Showing 39001 words to 42000 words out of 163036 words
garesu ba dan takaici har suka shige wata ƙofa ba ainahin ta Court ɗin ba. A take ya ga gurin ya sake ribcaɓewa, mutane sai faman ɗura kai suke cikin court ɗin. Maganar wasu samari da ke wuce motar cikin ƙaucin shiga kotun ta ɗan ja hankalinsa. Na farko mai riƙe da camara ke faɗin, “Yaufa akwai ƙura, dan na tabbatar barrister Mawaddat Jiƙamshi ba ƙaramin sabon shiri tayo ba duba da yanda Barrister Marafa ya nema zubar da ita a wancan zaman. Kasan fa ita bata taɓa bari a kaita ƙasa musamman a kan irin wannan case ɗin na fyaɗe, ga shi tasan aikinta lawyers ƴan uwanta da yawa har tsoron karawa suke da ita, dan ita ko waye ma ubanka akan fyaɗe sai tayi kutu-kutun turaka jail dan haka kullum ita bata kare mai laifi sai wanda aka zalunta musamman ƴan uwanta mat.......”
Bai ƙarasa jin abinda saurayin ke son faɗa ba dan sun masa nisa. Da farko baiyi niyyar shiga wajen ba, sai dai saboda gargaɗinta ya ƙudiri shigar dan yaga mizata iya masan. Ƙoƙarin fitowa yay a motar kira ya shigo wayarsa. Kamar zai share sai kuma ya cirota da ga aljihu. Ƙanwarsa ce mai bimasa Hawwah dake auren abokinsa. Ɗagawa yay, sai dai yana kaiwa kunnesa yay saurin janye wayar yana mai lumshe idanunsa. Buɗesu yay a hankali zuciyarsa na wani irin zallo. Cikin motar ya koma tare da sake kiranta. Ringing ɗaya ta ɗauka. Cikin matsanancin kuka ta ke faɗin, “Yaya dan ALLAH ka barni na taho gida. Wlhy na gaji da wannan rayuwar bazan iya ba. Inko ba haka ba wataran sai mahaifiyar Abban Nasreen ta kasheni a gidan nan....”
Iska ya ɗan furzar mai ɗaci, tare da faɗin, “Miya kuma faruwa?”. Sake fashe masa tai da kuka, da ƙyar ta iya faɗin, “Mai fa da nake suya airish ma Nasreen da zata wuce school ta kusa kwaramin yau a jiki Yaya. Ban san wane irin rashin ƙauna matar nan take min ba. Wlhy bazata taɓa canja halinta ba nima na gaji da haƙuri da ita.”
“Shi ina Sa'id ɗin yake?”.
“Yaya yana fa a gidan, gashi can ya jata wai yana bata haƙuri saboda ni ba'a san ciwona ba. Yanzu Yaya data sameni da man nan haka zai tsallakeni ya bita ke nan....”
“Kinga ya isa. Ki jirani gani nan zuwa gidan yanzu”. Da ga haka ya yanke wayar batare da ya jira abinda zata ce ba. Fitowa yay a motar ya kulle. Da ƙafa ya fita a habar court ɗin da ta yi tsittt alamar an fara shari'ar ko za'a fara. Yana fitowa a gate ɗin ya samu napep zuwa Daurawa anguwar da gidan ƙanwar tasa take. Kasancewar safiya ce basu wani samu matsala ba, dan haka suka iso da wuri. Bayan ya biya mai napep ɗin maimakon shiga gidan kai tsaye ko yin knocking sai ya ɗaga waya yay kiran abokin nasa Sa'id Ibrahim da sukai karatu a jami'a tare. Yanda Sa'id ɗin ya ɗaga wayar ta isa tabbatar da a rikice yake. Dan duk ya daburce sallamar ma da in ina yayi ta. Sai kuma ya shiga kame-kamen gaisuwa. Katsesa Smart ɗin yay da faɗin, “Gani a ƙofar gidanka ka turo min Hawwah zamu wuce gida”.
“G...g...gida kuma Mawashi? Miya faru ka...k...kake wannan maganar haka? Ko itace ta kira ka ta faɗ......”
“Sa'id!!”.
Ya dakatar da shi a harzuƙe. Sake tsurewa Sa'id ɗin yayi dan yasan halin abokin nasa sarai. Bai da yawan magana ko hayaniya, dan bai taɓa ji ko ganin abokin faɗan Smart Mawashi ba a rayuwa. Amma shi kaifi ɗaya ne akan komai da kowa. Duk yanda yake da kai bai yarda ka latsashi ba ko gasu abokai. Yanda ya rikice ɗin sai ya harzuƙa ran mahaifiyarsa da ta hanashi fita duba matarsa. Dan ta rantse ko bakin ƙofa yaje domin Hawwah ɗin sai ta tsine masa. Cikin masifa ta wafce wayar, kunnenta ta kai da faɗin, “To ɗan mulkin mallaka wai shin nikam ko kai ne ka haifa min Sa'id ne ban sani ba? To bazai zo ɗin ba, nace bazai zo ba idan ka isa kai duk abinda kake jin zaka iyayi, ko ita ƙanwar taka autar mata ce da in ya rabu da ita zai kasa cigaba da rayuwa har ya auro wasu huɗun. Aikin wofi kawai anga kuɗi an nanema yaro na”.
Har tayi ta gama bai ce uffan ba, sai da yaji tayi shiru ya yanke kiran. Yanda yake huci zai baka tabbacin sanin ran ƴan maza ya kai ƙololuwar ɓaci. Number Hawwah yay kira, bugu ɗaya ta ɗaga. Kafin tace komai ya ce, “Ɗakko mayafinki ki sameni waje”. Ya yanke kiran. Minti shida kuwa bata gama cika ba sai ga Hawwah da ƙaton akwati da Nasreen ƴar shekara huɗu biye da ita. Tana ganinsa ta cilla da gudu garesa tana faɗin, “Oyoyo Uncle”. Kaɗan ya saki murmushi, tare da duƙawa ya ɗauketa ita da school bag ɗin da ke goye a bayanta alamar an gama mata shirin makaranta ne. Sau ɗaya ya kalla ƙanwar tasa ya kauda kansa. Batare da yace komai ba ya amshi akwatin hanunta yay gaba tabi bayansa. Napep ya tare musu suka shiga, Nasreen nata zuba masa surutu dan yarinyar ko akku haka ta ganta ta bari kamar ƴar ƙwa-ƙwa akwai wayon jaraba. Dan bakinta ya girmi shekarunta. Sai da ya kaisu har gida sai dai bai shiga ba yace taje ta jirasa zai je ya dawo. Bata musa ba ta fita, shi kuma yace ma mai napep ya juya da shi babban kotun dake jaha. Ya samu har an fito da ga shari'ar, yanda harabar kotun ke'a harmutse da ƙayataccen murmushin da ya hango a fuskar Lulu ya sashi tsira mata idanunsa. Tsaye take a tsakkiyar lauyoyi ƴan uwanta wanda da alama duk ƴan ɓangare ɗaya ne a shari'ar, dan yanda fuskokinsu ke a washe kamar ita saɓanin waɗanda ke gefensu kaɗan zai baka tabbacin hakan. Ƴan jaridar da suka zagayesu ya sashi daina iya hangota, ɗauke kansa yay tare da buɗe motar ya shiga, a kallo ɗaya zaka fahimci damuwar dake zagaye da fuskarsa, dan babu abinda ke faman masa kai kawo sai batun ƙanwarsa Hawwah, shi shaida ne Sa'id na matuƙar son Hawwah, sai dai matsalar mahaifiyarsa da tun farko ta nuna bata son auren saboda ƴar ƙanwarta da taso ya aura shi kuma yaƙi tsayawar mahaifinsa ta sa ta janye ta amince ya auri Hawwah, sai dai tunda take gidan mahaifiyar tasa ke nuna mata hantara da ƙyara musamman idan Alh. Ibrahim mahaifin Sa'id ɗin baya gari. Tasha marin Hawwah ɗin dayi mata abubuwa masu cin zuciya shi yana zuwa ya sasanta bada sanin iyayensu ba. Sai dai a wannan karon ya fahimci dole ne fa a tauna tsakkuwa dan aya taji tsoro. Dan tsohuwar na buƙatar sanin Hawwah nada gatan iyaye da dangi itama, sannan dukiya ba itace rayuwa ba kawai akwai muhimman abubuwa da suka fita a zamantakewar rayuwa. Kai dai kai fatan kawai ALLAH ya rufa maka asiri kafi ƙarfin yau da gobenka. Idan kuma ya azurtaka da dukiyar ka bida ita ta hanyar da kai a karan kanka zakai alfahari da kanka watarana da zaka amsa tambaya akan dukiyar kwabo bayan kwabo........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣4️⃣
.........Gigitaccen knocking ɗin da akai ma glass ɗin motar ne ya sashi dawowa hayyacinsa. A hankali ya buɗe idanunsa da sukai mugun kaɗawar ɓacin rai ya sauke a kanta. Harara ta balla masa da juyayyun idanun nan nata da shaye-shaye ya gama canjawa yanayin kallo.
“Kai anya kuwa ka taɓa shiga ajin makaranta? Dan na fahimci baka san aikin ka ba, malalacin banza kawai ka zauna kanama mutane tunanin iska a mota, ko an gaya maka a banza ake mallakar irin motar har ai zaman tunani a cikinta Mtsowww!! Baƙauye”. Ta buɗe motar a fusace ta shige tare da rufe murfin da ƙarfi. Fitowar da yay niyyar yi buɗe mata ya fasa, batare da ya tanka mata ba kamar yanda ya saba yayma motar key. Bata sake bi takansa ba ta maida hankalinta a lap-top itama, yayinda shi kuma yake tafiya a nutsensa. Sunyi nisa sosai batare da ko sau ɗaya ta ɗago taga ina suke nufa ba, dan ita duk zatonta hanyar office ɗinta ya nufa da ita tunda Uncle Yousuf yace mata ya bashi komai nata a rubuce. Jinfa tafiya na neman ƙin ƙarewa ya sata ɗagowa. Da sauri ta ƙara ware Lulu ayes ɗinta tana kallon inda zata iya rantsewa bata taɓa sani ba ma, dan ita dai kusan yawonta wajen Kano a jirgi ne. Gabanta ne ya faɗi, zuciyarta ta shiga mata kai-kawon ko yayi kidnapping ɗinta ne? Amma sai ta dake a masife ta ce, “Kai malam mi kake ƙullawa ne? ina ne kake shirin kaini nan?”.
Shiru kamar bazai tanka mata ba, dan har ya kunnata ta ƙara ƙarfin hucinta. Sai kuma cike da rainin wayo ya bata amsa cikin halin ko'in kula da cewa “Asibiti ganin likitan ƙwaƙwalwa”. dai-dai yana ƙoƙarin shiga ƙaton gate ɗin asibitin na dawanau.
“What?! Wai nice ka kawo duba masu taɓin ƙwaƙwalwa kake nufi ko mi?”. Tana sake ware idanunta kan rubutun saman ƙaton ginin inda yay parking. Bai tanka mata ba har sai da ya kammala dai-daita motar a gaban wajen. Kasheta yay gaba ɗaya tare da kai idanunsa kanta ta cikin mirror. Kallon nasa kuwa take itama dan tsabar takaici ya hanata iya sake cemasa komai amsar dalilin zuwansu kawai take buƙata da ga garesa.
“Kinada kati anan ne ko yau za'a fara yankar miki? Dan naga kamar ƙwayar da kika sha jiyan bata kammala sakinki ba”. Ya faɗa a dakensa.
“Kai! Wai dama ni kake nufin inada taɓin ƙwaƙwalwar ma kenan?”.
Idanunsa da take kira na macizai ya wara mata cike da salon sake tura mata takaici. Sai kawai taji ƙwalla na neman cika mata idanu. Tunda take a duniya bata ko tuna an taɓa wulaƙantata makamancin yau ba, ba zuciyarta ba hatta numfashinta fita yake da sassarfa. Wai ita wannan ya kawo asibiti, asibitin ma na masu taɓin hankali. Babu abinda take ji a ranta kamar ta haɗama ƙyaƙyƙyawar fuskarsa jini da majina da maruka fiye da yanda ya yagata, ta dunƙule hannunta amma hannun ya gagara ɗaguwar aikatawa. Maimakon ma hakan kanta kawai ta dafe dan jin zuciyarta na barazanar tsagewa biyu. Batajin idan ta sake kai mintina sama da uku a motar nan bata shaƙe mutumin nan ya bar duniya ba. A wani irin harzuƙe ta bankaɗe murfin motar ta fita, inda yake zaune mazaunin driver ta buɗe. Shi kansa bai taɓa ganin ɓacin rai tattare da ita irin yau ba, dan tsabar masifa fuskarta har jaja takeyi....
“Fitar min a mota!!”.
Ta faɗa da ƙyar muryarta har rawa takeyi. Cikin deep voice ɗin nan tasa da sake dakewa ya ce, “Maizasa na fita bayan akan aikina nak.....”
“Wlhy zan kashe fuskarka da mari idan baka fitar min a mota ba tunda ban haɗa kuɗi da kai na saya ba!!”. Ta sake faɗa a wani yanayin da muryarta ke fita da cracking. Ya gama sanin ta kai ƙololuwar fusatar da yake buƙata, dan haka cikin taɓe baki ya fice yana wani murmushin da ke sake tafasa mata ruhinta shiko yana sake ƙayatar da kwarjininsa.
“Ka rubuta ka ajiye sai na wulaƙanta rayuwarka a mizanin mafi munin wulaƙanci”. Ta faɗa dai-dai tana fisgar murfin motar bammm! Ta rufe. Kamar yanda ta saba a guje ta fice a asibitin, dan Lulu akwai iya tuƙin ganganci da wauta balle yau da ya zama an kunnata ne, shiyyasa Daddy yafi son driver ya jata a mota. Da gaske tuƙi take irin na wauta da isa, har takai wasu drivers ɗin na zaginta idan tai wani abun cike da gadara. Tana kan round about ɗin da zata ɗauki titin office ɗinsu ta kusa haɗa accident sakamakon neman shallakewar ƙin tsayama traffic light data nema yi. A fusace drivern data dakarma mota ya fito, itako babu alamar ko ɗar a tare da ita ta ƙara sautin kiɗan wakar Shakira da ke tashi a motar, dan tana matuƙar son waƙoƙin mawakiyar, shiyyasa bata da wakar data bama amanna kamar waƙoƙinta musamman idan tana cikin ɓacin rai irin haka.
“Ke ƴar uban wacece da zaki da kar min mota ki cigaba da zama a ciki kamar bakiyi ko mai b........” ya gagara ƙarasawa saboda tozali da abinda baiyi zato ko tsammanin gani ba. “Ni ƴar gidan ubanka ce!!”. Lulu da dama take a harzuƙe jira take a taɓata ta fashe ta bashi amsa a fusace itama. Kansa ya ɗan dafe da wani irin salo yana juya jikinsa kaɗan, sai kuma ya sake jiyowa gareta da ɗan kuzari ya ranƙwafo a motar. “Oh Baby dama ke ce? Please am so sorry”.
Harara ta balla masa tare da jan sirrin tsaki ta ɗauke kanta. Zai sake magana ta ɗaga masa hannu, tare da ɗakko bandir na sabbin dubu ta jefa masa a harzuƙe. “Ko basu kake buƙata ba dama?”. Siririyar dariya ya saki mai ƙayatarwa. “Mai sunan gwaggo kenan, ni bance ina buƙata ba, sai dai idan kin bani ƙyauta ne zanso haka. Koba komai ƙyauta da ga masoyiya zuwa masoyi ai abin alfahari ne ko”.
“Tajuddeen bani hanya na wuce kafin kaja na sauke maka abinda ke kaina wlhy!! Dan inada abunyi”.
“Zan iya ɗaukar ko miye da ga kanki ko mi nauyinsa, sannan nima inada abunyi dan haka ma kika ganni da farar safiyar nan akan titi, duk da dai naci ribar fitar kodan ganinki da nayi”.
Maimakon amsa masa sai taja tsaki, tare da yin sama da glass ɗin motar. Da sauri yaja da baya dan neman takashi take yi. Cikin murmushi da cizar lips ya duƙa ya ɗauki kuɗin nan data jefesa da su a ƙasa yana kaisu hancinsa dan tuni ƙamshin turarenta mai ƙarfi ya mamaye su. Duk abinda ke faruwa akan idanun Smart ne da ke cikin napep kamar sauran mutane, dan tana baro asibitin yay murmushi, sai dai da sauri shima ya fito saboda ganin yanda ta fisgi motar cike da ganganci ya kuma san bata san hanya ba sosai, baya fata wani abu ya sameta a dalilinsa, cikin sa'a ya samu napep, dan haka yace masa su bita, sai dai tuni ta musu fintinkau saboda gudun da take zubawa dan har ta ɓace musu, sai gashi kuma sun haɗu a traffic light ɗin. Ƴar hayaniyace ta fara tashi, wasu na zagin Lulu wasu najin haushin Tajuddeen da ya taso gigigi ya kuma koma yay sakwat, daka gansa dai shima kasan akwai nerar balle ace saboda kuɗin data watso masa ne. Sai dai wasu sun fahimci ma dai kamar sun san juna ne shiyyasa, amma hakan bai hana ƙananun maganganun ba dai. Sirrin tsakin da bai shirya bane ya fita a bakinsa a karo na farko. Yana ƙoƙarin ɗauke kansa da yima mai napep maganar su juya titin anguwarsu dan ya fasa bin bayanta da yay niyya idon Tajuddeen ya sauka a kansa. Murmushi ya sakar masa da ɗaga masa hannu, hakan yasa shi dole fitowa fuskarsa a ɗan sake shima ya miƙa masa hannu suka gaisa. “Ya naga yau tafiyar taku daban-daban? Koda yake da alama yau ogar taka fitina take ji”. Tajuddeen ya faɗa da alamar ƴar damuwa, dan harga ALLAH yana matuƙar son Lulu. A karo na farko Smart ya ɗan saki murmushi mai sanyi. Cikin nutsuwar nan tasa, sai dai a can ƙasan maƙoshi ya furta “Ita dama kullum a cikin rigimar take ai. Tunda ta tsere mana ma zan juya gida ne kawai”.
“A'a ba'ayi haka ba. Bari mu ƙarasa dan office ɗin nasu kusa yake damu”. Badan Smart yaso ba Tajuddeen ya biya mai napep da ya ɗakkosa, shi kuma suka shiga motarsa a tare. Tunda suka bar wajen Tajuddeen ɗin ke jansa da hira. Shi dai nashi murmushi ne kawai bai iya cewa komai. Tajuddeen ya fahimci Smart bamai yawan magana bane, sai dai sam baza'a taɓa kiransa miskili ba. Kawai dai shiru-shiru ne shi bai cika hayaniya bane. Tafiya kaɗan ta kawosu, guri ne mai ƙyawun gaske da ɗan girma dan gaskiya ya tsaru. Tajuddeen yaso su shiga tare da Smart amma yaƙi ya ce ya barsa anan wajen, badan yaso hakan ba ya barsa nan jikin motar shi kuma ya shige. Ya ɗan gaisa da tsirarun ma'aikatan da suke kai kawo saboda sun sanshi dan lokaci zuwa lokaci yakan ɗan zo wajen Lulun, da ga haka ya nufi lifter zuwa 3floor. Offices ne kusan goma a wajen, a office na kusan bakwai, a hankali idanusa suka sauka kan rubutun saman da aka rubuta. *_Barrister Mawaddat Isma'il Ibrahim Jiƙamshi_*.
Kai tsaye Tajuddeen ya shige babu wani neman excuse, ƙaramin falo ne dan table ɗin sakatariyarta ne kawai sai kujeru uku 3sitter da 1sitters guda biyu da table a tsakkiyarsu. Da ga ɗan gefe kaɗan water dispenser ce mai ƙyau sai tv da ke maƙale acan sama. Glass ne ya raba wajen da office ɗin ta, dan haka ya iya hango yanda take ma wata dake tsaye gaban table ɗin ta masifa, duk da bajin mi take faɗa yake ba yanayin yanda take karkaɗa hannu ya bashi tabbacin hakan. Da sauri Tajuddeen ya tura ƙofar ya shiga, a tare Lulu da sakatariyarta da ke shan masifa dan a kanta ta hau juye takaicin Smart suka juyo........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya