Showing 18001 words to 21000 words out of 163036 words

Chapter 7 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

431

*zan koya miki sanaar Graphics design wanda zaki samu abin dog dogaro da kai. Kina zaune daga gida kina sanaarki.*
*Ga mai bukata a masa design ko wani iri, munayi insha Allah*

SERVICES PROVIDED
🌹Logos
🌹Flyers
🌹data flyers
🌹Pos banner
🌹Book cover
🌹 Invitation Card
🌹 Business Card
🌹 Banner
🌹 Save The Date
🌹 Bank Sticker
🌹 Video Invitation card
🌹 Birthday Videos
🌹Business logo
🌹graduation poster
🌹e t c

Muna kowani design a farashi mai kyau idan training kikeso ma munayi shima a farashi mai kyau insha Allah kedai kimin magana ta wannan number 👇🏻

*DM FOR ANY ENQUIRY*

07084515410

_____________________

........A ranar dai bai yi aikin komai ba sai zama tare da maigadi suka sha hirarsu, abinci ma daga cikin gidan aka kawo harda nashi. Yaso ƙin ci dan shi irin mutanen nan ne masu tsantsenin tsiya. Abu indai ba nasu ba kona gidansu sukan iya hana kansu koda suna buƙatarsa. A hakan ma kaɗan yaci ya cire hannu. Sai bayan sallar la'asar ya tafi kai Aunty Saliha asibiti tare da su Deen. Kasancewar da kayan abinci ta tafi ya taimaka mata wajen shiga da su ciki. Anan ne ya samu damar ganinta. Kwance take rai-rai a kan gado Mommy na zaune ta jingina da jikinta, a kallo ɗaya zaka tabbatar da taji jiki, dan kwana ɗaya kacal harta faɗa da ƙarayin wani fayau da ita. Bayan ya gaisa da su Mommy ya gaisheta da jiki itama a taƙaice. Kaɗan ta ɗago idanunta dake nuna yanayin halin da take ciki na ciwo ta dubesa. Maimakon amsa masa sai ta watsa masa wani kallon rashin mutunci ta ɗauke kai a yatsine.
       Mommy ce ta dubeta cikin ɗan faɗa-faɗa. Sai dai kafin tai magana Deen ya ce, “Aunty Lu Uncle Smart fa na gaisheki da jiki baki amsa masa ba kuma kina masa harara”. Harara ta zubama yaron, muryarta a ɗashe irin na mai ciwo tace, “To maganatu naƙi na amsa ɗin, an kuma hararesan. Yaro sai sa idon tsiya. Ko dokace kowane trash idan ya gaisheni sai na amsa”. Baki ya tura mata da matsawa jikin uwarsa yana ɗan ƙunƙuni. Zata sake magana Mommy ta tareta. “Wai nikam yaushe ne zakiyi hankali Muwaddat? Yanzu kina a gadon asibitin ma bazaki bar masifa ba. Jiya i yanzu fa kina nan keba matatta ba keba mai rai ba hankalin kowa a tashe. Haba ayi mutum babu haƙuri sam sai baƙin tujaran tsiya kamar mara mafaɗi”.
      Sosai ranta ya sosu ganin yanda Mommy ke mata faɗa a gabansa. Badai ta tanka ba amma tayi alƙawarin koya masa hankali tunda har akai mata haka a kansa. Bata sake magana ba ta gyara kwanciyarta ta juya musu baya, dan koyaya tana shakkar Mommy ɗin kasancewar bata yarda ta bata fuskar rainata ba duk da abinda Daddy kemata akanta tun tana a showal. Shima ficewa yay daga waje abinsa yana sake jinjina halin yarinyar mai ido a tsakar kai...

         *_BAYAN KWANA UKU_*

     Kwanakinta uku a asibitin aka sallamosu, dama shi Daddy tun washe gari aka sallamesa sai dai Dr Khalipa ya bashi shawarar ɗan yin nisa da asibitin har ya samu nutsuwa. Shiyyasa bai sake zuwa ba akan tsayawar Uncle Yousuf amma duk da haka kullum sai yazo da dare ya dubata. Alhmdllh jikin nata da sauƙi sosai. Sai dai har sannan batajin ƙarfinsa. Ga buƙatar kayan shaye-shayenta da take matuƙar yi sai dai babu damar shansu. Shine ya ɗakkota tare da Mommy. Yanda kowa ke tattalinta na bashi mamaki kamar wata ƙaramar yarinya. Musamman ma Daddy dake yi kamar zai maidata cikinsa. Ko yaya ta motsa sai ya tambayi ba'asi. Idan ko tace wash yaringa jera mata sannu kenan kaji har muryarsa na zuga dan damuwa.  Kasancewar sallamar dare akai musu yana ajiyesu ya wuce gida. Da ƙyar ya samu napep saboda yanayin anguwar tasu. Ana sallar isha'i ya shiga gida. Wanka ya farayi sannan ya shiga gaida su Ammah. Yau kam ya samu Umma da Mama na rikici akan yara, duk da abune da bai cika faruwa ba a gidan irin haka kaga suna faɗa a zahiri sai da yaji ransa ya sosu. Aunty Amarya ce tamai bayanin tushen faɗan wai Mubarak ne ya daki Sakina saboda ya aiketa taƙi zuwa har ya jimata ciwo a gefen ido fuskarta ta kumbura. Ita kuma Mama tai magana akan ita bata hanashi dukansu idan sun masa ba dai-dai ba. Amma yasan inda zai daka saboda gudun nakasa mutum. Umma kuma dake kamar a jirace ta amshe faɗan shine fa suka rikice haka. Daga inda yake ya ƙwalama Sakinar kira, fitowa tai da ga ɗakinsu da taimakon Yayarta Khadijah. Hankalinsa ya tashi shima da ganin yanda kusan rabin fuskar yarinyar ya kumbura, gashi ciwon kamar ma akan idon ne ba gefe ba.
      “Kawo mata Hijjab” kawai yace yana kallon Khadijan. Da to ta amsa masa. Su Umma dai nata sa'insar su Ammah na basu haƙuri. Shikam wayarsa ya cigaba da dannawa kamar ma bai san mi ake a gidan ba har Khadijah ta dawo. Mayafi ta kawo mata dan hijjab ɗin zai takura mata, baice komai ba yay gaba Sakina ta bisa a baya. A rukunin ɗakunsu na samari ya tsaya, kira ya dannama Mubarak dake ɗaki zaune shiru alamar akwai damuwar abinda ya aikata tattare da shi shima, dan tunda abin ya faru baya cikin nutsuwarsa yayi dana sani babu adadi, jin hayaniyar su Umma ta sake ɗaga masa hankali shine ya koma ɗaki ya rakuɓe.
      “Fito nan ina son ganin ka”.
Bai gama ajiye wayar ba Mubarak ya fito dan suna shakkarsa sosai a gidan. Gaba yay suka bisa baya su duka biyun, kasancewar akan titi layin gidansu yake a ƙofar gida suka samu napep, shi da Sakina suka shiga baya, Mubarak kuma kusa da driver. Wani babban canix na anguwar tasu dake can ƙasa sukaje, yanda suka tarbesa da alama sun sanshi sosai. Dan babu ɓata lokaci aka hau duba Sakinar. Bayan an rufe ciwon da bandeg mai camix ɗin ya basu shawarar kaita asibiti da safe gudun kar idonta ya taɓu. Godiya ya musu ya biya kuɗin suka fito. Dama Uncle Yousuf ne ya bashi su da safe dubu biyar.
       Sun sami gidan yanzu tsit, dan Umma da Mama na gaban Abba da ya gama musu tijara yace kuma su sameshi. Suna shigowa Sadiq yace suje Abba na kira. Su kaɗai suka shiga shi kuma yay shigewarsa ciki, ya zauna sun fara gaisawa da Amma Sadiq ya shigo shima yace yazo Abba na kiransa. Miƙewa yay yabi bayansa. Ya samu Abban nata zagin Mubarak, shi kuma kansa a ƙasa kamar ma yana kuka. Koda ya zauna yana kallon yanda Umma ke hararsa. Bai damu ba ya fuskanci Abban dake cigaba da zagin Mubarak.
         “Abba ayi haƙuri haka nan, yayi kuskure kuma dama nima zan hukuntashi akan laifinsa duk dai ya amsa laifinsa kuma ya bada haƙuri da yin nadama. Itama kuma tace ta yafe masa, amma duk da haka so nake taji sauƙi sai na zauna da su...”
    “Ikon ALLAH ƙarfin hali, ni kana bani mamaki a gidan nan Hydar. Ka dinga wani ɗaukar gabara kamar kaine ubansu. To ko Salim dake yayanku gaba ɗaya yana wannan aikin ne? Ko sai kai sarkin iya zartar da hukunci...”
        Tsawa Abba ya daka mata har sai da ta zabura. “Ke Usaiba ki kiyayeni a gidan nan. Da kike faɗin kamar ubansu ai uban nasu ne shi tunda babba yake garesu. Shi Salim ɗin dake babba miya amfanama kansa ma balle wani, shiko da kike ganin bai miki dai-dai ɗin ba tsaye yake akan tarbiyyar har ƴaƴanki. Badan Aliyn ba a gidan nan sai ƴaƴan ɗakinki sunfi kowa zamemun fanɗararru saboda banzan halinki nason ƴaƴan tsiya. Wlhy sonai ma ya masa dukan mutuwa shima ya fasa masa ido kamar yanda ya fasa mata...”
      “Saboda ita ƴar sonka ce da uwarsa. To wlhy ya dakesa ai gashi nan yaga in ban rama masa ba. Har yau ne yabo ya tashi a kansa gareka. Da kake kiran Salim mara amfani wlhy sai dai in shine mara amfanin. Dan koba komai yarona nada iyalinsa da gida da motar hawa ga aiki bashi dake yawon gal-gal ba babu makama sai watsewa a gari. Auren ma da zai ajiye iyali ya gagara sai bin ƴaƴan mutane ana lalubewa a sorayen iyayensu, da yake tsoron uwarsa kakeji ka kasa magana...”
        Sosai ya rumtse idanunsa dan jin zafin maganganun Ummar garesa. Cikin dakewar nan tasa da sanyaya harshe ya ce, “Dan ALLAH Abba kuyi haƙuri abar maganar. In dai Mubarak da Sakina ne zan hukuntasu akan laifinsu.”
       Mama da tun ɗazun batace komai bace ta karɓe zancen da faɗin, “ALLAH yay maka albarka ɗan halak, wannan shine girma na gaskiya ga babba Hydar, ba ɗagawa da alfahari akan abinda ALLAH shine mai badawa ba. Koda yake iyakar mutum ma alfaharin kawai tunda bai isa tanƙwara ɗan ya masa yanda yake so ba sai dai yaga yanama iyalansa”.
       A take falon ya nema sake rikicewa tsakanin Umma da Mama ɗan kai tsaye dai akan Salim ɗin da Umman ta gama kurantawa ne Mama ta yaɓa mata magana. Wata gigitacciyar tsawa Abba yay musu data sakasu nutsuwar dole su duka. Dan dama shi kam a yanzu ne kura tai lafiya saboda girman shekaru da yau da kullum. Amma tsayayyen mutum ne a gidansa kusan ma halayensa ne Uncle Smart ɗin ya ɗakko a gidan. Masifa sosai ya musu tare da wankesu tas. Shi dai bai sake magana ba har Abban ya gama ya sallamesu. Koda suka shigo gidan Umma nata cigaba da ƙananun maganarta kamarma zata maida faɗan kan Amma ne. Ammah nunawa ma tai bata san da ita take ba. Duk da ita mutum ce mai zafi da rashin ɗaukar raini, mace ce mai kawaici musamman akan al'amurin yaranta. Dole Ummar dai tagaji tai shiru dan kanta. Koda Uncle Smart kuma ya koma wajenta bai mata maganar abinda ya farun ba, ba kuma ta tambayesa ba, ya ɗan tsakuri abinci ya ƙarama su Asma'u karatun Alkur'ani da suke jiransa.
      Koda ya koma ɗaki ya jima maganganun Umma na masa kai kawo a zuciya da ruhi, yana jin matuƙar ciwo da zafi a duk sanda aka zagesa da ƙaddararsa a gidan musamman akan aiki. Dan shi akan aure bawani yana gabansa bane har yanzu. Zaima iya rantsewa bayan Kubrah ɗiyar ƙanwar Ammah da suka haɗasu daga ƙarshe iyayenta suka wargaza abun wai akan baida aikinyi bai taɓa tsayawa da ƴar wani da sunan soyayya ba. Ko ita ɗin da farko ko kallo bata ishesa ba, sai da Ammah ta zaunar da shi ta masa nasiha kasancewar gwaggon tasu ce ta buƙaci haka da kanta saboda son da yarinyar ke masifar masa. Har ranar aure an saka musu kafin abubuwa su rikice iyayen suga mai kuɗi suka canja shawara. Ko a yanzu haka da yarinyar ke'a gidan aure tana masifar son sa, dan a duk sanda ALLAH zai haɗasu sai tayi kuka dan ma baya nuna ya fahimci mitake ciki ne........✍️


____________________

https://youtu.be/y6YMU120RZI

Please subscribe to Rukayyat khalid YouTube channel fisabilillah. I only uploads videos na karatun Qur'an a tashar Please help me reach 1k subs soon insha Allah *RUKAYYAT KHALID*

*Assalamualaikum warahmatullah*

*Yar uwa shin mene amfanin wayar hannunki da bazaki koyi sana a da ita ba?*

*Kullum kina yawo a social media irin su Facebook, WhatsApp, tiktok,Instagram, twitter da ma sauransu.*

*Kina asarar data a banza kina zuba adashinda babu ranar dauka*

*bakya chas bakya as? Se chart kika iya 🤔*

*kin damu mijinki da BANI BANI?? Kizo nan ni* *~Graphics by Rukayyat~* *zan koya miki sanaar Graphics design wanda zaki samu abin dog dogaro da kai. Kina zaune daga gida kina sanaarki.*
*Ga mai bukata a masa design ko wani iri, munayi insha Allah*

SERVICES PROVIDED
🌹Logos
🌹Flyers
🌹data flyers
🌹Pos banner
🌹Book cover
🌹 Invitation Card
🌹 Business Card
🌹 Banner
🌹 Save The Date
🌹 Bank Sticker
🌹 Video Invitation card
🌹 Birthday Videos
🌹Business logo
🌹graduation poster
🌹e t c

Muna kowani design a farashi mai kyau idan training kikeso ma munayi shima a farashi mai kyau insha Allah kedai kimin magana ta wannan number 👇🏻

*DM FOR ANY ENQUIRY*

07084515410

______________________

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣3️⃣


______________________________
*_Wai wai wai_*
_wani kaya sai amale,don raqumi bazai iya dauka ba_

*MAAB LUXURY* _GIDAN ADO DA KECE RAINI_

*MAAB LUXURY* _DUNIYAR QAWATATTUN KAYAYYAKI_

*MAAB LUXURY* _TUNQAHON GIDA DA GININ GIDAN GABA DAYA_

_IDAN NACE ZAN LISSAFO BAZAN GAMA BA A NAN KUSA,DON SUN CANCANCI KOWANNE IRIN SUNA_

*DAME DAME SUKE SIYARWA NE?*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

_SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI… KWASHA KWASHA_

_SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI… INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_

_KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_

_KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_

_KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM: @Maabluxuryhome_
_FACEBOOK:@maabluxuryhome_

_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_

_A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_

_MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED… JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_

_08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_
_______________________



........Washe gari da ranakun da suka biyo baya babu wani ƙwaƙwƙwaran aiki da yayi kasancewar wadda aka ɗaukesa aikin a yanzu da ita bata fita. Sai dai yaje ya zauna wajen masu gadi har lokacin tashi yayi ya koma gida. Ganin hakan yasa yau bai fita da wuri ba yabi su Maryam makaranta kamar yanda yakan yi lakaci zuwa lokaci batare da sun sani ba. Yakan ɗan binciki halin da suke ciki da yanayin karatunsu. Sai goma yabar makarantar. Lokacin da ya iso gidan aikin nasa sha ɗaya saura kaɗan. Tunda ya turo gate ɗin ya shiga akanta ya fara sauke idanunsa. Tsaye take a can jikin wata farar mota da ke ƙaton compound ɗin nasu. Kallo ɗaya da yay mata bai sake marmarin ƙarawa ba saboda shegun kayan da ke jikinta. Skert ne blue da ya kamata ɗam-ɗam ya fidda mata halittar jikinta da ƙyau, sai ƴar riga mai santsi kalar gwaiduwar ƙwai. Babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta sai wani ƙaton glasses data toshe idanunta da shi, kanta da hula irin ta zamani da ake yayi. Dan ƙyau kam tayi ƙyau, sai dai ga ɗabi'a da tarbiyyar ɗiyan musulmi bahaushen arewacin Najeriya babu abinda shigar tata ke nufi ga duk wanda zai kalleta sai ƙarancin tarbiyya da wayewar banza. Ga wayayyu kuma irinta hakan normal ne.
     Tsaki ya ɗan ja a ƙasan maƙoshi yana ƙara tsuke fuska. Su maigadi dake zaune kamar a tsorace duk ya bama hannu suka gaisa. Yanda suke kamar a noƙe ya bashi mamaki. Sai dai yana niyyar kaiwa zaune mai wanki ke faɗin, “Ɗan uwa Hajiya Muwaddat fa kai take jira. Tsaiwar da kaga tayi can tun ɗazun take zuba tijara har mu ma nan sai da muka samu rabonmu na zagi, kasan ita sanda aka raba mutunci tana cikin bargo ƙudindine shiyyasa bata samu ba”.
        Shiru kamar bazai amsa ba. Sai kuma zuwa can a dake ya ce, “Tunda kun maida kanku sakarkaru gareta ba”. Da ga haka yaja bakinsa ya tsuke tare da ciro wayarsa da ga aljihu zai fara sana'ar danne-dannen nasa. Wata irin gigitacciyar tsawa Lulu data gama kaiwa wuya da takaicinsa ta daka masa. Sai dai ko gezau wai an tsikari kakkausa. Cikin takun nan nata na izza da yanga ta ƙaraso gate ɗin. Ashariya ta mulmulo tare da faɗin, “Wai kai ɗan uban wanene? Mi kake taƙama da shi ne, tsabar kai cikakken mara mutunci ne kazo a makare ina tsaye tun 8:30 ina jiranka amma kazo ka zauna anan irin ma kai baka gannin nan ba. Na rasa mi Daddy da Uncle Yousuf suka gani gareka suka takura da sai kai ne zaka zama driver na a gidan nan illiterate irinka..”
      A hankali ya rumtse idanunsa sai kuma ya buɗesu a kanta. Wani irin yankawa zuciyarta ta shigayi da sauri-sauri, dan wani irin kwarjini mai cika idanu yay mata. Amma saboda tsabar ƙarfin halinta da taurin zuciya sai ta cigaba da masifar kamar zata cinyesa ɗanye. Harda cewa sai tayi maganin rawar kansa a gidan. Sosai su maigadi ke'a rikice. Shiko yanda ya dake sai ma ka ɗauka ba dashi takeyi ba. Dan tuni ya maida hankalinsa ga wayarsa...
       “Wai ya akayi ne?”.
   Mommy da hayaniyar Lulu ke zuwa mata cikin kunne sama-sama tun ɗazun ta fito dan ganema idonta ta faɗa tana ƙarasowa. Cikin masifar nan tata ta juya tana faɗama Mommyn abinda yay mata. Dai-dai nan shima Daddy ya fito da alama ma wanka ya fito dan bathrobe ce a jikinsa. Mommy ta juya ga Uncle Smart, sai dai kafin tace masa komai ya shiga gaidasu ita da Daddyn da sai yanzu Mommy da Mawaddat suka lura da shi cike da girmamawa kamar bashine ya watsar da al'amarin Lulu ba tun ɗazun. Cikin kulawa suka amsa masa, Daddy ya dubesa cikin alamar sanyin yanayin daya riskesa a kwanaki biyun nan akan halin da Lulu ke ciki tare da faɗin, “Ya akai ka makara haka Aliyu Hydar?”.
        Bai iya ƙarya ba ko kwana-kwana. Sak yake shi akan komai. Dan haka kai tsaye ya ce, “Alhaji na ɗan biya ta school ɗin ƙannena ne dan sanin halin da suke ciki akan karatunsu tunda naga kwana biyu ba wani waje nake zuwa ba”.
      Lulu zatai magana a hargitse Daddy ya katseta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login