Showing 81001 words to 84000 words out of 163036 words
da Mommy da yaran gidan suma duk da sudai duk sun san mike faruwa dan tun a jiya da dare Daddyn ya sanarma Mommy, Uncle Yousuf kuma ya sanarma ƴan biyu shiyyasa tunda safe suka iso Kano. Haka ma su Mubeen duk Mommy ta sanar musu a yau da safe. Sun sha matuƙar mamaki yanda auren yazo damma dai basu san dawa za'a ɗaura ɗin ba har ita Mommy ɗin sai da sukaje wajen ɗaurin auren ne suka sani, bayan sun dawo ɗinne sukai zaman jinjina al'amarin.
Kallan kallo aka shigayi tsakanin Mommy da ƙannen Lulu jin wai da Smart drivern ta akai ɗaura mata aure yau. Karan farko Hussain yay murmushi har haƙoransa na bayyana bayan Mubeen ya gama basu labarin yanda take yaga Smart ɗin. Duk da ganin harar da Daddy ke masa bai iya haɗiye abinda ke bakinsa ba sai da yace, “Uncle You kuma itace tace tana son sa da kanta?”.
Murmushi Uncle Yousuf ɗin yayi shima da faɗin, “Hussain ai matar mutum kabarinsa inji hausawa. Fatan alheri yanzu suke buƙata garemu baki ɗaya. Sannan kuma sai kuyi himmar naku auren dan zamanku haka ya ishemu. Dan haka na baku da ga nan zuwa ƙarshen shekara inba haka ba kuma mu koma Jiƙamshi a duba a cikin dangi ni babu ruwana”.
Dariya Mubeen ya shiga tuntsurawa, su Amrah na tayashi ƙasa-ƙasa dan suna tsoron ta fita aci ƙaniyarsu. Da ga haka kuma aka cigaba da hira, ganin hirar na daɗi babu Lulu kuma Uncle Smart ya aika Suhaib yay kiranta. Koda ta fito taga har da su twins sai tai kamar zata koma. Sai dai kiran da Uncle Yousuf yay mata ya sata dole ƙarasawa. Kamo hanunta Mommy tai ta zaunar a kusa da ita tana murmushi. Ta ce, “Haba yarinyata miyasa zaki koma kuma?”.
Kasancewarta ba mutum mai ɓoye-ɓoye ba ta ce, “Mommy to bakowan kesan ganina anan ɗin ba. Kinga babu amfanin na zauna ko”.
Karan farko Mommy taji wani iri a ranta, dan yanda Lulu tai maganar cikin rashin sakewa zai tabbatar maka halin ko'in kula da ƴan uwan nata ke nuna mata yana cimata rai matuƙa musamman su manyan. Shi kansa Uncle Yousuf wani tunani ne ya fara zo masa a rai akan furucin nata. Daddy kuwa tuni fuskarsa ta nuna ɓacin rai, ya bi su Hassan ɗin da wani irin mugun kallo. Sai kuma ya miƙe tare da zuwa har gaban Mommy ya kama Hannun Lulu ga miƙar. “Tunda basu son ganinki sai suzo su kasheki ai Mawaddat, sannan su haɗa da ni nima” ya jata suka fice a falon. Babu wanda ya iya cewa komai sai Uncle Yousuf ne da ya kafe su Twins ɗin da kallo ya furzar da iska. “You see wannan shine abinda nake ta so ku fahimta tun ba yanzu ba. Amma sai kuka kasa fahimtar tawa saboda idonku ya rufe da cewar Yaya baya son ku sai Mawaddat. Anji shi kan kuskure yake, amma koyaya dai mahaifi sunansa. Amma ita minene laifinta tunda ba itace tace yay mata hakan ba tun bata san kanta ba. Sannan har yanzu Mawaddat bata san minene ya faru kafin haihuwarta ba, ta yaya zaku dinga hukuntata da laifin daba ita tayi ba. Duk da rashin jinta da ake gani a ranta tana matuƙar son kusanci da ku, sai dai rashin damar da kuke bata yasa ta zaɓi kaɗaice kanta bata da wani amini sai Yaya a gidan nan”.
“Amma Uncle ai Mommy ta jata a jiki Daddy yay katanga ma hakan saboda yana ganin zata cutar masa da ƴar gwal”. Hassan ya faɗa cikin ɓacin rai dan yanada zafi. Murmushi mai ciwo Uncle Yousuf yayi, “Yes Aunty Khareema ta jata Yaya yay ƙoƙarin hana hakan, amma ai ba Mawaddat bace ta ƙi aunty Khareema ko. Ku zauna kuyi nazari akan wannan matsalar kuma Kanada taku gudunmawar a ciki, sannan a yanzu na ƙara fahimtar a fanɗarewar Mawaddat harda dalilin ɗaukar kanta ware da kuke nuna mata. Ku manyanta ne, kun fita hankali da sanin ya kamata, ku kuma ajiye halin Yaya gefe ku zauna kuyi nazari akan duk abinda ke faruwa a tsakaninku da ita kuyi alƙalanci tun kafin kuzo kuyi nadama da ga baya”. Da ga haka ya miƙe batare da jiran cewar kowa ba yay ficewarsa. Shiru falon kowa ya kasa cewa komai, dan hatta Mommy kalaman Uncle Yousuf ɗin sun shigeta. Sai take gani kamar itama tana da nata kamshon mai girma da bata taɓa zama wajen matsa musu canja abinda suke kallo ba yanda yake faruwa ba tunda Mawaddat dai ba ita yace Daddy yay mata irin wannan rikon ba, sannan yarinyar bata taɓa ƙin ƴan uwan nata ba, barta dai da tsiwarta sai kuma gatan da Daddyn ke nuna mata na fitar hankali sama da sauran yaran a komai na rayuwa.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣6️⃣
.......Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, duk yanda take ta son dannewa hakan na neman gagara. Ga shi Kasancewar ƴaƴanta na nan ta rasa ta yanda zatai kiran aminiyar ta su tattauna wannan ruɗani da ke neman kaita ƙasa a yinin yau. Ganin hankalin duk jama'ar gidan ya koma kan halin da Smart ke a ciki ya sata sirarewa ta koma ɗaki. Can ƙuryar ɗakinta ta shige ta rufo. Takaicin yanda wayar keta ringing anƙi a ɗauka ya sata jin kamar ta kaima bango naushi. Sake kira na biyu tai bayan katsewar na farkon. Yanzu ma har ta fidda rai da za'a ɗaga ɗin, amma jin an ɗauka ya sata sakin wata wawuyar ajiyar zuciya. Cikin haushi da ƙosawa ta ce, “Haba Hajiya Naqiba ina kika shigane ke kuwa inata kiran waya..”
“Yi haƙuri ina falo ne da mutuniyarki, wai munafukan tazo tana faɗa min tsolon ƴar nan tata ragowar ciwo ta samu miji amma Alhaji ya ƙi saurarenta, acewarsa sai ta gama makaranta fa maganarsa ba canji”.
“Mtsoww aikin banza. Banda haukarta ma wannan sikila ɗin ko auren tai dawo mata zatai”.
“Hhhhh ashe kin gane Aminiya. Shiyyasa mafa ni yarinyar sam bata cikin lissafina wlhy........”
“Aminiya ina cikin tashin hankali wlhy yau ɗin nan, tun ɗazun na rasa taya zan kiraki ɗaki cike da Ƴaƴa kin san yau juma'ar ƙarshen wata”. Umma ta katse ƙawar tata Hajiya Naqiba.
“Tofa mike faruwa kuma Aminiya. Ke da kin gama kame gida tsaf baki da wata matsala a yanzu, banda ma waccan shegiyar sirikar taki matar Salim na neman buɗe mana aiki itama....”
“Aminiya masu son buɗe mana aikin ai sun ƙaru. Kin san shegen yaron da muka cimmawa da ƙyar yau Alhaji ya ɗaura masa aure......”
“Aure kuma? Wai kina nufin ɗan wajen Hafsatu”.
“Aminiya inba shi ba wane shegen tantirin yaro ne ke bani wahala a gidan nan. Kedai shaidace akan kuɗin dana dinga kashewa ga al'amarinsa sai da ƙyar muka samu malamin nan na zuru yay mana aikin da ya ci. Yau kuma wai sai ga Alhaji da wannan mummunar labari, abu mafi ƙona rai ka ƴar masu garin Kanon fa......” ta kwashe komai ta sanar mata har halin da Smart yake a ciki yanzu.
Sosai Hajiya Naqiba ta jinjina al'amarin. Dan tasan aikin Malam na-zuru kam garanti ne. Cikin jimami da taya ƙawar tata takaici ta ce, “A lallai dole ki shiga ruɗani Hajiya Yahanasu. Kuma bamuga ta zama ba dole mu shiga Zuru a gobe. Ƴar gidan Alhaji Isma'il Jiƙamshi fa? Kin san kuwa wanene wannan mutum? Shahararren mai arziƙi ne wlhy balle kuma wai jikan Alhaji Sufi Garko masu juya ƙasar nan a yanda suke so. To banda masifa ma irin ta wannan hatsabibin yaron ina ma suka haɗu? Ai in har kuka bari wannan yarinyar ta tare to kun gama kaɗewa, dan Hafsatu ta gama yi muku fintinkau. Shi ko kinga ai batun wani ƙwallo ya ajiye kuma ga komai a gashe sai dai ci. Ai ko ƙasar nan bana zaton zai cigaba da zama kuma....”
“Aminiya kina ƙara rikitani wlhy. Bakiji yanda kaina ya ƙara ɗaukar zafi ba. Yanda na tsani mutuwata haka na tsani yaron nan a gidan nan dan na jima da fahimtar son da Alhaji ke masa. Ga abinda malamin can ya faɗamin a kansa tun yana ɗan ƙaraminsa.......”
“Kinga ki kwantar da hankalinki, kawai dai duk ma yanda za'ai kiyi gobe ki fito muje mu wajen Malam Na-zurun”.
“To shike nan. Bari naje kar a juya ba'a ganni ba kuma a zargi wani abun kin san dai munafukan matan gidan nan musamman ma shegiyar Fatin can (aunty amarya) da take abu kamar Hafsatun ce ta haifeta, na rasa mitai mata masheranciyar take mata irin wannan biyayyar itama shegiyar ta biyu”.
“Duk zamuyi maganinsu. Itama sai a kaita ai gobe a sabunta mana aiki a kanta kawai.”
Sosai Umma taji daɗin wannan shawaran. Dan haka ta ƙara jerama aminiyar tata godiya sannan sukai sallama jin Hannatu ƴarta na ƙwala mata kira da ga falo.....
(Ke kuma Umma haka kike ashe. ALLAH ya rabamu da ɓatan basirar zamowa mushrikai akan kishi da abin duniya🤦, duk abinda ka gani rubutacce ne da ga ƙaddarar mutum. Kai baka isa canjashi ko sakawa ba. Dan mi zakaita wahal da kanka da ɗorama kai zunubi ga asarar kuɗi. ALLAH ka shiryar damu dai🙏).
____________________
A falon Daddy Uncle Yousuf ya samu Mawaddat kwance, yanda tai lamo sai ya fahimci kamar kuka ma tayi. Tausayi ta bashi, dan zuwa yanzu ya ƙara fahimtar akwai wani tabo a zuciyarta da take ɓoyewa kuma ya kamata ace sun sani. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da aro murmushi ya azama fuskarsa yana kaiwa zaune da kiran sunanta. Idanunta da ke a lumshe ta buɗe tana kallonsa. Sai kuma ta tashi zaune fuskarta har yanzu da alamar damuwa ta ce, “Uncle You sai yaushe ƴan uwana zasu daina jin tsananta ne?. Na rasa mina musu da girma haka. Na rayu ba'a cikinsu ba, kullum cikin begen son ganinsu neke a zuciyata duk da basu taɓa zuwa inda nake ba sai a hoto idan ka nuna min su. Amma sanda na iso da zumuɗin ganinsu fuskar da suka fara tarbata da shi shine na tsana. Har yanzu kuma irin wannan tsanar nake gani a cikin idanunsu bata taɓa sauyawa ba. Su Amrah ne kawai ke sakewa da ni, suma a wasu lokutan nasha samunsu suna zagina sai dai ban taɓa nuna musu na sani ba. Kodai dan ba Mommy ta haifeni ba kamar su shiyyasa basa sona....”
Kai Uncle Yousuf ya dafe, sai kuma ya ɗago duk a lokaci guda yana girgiza mata kansa. “No Mawaddat ba haka bane ba. Amma ina so ki kwantar da hankalinki zamuyi magana a nutse. Ni yau ɗin ma naga duk kin zama kamar wata raguwa kamar bake ba. Bakin duk ya mutu kar fa Aliyu yay miki dariya idan ya ganki haka yay zaton kin karaya ne”.
Baki ta tura gaba tana yamutse fuska. “ALLAH ya kiyaye Uncle You. Ni kawai yau bana jin daɗin raina ne. Ni bari ma na shiryo na bika wajen Aunty Saliha nai weekend a can kawai”. Kafin yace wani abu harta fice a falon. Ya buɗe baki zai kirata Daddy da ke fitowa a ɗaki yace, “Yousuf barta kuje can ɗin kawai.”
“Yaya yanzu fa tana da aure. Kasan ko bai dace ba. Amma ina zuwa ”. Yay maganar yana zaro wayarsa. Idanu Daddy ya tsira masa cike da zargi, sai dai bai ce komai ba. Tsaf Uncle Yousuf ya lura da shi, amma yay biris ya cigaba da kiran no ɗin Smart. Sai dai har ta yanke ba'a ɗaya ba. bai gajiya ba ya sake kira. Maryam ce ta ɗaga, cikin nutsuwarta tai sallama tare da gaishesa. Sannan ta ɗora da faɗin, “Yayan baida lafiya ne”.
Cike da mamaki Uncle Yousuf yace, “Baida lafiya kuma? Aliyu fa nake nema”.
“Eh shi ɗin”. Ta sake faɗa da ladabi. A rikice Uncle Yousuf ya ce, “Ya salam miya samesa? Yanzu fa babu jimawa muka rabu da shi. Kinga ina zuwa”. Ya faɗa yana yanke wayar. Number Abba yay kira, bugu biyu kuwa ya ɗaga suka gaisa da sakema juna bangajiya. Sannan Uncle Yousuf ya ɗaura da tambayar abinda ke bakinsa. A nutse Abba yay masa bayanin komai, tare da ɗorawa da faɗin, “Al'amarin Aliy ya fara bani tsoro a wannan gaɓar, dan in har ba shafar junnu ba to lallai dole akwai sihiri mai ƙarfi jikin yaron nan. Dan sai a yau na sake fahimtar wani abu. Halan ma auren da muketa matsa masa yayi amma yaƙi duk akwai dalili, sai yau da ALLAH ya kawo iyaka akayin kuma yazo cikin bazata shine hakan ta kasance?”.
Numfashi Uncle Yousuf yaja mai ƙarfi. “Tun lokacin da Hameed ya bani labarinsa na fahimci makamancin hakan gaskiya. Kuma malamin nan dama ya faɗa cewar sihirine mai ƙarfi tattare da shi wanda aka ƙulle duk al'amarin rayuwarsa masu girma. Sai dai kuma addu'a tafi ƙarfin komai da kowa, wata rana duk ƙarfinsa zai zama ya warware in har aka cigaba da gayama ALLAH shi maji roƙon bayinsa ne. Kuma insha ALLAHU muna fatan warwarewar lamuranne suka fara zuwa”.
“To ALLAH ya tabbatar da hakan Yusufa”.
“Amin ya rabbi malam. In sha ALLAHU yanzu zan zo gidan tare da malam ɗin ku kwantar da hankalinku”.
Bayan Uncle Yousuf ya ajiye wayar yayma Daddy bayani. Shima ya nuna alhini da jin tausayin Aliyun. Sai kuma ya ɗora da faɗin, “Maganganinka sun sani a ruɗani fa akan yaron. Har kayi masa sani irin haka dama Yousufa?”.
“Yaya na san fiye ma da haka akan Aliyu. Sai dai yanzu bamu da lokaci, amma ka bini bashi wataran zan maka bayani insha ALLAHU”.
Daddy bai ja zancen ba kawai ya gyaɗa masa kai da ƙara yima Smart addu'ar samun lafiya. A haka Mawaddat ta dawo ta samesu. Bai mace mata komai ba sukai ma Daddyn sallama suka wuce. Ko a hanya bai sanar mata halin da Smart ɗin ke ciki ba ya kaita gida ya ajiye. Sai dai bai shiga ba ya koma shi ita kuma ta shige cikin cike da zumuɗin son ganin Deen ɗin ta. Dan tana matuƙar ƙaunar yaron ita dai...
Bayan sallar magrib kaɗan Uncle Yousuf da Hameed (Coach) suka iso gidan tare da Malam da sukaje har gida suka ɗakko. Har ɗakin Smart ɗin suka shiga bayan su Gwaggo Sa'adah sun fito. Malam ya ƙara masa addu'a sosai tare da kwantar musu da hankalin in sha ALLAHU komai zai dai-daita. Yau ɗin ma dai ruwan addu'oin nan ya sake basu da sake jaddada musu dage masa da addu'a shi kuma ya ƙara dagewa da yin azkar da sadaka. Har suka bar gidan Smart bai farka ba yanata barci, sai kusan ɗaya ya farka da azababben ciwon kan da dole sai da aka nemo wani ma'aikacin asibiti a anguwar saboda yanda yake ta complain kansa kansa kamar zai fashe. Dubasa yay da yi masa allura ya kuma saka masa ƙarin ruwa sannan aka samu wani barcin mai nauyi ya sake yin gaba da shi.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣7️⃣
.......*_WASHE GARI_* da asuba da ƙyar Lulu ta iya tashi sallar da Uncle Yousuf ya sa aunty Saliha ta tadata yi. Dan kuwa dai daren jiya suna gama hira da Aunty Saliha ta shige ɗaki sakamakon dawowar Uncle Yousuf gidan a gajiye ta samu sirof ɗin ta da wani ya kawo mata a gidan bayan sallar isha'i ta fita a sulale ta amso bada sanin aunty Saliha ba har kwalba uku tasha. Dan yanda kanta yau ya ɗauki zafin nan ta tabbatar sai tazo kwanciya komai zaita dawo mata a rai ta kwana cikin damuwa. Sam bata buƙatar hakan kuma. Ga shi dama abin yazo mata a dai-dai wato weekend. Dan dama fa duk weekend kusan sune ranakun da tafi ƙwalewa son ranta ta sha barcinta. Kafin a gane tana shaye-shaye sai aita ɗauka gajiyar aiki ce ke sata mahaukacin barcin da take sha. Balle ma Daddy kan hana a tadota a cewarsa a barta ta huta. Hakan na bata dama ƙwarai da gaske ita kuma ta sha abinda take son batare da sun gane komai ba.
Sabon barci ta sake dasawa har kusan sha ɗaya sai da Uncle Yousuf nan ma yasa Aunty Saliha tadata. Tun a yanda ta fito ya fahimci wani abu ta sha a jiyan, bai ce komai ba kan haka duk da zuciyarsa tayi babu daɗi sai cemata da yay ta koma ta shirya yana jiranta zata rakashi wani waje. Kai kawai ta gyaɗa masa da komawa