Showing 9001 words to 12000 words out of 163036 words

Chapter 4 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

758

Murmushi ya saki mai ciwo a karo na farko. Ya ɗan dubi Uncle Yousuf ɗin sai kuma ya ɗauke kai. “Miye amfanin maimaita abinda bashi da muhimmanci koya wuce Alhaji. Kawai na ajiye shikenan ya wuce. Nasan insha ALLAHU zaku sami wanda ya fini, ni kuma zan tara gaba maybe abincina ba'a nan yake ba”.
         “Nasan bazaka juraba kamar na baya da suka shuɗe domin Kanada banbanci da su. Sai dai irinka na jima ina fata ni kuma, dan kai kaɗaine zaka iya da ita har ma ka tankwarata. Har yanzu nasan baka san ni wanene ba Aliyu Hydar, sai dai ka sani ban nema kamin wannan aikin ba dan kana buƙatar aikin da kuɗi zai shigo maka. Tun randa na ganka wajen abokina yayan abokinka Ahmad naji a raina ka cancanta zama wani ɓangare da zai jagoranci haska wata fitila ta rayuwarta. Ita ɗin a fanɗare take, tabbas a haka ta tashi shiyyasa tanƙwarata yayma kowa wahala a cikinmu. Ada kallon komai muke a bigire na ƙuruciya da tunanin wata rana zata daina, sai dai ranar har yanzu taƙi tazo, bamu san kuma ranar da zata zo ba, ko kuma tazo ne ta wuce batare da mun farga ba oho?. Nasan kana da ƙanni mata maybe ma harda yayu, kasan irin zafin da nakeji a raina koda a kwatance ka kwatanta da ace sune, miyasa bazaka gane ba ne....?”
      Yanda ya ƙare maganar a raunane cikin sigar tambaya yasa Uncle Smart fesar da iska mai nauyi. A ɗan zafafe batare daya dubesu ba yace, “In dai har ku da kuka haifeta kun gagara tanƙwarata ni kuma taya kuke tunanin iyawa? Mahaifinta fa na raye, hakama mahaifiyarta, sannan gaku ku ƴan uwanta, Alhaji Please kayi haƙuri bazan iya ba fa. Bana son raini, bana iya jurarsa ga kowa. Bana son wulaƙanci ko ƙasƙanci duk da kasancewata talaka mai nema. Ina ganin kimarka dan ALLAH karka bari mu shiga wata hanya daba ita ta dace mukai ba dan alkairi ya haɗamu kuma bazan taɓa na manta da kai ba, dan kamun abinda mutane da yawa basu minba na alkairi ka gaida gida”.
       Yana gama faɗa ya miƙe. Dakatar da shi Ahmad yayi, kamar bazai tsaya ba sai kuma ya dakata tare da juyowa. Miƙewa shima Uncle Yousuf ɗin yayi yana ɗan murmushi. Hannu ya kai ya dafa kafaɗarsa, “Shike nan na fahimceka kuma nagode sosai. Ina son mutum irinka mai tsayawa akan ra'ayinsa da riƙe mutuncinsa. Zan jima inajin raɗaɗin rabuwa da kai Aliyu. Amma dan ALLAH ina roƙon alfarmar kazo office ko zuwa gobe ne domin amsar hakkinka, kuma bana son kace da ni a'a”.
        Baki ya buɗe zai yi magana Ahmad ya dakatar da shi. “Dan ALLAH karkace a'a Smart, ban sanka da musu ba karka fara akan Yaya Yousuf, sannan kayi nazari akan roƙon da yay maka, nasan kanada damar taimakons.....”.
     Hararar da ya ɗan ballama Ahmad ɗin ce ta sashi yin ƙaramar dariya batare da ya ƙarasa ba. Ɗauke idanunsa yay da faɗin, “Shike nan insha ALLAHU idan na samu lokaci zanje, amma kai ma kasan kawai dai dan ta Yaya boss ne wlhy”.
        “Na sani Mawashi. Yaya boss kuma na godiya da wannan karamci”. Bai ce komai ba, sai murmushi da Uncle Yousuf dake saurarensu yayi. Har cikin rai ɗabi'un yaron birgesa sukeyi matuƙa. Yana son ganin mutum mai nutsuwa musamman matashi kamar haka. Ba irin matasan yanzu da shegen rawar kai yayma mafi yawansu katutu ba...

     Har mota ya musu rakiya. Bayan wucewarsu sai yaji ya kasa komawa cikin gidansu dan baisan da wane irin harshe zaima Ammah bayani akan sake rasa wannan aikin ba shima, duk da dai jikinsa yay ɗan sanyi da kalaman Ahmad na ƙarshe, amma dai bai yanke hukunci ba na sake amsar aikin har yanzu. Sai dai in ya tuno bayanin Abba ya kanji faɗuwar gaba. Tabbas yasan wanene Abbansu, sam baya magana biyu. Mutum ne tsayayye da idan yace e to e ɗinne da har ransa. Idan kuma yace a'a to a'a ɗin ce fa. Da ƙafa yabar cikin anguwar tasu, rashin abunyi da sanin ina zai dosa ya sashi miƙewa a titi yay ta tafiyarsa kawai. Yayi tafiya mai nisa da bai san ina yake jefa ƙafa da ɗaukewa ba ya fahimci kamar binsa akeyi a baya. Tsamm yayi na tsarguwa tare da tsayawa, sai dai abin mamaki babu alamar wani tare da shi a ƙafa, wanda ke a kan mashina ma da napep babu alama, hakama na mota. Dakewa yay ya cigaba da tafiyar, still dai ya sake jin tabbas akwai mai binsan. Yanzu kam bai juyo ba sai ya yanke titin ya shiga cikin wani layi, ya ɗan yi nisa da layin sosai ya samu rumfar wasu masu kayan kafinta ya ɗan dakata cikin dabara kamar mai gyara igiyar takalmi. Ta cikin mirror da aka jingine ya hango wasu samari biyu, sai dai suna ɗan waskewa cikin ɓadda kama. Hakan ya ɗan bashi mamaki, dan shi dai a rayuwa duk da yana da tsatstsauran ra'ayi bashi da abokin faɗa. Cigaba yay da tafiyar dan son gane iya gudun ruwansu badan yasan sirrikan layukan inda yake ba. Sai da sukaje ƙarshen layin sosai ya fahimci akwai matsala, ya ɗan ji wani abu a ransa amma sai ya dake, wata hanyar da yake ƙyautata zaton zata ɓillesa da titi ya bi, sai dai yana shan kwanar tsukin wajen suka sami nasarar rufesa ruf ata gaba da bayansa. Ɗaya bayan ɗaya ya bisu da kallo har ya sauke akan napep ɗin da aka faka a gabansa. Cikin dakewa da ambaton sunan ALLAH ya ce, “Ku kuma fa?”.
     “Zaka sani amma ba'a nan ba”.
Ɗaya ya bashi amsa cikin gatse da nuna masa bindiga dake soke a ƙugunsa. Bindiga bata kasance abar wasa ga kowa ba. Duk ƙarfinka da taurin kai a duk inda mai ita ya kasance shike zama a saman ƙarfin ikon ka. Dan haka ya shiga napep ɗin zuciyarsa na saƙa masa abubuwa masu yawa game da mutanen. Biyun da suka dinga binsa ne kawai suka shiga gefe-da-gefensa, mai napep yaja suka fice daga layin, sai da suka fita gaba ɗaya wanda ke gefen haggunsa ya jefa masa wani ƙyalle a fuska, da sauri na kusa da shi ya kama ya ɗaure masa idanu yayinda wanda ya fara jefa ƙyallen ya ɗora masa bindiga a gefen ciki ta yanda bai isa musawa ba. Duk da ya sake firgita haka ya dake a zahirance, a baɗini kuwa yana mai ambaton sunan ALLAH......

    Tofa, su kuma waɗan nan daga ina?. Wayyo Uncle Smart ɗinmu😫😢

          ∆••••∆ ★ ∆••••∆

   Tun daga main falour na gidan kana iya jiyo tashin sautin kiɗan dake fitowa da ga ɗakinta, duk da kiɗane mai taushi na mawaƙiya Shakira yanda ta ƙure voluen yasa ake iya jiyowa. Tun safe babu wanda zai ce ya ganta yau a gidan har zuwa yanzu da agogo ke nuna ƙarfe takwas da wasu mintuna. Mafi yawan yaran rai a ɓace suke fitowa daga ɗakunan su dan sautin kiɗan data saka ya takurasu da hanasu barcin safen. Hatta da ƙananun Suhaib da Imran da fita makaranta kan hakanasu barcin safen ji suke ta takura musu, musamman Imran dake son ƙarasa Assagment ɗinsa amma ya gagara fahimtar komai. Kaf ɗinsu sun gama hallara a dining, sai dai fuskar kowanne a turɓune da takaici. A haka Daddy da Mommy suka fito suka samesu, a kallo ɗaya zaka fahimci itama Momy ranta a ɓace yake, sai dai shi Daddy kam ko'a jikinsa. Yaran ma na gaidashi bai wani saurarensu ba hankalinsa nakan kiran Tabawa mai aiki. Da ɗan gudu-gudu ta fito a kitchen hannunta riƙe da ƙaramin ludayi da alama girki takeyi.
       “Babyna fa?”.
Ya faɗa kai tsaye yana nuna upstairs. Itama upstairs ɗin ta kalla, cikin sake rissinawa tace, “Barci takeyi Alhaji, tace zuwa ƙarfe tara da rabi na tadata”.
     “Shi kuma wancan kiɗan da ga ina?”.
“Itace ta kunna”.
Nunin ta tafi kawai ya mata batare da ya sake cewa komai ba. Mommy da tai kicin-kicin da fuska ya kalla, sai kuma yabi sauran yaran nasa da kallo. Hafiz dake ƙoƙarin kai shayi bakinsa wanda a haihuwa shike bima Lulu ne ya ce, “Humm Daddy yanzu bazakace komai ba kenan?”.
    “Akan me?”.
“Aunty Lu. Ai ko kafiri ba kowa ke iya saka kiɗa ya kwanta da shi ba. Kuma ina da tabbacin ko sallar asuba batayi b.....”
     “Kai ban san shashanci da ƙazafin banza, wai Hafiz ita ɗin sa'arka ce? Kuma kai ubanwa yace maka batai sallar ba”. 
    “Ai ba sai wani ya faɗa masa ba abinda kowa ya sani ne. Ni ban san wane irin makahon so kakema Mawaddat ba a gidan nan, kuma ka sani wannan ba gata bane kashe mata rayuwa kakeyi matsayinta na mace. Da haka kowace yarinya ake rainonta a gidansu da baka gammu haka ka aura ba matsayin iyayensu Alhaji. Dan ALLAH ya kake so nayi da raina akan Mawaddat ne?”.
Wani banzan kallo ya galla mata ita da yaran baki ɗaya yana cika da batsewa, sanin yanzu zasuyi sama ya sata miƙewa tabar dining area ɗin zuciyarta na ƙuna da raɗaɗi. Ta rasa mike damun mijin nata akan babbar ƴarsu mace, yana nuna mata ƙazamar rayuwa a matsayin soyayya, iya bakin ƙoƙarinta tana yi akan Mawaddat amma abubuwa sake taɓarɓarewa sukeyi. A hankali hawaye masu raɗaɗi suka silalo mata saman kumatu.........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣





........A can falo kam tashin Mommy dai-dai da shigowar Uncle Yousuf, da murna yaran suka tarbesa. Sai dai ganinsa kamar rai ɓace yasa jikinsu sanyi. Abba da shima idonsa ke kansa ya baro dining ɗin ya nufosa. Kusa da shi ya zauna idanunsa a kansa ɗan uwansa, yana son ɗan ƙanin nasa namiji ɗaya tilo da ya rage masa a duniya.
    “Anya lafiya kake cika kana batsewa haka?”. Ya faɗa cikin kulawa da dafa kafaɗarsa. A hankali yace, “Ba komai. Sai kuma ya kai dubansa ga sashen Lulu. “Wannan kiɗan fa?”. Shima Daddyn kallon saman yayi, sai kuma yay ɗan murmushi da faɗin “Kaima ka sani sai dai ƴar gidanka ai”.
        Komai Uncle Yousuf bai sake cewa ba, sai rumtse idanu da yay cikin takaicin yayan nasa. Kusan mintuna biyu kafin ya buɗe, “Yaya mika yanke akan yaron dana kawo?”.
     Murmushi Daddy yay mai bayyana haƙwara. Ya ɗan bigi kafaɗarsa cikin sigar zolaya ya ce, “C-mon magajin baba saki fuskar mana, ni idan kana wannan cikar sai naga kamar baba ne ya dawo fa”.
        Baki Uncle Yousuf ya tura masa kamar mai shirin yin shagwaɓe fuska. Sai kuma ya kauda kansa saboda murmushin da ke son kufce masa. Sam baya iya dogon fushi da ɗan uwan nasa. Shima Daddyn murmushi ya sake saki da faɗin, “Yauwa ko kai fa. Yanzu kamun bayani yanda zan gane. Wane yaro kake magana a kai?”.
     A taƙaice ya ce, “Driver”.
  “Okay ni babu abinda na yanke. Dan Babyn ka har yanzu tace tana buƙatarsa ai”.
    “Shi kuma baya buƙatarmu dan ya ajiye aiki”.
         “Wannan ra'ayinsa ne ai. Idan itama ta haƙura sai a nema mata wani ba damuwa bane”.
    Wani shegen takaici ne ya sake kume Uncle Yousuf. Shi bai san wane irin mutum bane yayansa. Sam bai damu da damuwar kowa ba sai kansa da su ahalinsa. Kai kawai ya jinjina yana miƙewa. Daddy dake binsa da kallo ya ce, “Badai wucewa ba?”.
    “Yaya to mizan zauna nayi kuma. Ina son dai ka sake tunani a wannan gaɓar. Domin duk a yanda muke kallon rayuwa da ɗaukarta yaya watarana sai ta tsere mana ta ɗakko wasunmu a madadinmu. Zata iya yuwuwa kuma ta ɗakko waɗanda muke kallo ba kowa ba su kasance a saman tamu damar”.
          “Hakane Auta, sai dai ban san dalilin wannan gugar zanar ba”.
    Murmushi Uncle Yousuf yay mai ciwo. “Nasan ka sani Yaya, duk da ni ba gugar zana nake maka ba. Sai dai akan Mawaddat kana rumtse idanunka da kunnuwanka domin ƙin amsar gaskiya”. Daga haka ya nufi part ɗin nata. Yanda yake haɗa ɗan steps ɗin shiga sashen da bibbiyu zai baka tabbacin ransa a ɓace yake. Sai da ya rumtse ido lokacin daya ɗaura hannunsa kan handle ɗin ƙofar ɗakin nata. Batare da ya yarda ya kalla ɓangaren da gadonta yake ba ya nufi kayan kiɗan ya kashe. Kafin cikin daka tsawa ya ambaci sunanta. A firgice ta tashi tana mai yaye ƙaton lallausan bargon data jibgama kanta. Gaba ɗaya gashin kanta madaidaici a tsaho ya wani hargitse, sanye take da wando da riga na pyjamas farare tas masu santsi da ƙyalli. Kasancewar sun mata bujin-bujin yasa basu bayyana mata surar jiki ba. Ya ɗan samu nutsuwar ganinta da kayan mutunci, dan haka ya kalleta cikin ido babu wasa a tattare da shi ya ce, “Kinyi sallah?”.
        Tana son Uncle Yousuf matuƙa dan shima yana sonta da mata gata. Sai dai kuma baya wasa akan tarbiyyarta da gyara lamarinta shiyyasa take tsoronsa idan ya birkice, dan yasha kwasa mata mari mai gigitarwa. Akwai wani lokaci da ƙawaye suka yaudareta suka sakata dawowa gida a wani yanayi da ga club da ya ɗauketa da wani mahaukacin mari sai da ta yini jinta bai dawo ba. Tuni kuma ta watsakke daga makuwar da tayi.....
        “I say kinyi salla?!!”.
     Ya sake maimaitawa a tsawace fiye da farko. Daburcewa tai ta ɗaga masa kai ta kuma girgiza. Sai kuma ta sauka da gudu a gadon kamar wata ƙaramar yarinya ta nufi toilet ɗin ta. A cikin mintunan da basu gaza biyu ba ta fito fuska da ƙafafu jiƙe da ruwa wai tayi alwala. Abin salla da Tabawa ke faman ajiya a ma'ajiyarsa kamar na ado dan ba sallar take ba sai randa taso ta ɗauka ta shimfiɗa. Akan kayan barcin ta zumbula hijjabin da shima dai baida banbanci da kayan decorations na gida gareta. Uncle Yousuf na daga inda yake tsaye har yanzu cikin ƙunar rai. Fara sallar da bata da fasali balle makama da gamata ba'a ƙulla mintuna biyu cikakku ba. Hankalin Uncle Yousuf ya ƙara tashi. Dan yau ne karan farko da ya fahimci Mawaddat bata iya ko salla a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un” ya shiga maimaitawa jikinsa na tsuma. Baima san sanda ya kai zaune jagwab cikin kujerar kusa da shi ba. Yanzu nan kamar Mawaddat mai shekara ɗai-ɗai har ashirin da huɗu tana cikin ta biyar, mai karatun matsayin cikakkiyar lauya da duk wanda ta tsayama a shari'a zai iya alfahari da itace babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninta da UBANGIJINTA a ɓangaren bauta masa irin haka. Wane irin sakaci sukan sukai da shagala akan al'amarin yarinyar nan har haka?.....
        “Uncle You! please kayi haƙuri kar kai fushi da ni”.
    Kalamanta cikin damuwa suka katse masa tunani. Tuni ta rarrafo gabansa ma hijjab ɗin na harɗeta batare da ya sani ba. Idanu kawai ya zuba mata dan shi kam tausayi ma take bashi wlhy. Shi mutum ne mai zafi amma kuma yana da saurin sauka da kuma sauƙin kai shiyyasa yaran ɗan uwan nasa ke sonsa, dan ya taso ne kamar duk shi ya raine su. A hankali ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Muryarshi a rissine bakamar ɗazun ba ya ce, “Mawaddatan-wa'rahmah!”.
        A hankali ta ce, “Yes Uncle”.
   “Mi kikayi haka?”.
“Uncle salla mana da kace”.
“Bani nace ba ALLAH ne yace ayi kuma ba haka akeyi ba. Mawaddat wannan ranar ita nake gudun zuwa gareki shiyyasa nake zaneki idan kikaƙi zama Islamiyya a shekarun baya kafin abar ƙasar nan da ke, shiyyasa kuma na dage a nema miki malamin da zai koyar da ke addini bayan Yaya ya maidaki can. Yanzu ace kamarki, ɗiyan musulmi hausawa ƴar ƙasar Nigeria a arewa amma baki iya salla ba? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Mawaddat da duk mi kike yi ke kuwa a duniyar nan haka? Mi kikaima kanki tanadi na tunkarar UBANGIJI da har kikejin ƙwarin gwiwar baje kolinki a duniya da abinda ke cikinta kawai? Anya kin yarda zaki mutu kuwa? Za ki kuma kwanta kabari? Za kuma a tasheki? Za'a kuma miki hisabi sannan ki ƙarɓi sakamakon makomarki?. Makomar da gida biyune kacal dole kuma ka tsinta kanka a ɗaya wuta ko aljanna.........”
       “Uncle Please kabar zancen mutuwan nan mana. Badai sallan bane kuma nayi. Kaga inama da zuwa court zuwa ten ga shi har nine na neman wucewa.”
    “Wato shi zancen sallan baida muhimmanci ko?”.
    “Noo Uncle You! Bance ba fa. Kawai dai ni.....”
    Sai kuma tai shiru. Kansa kawai ya girgiza dan y fahimci ba irin wannan zaman na kai tsaye Mawaddat ke buƙata ba. Yana buƙatar yin nazari akan al'amurinta kafin ya nemo mafita mai ɓullewa. Da hannu yay mata nunin ta tashi da faɗin, “Okay jeki shirya”.
     “Yawwa Sweet Papa na!!!”.
Ta faɗa da ihu tana miƙewa. Kansa kawai ya girgiza yana mai karanto mata addu'ar shiriya wajen UBANGIJI kamar yanda ya saba akoda yaushe ya tashi ya fice dan bata damar yin shirin....

∆•••∆ ★ ∆•••∆

    Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da sukai masa tsananin nauyi ya fara bin inda yake da kallo. Falo ne babba mai ɗauke da kaya na alfarma. Sai garadan samari guda biyu dake tsaye a kansa da alama sune suka ajiyesa a wajen. Akan mutumin dake zaune cikin kujera mai zaman mutum ɗaya ya tsaida idanun nasa. Shima kallonsa yake yi. Fuska ya ƙara tsukewa tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login