Showing 111001 words to 114000 words out of 163036 words

Chapter 38 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

457

tunda ya buɗen ƙofar yake min kallon banza kin san shi dai da baƙin halin tsiya, balle yanzu yana ganin ya auri ƴar masu kuɗi kamar yafi kowa a gidanmu.”
         Ƙwafa Umma tai da ƙarfi zuciyarta na sake ƙuntata, cikin fusata da jin haushin lusarancin Huwailar ta ce, “To ke bazaki tashi ki bisu ba. Kije duk ma uwar da akeyi a ɗakin ayi da ke. Ki kuma tabbatar kin kwaso min abinda na sakaki”. Ƙitt ta yanke kiran batare da Huwaila ta sake samun damar cewa wani abu ba. Tasan hanlin Ummar su sarai akan jarabar tsiya, dan haka ta miƙe ta nufi inda taga Asma'u ta shiga. Ba knocking ba komai balle aje batun sallama ta afka musu. Asma'u da ke gyaran gado tai saurin jiyowa, hakama Lulu da ke waya da Sakatariyarta Zainab yanzu idanu ta zubama Huwailar.
       “Kai Adda Huwaila ALLAH har kin ban tsoro shigowa haka ba sallama”. Asma'u ta faɗa cikin jin takaici sai dai ta tausasa harshenta. Harara Huwailar ta zuba mata da taɓe baki ta nufi sofa ɗin bedroom ɗin mai azabar ƙyau da ɗaukar ido ta zauna, itama sai Asma'un ta watsar da ita ta cigaba da gyara gadon cikin takaici. Harta kammala ta shiga toilet shima dan ta gyara Huwaila na cigaba da harare-harare, sai dai fa ɗakin ya mata masifar ƙyau, ji take inama a cikin ƴan ɗakinsu ne suka samu wannan duniyar haka.
     Lulu kam tun kallo ɗayan datai mata bata sake ba tana cigaba da wayarta da Zainab da kuma gyara gashinta data kammala busarwa, so take sai ta kammala taji wace ita da kuma dalilin shogo mata ɗaki haka ba knocking. Asma'u data fito daga Bathroom alamar ta kammala ta yafito da hannu, koda ta iso batare da tayi magana ba ta miƙa mata ribbons da yimata nuni da gashinta alamar ta ɗaure mata. Amsa Asma'u tai da murmushi akan fuskarta, ta shaƙi fitinannen ƙamshin da gashin keyi ta lumshe idanu tana tattarosa cikin hanunta. Dai-dai nan Smart ya shigo ɗakin da sallama. Yayi masifar ƙyau cikin wani kwantaccen yadi da ya sake fiddo nagartarsa ta cikakken bahaushen arewacin Nigeria nutsatstse, daga ita har Asma'un ya zubama ido, sai kuma ya ɗan kalla Huwaila da ke gefe ta baje cikin couch tana ta wani faman hura hanci, sai dai shigowarsa ta sata ɗan nutsuwa dan tasan halinsa sarai.
“Ku tashi mu wuce ku kuma ko?”.
Ya faɗa babu alamar wasa tattare da shi. Asma'u ta ce, “To Yaya can gidan zaka kaima”. Kansa ya ɗaga mata kawai batare da yace komai ba, amma sai Lulu da ke ɗan kwallonsa ta cikin mirror ta juya kujerar tana dubansa da ƙyau tare da janye wayar kunnenta alamar ta kammala. Kallon ido sukaima juna, kowanne ya janye nashi cike da basarwa. Ƙasa-ƙasa ta ce, “Please ka barmin Auta anan dan su Afrah ma na zuwa kawo min phones ɗina”.   
         Zuba mata idanu yay sosai da alamar mamakinta, dan shi dai bai san yaushe ta fara son mutane haka ba da har ma tasan ana kiran Asma'u da Auta. Maimakon bata amsa sai ya dubi Huwaila da Asma'u. Da sauri suka fice dan dama Asma'u ita tayi niyyar yin hakan, Huwaila ce dai dake kallonsu ta ƙasan ido bata da wannan niyyar. Lulu da ke kallon yanda yaran ke rige-rigen ficewa ta wani taɓe baki, “Kai kowa ma sai ka nuna masa halinka ne, jibi yanda yara ke fita kamar zasu ci da ka”.
      “Oh ni har wani hali ne da ni kuma wanda ban sanshi ba?”. Ya faɗa cikin ɗan ɗage gira ɗaya da ƙanƙance idanunsa. Nata tai saurin ɗaukewa da ƙara taɓe bakin ta koma ta juya ga mirror ɗin batare data bashi amsa ba. Ƙarasa takowa yay jikin mirror ɗin shima ya ɗan jingina tare da ɗaukar wayarsa ya duba dawa-dawa tai kira. Ganin number Uncle Yousuf da dama yana da ita, data Zainab da itama dai yana da itan dan tun randa ya kaita gida ya amsa saboda wataran. Ya ɗan ji nutsuwa dan shikam yanzu ya fahimci sai yayi takan tsantsan, tunda har jiya tai amfani da shi wajen sayo mata ƙwaya batare da ya fahimci komai ba dole ne ya nutsu ya fahimci duk wani dabarun su. Iska ya ɗan furzar kaɗan da gyara tsaiwarsa da ƙyau sai kuma ya fara magana a hankali tare da maida hankalinsa sosai ga kallon yanda take tufke jelar gashin bayan ta sharceta da comb. Yana matuƙar son gashi a jikin mace, dan haka natan ke matuƙar ɗaukar masa hankali.
       “Zanje na gaida su Ammah na dawo bazan jimaba, sai dai ki sani kar fita ta ta baki damar aikata wani abu daban, dan shaye-shaye babbar hanyace ta maida ɗan Adam baya akan dukkanin nasarorinsa da kima da mutuncinsa. A duk inda mai wannan ɗabi'ar yake zakaga baida farin jinin al'umma, kowa bai san raɓarsa balle huɗɗa da shi da ga sanda aka fahimci yanayi. Shi a karan kansa kuma yakan rasa damammaki da yawa na cikin burinkansa ko nasararsa ta duniya da lahira. Misali ga barin salla, da wahala a samu mai wannan ɗabi'ar da tsaida salla akan lokacinta, hakan kuma babban naƙasu ne ga rayuwa. Karatun Alkur'ani, ambaton ALLAH da sanin mi rayuwa take ciki kota dosa duk dama ce dake kufcewa a hannunsa. Ga ɗiya mace in har tana wannan ɗabi'ar hanya mai sauƙi ce a samu damar keta mata mutuncinta. Shin mi kika rasa a rayuwa na ni'imomin ALLAH da bai miki ba, miyasa ki ka zaɓi gode masa ta wannan hanyar? Miyasa kika zaɓi sakama iyayenki da wannan tukuycin da duk iyayen da suka fuskanci yaransu nayi basu da sauran nitsuwar zuciya, ki tuna kema uwa ce wataran. Bazance miki ki kiyaye ba, dan ban isa hanaki ba, sai dai ki sani wannan itace ɗabi'a ta biyu da bazan ɗauka ba bayan barin salla. Ki zauna kiyi nazari. Ga break fast can su Asma'u sunzo da shi. Nima yanzu zan dawo sai na karya a nan ɗin, ina son yin abu mai muhimmanci ne acan”. Da ga haka ya nufi hanyar fita abinsa batare da ya ko waiwayo ba balle yaga halin da tasirin da maganganunsa sukayi gareta. Lulu da tun fara maganarsa abu ya tokare mata maƙoshi ta raka bayansa da kallo wani shegen takaicinsa da mamakin gadarar nan tasa da yake son fara bayyana mata a fili. Wai mi wannan mutumin ke nufi da ita ne? To duk abinda ya shirya ita a shirye take da mafiyinsa su zuba ita da shi a gidan nan ɗan halak ka fasa, ina ruwansa da rayuwarta....
     Dawowar Asma'u da kayan shara ɗakin ya maidota hayyacinta. Ta kalleta tana ɗan waro idanu waje. “Ya barki ne?”. Cikin zumuɗi Asma'u ta bata amsa da “Eh, amma yace yana dawowa zan wuce. Shiyyasa zanyi sauri na shashshare miki aunty dan shifa Yaya baya magana biyu”. Yanda ta ƙare maganar da ƴar shagwaɓa ya sanya Lulu sakin murmushi. “Uhhm kudai autocin nan ko'a ina sai kun nuna hali. Kinga bar batun sharar nan karki wahal da kanki nace su Amrah su taho da Iya tabawa zatazo duk ta gyara ko'ina”.
       “A'a aunty ki kirasu ma kice su barta basai sunzo da ita ba. Zan gyara yanzun nan dan nan ma sharane kawai da gogewa ya rage. Nifa kin san ina son aikin gida sosai, shiyyasa su Aunty Bilkisu idan suna jin lalacinsu har zuwa suke su ɗaukan na musu hutu koda Ammah zataita ƙorafi ne sunta lallaɓata kenan”.
      “Uhhmm sannu busy body ke baƙya gajiya ma kenan. To nidai bazakimin aiki ba, amma zanso Ammah ta bari ki dawo mana nan kinga na samu abokiyar hira ko.”
          “Tab aunty Ammah bazata bari ba, ba irin nacin da mijin Aunty Bilkisu baiyi ba kan a basu ni amma taƙi ita da Abbah. Amma ke ƙila taji kunyarki ta yarda ko weekend nake zuwa dan tasan dai halin Yaya bai son yin magana sai yaso, kina buƙatar abokiyar hira”.
      “Zan gwada na gani to, ALLAH yasa su bani, bari na shirya naci abinci ina ɗan jin yunwa kaɗan-kaɗan, kema ajiye kayan sharar nan Please”.
     Magiya Asma'u tai taima Lulu har sai da ta barta tai aikin nan, dan danan kuwa ta tsaftace ko'ina ta baza kayan ƙamshi. Itako tana zaune a falo tana tsakurar abincin da su Asma'u suka kawo, sai dai tana buɗe wanda Huwaila ta kawo ta maida da sauri ta rufe saboda jin ƙamshin korin da aka zambaɗa a miyar fankason ta dakar mata hanci, sam ita bata ƙaunar kori a abinci shiyyasa ma idan har an saka batacin sa komai son da take masa. Sai kuma ma akai rashin sa'a fankasu ba abincinta bane shima, duk randa ma Iya Tabawa tayisa a gidan to ita sai dai ai mata wani abun, hakama idan taje gidan Uncle Yousuf ko gidan Grandpa ta tarar anyi bataci, bata son su shi da tuwo sam musamman miyan yauƙi ko wani taga yanaci sai zuciyarta ya hau tashi. Wanda Asma'u ta kawo ta buɗa, a hankali ta saki ajiyar zuciya ganin lafiyayyen yam balls ne a kular farko, ta biyu farfesun naman kaza ne yanata tashin ƙamshin attaruhu da albasa. Sai jug irin mai riƙe zafi ɗin nan ɗauke da kunun gyaɗa da yay ƙyau yanata ƙamshi har da su ƙwa-ƙwa a cikinsa. Sai shayi a flaks da yaji kayan ƙamshi shima, anan kam ajiyar zuciya ta sauke harda sakin guntun murmushi ta zuba kunun gyaɗar da farfesu kaɗan ta fara tsakura tana bin Asma'u da keta aikinta a nutse da kallo da sauraren labarin da take bata akan yanda suke matuƙar jin daɗin abinda take yi game da case ɗin fyaɗe. Haka kawai jin ƙaunar yarinyar take a ranta, balle jin abinda take faɗa na yanayin da suke shiga na jin daɗi har itama tana burin zama lawyer kamarta........✍️

         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣3️⃣



.......A ɓangaren Smart kam suna isa gidan sashen Abba ya nufa domin gaidasa, yayinda Huwaila ta shige ciki fuuu tana ƙunƙuni. A falo ta iske Umma zaune suna karin kumallo da sauran ƴan uwanta da ƴaƴansu da duk ke shirin wucewa gida a yau tunda biki dai ya tashi. Umma ta bita da kallo kamar a firgice, sai dai kasancewar bata son tace wani abu a gaban sauran yaran ya sata ƙyafta mata ido ta cigaba da cin abincinta. Amma Huwaila sai ta dinga ƙunƙuni, da ga ƙarshe dai ta fara bama ƴan uwanta labarin ƙarya da gaskiya akan wai an mata wulaƙanci a gidan Smart, sun shige ɗaki sun barta, yanzu kuma yace Asma'u ta zauna can ita kuma ya taso ƙeyarta sun dawo. Da yawansu sun hau sun zauna. Sai Ismaha ce dai ta ce, “Humm Huwaila gaskiya ban yarda ba. Koda ace hakan da kika faɗa ma ta faru sai dai idan yanada manufarsa, kowa dai yasan Yaya Hydar a gidan nan kan rashin nuna bambanci a tsakaninmu da ƴan ɗakinsu. Da dai Yaya Salim kikace yayi hakan ko musa miki bazanyi ba...” tana gama faɗa ta tashi tai ficewarta. Cikin ƙanƙanin lokaci falon ya kaure da ka-ce-na-ce, kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Da wannan damar Umma da hankalinta sam ba'a jikinta yake ba ta miƙe tana kama hannun Huwaila suka shige uwar ɗaka.
        “K lafiya? Ina abinda na aikeki yi na ganki hannu rabbana”.
    “To Umma ya kike so ki ganni, a gabanki fa na faɗi irin wulaƙanci da akai min a gidan can”.
    “Ke tafi can wawuyar banza da wofi, kin ko san muhimmancin abinda na turaki yi da zaki dawo min da wani shirmenki na banza. Wai ke ko Huwaila yaushe ne zakiyi hankali a rayuwarki. Ƙanwar-ƙanwarki Asma'u har ta fiki wayo amma ke gallaƙeƙiyar budurwa da ake shirinma aure baki son ciwon uwarki ba....”
           “To wai ni Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Ni Wlhy ko ƙyallin wani kayan da suka saka jiya suka cire ban wani gani ba a gidan. Tunda kina ganin banyi miki ƙoƙari ba sai kije da kanki ai”. Tana gama faɗa tai waje abinta. Duk irin kiran da Umman ke ƙwala mata ko waiwayenta batai ba. Sai ma jiyo muryar Smart da tai alamar ya shigo gaishe ta. Sai dai yanda taji ƴaƴan nata na gaishesa a gatsine ya sata fita wuff dan taga suna neman ɓata mata shiri, saboda Malam Na-zuru ya jaddada mata a waya ɗazun da safe sai fa ta rage nuna abinda ke ranta a garesu, musamman ma matar tasa tai duk yanda zatayi ta shiga jikin yarinyar hakanne zai sakasu cin nasara cikin sauƙi. Cike da fara'a ta amsa gaisuwar da Smart ke mata tana tambayar ya baƙuntar sabon waje da amarya. Kansa a ƙasa cikin jin nauyi da girmamawa ya ce “Lafiya Lau tana gaishe ku”.
      “To madalla ALLAH yay muku albarka. Kamayi ƙoƙari ai da ka fito tunda safe haka banyi zaton yau zamuga idonka ba a gidan nan kwata-kwata.”
     Shi dai murmushi kawai yay yana miƙewa batare da ya bata amsa ba ya fice abinsa. Sashen Ammah ya shiga dan ya gaisa da mama da Aunty Amarya. Nan ma dai zama yay suna gaisawa da dangin mahaifiyarsa da ke ta jansa da kiransa babansu babansu. Daga haka suka sake ɗora masa da nasiha mai ratsa jiki tare da addu'oin zaman lafiya mai ɗorawa da zuri'a mai albarka. Bai jima ba sosai Adda Suwaiba tace ya tashi yaje yabar matarsa dan ma Asma'u nacan. Daga haka yay musu sallama ya fito bayan sun ɗanyi magana da Ammah a gefe ya kawo kuɗin jikinsa na gudunmawa da ya ɗan sassamu ya bata akan ta basu suyi kuɗin mota. Daga haka ya juya ya tafi akan zuwa anjima zai dawo kafin su tafi gidan su Lulu godiya ta al'ada da ango kanje da abokansa gidan dangin amarya washe garin tashin biki.....

      Har lokacin da ya shigo gidan Lulu na zaune tana tsakurar abincin nan, yayinda Asma'u ke ƙarasa saka turaren ruwa a carpet ɗin falon da labuloli. Ɗaga kai kawai tai ta kallesa ta maida kan abincinta batare data amsa masa sallamar ba. Sai Asma'u ce ta amsa tana masa sannu da zuwa cikin girmamawa. Amsa mata yay da kansa kawai. Da yake hankalinta ba'a kansu yake ba ita bama ta lura Lulu bata amsa masa sallama ba. Ta kammala ta maida turaren a inda ta ɗauka Lulun na mata sannu cikin murmushi. Ta gefen ido yake kallonta da mamakin yanda take sakema Asma'un. Baki ya ɗan taɓe batare da ya kalla Asma'un ba ya ce, “K zoki bani abincin nan na karya”. Amsa masa tai da to Yaya, sannan ta nufi kitchen ɗin ɗakko masa plate kamar yanda ta ɗakkoma Lulu ɗazun. Sai lokacin ya dubi Lulun a kaikaice, cikin deep voice ɗin nan tashi a dakensa ya ce, “Ke baki iya amsa sallama ba balle sannu da zuwa ko, amma kin iya tasa abinci kina ci”.
       “Sauƙin ma bakai ka bani ba balle kamun gori shishshigi master”. Ta faɗa tana balla masa harara. Lips ɗin ta dake motsawa a hankali yabi da kallo, sai kuma ya ɗan cije nasa da ɗauke kansa yana jin wata irin kasala na sake saukar masa fiye data barcin da yake ji. Bai sake magana ba saboda fitowar Asma'u, ta jawo basket ɗin gabansa tana buɗe kulolin da faɗin, “Yaya mizan zuba maka bayan kunu dan nasan dai shikam ba canji”. Ƙaramar hararar data sata saki siririyar dariya ya sakamar mata, sai kuma ya nuna mata yam balls ɗin da faɗin, “Karki sakama kunun komai”. Da to ta amsa masa, sannan ta zuba komai yanda ya kamata kuma dai-dai adadin da tasan zai cinye dan shima yam balls ɗin ma masoyinsa ne. Lulu da ke satar kallon abincin ta gefen ido ta ce, “Hu'umm kuma duk cinyesa zakayi?”. Yanda tai maganar da ɗan waro Luluu eyes ɗinta waje tana riƙe haɓa ya bama Asma'u dariya, sai dai ta danneta da ƙyar ta tashi ta fice da ga falon gaba ɗaya taje waje tai abarta son rai. 
       Smart ya ɗan laɓe baki batare da ya kalleta ba ya fara cin abincinsa da faɗin, “Mi kike tsoro ne a cikin cin abincin nawa? Kina gudun kar ki gagara ɗaukata ne?” ya ƙare maganar da ɗago idanunsa da take kira na macizai ya zuba mata su. Baki ta taɓe cikin masa kallo mai kama da harara ta ce, “Kamar ya? Miya shafen da nauyinka?”.
      A karan farko ya saki wani makirin murmushin da aduk sanda yayisa yake tunzurata dan tafi kwallonsa a murmushin rainin hankali ya cigaba da cin abincinsa. Siririn tsaki taja da ɗauke kanta itama ta cigaba da shan romon farfesun da yaci ace tama manta ta gama ci. Amma ina gayu da yanayinta yasa anata tsakurarsa, ga shi yamata daɗi matuƙa ta yanda ta gagara ajiyesa. Duk da yaji tsakin nata bai sake yin magana ba ya maida hankalinsa ga cin abincin harya kammala zai tashi, sai lokacinne itama take kammalawar. Asma'u ya ƙwalama kira, ta amsa da ga waje dan ta gama zagaye gidan ne tana jin daɗin kallon flowers ɗin da aka ƙawatashi da su. “Zoki wuce gida” ya faɗa yana miƙa mata ɗari biyu. Lulu Asma'u ta kalla cikin shagwaɓe fuska, itama Lulun shi take kallo, ta ce, “Kamarya tazo ta tafi? Nan fa zata kwana”. Yanda take maganar itama kamar a shagwaɓa-shagwaɓa ya sashi kallonta. Sai kuma ya ce, “A ina ɗin zata kwana? No karma ku fara abinda bazaku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login