Showing 159001 words to 162000 words out of 163036 words
yayinda wanin sashe na zuciyarsa ke matuƙar jin tausayinta da jin haushin kansa mai tsananin gaske. Sai da ta shafe kusan minti biyu tana fisge-fisgen kafin ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya tana mai ambaton sunansa da kausasashiyar muryar ta data gama ɗashewa cikin roƙo da magiyar ya barta, karya aikata. Kalamaine data dinga roƙonsa da su a lokacin da ya gaza amsa mata dan yakai fagen da bazai iya fahimtarta ba a lokacin. Goshinsa ya haɗe da nata yana ambaton, “Kiyi haƙuri Mawaddat kiyi haƙu......”
Bai kai ƙarshen kalma ta ƙarshen biyar ɗin ba ta ƙwalla wani masifaffen ƙara da zabura........✍️
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣8️⃣
.........Aunty Khadijah bata ma san sanda ta afko bayin ba. Da ƙyar suka iya riƙe Lulu su biyun, alamar ya fita aunty Khadijah tai masa, badan yaso ba ya fitan ita kuma ta shiga cikin ruwan ta riƙe Lulun da jikinta ke karkarwa sosai. Ta gama fahimtar minene matsalar Lulun, ko muryar Smart ɗin bata son ji sam dan firgitata take sake yi, dan haka ta fara mata magana cikin lallashi da kulawa, sannu a hanakali yanayin nata ya shiga canjawa, ta koma laƙwas sai kuma ta saki kuka da riƙe aunty Khadijah. Cigaba da lallashinta Aunty Khadijah tai da canja mata ruwa har sai da ta tabbatar ruwan zafin yay mata ratsawar da zai iya bata nutsuwar da take buƙata sannan ta fito ta ɗaukar mata kaya. Smart na zaune ya dafe kansa bayan ya gama ƙarfin halin yaye bedsheet ɗin saman gadon ya canja da wani. Shiya ɗakko kayan ya bama aunty Khadijah ta koma bayin, babu jimawa sosai sai gata ta fito riƙe da Lulu da ke takawa da ƙyar tana hawaye. Ya nufosu da niyyar taimaka musu aunty Khadijah ta girgiza masa kai, dole yaja ya tsaya badan yaso hakan ba. Sai matsanancin tausayinta da ke ratsa shi ganin yanda take tafiyar a wahalce duk da dama rabin jikinta a jikin aunty Khadijah yake. Saman gadon ta kwantar da ita sannan ta ɗaura mata ruwan data riga ta haɗama alluran barci a ciki masu ƙarfi. Cikin sa'a ruwan baifi mintuna bakwai da fara shiga jikinta ba barci mai nauyi ya ɗauke ta, ajiyar zuciyar da take saukewa a jajjare kawai kake iya ji.
Aunty Khadijah ta sauke numfashi da ajiyar zuciya tana kallonsa, yanda ta kafesa da idanun ya sashi kasa jurewa yay ƙasa da nasa. Zama tai a bakin gadon da masa nunin ya zauna shima. Zaman yay kamar yanda ta buƙata.
“Aliyu ka kwantar da hankalinka abinda ya faru bashi bane dalilin shigarta a wannan halin.”
Da sauri ya ɗago ya kalleta, cikin nuna mamaki ya ce, “Amma aunty kafin yau ban taɓa ganinta a irin wannan yanayin ba”.
“Bazaka gantaba dama, saboda ba'ai mata abinda zai kaita ga shiga irin yanayin bane. Dan akwai ɓoyayyen al'amari a rayuwarta. Yanayin da ta tsinta kanta a ciki yayi kama da na mutanen da aka taɓa ma fyaɗe....”
“Fyaɗe!..”
Ya maimaita kalmar da wani irin yanayi mai kama da almara. Ko ruɗani.
“Tabbas fyaɗe Aliyu, shiyyasa a wannan gaɓar abinda ya faru a baya ya shiga tariyo mata kansa, dalilin da yasa ta firgita kenan har tana neman rasa tunaninta”.
Kai ya shiga girgizawa da sauri. Duk da yau ne karansa na farko da fara mu'amulantar mace bazai yarda da hakan ba. Shi mai ilimi ne, sannan mai zurfafa bincike akan abubuwan da yake buƙatar sani tun bai kai haka ba. Ya nema sani matuƙa akan mace da suffofinta. Taya ma zai yarda waninsa ya aikata abinda shi shaida ne akan zama na farko a yau ɗin nan bayan wasu awanni kaɗan. Sake girgiza kan nasa yay da janye idanunsa da ya zuba akan Mawaddat ya maida su ga Aunty Khadijah. “Aunty mudai yi wani tunanin ba wannan ba, Mawaddat she is virgin hundred percent”.
Cikin mamaki ta ce, “Aliyu kasan mi kake faɗa kuwa?”.
“Tabbas wannan shine gaskiya. Na baki kowace irin dama kuma ta tabbatarwa ta hanyar aikin ki”.
Sosai hakan ya nema saka Aunty Khadijah a ruɗani, amma kuma tabbas ta san Aliyu akan gaskiya da furtata, sannan ita kanta a yanayin data ga Mawaddat ya tabbatar mata yau ta fara sanin ɗa namiji a rayuwarta, dama tana son sake tabbatarwa ne. Miƙewa tai tsaye ta fara kaikawo kusan na minti guda, sannan ta juyo tana kallon Smart da ya sake zubama Mawaddat dake barci da sauke ajiyar zuciya har yanzu idanu. “Aliyu indai hakane kuwa akwai ɓoyayyen al'amari ƙunshe da rayuwar Mawaddat. Tunda har ka tabbatar min na yarda da kai, amma tabbas an taɓa harar rayuwarta da wannan siffar kuma lamarin bai kasance ƙarami a gareta ba, dan ta ajiyesa a zuciyarta da har takai yake iya firgitata irin haka. Ba kowa ne ake kai masa harin fyaɗe ya ke tsintar kansa a irin matsanancin firgicin nan ba har sai ya tabbata an aikata masan. Shiyyasa kaji nace maka an aikata matan da farko”.
Kansa yake jinjinawa cike da nazarin kalamanta. Tare da haɗasu waje guda da wasu ɗabi'un Lulu da mabanbanta kalamanta a wasu lokuta. Idan ya ɗauki kalamanta na safiyar yau da ta tabbatar masa zata iya halakashi kamar yanda ta kashe wancan, hakan na nufin abinda Aunty Khadijah ta faɗa tabbas dole ne ya zama gaskiya, sai dai ba'a cimmata ba. Idan aka ɗauki yanda take kallon maza, da yanda ta tsani duk wani da ya aikata fyaɗe da tsaiwar da take akan case irin hakan cikin zafi da zafafawa. Waɗan nan duk hujjojine abin kallo da dubawa. Maganar Ammah a randa ya kaita gidansu da take ce masa ya kusanta kansa da ita ya fahimci damuwarta, dan akwai ɓoyayyen al'amarin data fahimta game da ita a cikin hirarsu. Anya kuwa ma shaye-shayen yarinyar nan baida alaƙa da wannan al'amarin? “Oh my God!” ya faɗa a zahiri yana furzar da iska mai zafi.
Aunty Khadijah ta ce, “Ka kwantar da hankalinka Aliyu. Wannan damar gareka take na bincika ainahin gaskiya a yamzu. Dan inhar ta iya faɗar duk abinda ke a ranta tamkar mun yaƙi kaso sittin ne cikin ɗari na halin da take a ciki, in ba hakaba zakuyita fuskantar matsala ne kai da ita matsayin ma'aurata dan kaima zata dinga kallonka ne da wannan siffar a duk sanda ka raɓeta. Dan al'amarin ya matuƙar taɓa brain ɗinta da rayuwarta.”
“Insha ALLAH Aunty zanyi iya bakin ƙoƙarina akan hakan. Sannan ni kaina ina son sanin kowanne tsinanne ne wannan domin ɗanɗana masa fiye da azabar daya dasama ruhinta na tsawon lokaci. Sai dai ina roƙon alfarmar kar wanda yasan wannan zancen dan ALLAH”.
“Karka damu Aliyu aikina ne hakan. Akwai amana tsakanin likita da majiyaci, balle ma abinda ya shafeka muma ya shafemu. Kallon ɗaya daga cikin ahalinmu nake maka tamkar Ahmad. Haka itama Mawaddat tana da alaƙa damu mai ƙarfi. Dan haka in sha ALLAH a duk sanda kake buƙatar wani taimako ka nemeni”.
“Insha ALLAH aunty Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi”.
“Amin. Sai kuma kayi haƙuri dan yanzu koda ta farka gaskiya akwai daru, dole sai ka kauda kai dan itama ba daga gareta bane tun farko an dasa mata tsoron hakanne a zuciya. Dan ma kayi matuƙar yin farar dabarar kiran Ahmad ɗin kuje asibiti, da ace kace sai har zuwa safiya brain ɗinta zai iya birkita fiye da hakan. ALLAH dai ya rufa mana asiri yay mana maganin azzaluman mutane”.
Ya amsa mata da amin zuciyarsa na masa ƙuna. Da ga haka ta ajiye masa magunguna suka fito falon inda Ahmad ke zaune cikin damuwar daɗewar tasu. Dan a ƙalla sun samu cikakkiyar awa guda a ciki. Suna fitowa ya miƙe zumbur idanunsa akan Smart. Aunty Khadijah batace masa komai ba ta nufi hanyar fita tana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunta. Smart zaiyi magana Ahmad ɗin ya taresa da faɗin, “Please Mawashi ka gafarce ni!”.
“Akan me? Ahmad kaida ka taimakeni ka kawo min aunty Khadijah akan lokaci, ni ya kamata na nema afuwar taso ku da nai a daren nan”.
Kai Ahmad ya girgiza masa da cewa “Aliyu laifina ne, na aikata kuskure”.
Sosai ƙirjin Smart yay masifar bugawa, dan abinda Ahmad ke nufi daban shi abinda zuciyarsa ta kawo masa daban. Sai kuma yay saurin ture hakan a ransa ya zubama Ahmad ɗin idanu. “Mi kake son faɗa Ahmad, ka bani abuɗe kasan bana son kwana-kwana”.
Hannu Ahmad ya kai saman kansa ya shafa, sai kuma ya furzar da huci mai ƙarfi. “Na zuba abu a cikin FURAR nan ɗaya. Saboda ma an tabbatar min maganin nada ƙarfi yasa na saka ɗaya kawai, sai dai zuciyata taita angizani akan na ƙara ta yadda zaka kasa control ɗin kanka har sai ka tabbatar da abinda muke fata.”
Shiru kawai Smart yay yana kallon ƙasa hannayensa duka a cikin aljihun dogon wandonsa. Kamar bazaice komai ba sai kuma ya ɗago ya dubi Ahmad ɗin yay ƙaramin murmushi da sai ka ƙura masa ido zaka tabbatar yayi. “Baka jin magana Ahmad sam wlhy, ban san mi kake nufi zakai kenan ba ai da ban yarda munsha furar da ka kawo ɗin ba. Amma ka rubuta ka ajiye zan rama nima”.
Ba haka Ahmad yay zaton ji ba dan haka ya zuba masa idanu kawai yana kallonsa. Ɗauke kai Smart yay gefe da sake faɗin, “Ban san kallo malam kaje ka kai aunty Khadijah gida ta huta”.
Yanda Smart ɗin yayi duk sai Ahmad ya sake jin jikinsa yay sanyi. Sai dai dole suka fito dan dare yaja kusan ƙarfe biyu. Godiya Smart ya sakema aunty Khadijah tare da harar Ahmad da ke kallonsa har yanzu dan shi gani yake tamkar Smart ɗin ya shanye komai ne kawai a ransa dan ganin aunty Khadijah. Bayan wucewarsu ya rufe ko'ina da kashe komai. Ɗakin ya koma inda Lulu da aka sakama ƙarin ruwa take. Ya jima tsaye yana kallonta wasu abubuwa masu girma game da ita na sake hauhawar farashi a zuciya da ɓargonsa. Kafin ya lumshe idanunsa tare da ramƙwafawa kanta ya sumbaci goshinta da idanun nan da suka sha kuka yau da bakin tsiwar da ya tabbatar kona dare ɗaya ne dai ya mutu murus yau. “ALLAH yay miki albarka _Noorun Nisaaa_” ya ɗan ja sunan da hura mata iska akan idanunta yana murmushi mai sanyi ƙasan zuciyarsa cike da ɗunbin tausayinta...
Da ga haka ya miƙe ya nufi bedroom yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Jikinsa ya tsaftace. Koda ya fito maimakon kwanciya sallaya ya shimfiɗa ya fiskanci alƙibla domin miƙa godiyarsa ga UBANGIJIN talikai mai rahama mai jin ƙai. Sai gabannin asuba da ya fuskanci ruwan daya saka mata na biyu da Aunty Khadijah ta bari ya ƙare ya je ya cire shi ma. Zama yay kawai ya saka hannunta cikin nasa ya zuba mata ido, yanda take barcin da sauke numfashi a hankali lokaci zuwa lokaci takan saki ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa yake nazarta a kanta. Tun daga randa ya fara ganinta a airport da yaje ɗakkota har zuwa masifar da ya dinga ci a wajenta, aurensu da zaman sati uku da kwanaki huɗu yau cikon na biyar. Ya bata sunan HAWAINIYA da kan canja akowane lokaci da kuma kowane irin yanayi. Kai tsaye baka yanke mata hukunci akan kanta dan sanin ainahinta sai ALLAH. Wato duk bawan da kake kallo yana rayuwa akan kuskure ashe kai tsaye yanke masa hukunci da abinda idonka ya gani a kansa tamkar son zuciya ne. Duk wanda zai baka amsa a kanta zai ce maka she is bad girl ne kai tsaye, domin da wannan siffofin take bayyana kanta wa duniya. Dalilin shine haka aka raineta, haka ta tashi, da hakan kawai tai imani a matsayin gaskiya. “Lokaci yayi da zan san wacece ke Mawaddat? Wace irin turnuƙun ƙura kika tsallake a baya data gina miki rayuwa kamar haka? Wanene yaso lalata miki rayuwa? Miyasa mahaifinki ya nuna miki soyayya amma ya gagara tsayawa akan tarbiyyarki? Miyasa ahalinki sukai sakacin fuskantar rayuwarki na cikin wani ƙulli tun a gaɓar da ya dace ace sun fuskanta ɗin? Ina son sanin waɗan nan amsoshin da ga bakinki MATATA. na miki alƙawarin sake gina nagartacciyar rayuwar da zata fahimtar da ke tsakanin fari da baƙi koda sun gauraye a mazubi ɗaya da izinin ALLAH. In sha ALLAHU zan share miki dukkanin hawayenki na zuci dana bayyane da tafukan hannayena na maye gurbinsu da tarin farin ciki Mawaddatan'warahmah”. Motsawar da tai ya bama hannunsu damar sake matsewa cikin na juna tamkar mai jaddada masa ta amshi dukkan kalamansa itama. Hakan ya sakashi lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya...........✍️
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣9️⃣
.......A ɓangaren Alh. Sulaiman Garko yana barin wajen Dada Alh Baita ya kira a waya. Wanda ya shaida masa yana gida yau kam bai fita ko'ina ba. Ya tabbatar masa yana buƙatar ganinsu su dukansu a daren nan dan magana ce mai muhimmanci da shi. Babu musu Alh. Baita ya amsa masa tare da bashi address ɗin inda zasu haɗu. Sannan yay kiran su Hon. Nakowa suma. Cikin abinda baifi awa ɗaya ba suka haɗu a gidan hutawar Hon. Misau dake anguwar Farawa. Tsaf ya zayyane musu komai da suka tattauna da Dada, su kansu sun girgiza da jin wannan ƙulli. Hon. Nakowa ya ce, “Wato su waɗan nan na kula makirci a cikin jininsu yake. Yanzu shima shegen Yousuf ɗin nan ashe tsagerane a haka kamar na ALLAH yana wani sim-sim da kai. To anya kuwa Isma'il bai sanar masa sirrin dake a tsakaninmu ba kuwa?”.
“Abinda nai tunani kenan yasa ni nemanku da gaggawa. Dan in har zai iya irin wannan ƙulle-ƙullen kamar haka dan kada yarinyar nan ta auri ɗaya daga cikin kai da Tajuddeen to inaji a raina wannan taƙamar da hura hanci da Isma'il keyi nada alaƙa da ya sanarma yaron nan komai kuwa. Dan haka nake ganin plan B dole ne mu canja labarin da ga Isma'il zuwa Yousuf, hakan zai bamu damar jifan tsuntsu ɗaya da dutse biyu, sannan zamufi gigita rayuwar Isma'il ɗin da haukatashi”.
“Su kuma yarinyar da yaron fa?”.
Cewar Hon. Nakowa cikin zumuɗi. Duk da Alh. Sulaiman ya fahimci inda ya dosa, amma sai bai nuna masa a fuska ba, sai ma murmushi da ya saki kai tsaye ya ce, “Wannan aikin Dada zata ƙarasa mana shi. Bayan ta ɗauke ta daga wajensa sai muje plan c akansu ita da yaron, dan dama akwai tawa da shi a ƙasa”.
Nan ma sun gamsu matuƙa. Daga haka suka cigaba d tattauna abinda ya shafesu, musamman game da sabuwar alaƙar da suke shirin sake ƙullawa akan business. Har gabannin asubahi sannan suka watse.....
__________★
Yanda Smart yaga rana haka yaga wannan dare ko sau ɗaya bai rintsa ba har akai kiran sallar asubahi. Da kyar ya iya dauriyar fita massalaci. Ana idar da salla ya dawo gidan. Inda Lulu take ya sake komawa. Har lokacin tana a yanda ya barta bata farka ba. Yana tsaka da tunanin tadata ko ya barta har sai ta tashi da kanta kira ya shigo masa a waya. Yayi mamakin ganin Coach, amma sai ya ɗaga. Jin muryar aunty Khadijah saɓanin wanda yay tunani ya sashi sauke ajiyar zuciya tare da gaisheta cikin girmamawa.
Tambayar data jeho masa akan Lulu ya sashi kallonta, sai da ya ɗan furzar da iska sannan ya bata amsa da “Har yanzu bata farka ba dai”.
“Alhamdullah to karka tada ita, inasha ALLAH ina nan zuwa yanzu nan. Dan a yanayin da take a ciki bamu da tabbacin bazata sake tashi a firgicen ba. Hakanne kuma ba'aso da ga gareta”.
Ya gamsu, dan haka yayma Aunty Khadijah godiya ya na yanke wayar. Kwanciya ya ɗanyi a kan sofar ɗakin ya faɗa duniyar tunani, hakan ya Bama barci damar dinga figarsa kaɗan-kaɗan. Tsakanin wayarsa da aunty Khadijah baifi mintuna arba'in ba sai gata tazo. Sosai yaji daɗi da ƙara jin kimar waɗan nan bayin ALLAH. Bayan sun ƙara gaisawa ya fita ya basu waje. Cikin hikima ta tada Lulu wadda ta farka a firgicen kamar yanda Aunty Khadijah tai hasashe, sai dai Alhmdllh cikin ƙwarewar aiki ta nutsar da ita, tare da taimaka mata zuwa bathroom ta sake haɗa mata ruwa mai ɗumi. Shawarar sake gasa jikinta ta bata ta fito. Lulu da komai ke dawo mata dalla-dalla batai musu ba ta shiga ruwan zafin, sai da taji ya ratsata tako ina ta sake samun nutsuwa sannan ta tsaftace kanta ta hanyar wankan tsarki da shi da kansa ya koyar da ita a cikin karatunsu duk da dai dama tanayi makamancinsa bayan period, amma ko randa ya koya matan yasha harara dan yay mata bayani dalla-dalla ne. Ji take jikinta ya mata nauyi sosai, ga tauna da ƙasusuwata keyi. Bata son tuna abinda ya faru saboda ƙunar da zuciyarta ke mata. Da taimakon aunty Khadijah tai salla, bayan ta idar ta jima zaune shiru tana nazarin tushen faruwar komai na daren jiyan. Kamar wadda aka tsikara ta miƙe da sauri dan ta manta yanayin nata. Komawa tai da sauri ta zauna tana dafe kanta ta cije lips. Ƙaramar ƙarar da tai ya saka hankalin aunty Khadijah dawowa kanta. Ta nufota da sauri tana faɗin,
“Mawaddat yi a hankali banda garaje kinji”. Bata iya cema aunty Khadijah komai ba sai hawayen da suka silalo mata masu zafi. Cikin muryarta da ke a disashe har yanzu ta ce, “Aunty dan ALLAH ina son ki kaini gida”.
“Gida kuma Mawaddat?”.
“Eh aunty,