Showing 96001 words to 99000 words out of 163036 words
shiga rai. Bayan Company sun kammala aune-aunensu su Aunty Saliha suka dawo gida suka barsu suyi aikinsu. Dan gidajen biyu sun fara cika da ƴan uwa na jiƙamshi da abokan arziki musamman na tsohuwan anguwar da su ka rayu tun suna ƙanana kasancewar mutanen da da zuminci ga shi kuma Aunty Saliha ma ƴar canne. Anan gidan su Smart ma dai an dawo da labari mai daɗi na tarbar da suka samu da karramawa. Yayinda Umma keta faman haɗiyar zuciya, data samu abokin gulma kuwa tace “Anya yarin nan ba asiri yay ma mutanen ba kuwa? To wannan haba rawa har ina. Ga mutane a jiƙe cikin kogin dukiya amma sunama waɗan nan ɗan abinda muka kai haba rawa haka”. Wasu idan tace musu hakan sukan kulata, wasu ko su gwaleta. Wannan kai lefe ya sake yayata sanin ƴar wa Smart ya aura a anguwar, dan dannan fa masu hassada da masu taya murna aka kafa teburan kace nace kowa na faɗar albarkacin bakinsa. Oho shi baima san sunai ba. Yana can yana nashi ƙoƙarin na ganin walimar da suma suka shirya anan gidan a gobe idan ALLAH ya kai mu juma'a ta tafi dai-dai. Ga kuma can gidan da Company ke saka kaya dole suka raba hankalinsu biyu shi da Ahmad da wasu tsirarun abokansa da basa fushi da shi duk yanda yake sharesu a baya. Harda Sa'ad mijin Hawwah.
Zuwa washe gari suma fa nan gidan ya cika da dangi, musamman ma dangin Ammah kai harma dana Abban da kuma nasu aunty Amarya, ga ƴaƴan gidan duka dai duk sun hallara ƙwai da kwarkwata. Duk da wasunsu aikinsu tsogumi ne da kushe kamar yanda iyayensu keyi. Bayan an sakko massalacin juma'a aka fara walima da aka gayyato manyan malamai da zasu kwarara wa'azi. Abin mamaki sai ga gayyara Alhaji Sufi Ado Garko a wajen da na Uncle Yousuf da wasu a cikin mata ƴan biki. daddy dai baizo ba, Mommy ma saboda baƙi doke ta haƙura, sai Aunty Saliha ce ta jagoranci matan da akazo da su sai yazam kamar an raba Mommy nacan ita tana nan. Sosai suma gidan su Smart ɗin suka maida alkairi da alkairi, dan sun musu tarba ta mutuntawa duk da ba'asan da zuwansu ba. Amarya dai banda ita, tana can ana mata ƙunshi bayan Uncle Yousuf ya mata filla-filla da masifa yau dan da taƙi yarda ayi, tun yana lallashinta yaga taƙi saurarensa sai ma sake tuburewa take akan itafa babu inda zataje ya sashi yau buɗe mata wuta irin wanda bata taɓa gani daga garesa ba, dan har rantsuwar marinta yay idan bata shiga hankalinta ba. Ga wayoyinta dama ya ƙwace kusan kwana uku kenan. Dole dai ta haƙura ana can ana yarara mata wani lalle na nunama sa'a da tsara. Sosai walima tai matuƙar ƙayatarwa. Ango yasha ƙyau cikin dakakkiyar shadda sai kaiƙo take. Tana ɗaya daga cikin ɗinkunan da Abba yay masa har kala biyar domin fitar biki, sai kuma ga Ahmad da nasa kayan mamakin a safiyar yau da ƙaton akwati guda da ɗinkakkun kaya masu ƙyau har kala ashirin shima matsayin tasa gudummawar. Har ƙwalla Smart yayi a ɓoye na godiya ga UBANGIJI da ya rufa asirinsa. Dan baiyi zato ko tsammanin haka ba shikam. Walima ta matuƙar ƙayatarwa ga armashi data ƙara dalilin zuwan dattijon ƙwarai Alhaji Sufi Ado Garko da tawagarsa ta ƴan siyasa har da gwamna da yazo daga baya shi. Aifa sai gashi ƴan jarida sunyi caa anata ɗaukar rahotanni, labaran daran juma'ar nan sai gashi ya zo harda wannan taron walima darajar zuwan su Gwamna wajen. Ranar fa anguwar fagge kamar zata fashe (Kar wani ɗan fagge naji yayi magana😏🥱😂). Duk da babu inda abincin da aka tanada yajema mutane kasancewar abin ya zarce yanda aka tsarashi mutane basu damu ba. Ko'a tv kaga kanka ai ka more🤣 (Su Smart an auri ƴar gidan madara an samu promotion 😜). Tarofa yayi taro fiye da zato, dan da ƙyar aka tashi bayan sallar magrib. Dauriya kawai ango yake da ambaton addu'oi a cikin ransa dan gabansa haka kawai yake ta faɗuwa. Ga ciwon kai ƙasa-ƙasa dake nuƙurƙusarsa. Haka dai yayta dauriya bawan ALLAH dan manyan mutanen nan sai da Uncle Ameen ya kama hannunsa ya kaisa gaban kowanne suka gaisa. Da yawansu sun yaba da nutsuwar yaron, har wasun su najin sha'awar yin koyi da wannan al'amarin aure da a yanzu al'ummar mu suka daina. Da wahala kaga ɗan masu kuɗi ma ya aure mace ƴar talaka balle wannan ace namiji ne ɗan talaka ya auri ƴar masu kuɗi, kuɗin ma irin na gidan Alhaji Sufi Ado Garko da Alhaji Isma'il Ibrahim Jiƙamshi. Lallai wannan abun ayi koyine gaskiya dan sun kafa tarihi matuƙa. Washe gari asabar biki ya koma gidan su Amarya Mawaddatan'warahmah Isma'il Ibrahim Jiƙamshi. ALLAH sarki Uncle Yousuf, yau dai kam duk sai jikinsa kuma yay sanyi, dan haka tun da safe yasa aka kira masa Mawaddat ya lallasheta sosai da mata nasihar ta nutsu dan ALLAH ayi komai yanda wani bazai fahimci akwai wata a ƙasa ba. Ayi a gama cikin farin ciki. Yanda taga yanata lallaɓata da nuna damuwarsa sosai, ga dangin mahaifiyarta tako ina kowa na tattalinta da janta a jiki musamman auntyn ta matar Uncle Khamil Aunty Naja'atu ta Abuja da tasu tazo ɗaya daman. Ga ƴan uwanta su Amrah nane da ita, su twins kansu yau har murmushi sukai mata da tsokanarta da amarya suna faɗa mata har sun fara kewarta duk sai ta karaya harda kukanta. Gefe kuma rashin samun kayan shaye-shayen ta na samunta, ya kumayi matuƙar tasirin sake sanyaya mata yanayi yau ba masifa ba ko maganar kirki ma bata iyayi. Ga mafarkin mamarta da tayi a daren jiya shima ya tsaya mata a rai. Duk sai komai ya haɗu ya tankwarata a yanda su Uncle Yousuf basuyi zato ba. Mai kwalliya ta musamman aunty Naja'atu tazo mata tun daga Abuja, kuma daga Lagos ma aka ɗakkota. Ga Mommy ta mata akwati guda na kayan fitar biki masu tsadar gaske. Dai-dai da gold Mawaddat an saya mata na nunama tsara ne, karku manta itace za'a fara aurarwa a jiƙamshi family bayan auren Daddy da na Uncle Yousuf.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣4️⃣
.......Itace ɗiya ta farko da zasu aurar. Dan haka kowa burinsa nuna mata ita ɗin cikakkiyar ƴar gata ce. Hatta Hassan da Hussaini ba'a barsu a baya ba wajen nuna tasu bajintar ta saya mata ƙyauta ta musamman. Ƙyau iya ƙyau Lulu ƙamshi tayisa. Dan a yau ta fito a ƙamshinta babu ƙarya. Da safe sunyi kamu anan cikin gidan Uncle Yousuf kamar yanda ƴammatan family ɗin Garko suka shirya, kamu ne da sisters event a tare, abin ya ƙayatar sosai. Yayinda Lulu ta zama ƴar kallo kawai tana mamakin kanta matuƙa wai a matsayin matar Aliyu driver ɗinta fa, wannan illiterate ɗin nan velleger da take faɗi kullum. (Ki kwantar da hankalinki auren wata ɗaya ne fa kacal, yanzu ma anci sati ɗaya a ciki, duk wannan taron da kike gani nuna komai ba komai ba ayishi shine mafitar da wani bazai zargi komai ba balle Baba ya ce zai aura miki ɗaya da ga cikin su Hon. Haruna) waɗan nan kalaman na Uncle Yousuf ne ke ƙara mata ƙwarin gwiwa da nutsuwar shanye komai ta na bin kowa da ɗan murmushin yaƙe. Sai yanda ƴan uwanta keta haba-haba da ita musamman yayunta maza biyu da sai zuwa suke ɗaukar hoto da ita na ƙara sakata jin daɗi. Mubeen da su Afrah kam ai sune ma kamar ƙawayen nata. Ko'ina suna nane da ita, duk sherin da akema Mubeen na kasancewarsa namiji bai bar wajen ba. (Wannan duk yana cikin shirin Uncle Yousuf daya tattarasu bayan ya tsigesu da masifa ya koma lallashi da nasiha tare da tsara musu yanda zasu kasance da ita a wajen taron bikin dan su taimakawa nutsuwarta komai ya tafi dai-dai. Sun kuma yi ɗin suma har a cikin ransu suna jin daɗin hakan kuma). Bayan tashi da ga kamu & sisters event aka ɗunguma da amarya zuwa gidan Daddy inda Mommy da Aunty Saliha zasuyi yinin biki. Gida ya cika tanƙam d jama'a, kowa burinsa yaga amarya data sake shiga ta musamman acikin wani ubansun shadda da taci aiki mai ƙayatarwa. A take ƴan uwa da abokan arziƙi suka zagayeta ana kwarara mata addu'a, sai ga Lulu da hawaye dan gaba ɗaya jitai komai ya sake kwance mata. Balle ma da Daddy ya rungumeta shima yana hawayen. Hotuna dai an shasu kala da iri har babu adadi. A sannan ne kuma tawagar dangin ango su Aunty Bilkisu da basu sami zuwa Kamu & sisters event ba suka isa gidan. Karan farko da sukaga amaryarsu, itama ta gansu. Duk da ba ƴan ɗakinsu kawai bane a kallo ɗaya Lulu ta gano tsananin kammanin Smart a fuskar Hawwah da Aunty Bilkisu. Yanda kuma suka nuna kulawarsu gareta da yanda Hawwah keta faman kiranta da auntynsu duk da tasan ta girme mata ya sata jin wani irin kimarsu da kwarjini. Suko sun ruɗe matuƙa dajin daɗin ganin yanda Yayan nasu ya samo tsuƙeƙiyar mata ƴar gata kuma ƴar ƙwalisa. Da zasu wuce tasa su Amrah ƙara musu gift da aka raba duk da an basu. Hakan da tayi sai ya ƙara mata kima a idon su Aunty Bilkisu suka tafi suna mai yaba mata da murnar kasancewar ta tasu. Duk da ma kwalliyar fuskarta yasa basu gano cewar itace lawyer ɗin nan dake matuƙar burge Ammah ɗinsu ba. Koda suka isa gida camma dai yau cike yake, dan ma sai gobe in ALLAH ya kaimu Ammah ke yinin bikinta, amma hakan bai hanasu kutsawa su kai mata abinda aka basu a gidan su Lulu ba da yabama tarbar da akai musu da karramawar da amaryar ta sake musu. Hakan bai ishi Hawwah ba sai da ta kira Smart da ke tare da su Ahmad acan stadium ana shirin buga gagarumin ƙwallon da coach ya shirya ta kwankwasa masa labari. Ta kumace ya buɗe data ta tura masa hotunan amaryarsa. Shi da farko baima yarda wai Lulun ce tai musu abinda ta faɗa ɗin ba, dan shi dai yasan wacece ya aura basai an bashi labari ba. Dan haka koda ya yanke kiran ma bai buɗe data ɗin ba ya cigaba da harkokin gabansa. Shi dai Coach ya hanashi shiga wasan, dan haka yana cikin ƴan kallo kawai. Stadium ɗin tayi matuƙar cika maiban mamaki, can dai kamar wanda aka tsikara ya ciro wayarsa da ga aljihu ya buɗe data bayan ya shiga WhatsApp nashi. Akan idonsa hotunan suka buɗe zuciyarsa sai motsi take a ƙirjinsa, sai yayi kamar zai fasa sai kuma dai ya daure har suka kammala buɗewar dan sunada yawa. Hoton farko dai babu ita a ciki, na biyu ma haka. Na uku ita kaɗaice zaune ta kare fuskarta da waya alamar bata son hoton, yawu ya haɗiye a hankali dan duk da fuskarta bai fito ba tayi ƙyau. Ƙara matsawa yay na gaba ananne da sai da tsigar jikin yan maza ta tashi, ya ɗan lumshe idanu ya sake buɗewa yana mai furzar da huci kaɗan. Anan kam raɗam ta fito daga sama har ƙasa aka ɗauketa kuma, ta ɗan juya Luluu eyes ɗinta gefe kaɗan tana kallon gefenta. Ɗan bakin masifar nan da yaci lipstick pitch da maroon kaɗan yay wani irin masifar fidda shape ɗin sa. Haka ma zagayayyar fuskarta mai ɗauke da hanci da yay dai-dai da ita ga manyan idanu masha ALLAH. Yau ne karo na farko da ya ga kwalliya a fuskarta. Sake furzar da iska yay kaɗan gaba ɗaya ma ya rasa yazai fassara yanayin da ya shiga. Sai kawai ya zaɓi kife wayar ya ajiye yana mai harɗe hannayensa a ƙirji ya kwantar da bayansa zuwa kansa luf a kujerar da yake zaune ya ɗan lumshe idanunsa sai dai bai rufesu duka ba yana kallon tarin abokan kwallonsa da sukazo da ga gari-gari domin tayashi murnar aure ƙasa-ƙasa.
Suma wasan nasu yayi ƙyau, sai da akai kiran magrib suka tashi sai kuma an haɗu a wajen dinner, dan Coach shi yay ƙoƙarin bama baƙinsu masauki duk da wasu ma sai yau suka iso dai shine kuma mai gayyatar da Ahmad. “Wai ya naga duk jikinka yay wani laƙwasa ne? Ko ciwon kanne bai saukaba still?”.
Cewar Ahmad cikin damuwa. A hankali ya ɗan furzar da iska tare da shafo goshin nasa ya ce, “Ai ciwon kan nan inaga kozai barni sai an gama hayaniyar nan. Harma na saba da shi a kwana biyun nan”.
Sannu Ahmad ɗin yay masa cikin damuwa. A haka suka ƙarasa gidansu Ahmad ɗin dan acan zasu yi shirin tafiya dinner ɗin, kafin su wuce su ɗauki amarya a gidansu.....
*_DINNER HALL_*
Ƙaton waje ne na gaske Alhaji Sufi Ado Garko ya kama domin ya gayyaci manyan abokan kasuwancin sa dana siyasa a ciki da bai ɗin Nigeria. Gashi kuma mafi yawansu sun san Daddy shima tun da babban yaronsa ne na amana da duk wanda yasan Alhaji Sufi Ado Garko to yasan wanene Alhaji Isma'il Ibrahim Jiƙamshi a wajensa. Iya tsaruwa wajefa ya tsaru, ga abinci iri-iri an tanada. Haka ma manyan mawaƙa na Hausa dana turanci duk sun hallaro. MC kansa mashahuri aka ɗakko domin gabatar da komai. Ta gefe ɗaya ƴammata da samarin Garko family da suka haɗe da jiƙamshi family sun haɗa babban show mai ƙayatarwa domin nishaɗantar da jama'a. Duk da girman wajen da alamu ya nuna zai ɗauki mutane masu yawa duk wanda zai shiga sai da i.v ɗin sa ne zai zama masa gate pass. Dan haka su kansu su Smart da ahalinsa suka shirya komai a tsari domin mutunta kansu a wajen. Duk da dai Alhmdllh ALLAH ya riga ya mutuntasu, tunda da har zuwa yanzu babu wata ɓaraka data shiga na raina juna a tsakani, ko Umma daketa neman hanyar baƙanta Smart wajen wani a cikin dangin matar tasa har yanzu ALLAH bai bata damar ba. Kafin takwas waje da ya cika yay hani'an da manyan mutane ƴan siyasa da ƴan kasuwa har ma da ƴan bokon da iyalansu. Kowa ka gani shar da shi, dan duk da ba'ai anko da zai zama komai da komai iri ɗaya ba sun rubuta kalar kayan da ake buƙatar ƴammata da samari duk su saka. Koma wani iri ne ka saka kala kawai ake buƙatar tazo ɗaya. Manya ne dai kowai yay yanda yake so....
Masha ALLAH na faɗa a lokacin da idanuna suka sauka akan ANGON ƙamshi Aliyu Hydar Smart mai masoya da yawa cikin wata dakakkiyar shadda mai tsananin ƙyau da maiƙo taji aiki na musamman. Itace kawai abinda ya yarda ya amsa da ga dangin amaryar tasa dan Baba ya aiko masa da ita matsayin wadda zai saka a yau ɗin, kamar yanda itama amarya ganin nata kawai tayi. Farar shadda ce da akaima wani shegen ƙawataccen aiki da kalar golden mai ɗaukar ido. Takalmar ƙafarsa haif cover suma golden da ratsin fari, haka ma hularsa golden da ratsin fari kaɗan. Sai agogonsa golden shima. Ga gyaran fuska da ya ƙara masa kwarjini da cikar kamala an masa. Sam wannan Smart ɗin ya banbanta da wancan Smart dirver da kuka sani. Ƙamshi har ba'a magana. Tun a gida Ahmad ke jera mar hotuna dan yakai a ɗaukesan. Ya kuma tubure bazai tafi ba sai yaje Ammah da Abba sun gansa. Dole sai da su Ahmad suka kaisa gidan kuwa Ammah da Abban suka gansa da tsaffin da bazasuje dinner ɗin ba. An masa hoto da iyayensa Abba ya rungumesa. Duk kauce-kaucen Ammah sanda za ɗauke su hoto itama sai ya kwanta da kansa a kafaɗarta, hakan yasa ta juyo kamar zata hararesa shi kuma yay murmushi cikin salon shagwaɓe fuska, ga Abba ya kallesu shima yana murmushi. Hoton sai ya zama na musamman........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣5️⃣
......Daga nan gidan Daddy suka ɗunguma ɗaukar amaryar ƙamshi. Lulu lu'u-lu'un Jiƙamshi family, tauraruwa abar buƙatar son ganin kowa.
“Ya arrahaman!” Ango Smart ya ambata a hankali lokacin da Hussaini ke fitowa da ga gidan riƙe da hannun Lulu. Ni kaina masu karatu sai da alƙalamina yay adungure ƙasa da ƙyar na kamosa na cigaba da muku burutun. Amarya da tayi jiƙaƙƙen ƙyau, idan nace muku ƙyau ina nufin ƙyau maƙurar ƙurewa a cikin ƙarshen ƙure. Wani irin shegen material ne golden color da aka ƙawata da adon fararen stones masu walwali da ɗaukar idanu. An masa ɗinkin gown data kama mata jiki, sai aka ɗaura wani ƙawataccen alƙyabba fara da adon golden kuma a sama, ta rufe jikinta gaba ɗaya tana ɗan jan ƙasa kaɗan. Ɗauri iya ɗauri, ga shi kwalliyar da akai mata ƴar dai-dai misali da bata ɓatar da ainahinta ba a yanzu. Kayan yari komai yaji, ƙamshi kam ba'a magana wayyoni ALLAH kai jama'a. Yaufa Lulu ƙamshi a ƙamshin take ɗan gaske. Takalman ƙafarta su kansu abin kallo ne, suma farare ne da kwalliyar golden sai pos ɗin ta itama farace da kwalliyar golden stones. Kamar shock ne ya jasu a lokacin da Hussain ya kamo hannun Smart ya saka masa na Lulu. A tare suka zabura zasu janye amma tsabar muguntar