Showing 90001 words to 93000 words out of 163036 words

Chapter 31 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

461

Wata shashashar dariyar rainin wayo Smart ya saki cikin katsesa ya ce, “Da ace alƙalamin ƙaddarata a hannunka ya ke da tun kafin yau na kasance a ƙarƙashin inuwar tsoron cika bakinka. Sai dai kash kai baka isa ko dakatar da kaɗawar daƙiƙa ba na cikin ƙaddarata. Aliyu M. Idris Mawashi UBANGIJINSA kaɗai yake tsoro ba ɗan adam irinsa mai kashi da barci ba. Amma zan baka shawara idan ka shirya ka koma ka canja shiri, idan kuma baka fara ba ka ƙaro matakan shirin naka dan da kura kawai ake wasa a cikin kasuwa ZAKI sai kallo da ga nesa dan ko shafar jikinsa sai da dabara. Kamar yanda na faɗa maka nafi ƙarfinka kuma ni ba'amun barazana. Dan haka shawara ɗaya da zan baka ka goge tarihin alaƙar data taɓa alaƙantani da kai a baya, ka ɗauki sabuwar alaƙar zamantowarka suruki na sai mu amfana da tagomashi mutunta juna. Idan kuma ka ce a'a lallai zan cigaba da gara rayuwarka a tsakkiyar harabar gidan Alhaji Sufi Ado Garko fiye da yanda yara ke gara katantawar wasa a saman suminti. A yanzu bana buƙatar cewarka anan kaje kayi nazari. Na Barka lafiya sai nazo gasheka tare da AMARYAR ƘAMSHI bye Kawu”. Ya yanke wayar ƙittt. Kansa ya dafe yana wani irin furzar da huci a jajjere na ɓacin rai. Hannunsa ya kai saman goshinsa yana murzawa. Shi kam wace irin masifa ce wannan kuma ya shiga. Da ga wannan sai wancan. Sake furzar da iskar yay saboda abinda zuciyarsa ta ayyana masa cewar (Jarabawa ce).

       Haukacewa Alhaji Sulaiman ya nema yi jin Smart ya yanke masa waya bayan ya gama yaɓa masa maganganu masu zafi. Cikin wani irin bahagon ɓacin rai ya shiga ƙoƙarin sake kiransa amma ana nuna masa busy alamar yayi blocking ɗinsa ma kenan. Dai-dai nan kiran Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen ya shigo masa a ɗayar waya. Ɗagawa yay da sauri yana mai kaiwa kunnensa. Sai dai jin kukan data fashe da shi ya sashi zabura har da bugewa “Ke lafiya kuwa zaki ɗagamin hankali haka da kuka?”.
      Cikin kuka ta ce Alhaji babu lafiya. Tajuddeen ya farka gashi nan yana aman jini, shike nan zamu rasas......” ai kusan da gudu ma ya fito da ga sashen nasa har yana neman faɗuwa. Ba ƙaramar tsorata maigadi yayi ba. Hakama drivern sa da yaronsa Malami. Da ƙyar ya iya sanar musu “Muje asibiti” ya buɗe gaban motar ta shiga batare da ya jira an buɗe masa ba. Dole suma suka shiga da hanzarinsu....

      Tofa Tajuddeen yaya dai? Karfa ciwon son Lulun mu ya kasheka😔🚶.

        ___________________★★

   A ɓangaren su Umma da aminiyarta masu tafiya garin Zuru da ƙyar ta samu Abba ya barta bayan ta lafta masa ƙaryar zuwa garin su duba Innarta, acewarta ƙanwarta tai kiranta da dare ta sanar mata jikin Innarsu ya motsa. Bai kawo komai a ransa ba tunda yasan Innar tasu dama jiyya take kusan shekara huɗu kenan. Ya jajanta mata da bata izninin tafiya dan haka ana sallame sallar asuba taima ƴan gidan sallama ta wuce. Duk da asubancin tafiyar da sukai basu iso garin Zuru ba sai bayan sallar azhar. Burinsu su kammala komai su koma garinsu Umma ɗin a yau su kwana. Sun koyi sa'ar samun Malam Na-zuru a gidan kamar ma su yay zaman jira kasancewar tun kan su taso sunyi kiransa sun sanar masa. Bayan gaisuwa da tambayar juna bayan rabuwa ya dubi Hajiya Naqiba dan ita kam bata rabo da zuwa inda yake har ma ta saba dan ta riga ta gama kama mijinta a hannu a sake take kamar akuyar fulani. Umma kam Abba bai kasance a ƙarƙashin ikon nata ba ɗari bisa ɗari shiyyasa zuwan ke mata wahala kai tsaye sai idan gagarumin abu ne ya faru.
      “Hajjaju yau Aminiyar ki ta tuna damu kenan ko? Idan ban manta ba rabonta da nan kusan shekara uku kenan fa”. Cikin ƴar dariya Hajiya Naqiba ta ce, “Gaskiya za'ayi kam malam. Kasan ita akuyar ɗaure ce ganinta sai anyi sake ko tsautsayi ya gifta ta kufce”. Ta ƙare maganar tana kallon Umma. Dariya sukayi gaba ɗaya. Kafin Malam Na-zuru ya tsagaita da maida hankalinsa ga Umma yace, “Hajiya Yaha mike tafe da ke?”.
       “Abubuwane da yawa kashi-kashi malam. Sai dai mafi girma a cikinsu aikin yaron nan ne mai shegen taurin kai ya ke neman buɗe min wlhy....”
     “Tofa badai yaro mai tamaula ba ko?”.
    “Wlhy shi kuwa malam. Dan jiya-jiya aka ɗaura masa aure da ƴar wani hamshaƙin attajiri”.
          “Aure kuma? Ya akai haka ta faru Hajiya? Kina ina akai wannan babbar ta'asa bayan kin san da ƙyar muka samu yaron nan ya shiga hannun mu? Wannan kuma yana a cikin babban abinda muka ƙullesa da shi fa”.
      “Wlhy malam nima ban san yaya akai hakan ta faru ba. Sai dai na lura tsabar munafunci ne na ubansu ya sa aka rufe mana komai sai ɗaurin aure kawai mukaji bayan an riga an ɗauro. Malam ka taimakeni dan ALLAH. Kai kanka ka sanar min yaron nan yanada taurari masu ƙarfin gaske da zasu iya disashe kaf ƴaƴan gidan nan ya zam babu hasken wanda ake gani sai shi, bayan kai malamai kusan huɗu sun sanar min hakan wasu ma sun kasa aiki a kansa sai kai ne da kayi akaci nasara. Gashi kuwa na fara gani dan aure fa akai masa, kuma da ƴar Alhaji Isma'il Jiƙamshi, wannan abu ya hanani samun barci sam a daren jiya”.
          “Tirƙashi! Dolene ki kasa barci. Dan aurensa na ɗaya da ga cikin abinda muka ƙulle masa har sai ya tsufa a haka ta yanda babu mai ɗaukar ƴa ya bashi. Ba ƙaramin duka a ciki mijin nan yay mana ba gaskiya. Dan yaron nan yanada ƙarfin nacin ibada shiyyasa muka jima muna aiki yana tafiya a iska, na ƙarshen nan ma da ƙyar kina gani muka samu ya haushi da taimakon anfani da gashin mahaifansa da nashi.....”
      “Na sani Malam, dan ALLAH ka taimakeni wannan aure ya watse kafin ma cikar sati ɗaya na tarewar wannan yarinya. Sannan a matse minsu waje guda su rasa gabas su rasa yamma akan wajen da zai zauna da abinda zasuyi hidimar biki. A sakama duk danginta tsanarsa a zuciya hatta da jaririn yaro. A birkitamin lissafin yarinyar ta ce bata son sa”.
      “Aikin nan yana da wahala Yahanasu. Amma dai zaɓi ɗaya anan mu gwada mu gani”. Ya ƙare maganar da ajiye mata tazbaharsa gabanta. Da ƙyar ta iya tsaida nutsuwarta wajen ɗaukar ɗiyan tazbahar ɗaya ta miƙa masa. Amsa yay ya duba ya sake ajiye mata yace ta ɗauka. Sai da sukai haka sau uku sannan ya kalleta cikin jinjina kansa. “Gaskiya akwai babban aiki a gareki. Dan gaba ɗaya fa an riga an lalata aikin sai kaɗan ne bai bar jikinsa ba. Wanda kuma ya ƙulla wannan auren mutum ne mai nasibi matuƙa shima, dan komai yayisa ne da hikima kasancewar ya fahimci akwai ɓoyayyen al'amari akan rayuwar yaron......”
      “Kenan babu yanda za'ai malam? Sannan waye shi wannan matsiyacin da ke tare da shi haka ba sani ba tun da wuri?”. Umma ta faɗa kamar zatayi kuka. Malam Na-zuru yay gyaran murya yana gyara zama. “Baza'a rasa yanda za'aiba kam. Sai dai dole za'a canja taku kuma. Shi wannan mutumin da kike tambaya yanada alaƙa da yarinyar matuƙa, sannan yana ƙaunar yaron da zuciya ɗaya, mutum ne kuma mai wayo da hikima gaskiya. Samun nasara a kansa kuma shima sai munyi yaƙi na gaske. Amma ita matar da aka ɗaura masa auren da ita mu maida akalar aikin namu ta hanyarta kawai inaga hakan zai taimaka mana”.
     “To amma malam matar da ba'a bukatar ma ta tare miye amfanin kafa harsashin aiki kanta?”. Hajiya Naqiba ce yanzu tai masa tambayar dan Umma dai damuwar jin labarin waye Uncle Yousuf ya hanata magana ma. Amsa ya bata da faɗin, “Gaskiya in har kuna son cimma burinku akan yaron nan dole sai anbi ta hanyar ita wannan yarinya. Hakan na nufin kuma dole sai ta tare da shi sannan komai mu bisa a sannu.....”
          Da sauri Umma ta ce, “Malam kana nufin ma har sai ya kusanceta a shimfiɗa kenan?”.
       “A'a ba wannan nake nufi ba. Ko tarewa a gidansa tai matsayin mata to ya wadatar damu. Dan muna buƙatar kayan da aka kawota gidansa da shi a ranar, da wanda shi kuma zai shiga gareta da su. Sauran aikin ya rage namu mukuma”.
       Jimmm Umma tai alamar tunani kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya da faɗin, “Shike nan malam zanyi wannan ƙoƙarin. Sai kuma akan kishiyoyin nawa ina son a sabunta min aiki musamman uwar yaron nan. Dan na tsaneta fiye da kowa a gidan nan. Bana son koda ganinta matsiyaciyar. Yanda ta saka katanga tsakanina da masoyina har sai da ta fara zama matsayin matarsa na tsawon shekaru kafin ya kalleni bisa tirsasawar iyaye, wlhy itama sai na gunzuga mata baƙin cikin da har ta mutu bazata fita a cikinsa ba.”
         “Burinki zai cika kuwa. Mudai je zuwa mataki-mataki zaki sha mamaki”.
    Sosai farin ciki ya mamaye Umma, ta cigaba da zayyano ma Malam Na-zuru duk yanda take buƙata akan Ammah da zuri'arta. Suma sauran matan kowacce da kalar nata shirin da take so ai mata. Sai matar ɗanta Salim da itama ke neman zame mata ƙarfen ƙafa akan janye mata ra'ayin Salim ɗin. Basu dai baro garin Zuru ba sai bayan la'asar, a hakan ma ɗan basu tsaya yin koma ba. Sun jigatu kam gwargwadon iko sai kusan goma sha ɗaya na dare suka iso garin su Umma da nufin duba mahaifiyar Tata su kwana.......✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣1️⃣



.........Tunda suka baro gidan babu abinda Lulu keyi sai haɗiyar zuciya. Ko sau ɗaya bata tankama hirar da Uncle Yousuf ke mata ba, hijjab nema da ya tambayeta ina ta samo cikin takaicin da har yanzu yaƙi sakar mata maƙoshi ta amsa masa da, “Uncle You mutumin nan fa ni bazan tare ba na fasa ko zaman wata ɗayan. Shiko dai yanata danne dariyarsa har suka iso gida. Sai da yay parking ya dubeta cikin nutsuwa ya ce, “Saboda mi basai kin tare ba?”.
         “Ni dai kawai nama fasa. Dama na gaya maka mutumin nan baida mutunci, to kaga tun kafin ma na fara shuka masa nawa kalar rashin mutuncin kawai mu tsaya iya hakan”.
      “To banƙi ta taki ba, amma yaya kike tunanin duniya da Baba zasu kalla al'amarin? Dan Baba fa zai iya ɗaukar zafin da bamu taɓa zato ko tsammani ba. Ni dai da zakiji shawarata anan ki cigaba da kwantar da hankalinki ayi komai a yanda aka tsarashi. Shima kuma mu bisa a sannu a rabu lafiya batare da kowa yaji ko ya gani ba. Dama jira nake ya sake samun lafiya yazo muyi magana ma ta fahimta ok”.
     Sosai yanda Uncle ɗin nata ke mata magana cikin kulawa da sanyi ya sata jin bazata iya bijire masa ba. Dan haka ta jinjina kanta tana sauke tagwayen ajiyar zuciya ta ce, “Shike nan Papa. Amma dan ALLAH ka masa magana ya kama kansa”.
          “Zan masa kar ki damu”.
    Ya bata amsa cike da kulawa. Wata ajiyar zuciyar ta sake saki sannan suka fita. Da ƙyar Uncle Yousuf ya iya danne dariyarsa shi dai yana binta da kallo, tausayi take bashi, ba kuma ya ganin kowa da laifi sama da Daddy, ya raunana rayuwar yarinyar matuƙa da sunan soyayya, ya kasa fahimtar tarbiyyar uwa ga ƴaƴa daban take da komai a wannan rayuwar musamman ma ɗiya mace, amma sam Mawaddat bata samu ba, shiyyasa abubuwa masu muhimmanci ma duk bata sani ba kuma bata ganesu da yaren fahimta.....
        Koda ta shiga gidan ma aunty Saliha dake yanke ma Ra'is farce a falo sakin baki tai kawai tana kallonta. Ai ko sai ta sake tunzura fuuu aka shige ɗaki. Dai-dai nan Uncle Yousuf ya shigo shima. Da hannu ta nuna masa bayan Lulu. “Miya kunna ƴar taka? Ga shi naga an dawo da hijjab?”.
       Ƙaramar dariya ya saki yana kaiwa zaune. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Aikin surukinki ne”.
    “Woow dan ALLAH fa?”.
“Sosai”.
Ya faɗa cikin gyaɗa kai da lumshe ido abin dariya. Sai kuma ya nuna mata Ra'is da ido. Murmushinta ne ya ƙara faɗaɗa. Sai dai bata sake cewa komai ba....

       ★★......

   A matuƙar tashin hankali Alh. Sulaiman ya isa asibiti. Sai yay dai-dai da isar su Hon. Nakowa da sukaje duba Tajuddeen. Shi baima lura da su ba. Sai dai ganin yanda ya fita a mota a rikice yay cikin asibitin ya sa su tambayar drivern sa ba'asi. Shima ba sani yay ba. Sai dai ya tabbatar musu maybe jikin Tajuddeen ɗin ne. Jin haka suma sukai cikin asibin dan dama tafiyar sun yita a sirrance ne shiyyasa babu wani tare da su sai su ukun. Sun iske kam abubuwa sun ƙwaɓe matuƙa, Hajiya Turai da Alh. Sulaiman rungume da Tajuddeen suna kuka. Sam sunma ƙi bari likitocin suyi aikinsu. Hakan ya bama su Alh. Baita yin ruwa da tsaki akan komai. Dan take anan suka shiga ciku-cikun ganin amma fita da Tajuddeen a ƙasar ta wayoyi duk da sun san shima Alh. Sulaiman ɗin duk yana da wannan alfarmar. To da ace lafiya lafiya ne ko jirgi sukutum mahaifinsa yay niyyar nema dan akai Tajuddeen wata ƙasa neman lafiya hakan ba komai bane. Dan da gasken gaske Alhji Sufi Ado Garko ya tara dukiya irin wadda shi kansa bai san adadinta ba. Alhmdllh burinsu kam ya cika, dan zuwa yamma an kammala komai na fita da Tajuddeen, haka uwar da uban suka wuce batare da sun nema kowa a family ɗin ba. Ita kanta amaryarsa Hajiya Abasiyya sama-sama ya mata bayani lokacin da suka koma gida domin shiryawa......

       ★★★......

   Duk wani abinda ke faruwa har barinsu ƙasar Alhaji Sufi Garko ya sani sarai. Sai dai yaƙi yin ko tari akan hakan dan ransa a ɓace yake matuƙa da ɗan nasa. Babu irin haƙurin da matarsa bata bashi ba amma bai saurareta ba. Sai ma gargaɗin karta sake masa maganar Sulaiman a gidan yay mata. Tare da balbale ta da masifar cewar duk wata fitina da ke a tsakanin ƴaƴansa ai itace tushenta. Dan sakacinta ne saboda kasancewarta mace mai masifar son ƴaƴa. Badan shi tsayayyen mutum bane da kaf ƴaƴansa zasu tashi ne a lalace cikin fanɗararriyar tarbiya. Dan tabbas Hajiya Attine bata tsawatarwa yaranta tun ma da ƙuruciya. Komai yaro ke so shi yake yi, ba'a isa kuma ace yay ba daidai ba sai ta kareshi. Yanzu haka akan auren nan na Mawaddat sai da ta haura sama sosai da mijin nata. A cewarta ai itama tanada hakki akan Mawaddat tunda itace ta haifi uwarta. Ita bata yarda Lulu ta auri talaka ba kamar yanda uwarta ta auri ubanta da ga ƙarshe suka kashe mata yarinya dan suci dukiya. Shiko kasancewarsa jarumi mai tsayawa a gidansa ya ce idan ta isa taje ta warware auren mana. Sun haura sama ƙololuwa koma ace har yanzun a saman suke, dan taso fita duba Tajuddeen nan ma yace idan ta fita a bakin aurenta. Wannan kalma ta matukar girgiza mata zuciya dan bata taɓa tunanin fita da ga bakin mijin nata da suka ɗauki tsahon shekaru kusan saba'in tare ba. Ta san kuma zai aikata dan shi baya magana biyu. Dole dai ta haƙura da fitar tunda suma yaran har ma da jikoki ya tabbatarma duk wanda yaje asibiti duba Tajuddeen sai ya koya masa darasin rayuwa.....

        _______________★

  A cikin gida koda Nasreen taje da Deen a wajen Mubarak suke jin baƙin da sukazo duba Smart ne sukazo da shi. Babu wanda ya damu da sanin da ga ina, duk da dai zuciya na raya musu ko dangin matar tasa ne. Dan yaron dai da ganinsa kasan ɗan gidan madara ne. Kuɓul-ƙubul da shi. Sai dai abinda ya birgesu da yaron yanda duk da ƙanƙantar shekarunsa sai da ya gaidasu. Fuskar Ammah da murmushi ta ɗaukesa ta ɗaura saman cinya tana tambayarsa sunansa. Yako bata amsa da cewar Deen shalelen aunty Luu.. shalelen aunty Luu da ga faɗa ya sakasu darawa, abinka kuma da yaro shi ko'a jikinsa, sai ma janye ra'ayinsa da Nasreen tayi suka kama wasansu batare da ya sake tunawa su Aunty Lu zasu iya tafiya su barsa anan ba. Bayan sallar azhar Smart ya shiga cikin gidan. Sunta jera masa sannu da yaya jiki? Dan sun barsa ne dama saboda maza da keta faman shigowa ƴan nan cikin anguwa dubashi tun safe. Zaune ya kai yana amsa musu da Alhmdllh. Yaji daɗin ganin Deen nata wasanshi, sannan koda aka zuba musu abinci shi da Nasreen babu wani janjeni yaron ya zauna sukaci. Shine ya sake musu bayanin daga inda yaron ya fito, sai dai ba gaya musu harda amaryarsa akazo ba. Anan ya ɗan sake shan kunun gyaɗa kaɗan ya kwanta a doguwar kujerar Ammah yana sauraren tsare-tsaren biki da suke tayi, dan shi sai yanzu ma yake jin wai aunty Bilkisu da Hawwah ashe sun tara masa uban kaya na lefe da suketa saye a hankali da shirin dama duk randa ya tashi aure sai dai a ƙarasa abinda ba'a rasa ba. Idanu kawai ya tsirama ƴan uwan nasa yana jin matuƙar ƙaunarsu a cikin ransa. Suko sunata dariya da tsokanarsa. Shima dole yay murmushi yana haɗiye abubuwa masu dama da ke a ransa. Anan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login