Showing 33001 words to 36000 words out of 163036 words
tare.... Gaba ɗaya zuciyar Smart ta sake jagulewa da takaici, dan duk abinda Lulu da Nadiya ke tattaunawa yana jinsu batare da su sun lura da shi ba. Shigarsu da kusan mintuna uku sautin kiɗa ya fara tashi kaɗan-kaɗan saboda rufe windows da sukai duk dan kar kiɗan ya fita wa mutanen anguwa. Kansa ya ɗan dafe yana mai ambaton sunan ALLAH, gaba ɗaya ma ya rasa miya kamata yayi, duk da yazo nan ɗinne da burin ganin abokan sheɗanar tata da kuma hanata shan komai. To amma ta ina zai fara ma?. Ya kwashe kusan mintuna ashirin yana ƙullawa da kwance ta yanda zai shiga wajen.... Ƙarar hayaniya da ta fara tasowa kaɗan-kaɗan da ga cikin falon ta maidosa da ga dogon tunanin mafita da ya tafi, ajiyar zuciya yaja kamar wanda aka farkar da ga barci tare da tsurawa ƙofar idanu. Wasa-wasa hayaniyar ta daɗa karfi har yana iya shaida muryar Lulu saboda tsayawar ƙarar sautin kiɗan da ke tashi, da alama sun kashe ne ko wata matsala ta faru. Falon ya nufa da sauri batare da tunanin komai ba ko neman izinin ya tura ƙofar ya shige, yanda ya gansu a yamutse ga Lulu na ɗurama wani hamshaƙin Alhaji zagi har tanayi kamar zata tsole masa ido da ɗan yatsa ya sashi yin turus, mamaki ne ko takaici oho baima sani ba, kayan shaye-shayene da na ciye-ciye ko'ina a barbaje, yayinda alhazan nan guda huɗu da ya shaida fuskar biyu a cikinsu kasancewarsu wasu manyan ƙusoshin attajirai kuma ƴan siyasa masu faɗa aji a garin na kano ɗaya ke tsaye cikin fusata kamar zai daki Lulu, sauran ukun na zaune sun zuba mata ido harda wanda take zagin da shi fuskarsa ma ƙawace take da murmushi kamar bashi akema tujarar ba. Kalaman Lulu ne na ƙarshe-ƙarshe da kukan da ta fashe da shi ya dawo da shi hayyacinsa.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣0️⃣
........Cikin kuka da dafe kanta tana ɗan layi alamar ta fara shiga maye ta ke faɗin, “Wlhy! Idan baka fita sabgata ba sai na keta maka rigar mutuncin tufafi da mutanen gari ke kallonka da shi, dan dama shi kaɗai ya saura gareka. Nace banayi! Banayi wai na minene wannan takura duk inda na saka ƙafa kana biye dani, shine yau harda bani wine saboda kai tsinanne ne, ka taɓa ganin na sha wine ne duk rashin ji na azzalumi!! Shin wai ku kuna ɗaukar duk macen da ke shan wannan abubuwan dan bama kanta farin ciki ita ɗin ƴar iska ce ko me? Manyan banza manyan kawai, ku gama hura hanci ga al'umma ku dawo bayan fage kuna lalata musu tarbiyyar yaransu. Ka sani har gaban abada bazaka taɓa samun wannan jikin ba, bama kai ba duk wani maye sai gani sai hange dan ni ba mazinaciya bace, bar ganin ina wannan rashin jin nasan ciwon kai na wawa kawai da ƙi ƙ.....” ta kasa ƙara sawa saboda shuuu da tai zata faɗi. Da sauri Nadiya ta tarota. Fisge jikinta tai tare da ɗagowa gaba ɗayanta kan ƙafafunta ta ɗauke fuskar Nadiya da mari haggu da dama.. A fusace Alhajin nan da ke tsaye tun ɗazun cikin ɓacin ran zagin da Lulu kema abokin nasa yayo kanta. Hannu ya ɗaga zai kwasheta da mari shima, sai dai cak ya tsaya jin an riƙe masa hannu ta baya. A karo na farko duk wanda ke'a falon ya farga da shi. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Alhajin da ke faman huci. Idanu ya lumshe cikin girgiza kansa da faɗin, “Haba kai kuwa ai babba babba ne, ba'asan namiji kuma da faɗa da mace ba. Bakaga abokinka yanda ya nuna mazantaka ba? Tunda kun gama zubar da kimarku garesu banga abin tada jijiyar wuya ba idan irin haka ta taso a tsakaninku ai......”
“Kai kuma a matsayinka na ubanwa anan?”.
Maimakon amsa sai ya ƙara tsaresa da idanunsan nan masu kwarjini da suka gama ƙwarewa a kallo mai girgiza zuciya cikin nuna gargaɗi (Na macizai inji Lulu😂). Sakin hannun Alhajin yayi, kafin cikin yanayin nan nasa a daƙile da kowa ke ɗauka girman kai ya ɗage kafaɗunsa da ɗan taɓe lips ɗinsa. “Sanin ɗan waye ni bazai maka amfani ba, idan dani kake son sani sai na baka amsa da cewar drivern ta ne”.
“What?! Driver fa?!!. Ubanwa to ya baka damar shigo mana nan har da tsoma baki a cikin abinda bai shafeka ba?”.
Shi ba mai yawan magana bane, dan haka maimakon amsa masa a yanzun ma sai kawai ya zuba masa ido. Hon. HD Nakowa sai ya sake fusata. Magana zai sakeyi cikin fusata Alhaji Ɗan-kande Baita ya dakatar da shi.
“Kaga HD please it's ok mana. Kai ɗan saurayi jeka kawai waje ka jirata nan ba huruminka bane ba”.
Wani banzan kallo Smart ya watsa musu su dukan, sai dai baice komai ba ya juya ga Lulu da ke zaune a kujera sharɓe tanata surutai da zagi har yanzu. Hanunta kawai ya fisga ta miƙe, batare da wani binta a hankali ba ya jata tana turjewa sukai waje. Da ƙyar ya iya kaita har motarta, dan haka ta maido da zagin da take ma Hon. Babale Misau kansa. Hakan bai damesa ba, sai ma rufeta da yay a motar ya koma falon ɗaukar handbag ɗin ta dan key ɗin motar na ciki....
“Ban yarda da wannan yaron driver bane ba, dan haka ina son a binciko min ɗan uban wanene shi a faɗin garin nan na kano”. Hon. HD Nakowa ne ke faɗa dai-dai Smart na sake shigowa falon ɗaukar tarkacen Lulu. Nunawa yay kamar baiji mi Hon. Nakowan ya faɗa ba, ya nufi handbag ɗin da ya gani ɗazun a hanunta da takalmanta masu azabar tsini ya kwashe ya sake juyawa ya bar falon ko kallo basu ishesa ba.....
Gotawarsu kaɗan da gidan wata dalleliyar mota ta iso ƙofar ita kuma. Horn yay aka buɗe masa. Yanda sautin kiɗa ke tashi a cikin motar zai baka tabbacin yana cikin nishaɗi matuƙa. Duk da yasan taro ake a gidan nasa hakan bai hanashi jin mamakin ganin wasu manya-manyan motoci guda uku ba, bawai ƴammatan bazasu iya zuwa da motocin bane, a'a kawai dai yasan sun musu girman da bazai yiwu ace sune suke hawansu ba. Cikin kai-kawo zuciya ya fito yana ƙara ƙarema motocin kallo, cikin ɗan basarwa irin na masu akwai ya ɗage kafaɗu da ɗan taɓe baki yay ciki abinsa ransa fal nishaɗi yau zai haɗu da mafarkinsa. Yayi alƙawarin sai ya ɗanɗani yarinyar nan dan ta tsare masa ko'ina na zuciya tun a randa ya ganta. Da wani irin sauri yaja birki ya tsaya yana ƙarema falon nasa da ya hargitse kallo, bawai na tarkacen da suka zube bane kawai dan yasan wannan ne ya kawosu ai. Iya shegen da ake aikatawa a falon duk da shima yasan yana aikatawa ya sashi zama turus, dan shi dai Nadiya batace masa zasu gayyato namiji ko ɗaya ba. Amma sai ga har mutum huɗu manyan mutane sa'ar Daddynsa, kai abinma tashin hankalin shine harda abokan Daddyn nasa ma da suka sanshi ya sansu. Da baya-baya ya koma ganin hankalinsu su bai kai kansa ba saboda shagala a ɓarnar da suke aikatawa da yaran mutane. Duk cikinsu baiga Lulu ba, gashi kuma an tabbatar masa da tazo wajen awa biyu baya da suka shuɗe. Waya ya ciro yay kiran Nadiya, an jima ba'a ɗauka ba dan har tana batun tsinkewa sannan aka ɗauka. Cikin wata irin murya ta ce, “Ranka ya daɗe barka da dare”. Sai da ya ɗan cije leɓen haushi kafin ya amsa mata da “Ta iso ne?”. Cikin muryar nan na wadda ta gama buguwa da shiga yanayin masha'a ta amsa masa da “Tazo amma shegen driver ɗin nan nata ya kwasheta sun tafi”.
“What!!” MM Atik Kumo ya faɗa da ƴar tsawa. Bai jira cewar Nadiya ba ya yanke wayar ransa a ɓace. Mota ya shige ya zauna tare da kwantar da kansa kan steering. A karo na biyu ya rasa damarsa akanta, tunda yake wata mace bata taɓa shiga ransa irin haka kamar yanda Lulu ƙamshi ta shiga ba. Da gaske sonta yake, yana kuma tsananin buƙatar mallakarta. Bai damu ace sai da aure ba, dan shi a halin yanzu babu maganar aure ma a gabansa duk da kullum faɗan momynsa kenan shine yay aure. Sai dai da to kawai yake amsa mata a duk sanda ta titsiyesa. Tun randa suka haɗu da Lulu a airport ya kasa hutawa da tunanin surar yarinyar da tsiwarta, burinsa kawai ya gusar da ƙishinsa gareta dan kowace mace tama daina birgesa a dalilinta yanzu. Sake kaiwa steering duka yay tare da tashi zaune yayma motar key a fusace ya bar gidan......
★★
Driving ɗin yake cikin ɓacin rai da takaici, yayinda ita kuma ta keta faman surutai da zaginsa akan ya maidata sai ta koyama Hon. Babale Misau da Nadiya da suka haɗa baki hankali. Faɗi take ita ba ƴar iska bace, duk wanda yace zai mata iskanci sai ta wulaƙanta shi.....
Wani irin baƙin ciki ne ya sake turniƙe zuciyar Smart dan surutanta sun ishesa, sake tunzura fushinsa suke zuciyarsa na ƙuna. Wani shegen birki ya taka a harzuƙe har sai da tai gaba ta bugu da kujerar gabanta ta sake buguwa da jikin ƙofa sannan ta koma ta zauna daɓar. Dafe kanta tai dan azaba kamar zata fasa kuka, sai kuma ta harzuƙo cikin fushi da masifa ga rashin kasancewa a hayyaci da ya ƙara hauhawar masifar tata ta ce, “Kai wai miyasa baƙauye ne akoda yaushe? Mugu so kake ka kasheni ka gudu da motan ko? Illiterate kawai, ba abinda ya iya sai shashashanci baƙauye”.
Idan motar nan ta motsa Smart to shima ya motsa, yakai matuƙar wuya so yake ya mata masifa dan maƙogwaronsa sai kaikawo ya ke a wuya amma yanata ƙoƙarin hana kansa, sai ma wayarsa da ya ɗauka ya fara danne-danne abinsa. Hakan ya sake fusata Lulu, da ma yaya lafiyar kura balle ta tsinke. Tana ƙalau ma yaya aka ƙare da jaraba balle yanzu da ya haɗa da maye. Sosai ta cigaba da zazzaga masa masifa ko haɗiyar yawu ma batayi, ganin badai zai kulata ba ta kama murfin ƙofar zata buɗe ta fita amma sai taji yayi lucking motar. Wayyo azabatun azaba. Yau dai kam yaga masifar ƙare dangi, dan bakinta baiyi shiru ba har sai da barci ya fara rinjayar mata idanu. Da wahala kaga Lulu tasha abu ya sakata barci, shiyyasa ko cikin abokanta ake ji da ita da kwarzanta ƙarfin kanta, amma yau da yake wani mugun haɗine MM Atik yay mata batare da ko Nadiya ta sani ba yasa abinda yafi ƙarfin kanta kala-kala wani ma bata taɓa shansa ba. Tun randa suka haɗu a airport bai huta ba, biye yake da ita yana ninƙaya cikin al'amurranta har sai da ya gama sanin ita ɗin wacece. Dan haka ya jawo Nadiya a jikinsa ya dinga jiƙata da kuɗaɗe harta amince da shi bawai yazo dan ya cutar da aminiyar tata bane son gaskiya yake mata. Ita da shi suka haɗa plan ɗin wannan phaty na samun lafiyarta, ya kuma saya musu duk kayan shaye-shayen tare da basu gidan hutawarsa da ya gama ginawa kwanan nan, shi yayi hakane dan ya rutsa Lulu a can, yayi imanin in har ya sameta sau ɗaya da kanta zata cigaba da nemansa kamar sauran ƴammatansa tana kawo masa kanta. Sai dai kuma kash, bayan ya gama wahalar haɗa dukkan plan ɗinsa wani shegen driver ɗinta ya zo ya rusa masa komai.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣1️⃣
........Wayar da yake faman daƙila ya ajiye, dan dama yana dannawar ne kawai badan yana fahimtar komai ba da yake yi. Ta cikin mirror yake kallonta, sai kuma kamar wanda aka tsikara ya janye yana jan tsuki. Da sauri ya furzar da iska zuciyarsa tana masa kai-kawon tunanin ina ya dace ya dosa da ita. Gidansu ko gidan Uncle Yousuf?. A gidansu tana da ƙanne, kuma basu san halin da take ciki ba bayan iyayensu, ganinta a haka garesu zai ƙarasa zubar mata da mutunci ne a idonsu har ma da ma'aikatan gidan nasu da take takawa kamar ƙasa a duk sanda taso. Gidan Uncle Yousuf kam yaransa basu da wayo sosai kasancewarsu ƙanana, zai ma iya yiwuwa yanzu sunyi barci, ajiyar zuciya ya ɗan sake ja da kallonta ta mirrorn sai kuma ya janye idanunsa a lokaci ɗaya. Har ya ɗauki waya da nufin kiran Uncle Yousuf ɗin sai ya fasa, key yayma motar kawai ya cigaba da tafiya. Kaɗan-kaɗan sai ya dubeta ta mirror har suka iso gidan. Horn yay maigadi ya buɗe ƙofa ya fito, dan ba'ace masa wani zaizo gidan ba a irin wannan lokacin dan ƙarfe sha ɗaya saura. Ƙarasowa yay jikin motar sosai, Smart dake kallonsa shima yay ɗan murmushi da faɗin “Baba Barka da dare yaya aikin?”.
Murmushi shima maigadi yayi, dan ya ganesa. Cike da kulawa ya ce, “Mazan fama kaine yanzu da dare haka?”.
“Eh baba na kawo wannan ne”. Yay maganar yana nuna baya, ɗan leƙawa baba maigadin yayi, ganin Lulu kwance a bayan ya sashi ɗan yin baya yana dafe baki dan shi a zatonsa ko barcin isa ne take yi. Da sauri ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Har gaban ƙofar shiga falon gidan Smart yay parking. Sai da ya kashe motar ya fito sannan ya ɗaga waya ya kira Uncle Yousuf. Ba'a jima ba aka ɗauka. Shi ya fara gaidashi dan a girme dai ya girmesa. Uncle Yousuf ya amsa da ƴar fargaba, sai yay saurin tambayarsa badai wani abu ya sake haɗasa da Mawaddat ba?.
“A'a Alhaji komai bai faru ba. Itace dai na kawo nan ɗin gamu a ƙofar falo”.
Da mamaki Uncle Yousuf ya miƙe zumbur, Jallabiyarsa ya ɗauka ya zura dan har sun kwanta ma. Ko amsa tambayar lafiya da Aunty Saliha ke masa baiyi ba ya fice cikin sassarfa yana faɗin, “Ina zuwa”. Shi da kansa ya buɗe motar ya leƙa, ƙirjinsa yay matuƙar bugawa, ɗagowa yay yana kallon Smart kallo na neman ƙarin bayani. Fahimtar hakan shi kuma ya sashi furzar da iska kaɗan. “Bayan tafiyata ta fita, jin hirarsu da ƙawarta a ɗazun ya sani sake dawowa, sai na samu zata fita shine na bita”.
“Ya Arrahaman harma ta sha kenan?”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin matsanancin damuwa.
Tausayi sosai ya bama Smart, ya ɗan cije lips da faɗin, tana buƙatar saka ido sosai dan koba wannan halayyar bai dace ace mace kamarta tana fitar dare ba haka Alhaji”.
“Gaskiya ka faɗa Aliyu, na kuma gode sosai da ƙoƙarinka, duk laifin na yaya ne da bazai iya tsawata mata ba a duk sanda yaga zatai fitar, amma inasha ALLAH zan ɗauki mataki ni da kaina. Sai dai abin damuwar nima ɗin wani lokacin bana nan tunda ina tafiye-tafiye, da zaka min alfarmar dawowa kusa da mu da naso haka Aliyu, wlhy na yarda da kai, ina jinka tamkar ɗan uwana na jini, zan iya bar maka amanar Mawaddat batare da jin ko ɗar ba a zuciyata....”
“Nagode sosai da wannan karamci Alhaji. Sai dai maganar dawowa nan kam abun ne mai wahala gareni, dan Abba ma bazai yarda ba balle kuma Ammah. Sannan nima inada ƙanne, kuma suna buƙatar saka ido duk da dai ba wayona ke tsaremin su ba ko jajircewa. ALLAH ne gafurin rahimun”.
Duk da Uncle Yousuf ya gamsu da bayanin nasa amma bai so hakan ba. Dan yana matuƙar buƙatarsa tare da su. Yaron nada wata nagarta mai matuƙar ƙayatarwa. Ga nutsuwa da cikar kamala tamkar ba talaka ba. Godiya yay masa tare da fiddo Lulu da ke sharɓan tana ɗan surutanta jefi-jefi a cikin barcin, wanda ba komai bane sai zagin Hon. Baita. Shi dai sallama yay masa zai wuce. Dakatar da shi yay da faɗin, “Kaga dare yayi yanzun. Kaje da motar gida dan abin hawa zai iya maka wahala”.
Kamar zai ce a'a sai kuma ya tuna maganar Uncle Yousuf ɗin gaskiya ce. Dan haka ya gyaɗa kansa tare da godiya. Saida ya ga ya shige ciki sannan shima ya shiga motar ya tayar ya bar gidan. Mubarak kawai ya samu a waje alamar dai shi ake jira, cikin washe baki Mubarak ɗin ya taso yana masa sannu da zuwa da shafa motar har ya kasheta ya fito yana lucking. “Yaya ka sayi mota ne?”. Mubarak ɗin ya faɗa cikin zumuɗi. Karan farko yayma yaron ɗan murmushi. Cikin deep voice ɗin nan tashi da ta gaurayu da gajiyar son yin barci ya ce, “Daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi Mubarak? Ta mutane ce”. Kamar an zarema Mubarak lakar jiki ya ɗan rausayar masa da kai gefe kawai. Daga haka suka shige ciki gidan shiru alamar duk anyi barci, sai wasu a ƴammatan dake waya da samarinsu, idan ka cire Asma'u da Maryam dako wayar Yayansu yama hanasu riƙewa sai ta Ammah suke ɗan ɗauka. Ɗaki kawai ya shige dan kwanciya yake matuƙar buƙata.......