuf tana mazurai. Sosai take zazzaro idanun mamaki, shiko ya watsa mata harara da faɗin, “Karna dawo Massalaci na tadda baki tashi kinyi salla ba, zan matuƙar ɓata miki rai”. Kai kawai ta gyaɗa masa mamaki fal ranta akan ganinta nan ɗin. Sai kuma abinda ya faru a daren jiya ya shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya. Cikin wani irin takaici da jin ƙuna a rai ta dafe kanta tana jan tsaki. A fili ta furta, “Sai nayi maganinka wlhy, illiterate kawai ko wa yace ya kawoni nan? To wai ubanwa ma ya nuna masa can ɗin da har ya bini?” Anya mutumin nan baida iskoki bisa kai ko? To inba mai iskoki ba itako mizata kirashi? A jiya dai tasan ya tashi a aiki ai da wuri ma. Amma kuma sai gashi ta gansa a inda babu wani mahaluki da yasan zataje. Kai wannan lamari da mamaki, dole ne tasan yanda ma akai ya bita can, kuma sai ta koya masa hankali akan shiga abinda bai shafesa ba. Nadiya ma sai ta shuka mata rashin mutuncin da bazata taɓa mantawa da shi ba da ga ita har su Hon. Baita ɗin. Jin ana neman idar da salla ya sata sauka a gadon dan tasan Uncle Yousuf babu wasa ne, ba ruwansa rufe ido zaiyi yaci mata uwa babu ruwansa da shirin da sukeyi. Wanka ta farayi sannan ta ɗauro towel Dan tana so ta sake wattsakewa. Batako zaman jiran tsanewar jikinta ba ta zura abayar Aunty Saliha. Sallar tai babu wani nutsuwar a cikinta, tana zaune a inda ta idar tana kulla mai fishseta Uncle Yousuf ya leƙo, gaidashi tayi, sama-sama ya amsa mata duk da yaga yanda ta koma kalar tausayi. Ba yanzu ya shirya mata magana ba dan haka yay ficewarsa. Ji Lulu tai gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi, sam bata ƙaunar fushin Uncle You a rayuwarta, har gara ma Daddy yay fushi da ita dan shi tasan abu ɗaya zata masa ya rikice ya dawo lallaɓata. Kuka take so tayi, sai dai ita mai juriya ce da shegen taurin kai, ba a komai take iya kuka ba komai ƙololuwar ɓacin rai ko tashin hankali da zata tsinta kanta a ciki. A karan farko taji kunyar haɗuwa da mutanen gidan, tashi tai jikinta duk babu ƙarfi, bata ko nemi jakarta da takalminta ba ta fice cikin sanɗa, taji daɗin rashin samun kowa kuwa, da sauri tabi ta ƙofar kitchen ta baya. Tunda ta fito bayin fulawoyi ke mata kallon mamaki da ga nesa, dan shi dai bai san sanda tazo gidan ba kam, ƴar tsawar da tai masa ta sakashi dawowa a hayyacinsa. “Wawa mi kake kallo ne? Dilla buɗe min ƙofa!!”. Jikinsa har kakkarwa yake duk da kuwa a girme ma zai iya girmarta shima, kuma ba aikinsa bane, ta watsa masa harara lokacin da take ficewa tare da jan tsaki. Yasan laifinsa dan haka ma baiji haushi ba. Mawaddat ta tsani taga ana kallonta, gashi kuma yau shi ta kamasa dumu-dumu. Ya san dai bala'i bai ƙare ba, dan duk randa ta dawo gidan zai sha masifa. Ƙila ma harda zagin ƙare dangi za'a haɗa masa.
Da ƙafa ta isa gida, kasancewar garin da sauran duhu ga ɗan sanyi-sanyin da aka fara na lokacinsa. Acan ma sai da maigadinsu ya samu rabonsa na zagi. Dan shima dai galala yay yana mata kallon mamaki. Amma tunda ta fara danna masa na maguzawa sai ya nutsu ya koma gaisheta a daburce. Bata amsa ba tai shigewarta tana jan tsaki..........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣2️⃣
........Anan kam tasan basa barin ƙofa a buɗe, dan haka ta zagaya ta window ɗin ɗakin Iya Tabawa. Tana kuwa zaune tana addu'oi tun bayan idar da salla. Ba yau Lulu ta fara mata haka ba, shiyyasa koda ta kirata bata firgita ba. Sai ma miƙewa da tai a ɗan ɗarare. A kausashe Lulun ta ce, “Dalla Malama ki buɗen ƙofa kin wani tsaya kallo na”. Haƙuri Iya Tabawa ta bata ranta fal wasi-wasi. Zuciyarta ta fara raya mata ko dai yawon banza Lulu ke fita ne, tunda ba taɓa ganinta cikin maye tai ba. A ƙasar Hausa kam mafi yawan al'umma sukan fassara yawon dare na ɗiya mace da tazubar ne kawai, da wahala hasashensu ya wuce haka har su hango wasu abubuwa masu illa a rayuwar ƴaƴanmu mata bawai zina kawai ba. Sun manta a rashin ji duk abinda namiji yasa kansa iyawa wasu matan kan kwatantashi ba wai sai iskanci kawai ba. (Ya rabbi ka shiryar damu da zuri'armu baki ɗaya).
Tana shiga ɗakinta a saman katafaren gadonta ta zube tana mai sauke numfashi, lamo tai cikin lallausan bedsheet da duvet ɗin gadon masu ltaushin tsiya da ƙamshi. Tunanin matakin da zata ɗauka akan tsageran driver ɗinta takeyi, da su Hon. Nakowa, sai dai kuma barcin da bai gama fita idonta ba ne yaci ƙarfinta......
★Kasancewar alerm data saita ƙarfe takwas ta farka badan barcin ya isheta ba. Sai dan tana da shari'a mai zafi a yau ɗin da zata gudanar wadda a yau ɗin take fatan alƙali ya yanke hukuncinta. Cikin rashin kuzari ta tashi ta faɗa toilet, sai da ta gamsu da gyara jikin nata a fannin wanka sannan ta fito. Shiri tayi tsaf da ita cikin suit na mata kalar baby pink, rigar cikinta fara. Dan ƙyau kam tayi ƙyau, ga shegun takalmanta masu dogayen dudduge ɗin nan da tsabar ƙwarewa a sakasu yasa ko gargada batayi a tafiya da su. Yau dai anyi abun arziƙin saka ƙaramin baby hijab fari da yay mata ƙyau sosai, sai dai iyakarsa kafaɗarta dan ƙaramine. Ƙamshin nata na fitar hankali ta bulbula a jiki har ita da kanta tanajin ƙamshin na hawa mata kai, sai dai haka take buƙatarsa. Cikin takun nan nata na isa da gadara ta fito, illahirin jikin nan na motsa kansa kamar wata tarwaɗa a ruwa. Mubeen kawai da Daddy ta samu a dining suna breakfast, sai Mommy tana tsaye a tsakkiyarsu da alama abincin take haɗa musu.
“Good morning Daddy & Mommy!”. Ta faɗa kanta tsaye babu wani alamar respect gareta matsayinsu na iyayenta. Musamman ma Daddy dake amsa sunan mahaifi. Kowa dai yasan yanda ƴaƴa ke shakkar iyayensu maza fiye da mata a ƙasar hausa. Mommy dai kallonta kawai tai ta girgiza kanta. Shiko Daddy fuskarsa a washe da murmushi, duk da dai kamar alamunsa na nuna yana cikin damuwa ne yake dannewa.
“Morning sweet heart. Kin tashi lafiya? Yaya ƙarfin jiki”.
“Komai normal Daddy”. Ta faɗa tana ɗaukar shayin gabansa da yake sha ta kurɓa da ga tsayen da take. Da kallo ya bita har yanzu da murmushi a fuskarsa. “Babyna zauna mana kisha ba ƙyau shan abu da ga tsaye ai”.
“No Daddy, hakan ma it's ok for me. Ina sauri ne 9:30 inada Shari'a”.
“Allah yay miki albarka, ya kare munke ga duk wani sharrin maƙiya na gida dana waje”.
“Amin sweet Papa na”.
Sarai Mommy ta fahimci harda ita a addu'ar tasu. Hakama Mubeen. Dan tuni sun gane abinda mahaifin nasu kema Mommy akan ƴar uwarsu. Sai dai ko sunce zasu ɗauki mataki hanasu yin hakan Mommyn take yi. Babu yanda suka iya dole suke haƙura. Amma badan jajircewarta a kansu ba ba ƙaramar tsanar Lulu sukeji ba a rai. Wani lokacin ma hatta shi Daddy ɗin takaici yake basu shiyyasa su ƴan biyu sam basu son zaman gidan. Harta ɗan sha shayin na Daddy kusan sau bakwai ta ajiye Mubeen bai mata magana ba itama batai masan ba. Batama nuna tasan da zamansa a wajen ba kamar yanda shima ya nuna. Tana shirin sauka a ɗan steps ɗin hawa dining ɗin Daddy ya dakawa Mubeen ɗin tsawa.
“Kai dan uwarka ita ɗin sa'arka ce da bazaka gaishe ta ba?!”.
Kallon Daddy ɗin Mubeen keyi zuciyarsa a bushe, sai kuma yaja numfashi mai nuna zuciyarsa na yunƙurowa, sai dai kallon gargaɗi da Mommy ke masa ya hanashi cewa komai da ga tarin abubuwan faɗar da ke cikin bakinsa game da mahaifin nasu. A hankali ya furta “Daddy kayi haƙuri” kawai yaja bakinsa ya tsuke.
Tsaki daddy yaja dai-dai Lulu na ficewa a falon gaba ɗaya. Bata jira jin abinda Daddyn ke shirin faɗa ba. Karo na farko a rayuwarta taji kamar babu daɗi akan abinda Daddy ɗin kema ƴan uwanta saboda ita. Har ga ALLAH tana ƙaunar ƴan uwanta, hasalima bata haɗa son su da komai ba. Hatta su Yaya Hassan batajin daɗin rayuwar doya da manjan da ke a tsakaninsu. Dan ko gidan su ƴan biyun sukazo basa kulata bata kulasu, saboda sun riƙe abubuwan da mahaifiyarsu ta fuskanta da ga mahaifinsu dalilin mahaifiyarta da ita kanta. Goshinta da yay mata nauyi saboda abinda ta sha jiya bai gama sakinta da ƙyau ba ta ɗan shafo tana furzar da iska. Ba ƴan uwanta kaɗai ba hatta Mommy tana jin ƙaunarta, dan kallon uwa take mata a zahiri da baɗinin rayuwa. Ta sani duk wanda yasan gidansu ma ya sani Mommy bata taɓa cutar da rayuwarta ba koda da harara, idan dai tayi laifi yanda take ma yaranta faɗa itama haka take mata. Shiyyasa duk rashin mutuncinta har abada bazata taɓa kwatantashi ga Mommy ɗin ba. Musamman ma idan ta tuna nasihar da Kakanta Alh. Sufi Garko kanyi mata a duk sanda taje garesa game da Mommy ɗin da halaccinta ga zamantakewarta da mahaifiyarta. Duk da dai itafa har yanzu bata taba jin labarin ainahin zaman da Mamanta tayi da Mommy ɗin ba...... Gaisuwar da ma'aikatan gidan ke mata ce ta katse mata tunani, batare data kalli ko guda a cikinsu ba take wucewarta kawai da takun nan nata na yauƙi da isa. Tana gab da isa motar da take buƙatar hawa idanunta suka sauka akan Smart da ke zaune wajen maigadi kamar kullum hankalinsa a waya yana buga game ɗin ball da yake matuƙar bege. Sake tamke fuska tai da ɗauke kanta, abinda ya faru jiya ne ya shiga mata kaikawo cikin kai. Sosai taji ɓacin rai ya sake baibayeta da takaicin su Nadiya da suke son jamata rainin nan wajen wannan shashashan, ta jima tana shaye-shaye, amma duk wanda yay mata sani na haƙiƙa bai san wannan halayyar tata ba, a koda yaushe cikin ƙoƙarin binne sirrinta take, amma sai gashi a haɗuwarta da mutumin da tafi tsana fiye da kowa a duniya shi ya ganta a yanayin. Ƙwafa tai da balla masa harara, cikin borin kunya ta cilla masa key da sake jan tsaki. Idanunsa da ke nuna alamun barci bai ishesa ba ya ɗan lumshe ya sake buɗewa, batare da ya kalleta ba ya miƙe zuwa gaban Motar data ɗakkoma key ya buɗe mata bayan, sai da ta shiga ya maida ya rufe sannan ya koma mazaunin driver, motace mai tsadar gaske da ɗaukar hankali, kasancewarta ƴar gatan gidan hatta Daddy tafi yawan motoci. Dan motarta biyar kuma duk ƙosassu, sai ƙarama ɗaya da sha'awa kawai ya sata matsawa Uncle ɗinta Khamil ɗan uwan mahaifiyarta dake Abuja saya mata ita. Dai-dai suna barin kan titin layin nasu ya miƙa mata handbag ɗinta ta jiya da key ɗin mota, a hankali ta ɗago da ga duba takardun da takeyi ta ɗan sake hararsa sannan ta kalla kayan a yamutse. Murya a dake sai dai acan ƙasan maƙoshi ta furta, “Waya gayyaceka inda nake jiya?”.
Sarai ya jita, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita ya haura kan babban titin bayan motar da ya dakatama ta shige layin da ya fito. “Malam da kai nake yi”. Ta sake faɗa cikin zafin rai da borin kunya. Karan farko ya ɗan ɗago idanu ta cikin mirror ya dubeta. Ido suka haɗa, tai saurin kauda nata zuziyarta na tsirgawa. Itafa komi za'ai ayi amma kar ya kalleta da wannan shegun idanun na macizai (kamar yanda ta raɗa musu😂🥱). Yanda tai ɗin sai ya so bashi dariya, amma sai baiyi ba ya ɗan saki murmushin gefen baki da maida hankalinsa ga titi cikin salon lumshe idanun nasa kamar yasan suke razanata, babu alamar zai bata amsar da take buƙatar son ji. Ba ƙaramin takaicinsa bane ya kume Lulu, ga wayarta ta isheta da ruri. Nadiya ce keta faman kiranta tun ɗazun, sai dai taƙi ɗagawa dan tai alƙawarin sai ta koyama ƙawar tata mafi kusanci hankali. Tsaki taja a karo na babu adadi, ta fisgi wayar da ke kan rigarta ta lauyoyi ta kashe tare da sake cillar da ita kan rigar da ke a gefenta. Haushin Nadiyar dana sharetan da yay ta tattaro gaba ɗaya ta nufesa da shi.
“Wai kai mika ɗauki kanka ne da har ina maka magana kana wani cika da batsewa?”.
Yanda tai maganar muryarta har tana zuga kamar wadda kuka ke son yunƙuromawa sai dai ƙarfin halinta na dannesa ya sashi sake dubanta a karo na biyu ta cikin mirrorn. Sake maida kansa yay ga titin sai kuma ya ɗan muskuta zamansa da furzar da iska. Ƙasa-ƙasa na rashin kuzarin da kasala irin na wanda barcin bai ishesa ba cikin deep voice ɗin nan ta shi ya ce, “Mi kike son sani?”.
Wata irin kasala muryar tasa ta nema saukar mata saboda yanda yay maganar cikin sanyi da tausasa lafazi, sai dai cikin yaƙi da kai da nuna juriya irin ta masifaffun mutane ta watsa masa kallon banza da yin ƙwafa tana maida kanta ga takardun da take dubawar. Kamar bazata ce komai ba sai kuma bayan kusan minti ɗaya ta ce.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣3️⃣
.........“Waya aike ka inda ka sameni jiya? Miye ma dalilinka na bina?”.
Idanu ya lumshe tare da buɗewa a lokaci guda. Kamar yanda yay magana ɗazun a tausashe yanzu ma haka yayi. “Baki so asan kina aikata abinda na gano ɗin ne?”.
“Kai ɗin banza da zanji ina son ɓoye maka abu. Shiga abinda ban saka ka bane ya sa nake neman ba'asi dan bana son shiga sharo. Idan kuma kace zaka cigaba da shiga min hanci wlhy zan saka ka dana sani kai da duk wanda ma yake maka kallon arziki. Tsabar kai ɗan haɗin masifa ne ka ɗauke ni ka kai gidan Uncle you.., wlhy kasan mima zaka faɗa masa, in ba haka ba sai naje har gidanku kaima na maka ƙullin da har gaban abada baka isa ka kwancesa ba ɗan sa ido kawai. Idan kuma kaji ƙarya mu zuba ni da kai mai shishshigin tsiya, kai a dole sai ka shiga jikin iyayena dan maular tsiya irin ta talaka”.
(Maula! Talaka!) Zuciyarsa ta maimaita cikin jin ƙunar kalmomin. Kamar zai yi magana sai kuma ya haɗiye abinsa dan ya fahimci al'amarinta na buƙatar sai da uzuri, idan yace zai biye mata sai ma su zama ɗaya. Yanda bata sake magana ba tana ta faman duba takardun nata shima bai sake kallon inda take ba, sai dai ƙamshin turaren data bulbula ya addabesa har yana hawar masa kai kamar yanda itama nashi ke cizon can ƙasan zuciyarta. A cikin tsare-tsaren da Uncle Yousuf ya bashi nata ya sashi sanin inda zasu je a yanzu ɗin, dan haka kai tsaye babbar kotun da muke kira da (kotun ALLAH ya isa) dake a jiha ya nufa. Tamkar ba safiya ba harabar court ɗin cike da mutane, hancin motar na kunna kai cikin gate ɗin wasu gungun ƴan jarida suka yomusu caa, isowar securitys da ke son hana ƴan jaridar isowa garesu ya ɗan maido hankalin mutane kan motar suma. Kafin ya gama kashe motar har an buɗe mata. Fuska a yamutse da ɗan jan tsoki ta kalla harabar court ɗin. Wanda ya buɗe matan ta miƙama tarkacen hanunta tare da rigarsu ta lauyoyi. Ita kuma ta ɗauki handbag ɗinta bayan ta toshe fuska da wani shegen gilashi mai tsananin ƙyau ta haɗa da hular, dai-dai tana ficewa ta balla masa harara da faɗin, “Saura nan ma kace zaka biyoni kaga yanda zan baka mamaki”.
Da kallo kawai ya bita, sai kuma ya ɗan furzar da iska ransa fal mamakin yanda bata gajiya da masifa. Da ga can ƙasan ransa kuma yanda ake ta bata wani girma da kariya da ga security ɗin da zallon da ƴan jarida ke faman yi na son isowa gareta ya ƙara ɗaure masa kai da jin takaicin da sun san wacece a zahirinta da ko kallon mutuntawa bata cancanta a garesu ba. Bai iya ɗauke idanunsa