Showing 69001 words to 72000 words out of 163036 words
na ciki. Bayan wucewarsu Baba ma addu'a ya saka ayi ya sallami kowa, sai dai banda Daddy da Uncle Yousuf da Smart. Amma har Lulu yace taje. Koma ba'ace taje ɗin ba batai niyyar zama ba, dan in har ta cigaba da zama a falon zata iya aikata ɓaranɓaramar da komai zai tashi a wajen....
Tambayoyi na mutuntawa Alhaji Sufi Ado Garko ya sake yina Smart, shiko ya amsa masa cikin nutsuwa kuma kansa tsaye. Hakan ya saka Uncle Yousuf jin farin ciki, sai dai umarnin Baba na ƙarshe akan Smart na cewar ya je ya sanar ma iyayensa suzo a cikin satin nan ya girgiza Daddy matuƙa har ya ɗan waro ido sai da Uncle Yousuf ya zunguresa. Shi kansa Smart maganar ta girgiza shi, dan da ƙyar ya iya haɗiye yawu ya gyaɗa masa kai.....
🤣Wayaga cakwakiya mai taurari. Kai Smart ka ɗauka abin wasa ne kenan, ai gashi nan Baba yay maka ɗaurin huhun goro 🤪🚴.
★★★.....
“Kai Yousuf bazai yiwu ba. Ina bazan taɓa yarda Mawaddat ta auri yaron nan ba gaskiya. Da ace nasan wannan shawarar ka yanke dana kwaɓeka tun farko. To gashi nan DAGA WASA KARAMAR MAGANA NA NEMAN ZAMA BABBA. Dama kai kana tunanin yin wasa da hankalin Baba ne?”.
Daddy ne mai wannan magana cikin tashin hankali da damuwa wa Uncle Yousuf da ke driving. Cikin dakewa da nuna alhini kamar gaske shima Uncle Yousuf ɗin ya ce, “Yaya sam ba haka nai tunanin kasancewar al'amarin ba fa. Banyi zaton zaice Aliyu ya turo magabanasa da wuri kamar haka ba. Shima fa yaron da ƙyar na shawo kansa ya yarda zai mana aikin. Ni yanzu ma gaba ɗaya kaina ya kulle na rasa mima ya kamata nayi”.
“Faɗama Baba gaskiya mana. Dan nasan Mawaddat bazata taɓa yarda ta auri drivern ta ba. Kai koni ma hakan bai min ba Yousuf. Ina impossible kamar yarinyata mai daraja irin Mawaddat ta ƙare da auren drivern ta, sai kace wani almara ma”.
Ɓacin raine sosai ya dunƙule zuciyar Uncle Yousuf, cikin matsanancin takaici yake duban Yayan nasa, sai dai baiyi magana ba ya sake maida kansa ga titi har suka isa gida. Shima Daddyn ya fahimci ran ƙanin nasa ne ya ɓaci, amma bai fahimci ainahin miya ɓata masa ran ba. Suna isa gida Uncle Yousuf baiko fita a motar ba yay shirin juyawa. Da mamaki Daddy da ke kallonsa ya furta, “Ya zaka koma kuma bamu gama magana ba Yousuf”.
Idanu Uncle Yousuf ɗin ya rumtse sai kuma ya buɗesu akan Daddy. “Yaya to wace magana kuma ta rage? Kace bazata auri driver ba, shike nan magana ta ƙare ai, dan ni kam iya abinda zanyi nayi k....”
“Kaga sakko muje ciki wannan ba maganar mota bace.” kamar zai ce a'a sai kuma dai yabi umarninsa ya fito. Falon baƙi suka nufa, dan in har zasu maganarsu ta sirri sunfi buƙatar zuwa can kasancewar babu wanda zai iya jinsu. Suna shiga Daddy ya ce, “Yousuf ka fahimceni mana. Ni fa ba ina nufin bakai ƙoƙarinka bane ba. Amma Please ka duba mana. Yaron nan fa driver ɗinta ne....”
“Shi driver ba mutum bane? Ko kuwa shi dama mai arziƙi ALLAH ya tabbatar masa shine mafifici ga kowa a duniya da da lahira?. Gaskiya yaya ka fara bani tsoro, matuƙar tsoro ma kuwa. Wai kai kuwa wani irin so mara fasali kake ma Mawaddat? Ko kai ne zaka aure ta....”
“You'r vary stupid Yousuf! Wane irin banzan magana ne wannan?”.
“Dolene na faɗi hakan ai Yaya. Dan al'amarin naka ya fara wuce makaɗi da rawa kuma. Idan ka manta shekarun Mawaddat ashirin da huɗu har da watanni balle kace bata isa aure ba. Tun tana shekara ashirin aka saka mata ranar aure ka goya da bayanta al'amarin ya wargatse. Idan kace wancan yana da wani aibu shi wannan minene aibunsa? Dan kawai ya kasance driver mai neman halaliyarsa? To wlhy bakai ya kamata kace Mawaddat tafi ƙarfin Aliyu ba. Aliyu ne ya kamata yace yafi ƙarfin Mawaddat kodan halin da take a ciki wanda kai ne gaba-gaba wajen zama silarsa. Kai ne ya cancanta kai ƙoƙarin ganin ka gyara ko neman hanyar da zata gyaru ta zama cikakkiyar mutum kafin kowa amma baka ƙoƙarin yin hakan sai sake bata damar ma da zatafi yanzu lalacewa kake yi. Ina ji maka tsoron ranar da Baba zai fahimci halin da Mawaddat take a ciki, in dai maganar Aliyu ce kuma na bari.....”
Da sauri Daddy da jikinsa yay sanyi ya riƙoshi. “Kaga kayi haƙuri auta.”
Batare da Uncle Yousuf ya yarda ya juyo ba ya ce, “Kai zan bama haƙuri ai Yaya. Dan na shiga hurumin daba nawa ba. Na manta Mawaddat ƴarka ce kai ɗay....”
“Shiiii! Ni ba haka nake nufi ba auta. Amma tunda zuciyarka ta kaika ga hakan amin afuwa. Ni kaina wani lokacin yanda nake ɗaukar al'amarin Mawaddat na bani tsoro. Amma dan ALLAH ka tayani da addu'a. Sannan kayi haƙuri ka cigaba da duk yanda kake ganin shine dai-dai. Ba Mawaddat ba ko ni ka isa dani ai ko. Wlhy a duk sanda kake faɗamin gaskiya akan lamarin Mawaddat fuskar Mahaifinmu nake gani akan fuskarka, yayinda muryarka kan juye min tamkar ta mahaifiyarmu. ALLAH yay maka albarka auta. Ina alfahari da kai a matsayin ɗan uwana da ga kai har Kareema. Wlhy itama fahimtata ne kawai batayi tun farko, amma tana da wata daraja da kima mai girma a gareni”.
Tsira masa idanu kawai Uncle Yousuf yay kalaman nasa na bashi mamaki da al'ajabi. Anya kuwa Yayan nasa bashi da Alhaju? Dole ne yace haka, dan yau wai bakin Yayansa ne ke yabon Aunty Kareema. Kai anya kuwa dai.....
Kamar Daddy ya fahimci abinda ke a ran ɗan uwan nasa ya saki murmushi mai ciwo. “Mamaki kake ko auta? Kana mamakin yabon Kareema a baki na. Humm bazaku gane bane, dan tun farko bakubi hanyar da zaku gane ɗin bane shiyyasa kuke min kallo irin wanda bashi ya kamata kumin ba. Kaje kawai abinka. Na kuma maka alƙawarin bazan sake saka baki ba akan al'amurin auren Mawaddat dan kai ne ubansu dama ni ɗan kallo ne. Sai dai a wannan gaɓar ina tunatar da kai suma su ƴan biyu ya kamata ka sakasu suyi aure fa. Kaje ALLAH ya huta gajiya”. Da ga haka Daddyn ya fice idanunsa taf da ƙwalla. Da kallo kawai Uncle Yousuf ya bisa zuciyarsa na kaikawo a ƙirji. Dan ba ƙaramin ratsa masa zuciya kalaman ɗan uwan nasa sukai ba yau......
★★....
A ɓangaren Lulu da bata san hukuncin da Baba ya yanke ba suna fitowa a street ɗin gidan Baba a gadarance ta cema Smart “Malam tsaya da motar nan”. Kamar zai shareta sai kuma ya gangara dan yanzu ba shirmenta bane a gabansa. Abubuwa ne masu yawa ke masa kaikawo a zuciya. Fita tai ta koma baya, bai ce komai ba ya sake tada motar suka cigaba da tafiya. Sun ɗan ƙara nisa motar shiru babu mai magana, shi hankalinsa ya rabu biyu, wani a tuƙi wani a tunanin al'amarin da ya faru yanzun nan. Ita kuma hankalinta nakan tab... Ɗinta ne tana aiki har suka iso. Ita ta buɗe da kanta dan hankalinta nakan abinda takeyi, sai da ta zura ƙafarta ɗaya waje zata fita sannan tai magana batare data kallesa ba. “Malam ina fatan baka ɗauki abinda ya faru a gidan Grandpa wani abu ba. Idan kuma ma ka ɗauka ɗin to ka ajiyeshi a motar nan karma ka koma gidanku da shi dan zai zame maka dakon wahala ne, dan ba Mawaddat ba ko mai aikin gidanmu tafi ƙarfin nunaka matsayin abin sonta balle ni, ka cigaba da zama matayinka na yarona kana amsar albashinka hankali kwance a samu na koko da ƙosai”. Ta ƙare maganar da balla masa uwar harara da jan tsakin tabbatar da gargaɗinta ganin yanda ya wani tsareta da idanu ta cikin mirror. Kansa ya ɗan girgiza bayan ficewar tata, sai kuma ya saki wani shegen murmushi da cije lips ɗinsa yana mai kai hannu ya shafa tattausar sumar ƙasumbarsa. A hankali ya furta, “Kema lokaci yayi da zaki fara cin koko da ƙosan ai ƴar gidan madara”. Ya ƙara cije lips ɗinsa da kashe ido ɗaya....
(Makiri Smart. Mi kake shirya mana ne🥱😨).
______________________
“Dad! Wlhy wannan abun ƙarya ne shiri ne kawai. Amma babu wata soyayya a tsakanin Mawaddat da shi. Drivern ta ne fa, hasalima Alhaji Yousuf dani muka zauna muka roƙesa akan ya tuƙata saboda muna son ya bibiyar mana al'amarinta akan s.....”
Sai kuma yay shiru tuna ɓaranɓaramar da yake neman yi ga kallon da mahaifin nasa ya kafesa da shi. “Ya ka dakata? Ƙarasa mana akan mi?”.
“No Dad share. Wannan bashi bane mai muhimmanci, musan gaskiyar zancen da tabbatar ma Grandpa shine nafi buƙata a yanzu. Idan ba hakaba wlhy sai na tada hankalin kowa a family ɗin nan dan Mawaddat kaɗai nake so, da ita kawai nake buƙatar zaman aure”.
“Tajudden ka kwantar da hankalinka, in dai Mawaddat ce babu fashi kai ne mijinta. Yaron nan kuma nima na tabbatar sakashi akai ko kuma shine ya sa kansa. Amma barni da shi, zan tabbatar masa wanene ni dan naga yana son yin wasa da wuta ne a tafin hannunsa batare da ya sani ba. Kaje ka cigaba da shirye-shiryen aurenka nan da kwanaki takwas”.
“Amma miyasa ba gobe ba Dad? Ni gobe nake so Friday a ɗaura. Next Friday ai shagalin biki na nunawa Sa'a ta tare a gidana.”
“Ka ɗauka yanda ka tsara labarin, haka za'a bugashi a jaridu da mujallu a yammacin gobe cewa Tajuddeen Sulaiman Sufi Garko ya zama angon Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi”.
“Thanks You Dad”.
Tajuddeen ya faɗa cike da zumuɗi yana mai rungume mahaifin nasa, dan yasan baya magana bai tabbatar da ita ba......
Gaba ɗaya tattaunawar ɗa da mahaifin acikin kunnenta ne, dan tun farawarsu ta iso ƙofar falon bisa umarnin auntynta da ta aikota. Da sauri ta tallafe tray ɗin dake hanunta mai ɗauke da kayan motsa baki jin zai suɓuce mata. Juyawa tai da sauri zuwa apartment ɗin yayarta cikin sassarfa kamar zata faɗi ga idanunta na kwarar da hawaye masu zafin gaske........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣0️⃣
.......“K! K! Lafiya kuwa naga kin dawo min da shi haka kamar ma wadda take a firgice?”.
Ƙasa ta dangwarar da tray ɗin tare da faɗawa jikinta ta sake fashewa da kuka. “Aunty Abasiyya wannan karon ma zan rasashi. Dama ashe abinda ake ƙullawa a gidan nan kenan amma baki faɗamin ba kika barni inata shirme na?” ta ƙara fashewa da kuka. “Mtsoww! Wai nikam Ramlah yaushe ne zaki hankali? Kimin bayani danni ba fahimtarki nake ba. Kinga tashi zaune”. Babu musu Ramlah ta tashi, ƙyaƙyƙyawar yarinya kuma ƴar gaye. Bata damu da share hawayen da suka gagara tsaya mata ba, ta ce, “Aunty Abasiyya zaki cemin baki san shirye-shiryen auren Tajuddeen ake ba a gidan nan kuma da mayyar yarinyar can dai”.
“What! Auren Tajuddeen fa? A gidan nan kuma ban sani ba? Lallai Alhaji ya sake zama abinda ya zama. Wlhy Ramlah sam ban san da zancen ba, sai dai tabbas naga anata wani ƙus-ƙus tsakaninsa da matarsa na munafunci tun jiya, yau kuma ya ɗauketa suka fita sai dai ban san ina sukaje ba”.
“To Aunty babban gida sukaje, dan inaga Baba ya dawo.....”
Ta kwashe kaf abinda taji Tajuddeen da babansa na tattaunawa ta sanar mata. Tare da faɗin, “Aunty dan ALLAH ki taimake ni, wlhy idan na ƙara rasa Tajuddeen a wannan karon zan iya rasa rayuwataa gaba ɗaya ina sonsa matuƙa fiye da yanda nake son kaina”.
“Hummm Ramlah kenan, badan nasan minene zafin soyayya ba da nace baƙya kishina. Ina matsayin yayarki uwa ɗaya uba ɗaya amma kina son ɗan kishiyata da bata taɓa ƙaunata ba a gidan nan, da ace ma tanada dama da tuni ta kawar dani a duniya. Gaskiya wannan soyayyar taki bataimin adalci ba. Sai dai bazanƙi taimakonki ba, dan nima hakan zai taimakeni wajen ƙuntata rayuwar Hajiya Turai. Dan haka ki kwantar da hankalinki, yanzun nan zan warware musu ƙullin nasu ta inda basu taɓa zato ko tsammani ba.”
Cike da ɗoki Ramlah ta ce, “Aunty mi zakiyi?”.
“Jira ki gani”.
Ta faɗa tana janyo wayarta. Daddanawa tai takai kunne tare da miƙewa ta shige ciki tana faɗin, “Baba barka da rana.......” iya abinda Ramlah taji kenan.....
★ Alhaji Sulaiman kam da basu san Ramlah ƙanwar amaryarsa da take riƙo taji tattaunawar tasu ba tuni Tajuddeen ya fice da waya a kunne yana waya da telansa kan ya jirashi a shago yanzu zai zo da ɗinkin ujila... Da kallo Alh. Sulaiman ya bisa yana wani murmushin mugunta. Shima ya kai wayarsa kunne. Bugu ɗaya Malami ya amsa da ga can. Batare da ya amsa gaisuwar Malamin ba cikin bada umarni ya furta, “Yaron dake mana aiki a gidan Isma'il Jiƙamshi ina buƙatarsa”.
“Angama ranka ya daɗe”.
Malami ya faɗa cikin tsantsar girmamawa tamkar yana a gaban ubangidan nashi ne.....
★★......
Alhaji Sufi Ado Garko da ke zaune a falonsa na baƙi har yanzun, dan bayan fitowa sallar la'asar ya sake wasu baƙin da suka sake rikita masa lissafi. Ba kowa bane face tsohon gwamna sannan babban ɗan kasuwa M Atik Kumo mahaifin MM Atik Kumo da tawagar abokansa uku neman izini wa ɗan nasa fara neman soyayyar Mawaddat. Sun gama masa bayanin kenan ya tabbatar musu da abinda ya faru game da kawo wanda Mawaddat ke so a yau har ma sun basa damar turo magabatansa suka masa godiya da bada haƙuri dan mahaifin MM Atik mutumin kirki ne. Ya fahimci bayanin Baba ya kuma gamsu suka rabu cikin girmama juna dan Baba ya kasance tamkar uba ga duk wani ɗan siyasa to. Bayan fitarsu ne yana ƙoƙarin tashi ya shiga ciki dan ya huta da hayaniyar da ya sha kiran matar ɗansa Alh. Sulaiman ya shigo masa. Bai kawo komai a ransa ba dan shi surukansa tamkar ƴaƴa suke garesa. Bayan sun gaisa tai masa barka da sauka da yaya jiki tare da bada haƙurin rashin zuwa tarbarsa saboda batajin daɗi ne. Ya gamsu da abinda ta faɗa tunda tabbas bai ganta ba a cikin gidan dan haka ya saka mata albarka. Ɗan jimm da tai ya sakashi fahimtar akwai wani abu, dan haka ya tambayeta. Sai da ta sake kwantar da murya cike da kissa ta zayyano masa dukkan abinda ƙanwarta ta tabbatar tajiyo, sai dai tace itace taji ba ƙanwar tata ba. Ta kuma kira ta faɗa ne dan kar abinda zasuyi ɗin ya taɓa kimar Baba da Family ɗin. Amma dan ALLAH bata son kowa yasan ita ta faɗa gudun abinda zaije ya dawo. Murmushi Baba ya saki irin na manya. Ya sake saka mata albarka sannan sukai sallama. Yasan Sulaiman zai aikata abinda ma yafi hakan, kuma shima yayi tunanin wani abun zai iya ɓullowa game da hukuncin nasa. Sai dai abinda ya bashi mamaki mi yake faruwane haka maneman Mawaddat ɗin keta karakaina a wannan gaɓar? Ko dai rawar data taka ne game da shari'ar mutumin nan ta kwanan nan data ɗauki hankalin mutane da yawa ce? Dan duk da baya ƙasar kunnensa da idanunsa na a Nigeria ɗin. Yafi zaton hakan shiyyasa bai ɓata lokaci wajen zurfafa tunani ba. Sai ma ya dannama Uncle Yousuf kira dan ya gama tsara kafin Sulaiman ya ƙulla abinda yake tsarawa shi zai tabbatar masa wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi......
★★.....
Sosai mamaki ya dabaibaye Uncle Yousuf da ke sauraren Baba. Dan ya masa bayani ne akan zuwan su M Atik Kumo kafin hukuncin da ya yanke a yanzu-yanzu saboda labarin da ya samu na shirin ɗansa da jikansa. Cikin girmamawa da godiya Uncle Yousuf ya tabbatar masa yanzu nan zai tura a isar da saƙon in sha ALLAHU. Suna yanke wayar kuwa yay kiran abokinsa Coach ɗin su Smart Abdull-Hameed, wanda ta sanadinsa ya fara sanin Smart ɗin dama. Tun yana waya da Hameed ɗin kiran Yayansa (Daddy) ke shigowa, bai ɗaga ba har sai da ya kammala da Hameed ɗin. Wani kiran ne ya sake shigo masa, ya ɗaga yana kaiwa kunne da faɗin, “Yaya irin wannan kira lafiya dai ko?”.
“Inafa lafiya Yousuf! Wai kaji suma su M Atik Kumo sunzo nemawa ɗansu izinin neman Mawaddat. Anya abunnan na lafiya ne? Ni bama wannan ya damen ba, dan M Atik mutumin kirki ne, ɗan nasa ne kawai sai a hankali, dan wlhy da ace ya kasance mutumin kirki kamar mahaifinsa da hankalina zaifi kwanciya da aura masa Mawaddat fiye da yaron nan daka kawo....”
Cikin gatse Uncle Yousuf ya ce, “To kodai a bama ɗan M Atik ɗin dama kawai, tunda shi dai ai ba wani abu ya taɓa aikata mana ba. Sannan a a bayyane ban taɓa jin ance ga aibun yaron ba...”
“No no no Yousuf bar wannan maganar kai dai. Dan wlhy ina gama waya da Baba yanzu na ɗan fara bincike kan yaron wajen wani aminina al'amarin babu daɗin ji, dan akuyace lulluɓe da fatar kura bai gado uban nasa ba. Kayi haƙuri bakwai kushe yaron nan Aliyu nake ba. A'a kawai ina