Showing 105001 words to 108000 words out of 163036 words
mata tarba irin ta uba da ƴa, ya saka mata albarka sosai da yimata nasiha tare da addu'a, hakama ƴan uwansa. Daga nan ɗakin Ammah aka kaita. Itama dai kamar Abban ne, ta mata nasiha da sanya albarka a wannan aure tare da fatan alkairi. Hakama ƴan uwanta. Sai ɗakin Umma da taso yin abin kunya sai da ƴarta ta kwaɓeta, a hakan ma dai sama-sama tace ALLAH ya sanya alkairi. Hakan bai damu su Aunty Naja'atu ba, dan sun fahimci Umma sai a hankali, mace ce da bata iya ɓoye hassadarta. Sai wajen Mama. Ita dai ta matuƙar dannewa dan ƴaƴanta ita na ƙoƙarin ƙwaɓarta idan sukaga zatayi wata ƙwaɓar, ta tarbesu da yima amarya nasiha a taƙaice itama tai addu'a kuma. Sun koma ɗakin aunty Amarya itama tai fatan alƙawari sosai da addu'a. Sannan aka sake maidata ɗakin Ammah, da ga canne aka ƙarasa abinda ya rage na yima juna godiya da fatan alkairi sannan suka ɗauki Mawaddat domin maidata can gidan da zasu zauna. Baƙi na nan kuma suka ƙarasa shirinsu na tafiya dan jiya duk an kaisu sunga gidan amarya bisa tsarin Abba dan yau kar ta zama sun takura musu.
Sun iso gidan amarya lafiya, Lulu ta buɗe idanu da ƙyau tana kallon ko'ina tunda dai daga ita sai ƴan uwanta. Komai batace ba akan gidan da tsarinsa, ita babbar damuwarta a yanzu kawai ta samu kayan shaye-shayen ta ne, dan shine ya haifar mata da zama shiru-shiru da rashin ƙarfin jiki. Sarai aunty Saliha ta fahimci damuwarta, sai kuma yanzu ta sake gane hikimar Uncle Yousuf da duk ya tsara hanyar toshe mata inda zata iya samun komai da zata sha, dan a dalilin hakan gashi nan sun samu tayi laushin da kowa ke iya controlling ɗinta batare da an samu ko ƙaramar matsala ba. Suna shiga takai kwance a falo ta dunƙule jikinta waje guda ta rufe idanu. Suko suka shiga ɗan gyara abinda zasu gyara su Amrah nata santin yanda gidan ya tsaru duk da bai kasance katafare ba. Sai da suka daidaita komai yanda ya kamata, Aunty Naja'atu ta sakata yin sabon wanka wajen ƙarfe shida na yamma, kafin ta fito sauran mutanen dake gidan duk suka wuce, aka bar su Aunty Saliha kawai sai su Amrah dake ta ƙara goge inda aka ɓata da sassaka turaren wuta. Tsaye sukayi a kanta ta shirya cikin wasu ubansun yadi mai taushi da ɗaukar ido, sai yi take kamar zatayi kuka amma suna lallashinta dan sun fahimci matsalarta, sai dai kowa da yanda ya fahimta ɗin kasancewar aunty Naja'atu bata san Lulu na shaye-shaye ba, dan duk da tamafi samun damar yi idan taje wajensu a Abuja amma iya takunta yasa basu taɓa gane komai ba da ga ita har Uncle Khamil. Sai da suka tabbatar komai ya dai-daita a yanda suke buƙata sannan suka zare jikinsu suka fito a ɗakin, ita dai tana kwance a tunaninta zasuje falo ne, koda taji gidan yayi tsitt barcin dake rinjayar idanunta yasa bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da saƙa ta yanda zata samu abinda take muradi........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣9️⃣
......Smart zaune gaban su Abba da Ammah suna masa nasiha. Yayi matuƙar ƙyau cikin yadi mai taushi grey color, ga ƙamshi mai daɗi da saka nutsuwa yana yi. Nasiha mai ratsa jiki Ammah da Abba sukai masa sannan suka rufe da addu'oin samun zaman lafiya da nasarar rayuwa. Tare da tuna masa muhimmancin cigaba da tsayawa akan gaskiya da addu'a da ibada. Kar yaga ya koma bayan idanunsu ya aro halin da basu sanshi da shi ba. Ya ji tsoron ALLAH ya riƙe matarsa da zuciya ɗaya bisa koyarwar MANZON ALLAH (S.A.W) karya barta tai kuka akan abinda yanada ikon share mata hawaye. Abba ya miƙa masa wata leda mai ɗauke da magungunan musulunci yana faɗin, “Ga wannan ɗazun naje na amso maka shi, dan yawan ciwon kan nan naka yana damuna. Ka kula dan ALLAH dayin yanda duk suka rubuta a kuma cigaba da addu'a dan itace gaba da komai muma muna muku ALLAH ya kawo iyaka”.
Ya amsa da Amin tare da masu godiya zuciyarsa a raunane. Ashe haka akeji idan za'a bar gida. Ashe ba mata ne kawai ke shiga cikin yanayin damuwa ba yayinda za'a kaisu gidan aure. Ji yake kamar ya saki kuka kawai ya huta. Amma dai ya daure ya cije da ƙyar yay musu sallama ya fita inda Ahmad ke jiransa. Sai da ya koma cikin gidan yay sallama da su Umma da dama abinda take jira kenan, cikin dabara tai masa hoto batare daya sani ba, dama sanda aka kawo Lulu haka tayi. Koda ya fito inda Ahmad yake sai da suka tsaya akai sallar magrib a masallacin anguwar sannan suka wuce. Basu ƙarasa sharaɗa ba sai da Ahmad ya tsaya yay saye-saye irin na rakkiyar ango, shi dai Smart baice komai ba, hakan yasa Ahmad komawa tsokanarsa wai kodai a samo masa mayafi ya lulluɓa kamar yanda amare keyi idan za'a kaisu. Dan ya lura shima ɗin fa kukan kawai ya rage yayi. Kunnen Ahmad ya kama ya murɗa da faɗin, “Kai wai bazaka daina sa ido ba ko”.
Hannun Ahmad ya buge masa. “Mugu ciremin kunne zakai dan kai ka samu ka tsallake.” murmushi kawai Smart yay baice komai ba. Koda suka iso sai da ya fita ya buɗe gate ɗin sannan Ahmad ya shiga, shi kuma ya rufe sannan ya samesa dai-dai yana fiddo ledojin sayayyar da yayi. “Mawashi ya kamata fa gidan nan a nema maigadi gaskiya”.
Cikin taɓe baki da ƴar harara Smart ya ce, “Yayi me idan an nemosa?”.
“A'a gadi mana, kana ganin ya dace ace kaine zaka dinga buɗe gate da rufewa idan kun shigo ko Madam ɗin. Sannan shi amfanin mutum a gida ko tafiya kukayi baku da ɗar akan barin gidan babu kowa.”
Duk da ya gamsu da maganarsa ta ƙarshe sai cewa yay “Kai share wannan batun muje kazo kayi ka wuce dare nayi”.
“A'a nazo dai nayi na wuce na baka fili kawai zakace malam. Kai jama'a wai kowa da yayi aure sai idonsa ya buɗe, bara dai nazo nai mai yiwuwa, in sha ALLAHU nima bazan ƙetare shekarar nan ba”.
“Da yafi maka”.
Cewar Smart yana murmushi. Daga haka suka ƙarasa cikin gidan. Wani irin ƙamshi mai ratsa zuciya ne ya tarbesu, falo kam ya tsaru iyakar tsaruwa dan Uncle Yousuf da gaske ya zuba dukiya a gidan nan ƴar gaske. Zaune Ahmad ya kai, shima Smart sai ya zauna ɗin yana furzar da iska. Ko yaya zata kaya musu a wannan gida cikin wannan rikitaccen aure mai cike da cakwakiya da ƙalubale oho. Yau dai ga shi da ga shi sai Lulu ƙamshi ƴar balaja'un ogar nan tasa da bata raina abin masifa matsayin ma'aurata. Shi yasan akwai babbar ƙura, idan yace ƙura yana nufin ƙura irinta turniƙewar yaƙi da ko tafin hanunka ganinsa bazai yiwu maka ba...”
“Oh oh tunanin mi kuma ka tafi?”. Ahmad ya katsesa. Iska ya ɗan furzar da sakin ajiyar zuciya. Ahmad yay dariyar shaƙiyanci yana miƙewa. “Ƙalau kake kuwa?” cewar Smart da ke kallonsa. Ahmad ya ɗage kafaɗa da faɗin, “Kafin kowa sanin ƙalau nake tunda gashi na rakoka wajen amaryarka. Ni kaga nayi nan asha angwanci lafiya kar dai a karya gado da safe a kiramu neman kafinta”.
“ALLAH ya shiryeka mara mutunci”. Cewar Smart yana miƙewa shima. Yanzun ma shi ya buɗe masa gate ɗin yana faman jera masa godiya. Dan Ahmad yayi matuƙar ƙoƙari a bikin nan. Ko shine angon sai haka. Sai da ya rufe ko'ina sannan ya sauke ajiyar zuciya da bin ƙofofin ɗakin uku da kallo. Duk da biyu a cikin corridor suke ƙaramin ɗakinne a ware shi kaɗai ɗan nesa da su ma. Zuciyarsa tafi kaisa a corridor ɗin dan haka ya nufi can kai tsaye, tafiya yake tamkar wanda ke jin kasala ko gandar takun nasa, hakan yay matuƙar jagorantar steps ɗin nasa wajen kasancewa a tsare, hannunsa ya kai saman handle ɗin ƙofar, sai ya samu kansa da ambaton sunan ALLAH kafin ya murɗa ya shiga da sallama can ƙasan maƙoshi. Hasken ɗakin ya bashi damar hangota naɗe a tsakkiyar gadon, ya ɗan zuba mata ido na wasu sakanni kafin ya ƙarasa cikin ɗakin da shima keta tashi ƙamshi, yana da ga tsayen ya kira sunanta a hankali, idanun ta buɗe da ƙyar dan bata da nauyin barci, ko abu tasha ta kwanta da wuya kaga barcinta yay nauyin da za'ai abu a kusa da ita bata farka ba. Maidasu tai ta rufe tana wani ɓata rai. Duk da yanda tai ɗin sai bai damu ba ya kai zaune a bakin gadon sai dai nesa da ita kaɗan, koba komai yau ai ita baƙuwarsa ce, ada bai kulata ba ma balle yanzun. Hannunsa ya kai saman goshinta, da zafi sosai alamar zazzaɓi yau ma.
“Yau ma zazzaɓin ne?”.
Kamar bazata kulashi ba sai kuma ta ɗaga masa kai kawai. Iska ya ɗan furzar a hankali. Sai kuma ya ce, “Tashi to kici wani abu sai kisha magani”.
Kalamar magani da ya ambata yasa kanta kawo wuta, cikin gamsuwa da dabarar data zo mata ta tashi zaune da ƙyar tana ƙara cin serious, sai da ta zauna sosai bayanta jingine da gadon sannan ta ɗan kallesa ta kauda idonta, ganin hankalinsa nakan wayarsa yasa taji ƴar nutsuwa dan bata ƙaunar kallo. Cikin ƙara dai-daita plan ɗinta murya a karye ta ce, “Nifa paracitemol bayamin maganin zazzaɓi”.
Ɗan ɗagowa yay ya kalleta, sai kuma ya sake maida idon nasa kan wayar yana faɗin, “Sai wanne?”. Handbag ɗinta da ke bedside drawer ta ɗauka ta zaro wata takarda a bayan zip ɗin ta miƙa masa. “Wannan shi nake sha in dai ina irin wannan zazzaɓin, in ba haka ba bana warkewa da wuri”. Harga ALLAH bai kawo komai a ransa ba tunda shi ba likita bane, dan haka ya amsa takardar, ganin rubutun Doctor ya sashi sake yarda. Sai kuma ya ɗan kalli agogo, takwas da kusan rabi dare baiyi ba. Idanunsa ya maida kanta, ta janye nata da ke kallonsa a sace cike da basarwa. “Ya kamata kici wani abu to kafin na dawo ko?”. A ɗan yatsine ta ce, “Karka damu har ka dawo.”
“Okay”.
Ya amsa mata yana miƙewa. Wani irin daɗine ya ratsa Lulu kamar ta fasa ihu dan farin ciki. Wai yayama akai wannan dabarar baizo mata ba tuni take a wannan bala'in. Zamewa tai ta kwanta tana murmushin da kakan daɗe baka gani ba akan fuskarta dan sai ta gadama take yi.
Napep ya samu ta kaisa har ƙofar pharmacy ɗin data kwatanta masa ana iya samun maganin, koda ya basu takardar yaron saida ya kallesa, amma sai baice komai ba ya dai wuce wajen ɗakko masa maganin. Koda ya dawo da maganin ya faɗa masa kuɗin ya cire daga aljihu ya bashi. Napep ya sake samu ta maidashi gida. Yanzu kam sai da ya rufe ko'ina da ɗaukar abubuwan da Ahmad ya siya musu sannan ya nufi ɗakin. Inda ya barta anan ya sameta, sai dai yanzu ta koma ta kwanta. Duk da taji sallamarsa bata motsa ba har sai da ya kai hannu ya yaye bargon data rufa har kanta. Jikinta har tsuma yake lokacin da ya fiddo maganin da ga leda mai tambarin pharmacy ɗin, amma sai tai ƙoƙarin kannewa.
“Yanzu mi zaki ci?”.
Ya faɗa yana ɗagowa ya kalleta. “Ni bana jin yunwa, naci abu tare da Mamy”. Ta bashi amsa idonta akan ledar nan dai. Bai san wa take cema Mamy ɗin ba, sai dai yanda tai maganar cikin serious ya sashi gamsuwa, sai kawai ya cire maganin biyu ya miƙa mata tare da goran ruwa. Bata musa ba ta amsa tasha. Sannu ya sake mata da tattare sauran maganin ya ajiye a bedside drawer da ruwan. Zamewa tai ta sake kwanciya da faɗin, “Sai da safe”.
Murmushi ya ɗan saki ƙasa-ƙasa. Dan ya fahimci korarsa akeyi. Baice mata komai ba ya tattare sauran ledojin ya fice yana rage mata hasken ɗakin. Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi, sai kuma ta miƙe zumbur da raka bayansa da harara ta dannama ƙofar key sannan ta dawo. Cikin rawar jiki ta fisgi ledar nan ta zazzage kusan ƙwayoyin maganin biyar a tafin hanunta ta afa a baki batare da ruwa ba. Sai da ta haɗiye sannan ta ɗauka ruwan ta kora kaɗan. Wani irin farin ciki take ji na samun kayan nan cikin sauƙi, sai kawai ta faɗa saman gadon cike da jishaɗi tai juyi ta sake juyawa........✍️
_(ALLAH ka rabamu da mummunar ƙaddara. Wlhy irin masu ɗabi'ar nan tausayi suke ban. Dan rayuwar kawai suke batare da sun san ina ta dosa ba, idan sukai nisa sai an dage kafin su bari, ku ga dai, kwana biyu batasha ba amma ta koma kamar mara lafiya. Iyaye dan ALLAH mu ƙara dagewa wa ƴaƴanmu, mu bar aibata ƴaƴan wasu idan muka gamsu a irin wannan halin. ALLAH ka shiryar damu😭🙏)._
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣0️⃣
........Koda Smart ya kai kayan nan kitchen ya adana wanda zai iya lalacewa a fridge sai ya nufi ɗayan ɗakin kasancewar duk yasan sirrikansu, hasalima key ɗin ɗakin na hannunsa dan a rufe yake tun da aka gama shirya masa kaya aunty Saliha ta damƙa masa ko ƴan ganin gidan amarya babu wanda ya leƙa cikinsa. Shima nan ɗin kayane lafiyayyu aka shirya, dan shine ma matsayin master bedroom. Ɗakin yayi ƙyau sosai, komai ya zauna a inda ya dace. Duk da gajiyar da yake ji bai kwanta ba sai ya zare rigarsa da ga shi sai dogon wandon da singlet ya nufi bathroom. Bai jima ba ya fito da alamar alwala yayi, lafiyayyen carpet ɗin gaban gadon ɗakin ya hau dan yin salla. Sallar isha'i yay da shafa'i da wutri. Bayan ya idar yay zaman yin addu'a mai tsayi kafin ya miƙe. Har ya zauna a bakin gadon sai kuma ya miƙe, zuciyarsa ke ayyana masa ya kamata ya binciketa ko tayi sallar isha'i, ya kuma duba ko zazzaɓin ya sauka. Sai dai me, yana taɓa ƙofar ya jita a kulle. Shiru yay yana kallon hannunsa da ke saman handle ɗin, sai kuma ya ɗage kafaɗunsa alamar ko oho ya juya ɗakin da ya fito yay kwanciyarsa dan barci yake ji matuƙa. Dan shi a tunaninsa ko Lulun tayi hakanne dan kar ya nema wani abu a gareta.....
_WASHE GARI_ koda ya tashi sallar asuba sai da ya ƙwanƙwasa mata ƙofa, ganin zai makara saboda ya tashi shima a ƙurarren lokaci ya sashi ƙyaleta ya wuce. Ana idar da sallar ya dawo gidan, ɗakin nata dai ya sake nufa ya ƙara knocking. Lulu da ke kwance a ƙasa ta buɗe idanunta da sukai matuƙar nauyi da ƙyar ta iya miƙewa cikin takaicin damunta da ake tun ɗazun ta nufi ƙofar ta buɗe, dan ta manta ma a ina take, dai da ta ɗan jingina da ƙofar na wani ƴan sakanni sannan ta murɗa key ɗin ta buɗe kaɗan. Da farko bai niyyar shigowa ba, dan haka yace da ita, “Kin tashi kinyi salla ne?”.
“Zanyi”.
Ta amsa masa cikin yanayin muryar maye da tura ƙofar zata rufe dan abun bai gama sakinta ba. Da sauri ya riƙe ƙofar gabansa na faɗuwa, bata da wani isashen ƙarfin dan haka ya samu nasarar shigowa. Yanda ya kafeta da idanunsa da suka kaɗa sukai ja a ƙanƙanin lokaci ya sata zabga masa harara itama da nata dake a juye ta bar masa wajen cikin ɗan tangaɗi na rashin ƙarfi ta je ta faɗa saman gadon a rufda ciki gashinta dake a hargitse ya lulluɓe fuskar tata gaba ɗaya. (Ina ta samu abinda tasha?) Zuciyar sa keta kaikawo wajen son hasasowa amma iya hasashen ya auna a ɗan tsukun lokacin baro gidansu zuwa nan hakan bamai yiwuwa bane, sai dai idan dama tana tare da abunta. Inda take ya ƙarasa ya ɗauki handbag ɗin ta gaba ɗayanta ya zazzage a saman gadon. Babu komai a ciki daya danganci ƙwaya, jakkar ya ajiye cikin furzar da iska sai idanunsa suka sauka kan ledar maganin jiya daya sayo mata, jawo ledar yay ya fiddo maganin, an ƙara ɗiba kusan shida a ciki, ya tsirama maganin ido kallon da yaron pharmacy ɗin ya dinga masa lokacin da ya bashi takardar na dawo masa a rai da zuciya. Tabbas wannan maganin tasha. Kallonsa ya maida gareta ya zuba mata idanu kawai maƙogwaronsa na kai kawo a cikin wuyarsa da ɗan sauri-sauri. Da ga ƙarshe ma sai ya tashi ya fice da ga ɗakin kawai.....
____________________★
Cikin ɓacin rai yake dubansa ganin yanda yake neman haukata kansa. Gaba ɗaya kwanakin nan baida wani aiki sai shaye-shaye tunda ya baro Kano. Ƴar ƙaramar robar giya da ke a hannunsa ya fisge cikin masifa. “Wai mi kake son maida kanka ne kai kuwa MM? Akan mace! Ka zauna ka susuta rayuwarka. Tunda ka dawo da ga kano an kasa gane kanka, ka bar zuwa aiki ka barma fita a gidan nan gaba ɗaya sai