Showing 54001 words to 57000 words out of 163036 words

Chapter 19 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

449

riga ka ƙwallafa ranka ka zama cingam boy kuma ita bazata samu ta sauƙi ba kawai kasa su Dad gaba aje maka neman aurenta.....”
       “Baka da hankali! Dad fa? Kasan waye Dad kuwa?!”.
     “Calm dawn mana my man. Lamarin fa duk lissafine. Yanda Dad keda alfarma na tabbatar sun san juna da babanta tunda kace itama ƴar manya ce. So da zarar magana ta shiga kai kuma sai kaita jan ra'ayinta harka samu cikar burinka. Daga haka mu ƙirƙirar mata laifin da shi Dad ɗin da kansa zai ce bazaka aurenta ba”.
     “Woow! Woow woow my dear wannan salon yayi kuma zai ƙayatar. Sannan ita kanta zan firgita lissafinta tasan ba irinmu ake ja a ƙasa ba. A safiyar yau ɗin nan zan zauna da Dad, nasan zai matuƙar ɗaukar abin da muhimmanci tunda dama burinsa kenan shi da Mom. Kai dai ALLAH ya barka da cingom gal taita ƙarar maka da ruwan kai bye”. Ya yanke wayar yana wani jin matuƙar farin ciki tamkar ya samu Lulu ƙamshi ɗin ya gama ne.
  
      Ni ko na ce, “Hummm!”
     

     ★★★

Kamar yanda Alh. Baita da Hon. Nakowa suka girgiza da jin Mawaddat ɗiya ce ga Alhaji Isma'il Jiƙamshi haka shima Hon. Misau yay matuƙar girgiza da batun. Dan abune da ko'a lissafin hasashe basu taɓa kawowa ransu ba. A take suka zauna teburin shawara. Dan kuwa tabbas wata dama ce a yanzu tazo hannunsu akan Alhaji Isma'il Jiƙamshin. Kuma lokaci ne na ɗaukar fansa da zai goge tarihin baya labarin yazo da salon alƙalamin da sune zasu zama masu rubuta shi.
     Tsaf suka kammala tsara komai a yanda suke buƙata. Fatansu kawai nasara da kuma sake sabon bincike dan ƙara riƙe hujjoji masu ƙarfi musamman akan Alhaji Sufi Garko da suka yanke shawarar tunkara a farko. Dan tabbas babban ɗaurin huhun goro suka shirya yima uban da ƴar gaba ɗaya dan su kasance gaba ɗaya a tafin hannunsu. Basu sa wasa ba tun a ranar suka nema appointment ɗin ganawa da babban ɗan kasuwar, kuma ƙusa a ɓangaren siyasar arewacin kasar musamman ma Kanon ta dabo Alhaji Sufi Ado Garko. Tsoho da kuɗi kenan abokin tafiyar yara, manyan kuwa baba suke kiransa dan ya kere ya kuma zarce koda a tsaransa. An tabbatar musu yaje Umrah sai dai nan da kwanaki biyu idan ya dawo washe gari su shigo. Sun samu wannan damar ne dalilin shaƙama babban yaronsa kuɗaɗe masu kauri, sai kuma mulki da Hon. Nakowa da Hon. Misau ke riƙe da shi wannan ma babban makami ne.....

     ★★★....

Ga Alhaji Sulaiman Sufi Garko ma ya gama shiryawa tsaf domin tunkarar mahaifin nasa game da auren Tajuddeen da Mawaddat. Dan a wannan karon ya ɗau aniyar koda yardarta, ko babu sai wanan auren ya ƙullun. Dan ya gama tanadar kalaman da zai tsara mahaifin nasa da su tsaf komai ya tafi dai-dai. Tajuddeen ya samu cikar burin shima ya samu nashi.....

      ★★★....

A ɓangaren Lulu ƙamshi da bata san mi suke ba gaba ɗaya hankalinta na kan case ɗin yarinya da akaima fyaɗe ne. Dan anata neman mijin matar amma an rasashi wai ya gudu yabar gari tun a randa yay abun. Wannan takaicin ne ya taru yay mata yawa ta tada hankalin su Sha'aibu ɗan sanda dama na duk wanda ke mata aiki idan irin wannan case ɗin ya taso. Hatta Daddy bata barsa ya huta ba. Ga takaicin Smart yaƙi dawowa aiki itako ta gaji da tuƙi dan sunata zirga-zirga. Shiko Uncle Yousuf ne yace ya zauna gida ya huta har sai jikinsa yay masa ƙarfi. A washe garin kwana na biyu da take saka ran dawowar Grandpa ɗinta da ga umra duk da tarin ayyukanta haka tai wancakali da su ta shiga tawagar ƴan tarbarsa a airport dan ya kwana biyu baya Nigeria, saboda daga uk ganin doctor ɗinsa ya wuce Saudiya Umrah. Tana kewarsa dan tana matuƙar so da ƙaunar kakan nata daya haifi mahaifiyarta da bata sani ba sai a hoto. Shi takema kallon uwa ga shi kuma shine kaɗai ya rage mata a kakanninta dama. Shima kuma a karan kansa yana nuna mata tsagwaron soyayya kasancewar ta ɗiya ga Mawaddat dinsa da ya rasa dan ita kaɗai ya taɓa rasawa a cikin ƴaƴansa shiyyasa yake matuƙar tausayin Lulu.
          Ƙarfe kusan sha biyu jirginsu ya sauka. Duk da hango ƴan uwanta jikokin Alh. Sufi Garko da tai su Tajuddeen da sukazo tarbarsa suma ƙin fitowa tai tana daga motar har sai da taji ance jirgin da ya taso da ga Saudiyan ya sauka sannan ta fita. Sanye take cikin gawn ta material mai taushi da santsi da sukai matuƙar mata ƙyau da fidda mata ƙyaƙyƙyawar surarta kamar wata ƴar tsanar roba. Ɗaurin kanta da Amrah (Hussaina) tai mata yayi ƙyau ya kuma rufe mata gashi, sai ta gaba kaɗan da aka zamashi ake iya ganinsa baƙi siɗik a kwance, Kasancewar a ɗaure yake da ribbon sai yay tilluwa a cikin ɗankwalin da aka rufesa da shi ruf. Siririn mayafi kalar material ɗin ta ɗora a kafaɗa babu zancen yafawa. Sai dogon takalmi kamar koyaushe duk da kuwa ita ɗin doguwa ce amma bacan ba tsaka tsaki. Ƙaramar handbag ɗin hanunta ta sake gyarawa da gilashin idonta da ya sake ƙawata kwalliyar tata duk da kuwa a fuskarta babu ko ɗigon kwalliya bayan hoda dan itafa bata kwalliya, sai lips glose data saka a lips ɗinta kaɗan. Yanda take taku kamar wata tarwaɗa da sautin da takalmanta ke badawa ga ƙamshin turarenta data bulbula ya sata janyo hankulan mutane gareta musamman na kusa da ita. Sosai numfashin Tajuddeen ya dinga kaikawo a ƙirji har ta ƙaraso garesu. Ya haɗiye busashen yawun da ya kasa wuce masa a maƙoshi yana ɗan sakin murmushi. Ɗauke kanta tai kamar bata gansa ba, sai ma yatsu biyu data ɗaga musu a taƙaice tare da faɗin, “Hy girls and boys”. Duk wanda yasan Lulu a family ɗin yasan ba kanwar lasa bace, ba kuma wani take ragawa ba. Duk da mafi yawansu sunada labarin tushen asalin arzikin mahaifin nata da ga kakansune wani bai isa furtawa ba tai masa wankin babban bargo ita babu ruwanta. Yanda tai musu gaisuwar cike da raini ya zafi wasu musamman ma matan amma babu wanda ya nuna, to ita bama ta tsaya sauraren amsawar tasu ba tuni tai gaba, dan a dai-dai nan Alhaji Sufi Garko ke fitowa da ga jirgi gefensa p.a ɗinsa ne da shima zai iya kai sa'annin su Daddy. Lallai ya tsufa kam, damma harka irin ta masu hannu da shuni mai wahalar sha'ani. Amma irin wannan tsoho ai kamata yay ace yana zaune gida jikoki zagaye da shi yana hutawa kawai. Cike da ɗoki da farin cikin murmushi mai bayyana haƙora da ke da tsada a fuskar Lulu dan kafin ka gansa ka yara ta nufi kakan nata ta rungume. Shima tashi fuskar ƙawace da murmushin ya tarbi abarsa yana mai farin ciki da jin kewarta har cikin ransa. Sai da ta gama nata farin cikin sannan sauran yaran suma suka matso garesa su Tajuddeen. Suma ya nuna jin daɗin ganinsu dan yana son ƴan jikokin nasa da a yanzu duk suka zama manya samari da ƴammata har ma da masu aure, dan su Lulu kusan sune ƙanana ma duk da dai suma akwai waɗanda suka girma. Da ga haka aka ɗunguma zuwa gida, inda Lulu ta tubure motarta zai shiga dole kuma akai hakan dan kowa yasan rigimarta original ce. Yanzu kam a hankali take tuƙin dan Alhaji Sufi yayi gargaɗi. Daga shi sai ita ne a motar, dan haka taketa masa hira shiko yan biye mata. Tausayinta yake ji fiye da kowa a cikin zuri'arsa saboda maraicinta, ga kuma ƙaunar da yakema mahaifiyarta itama ya shafeta. A gidan ma koda suka iso sai suka samu ƴaƴansa maza da mata da ke cike da gidan duk dai akan dawowar tasa. A duk sanda akai irin wannan taron da wahala kaga Lulu batai kuka ba koda a ɓoye ne saboda jin buƙatar mahaifiyarta itama. Yanzu ɗin ma da ƙyar take iya danne hawayenta, tama ƙi shiga gidan, tana ganin ƴaƴansa sun janyesa ta zame jikinta ta gudu. Tuƙi take tana hawaye da jin kewa mai tsanani, tasan Mommy uwa ce a gareta, amma da gaske tana buƙatar ɗumin mahaifiyarta koda sau ɗaya ne inda ace hakan zai yuwu, sai dai tasan har gaban abada bazai yiwun ba kuma. Gefen titi ta gangara a hankali ta kashe motar ma baki ɗaya ta lafe cikin kujerar idanunta lumshe tai shiru, so take tai kuka amma tana ƙoƙarin hana kanta hakan. Bata cika son shan komai da rana ba musamman a lokacin aiki, sai dai a yanzu babu abinda tafi buƙata kamar tasha ɗin. Duk yanda taso hana kanta taji shan kawai take buƙata. Cikin rawar jiki ta jawo handbag ɗinta, faudanta ta zaro tare da buɗeta acan ƙasa ta ciro wata takarda da'aka naɗa kamar ƙullin magani. Tana warwareta sai ga ƙwayoyi a ciki. Gaba ɗaya kusan fin biyar duk da ƙananu ne sosai ta afa batare da neman ruwa ba ta haɗe abinta tana wani sauke ajiyar zuciya. (Kamar wadda ta haɗu da uwar tata da take nema😔🤦. Ya rabbi ka shiryemu ka shirya mana zuri'a ka rabamu da mummunar ƙaddara😭🙏)...........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*


𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣2️⃣



........Motar taima key ta cigaba da tafiya duk da ta fara jin kanta ya ɗauka. Da ƙyar ta iya kai kanta office saboda abinda tasha ɗin ya fara aikinsa. A yanda ta shiga duk da bawai tana layi bane yasa mutane da yawa ɗan binta da kallo. Office kawai ta faɗa tare da maidashi ta rufe harda saka key. Tai jifa da handbag ɗinta da key da takalma har ma da mayafi da ɗan kwali. Zama tai jikin kujera ta dunƙule jikinta waje guda tana mai tura kanta data dafe da duka hannu biyu tsakanin ƙafafunta. Surutai takeyi ƙasa-ƙasa irin wanda idan ba kusa da ita kake sosai ba bazaka taɓa iya fahimta ba...

       _(Kai jama'a shaye-shaye baiyi ba. Shaye-shaye kan zubar da mutuncinka kowane matsayi ka taka. Yana maidaka baya komai ƙarfin ikon ka. Yana ƙasƙantar da kai komai darajarka. Ga lafiyarka kaima da ɓarnar kuɗi. Miyasa ƴan uwa? Mike birgemu? Mike ruɗarmu?. Kuɗi? Ƙawaye? Abokai? Samari? Gata? Kokuwa son zuciya?. Idan duk sune mu tabbata masu ƙarewa ne kamar ba'ai ba. Masu zama labarine kamar basu zo ba. Shaye-shaye wafce mana dukkan muhimman damammaki yake na cigaban rayuwarmu ta duniya da lahira. Kuduba ku gani, duk shekaru irin na Mawaddat bama tasan minene addininta ba, duk da tarin damammakin rayuwa da ALLAH ya bata wannan illar ɗaya take ta shaye-shaye da ke tare da rayuwarta na ƙoƙarin maidata baya. Tun tana ganin tana kiyayewa akan aikinta gashi ta fara kuma a cikin lokacin aikin, mi kuke tunani? Wataran aikin ma sai ta gagara yinsa gaba ɗaya. Da ga sanda ta rasa wannan damar kuma shike nan ta ƙarasa rushewar baki ɗaya sai jiran ta fara bin bola kuma duk da gatan ta😭. ALLAH ka shiryemu ka shiryar mana da zuri'armu da duk masu wannan mummunar ɗabia)._

     
      ★★.....

       Bayan sallar la'asar Daddy da Uncle Yousuf suma suka shiga jerin ƴan sannu da zuwa ga Alhaji Sufi Garko. Ya nuna farin cikin ganinsu. Dan mutum ne da ya san mutuntawa. Kallo yake musu suma irin na ƴaƴa tun kan aurattayya ta shiga tsakanin ɗiyarsa da Daddy balle yanzu ga Mawaddat ta ratsa duk da babu ɗiyar tasa data zama sanadi a duniya. A hirarsu ne ma suke jin cewar Mawaddat ce ta ɗakkosa da ga airport, yana ƙyautata zaton ma har yanzu tana a gidan tare da ƴan uwanta. Daddy yaji daɗin hakan har Uncle Yousuf ma kansa. Basu nemeta bata suka cigaba da hirarsu hankali kwance. Shigowar Alhaji Sulaiman (mahaifin Tajuddeen) ce ta saka Daddy yin shiru, sai kuma ya dubi Alh. Sufi Garko da suke kira da Baba cikin girmamawa ya ce, “Baba inaga bara mu wuce ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne”.
       Alh. Sufi ya tsatstsare Daddy da idanu batare da ya amsa ba, sai kuma ya maida dubansa ga ɗansa Alh. Sulaiman da ya koma can gefe zai zauna. Cikin bada umarni ya ce, “Isma'il koma ka zauna”. Babu musu Daddy ya koma ya zauna ɗin. Ya maida dubansa ga Alh. Sulaiman da faɗin, “Kaima zonan”. Gaba ɗayansu a gabansa sukaje suka zauna kowa na hararar ɗan uwansa kamar wasu ƙananan yara.
      “Ku yanzu kuna ganin wannan rayuwar bazaku ajiyeta ba. Ko a tinaninku har yanzu ku yarane? Ku duba gashin kawunanku furfura duk ta gitta a ciki. Tunda kun gagara faɗamin matsalarku a tsahon shekarun nan ni bazan cigaba da damuwa da sai na sani ba. Sai dai ku sani idan har abinda ya shafeku kuka bari ya shafi zuri'arku bazan yafe ba. Ku shaida hakan ko bayan ƙasa ta rufe idanuna ne”.
    (Anzo wajen) cewar Alh. Sulaiman a zuciya. Dan haka ya gyara zama cike da makirci ya sake raunana muryarsa. “Baba ni ba laifina bane, tunda kowa shaidane na biyo hanyar da zamu sasanta da shi a shekarun baya amma ya koma bayan fage ya zuge yarinya komai ya sake rushewa. Shine ya sakama ransa ni maƙiyinsa ne kawai. Shiyyasa naso haɗin auren Tajuddeen da Mawaddat dan ya tabbatar ba hakan bane ba. Kuma ko a yanzu in har zai amince ya cire komai a ransa ni a shirye nake komai ya zama labari. Mu kuma dunƙule ƴaƴanmu waje guda matsayin ma'aurata dan ƙara danƙon zumincinmu”.
        Wani irin kallon ɓacin rai Daddy ke masa. Sai dai baice komai ba. Alh. Sulaiman da ke masa kallon ƙasa-ƙasa ya saki wani irin makirin murmushi da kashe masa ido ɗaya. Ƙara tunzura zuciyar Daddy tai amma sai ya danne dan jin Baba ya fara faɗin, “Ni kaina zanso wannan haɗin zumincin, zan kuma so ya zama sanadin canja wannan gabar taku. Sai dai kuma bazan so ya rikiɗe daga manufarmu ya koma abinda bashi muke fata ba zumincin ya taɓarɓare ma fiye da yanzu....”
       “Amma Baba ai yaran suna matuƙar son junansu. Dama tun farko matsalarmu ce ta tilastasu haƙura a wancan karon ma”. Alh. Sulaiman ya faɗa yana sake sakin makirin murmushi. Baba da ba ganin abinda ke faruwa yake ba ya kai dubansa ga Daddy da baice komai ba. “Isma'il bakace komai ba. Abinda ɗan uwanka ke faɗa gaskiya ne?”.
          Murmushin mugunta Daddy dake ƙulla murtanin da zai maida ga Alh. Sulaiman ya saki. Cike da sake girmamawa ga surukin nasa kuma ogansa ya jinjina kansa. “Baba duk ina saurarensa. Sai dai na tafi wani tunani ne, kenan Mawaddat ƙarya tamun ko kuwa rashin jin nata ne ya sata kawo min wani a matsayin miji alhalin suna tare da Tajuddeen har yanzu...”
        “Miji?”.
    Alh. Sulaiman ya faɗa kamar a ɗan razane. Shiko Baba murmushi yayi da faɗin “Miji Mawaddat ɗin ta fitar?”.
   “Eh Baba. Dan dama dawowarka muke zaman jira muzo maka da batun. Saboda yanata ma damuwar turo magabatansa amma ina dakatarwa da cewar har sai ka dawo tukunna”.
        “Wlhy ƙarya kake Isma'il! Wannan makirci ne ka ƙulla dan kar Mawaddat ta auri Tajuddeen, an gaya maka tsoronka nakeji wai ne da na gagara ɗaukar mataki a kanka tun a baya”. Alh. Sulaiman ya faɗa yana miƙewa zumbur. Gaba ɗaya falon suka zuba masa ido. Sai kuma duk ya daburce dan fahimtar yana neman yin ɓaran ɓarama fa.
   “Ka ɗauki mataki a kansa! A wane dalili Sulaiman?”. Baba ya katse shirun. Kame-kame Alh. Sulaiman ya fara, hakan ya bama Daddy damar sakin murmushin mugunta. Sai kuma ya dubi Baba. “Baba ƙyalesa kawai shirmensa ne. Kasan shi Sulaiman idan ya fusata akan abu baida fahimta. Sannan ya iya sakin duk maganar da tazo masa a baki koda ba hakan bane a ransa. Ni dai ba ƙin haɗin auren Mawaddat da Tajuddeen nake ba. Kawai shashancin da tayi ne na kawo min wani matsayin miji da har na sanar da nawa dangin dama jiranka kawai muke ka dawo a tsaida biki alhalin tana tare da Tajuddeen kuma ne yasa ma harna faɗa. Amma ayi haƙuri ni zanje ga babanta Yousuf mu sameta a nutse na mata tambayoyi dan nasan halinta bajin magana take ba. Kaga idan Tajuddeen take so ni bazan hana ba, sai nasan dabarar yi wancan ya janye a rabu lafiya mutuncin kowa bai zube ba....”
       “Mizai hana w kirata yanzu ayita ta ƙare”.
   Cewar Alh. Sulaiman. Shiru kamar Baba bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da faɗin, “Ku dukanku kunzo da shawara mai ƙyau kuma duk na gamsu da maganarku. Sai dai muyi haƙurin goben sai a zauna a nutse kan maganar. Amma yanzu ina son a kiramin Mawaddat da Tajuddeen”.
      Sosai hankalin Daddy ya tashi, amma ya danne a ransa yana mai addu'ar ALLAH yasa kada Mawaddat ta watsa masa ƙasa a ido. Dan shifa bazai taɓa yarda ya haɗa zuri'a da Sulaiman ba. Shi kansa Uncle Yousuf zancen Yayan nasa ya sakashi a ruɗani. Duk da yasan akwai ƴar tsamar da har yanzu bai san tushen ta ba tsakanin ɗan uwan nasa da Alh. Sulaiman bai san dalilinsa na ambaton wani ba matsayin Mawaddat ta kawo bayan yasan ba hakan bane ba. Kusan a tare suka saki ajiyar zuciya shi da Daddy lokacin da ɗan aiken ya dawo ya tabbatar musu ai Mawaddat ance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login