Showing 99001 words to 102000 words out of 163036 words

Chapter 34 - Furar Danko Book 1 Hausa Novel Complete

19 Dec 2024

473

Hussain ya sake riƙewa gam ya hana hakan. Duk sai sukai diri-diri da idanu (kamar an kama suruki a ɗakin ƙawar kakar matarsa😂😜) cikin wani irin malalacin yanayi ta sakar ma Smart kasalalliyar Harara. Sai kawai ya samu kansa da ramawa shima. Shi Hussain ma sai abin ya bashi dariya. Amma sai ya danne daƙyar baiyi ba ya sake matse hannayensu cikin na juna da faɗin, “Yayana Aliyu Hydar Zakin zaki ga amanar ƙanwata na baka, har abada bana son ka saki wannan hannun ya kasance cikin laluben naka dan ALLAH”.
         Smart da Adams apple ɗinsa keta kaikawo a maƙoshi ya saki murmushi mai sanyi da faɗin, “In sha ALLAHU Yaya Hussain. Na kuma gode”. Murmushin jin daɗi Hussain ya saki jin Smart ya kirashi da Yaya, duk da kuwa yasan Smart ɗin zai iya girmarsa da kusan shekaru biyar ma. Hannayen nasu ya saki yana kallon fuskar Lulu da tai wani irin yin takwaf-takwaf tana neman zame hanunta dake cikin na Smart shi kuma ya hana faruwar hakan ta hanyar damƙesa da kyau, kansa ya girgiza mata da ɗan lumshe idanu alamar lallashi irin na yaya da ƙanwa. Dole ta haɗiye abubuwan da ke mata kaikawo a zuciya da maƙoshi a tare, Hussain ya buɗe musu motar da Ahmad ke ciki yana jiransu a mazaunin driver. Ita ta fara shiga, sannan shima Smart ɗin ya shiga, sai kawai Hussain ya shiga gaba dan Uncle Yousuf ne duk ya tsara musu hakan saboda dai kar mutuniyar ta bada ƙafa🤣 dan tabbas zata iya maida hall ɗin kudanci da ga gabashin da yake a gine😂. Ganin Hussain ɗin kam ya sake saka mata nutsuwa da ƙwarin gwiwa harda sauke ajiyar zuciya kamar Smart ɗin yazo ɗauketa kenan😂. Bata ƙara yarda ta kallesa ba duk da harga ALLAH ya matuƙar canja mata tamkar bashi ba. Ta kuma saka pos ɗin ta a tsakkiyarsu alamar karma yace zai raɓeta. Shima dai dama baiyi niyyar hakan ba, shiyyasa yay zamansa sosai jikin ƙofa suka bada gaf sosai a tsakkiyar. Da ga Ahmad har Hussain sai da suka ji dariya a zukatansu saboda yanayin zaman amarya da angon. Ga shi kowa ya juya kai ya kalli waje tsabar babu ruwan wani da wani ma kenan. Sai da suka fara tafiya Hussain da Ahmad suka gaisa. Da ga haka sukacigaba da ƴar hirarsu a hankali su biyu har suka iso. Wajen fita ne fa dole dai Lulu ta haƙura Smart ya fara fita, dan shine ya buɗe mata da kansa ya kuma miƙa mata hannunsa alamar ta ɗora nata. Ƙaramar Harara tai masa tana ɗauke kanta, sai kawai ya cije lips ɗinsa tare da ranƙwafowa gaba ɗayansa yana tattare hannun rigarsa bayan ya cire link ɗin, miƙa hannun yay alamar zai ɗauketa. Da wani irin bala'in sauri ta waro duka manyan idanunta waje da faɗin, “Kuttt! Mi zakayi?!”.
        “Ɗaukarki mana. Ba haka kike buƙata ba Madam”. Ya faɗa cikin salon ɗage gira ɗaya da kashe ɗayan idon. Tsabar abinda ya tokare maƙoshin Lulu sai taji kamar ta buɗe dukan muryarta ta ƙwala ihun da kowa da ke hall ɗin sai ya fito ma. Ta tsani wannan Madam ɗin da yake kiranta da shi tun daga randa sukaje duba shi. Ganin yanda ta fara cika ya sashi ɗage duka hannayensa (alamar wanda yay surrender) da gyara ranƙwafar da yay yana dungure kansa da faɗin, “Kai Aliyun nan ka nutsu a gaban Madam kake”. Sai kawai ta ƙara watso masa harara da tura baki gaba. Da sauri ya ɗauke idanunsa dan harga ALLAH sai da ƙassan jikinsa suka amsa akan tura bakin nan. Hussain dake dariyar drama ɗin tasu ne ya katsesu da faɗin, “Sorry kinjin Sister bashi hannun kinga su Baba duk suna ciki shigowarku ake jira kawai a fara abinda ya tara mutane”. A hankali ta ɗago yatsunta uku batare data kallesa ba. Shima sai ya saka nasa ukun tsakkiya kamar yanda tayin yana ɗan taɓe baki kamar yanda tayi, sai da ya riƙo hanun nata baki ɗaya sannan ya rumtse cikin nashi. Koda ta fito bai yarda sun bar jikin motar ba sai da yasa ɗayan hannunsa da kansa ya gyagygyara mata rigar alƙyabbar da ƙyau yanda ta sake suturta kuma hakan bai hana fitar ƙyaun da tai ɗin ba. Da ga haka suka ƙarasa inda abokan ango dana amarya ke jira suka tafi a nutse kamar yanda ake raka amarya da ango ƴan gata zuwa ga hi table. Matuƙar birgewa sun burge mutane da yawa, yaro da babba ƴammata da samari. Taro ne da ya haɗa harda manyan mutane da iyaye da kakanni shiyyasa babu wata shiririta ko baɗala a cikinsa. Amarya da ango ma tunda aka kaisu mazauninsu hatta cake a zaunen suka yanka shi. Koda ta ɗibo danta bashi maimakon yin hakan saita lakata masa a hanci. Abin ya burge mutane da basu dariya, dan yanda tayi ɗin sai ka ɗauka duk cikin soyayya ne, itako tayi hakanne danta bashi haushi.
        Shima daya ɗibo ya kai mata baki, buɗewa tai tana shiryama ranta muguntar gallara masa cizo a yatsun dake riƙe da cake ɗin, amma sai da yaje gab da bakin nata sai ya juya hannun ya lunƙuma a nashi bakin yana mata gwalo. Ai hall ɗin kamar zai fashe dan dariya saboda yanda ta sakankance zatayi mugunta amma aka rusa mata plan. Pos ɗin hannunta ta ɗan buga masa a damtsen hannu tana hararasa kamar zatayi kuka dan haushi.
       “Aliyu abin tausayi wannan harara dai ka banu da ita kai kam. Anya an taɓa angon da yasha harara a ranar aurensa sama da ni?” ya faɗa yana mangare kansa da kansa. Karan farko ya bata dariya amma sai ta gimtse, tama ɗauke kanta gefe tana ɗan taɓe baki, dan yau sam bata da ƙarfin yin masifa kuma. Da ƙyar aka samu hall ɗin ya lafa da dariyar batun cake aka cigaba da abinda ya tara mutane. Ko sau ɗaya Smart bai yarda ya tashi ba hakama Lulu bai bari ta tashi ba. Da an buƙaci ganinta a wajen fili zai riƙe mata hannu ya girgiza kansa, itama ɗin dama bata da sha'awar tashin, saita fisge hanunta tana harararsa dan yau ita kaɗai aketa faman antaya masa buhu-buhu. Har fa dai MC ya fahimci ango bai san amaryarsa ta tashi kamar yanda shima bai tashi ba. Masu musu liƙi ma dai sai dai su samesu anan. Alhamdullah duk wanda ya shigo wajen nan zai tabbatar maka yaci ya ƙoshi har ma da ƙullar takeaway,  Smart ya gaisa da mutanen da bai taɓa tunanin ganinsu koda a zahirin rayuwa ba, dan ƴan siyasa sun halarci taron nan matuƙa da manyan ƴan kasuwa. Har akai aka tashi bayan cake ɗin nan da ruwa baici komai ba a wajen, hakama Lulu ita daman cikin nata ya riga ya naɗe abincin ba damunta yay sosai ba. Ganin dare yayi dan sha biyu ta gota sanda aka tashi Uncle Yousuf yace su Smart ɗin suje gida abinsu zai koma da Lulu gida, dan tun a hall ɗin ya ga Smart nata faman dafe kai alamar bayajin daɗi dauriya kawai yake yi. Yako ji daɗin hakan da Uncle Yousuf ɗin yay musu, itama kuma mai gayya mai aikin taji daɗin hakan, dan ko sallama bata tsaya sunyi ba tai gaba tai shigewarta mota tana zare alƙyabba ɗin tata datai mugun damunta ita da ɗaurin ɗan kwalin....

*_WASHE GARI_*

   Washe gari safiyar Lahadi aka tashi da shirin kai amarya Lulu. Dan haka da safe Uncle Yousuf ya ɗauketa da kansa ya kaita gidan Baba. Inda yayye da ƙannen mahaifiyarta suka taru domin mata nasiha. Alh. Sulaiman ne kawai babu, sosai zuciyar Lulu tai matuƙar rauni, dan mahaifiyarta ce kawai babu a wajen bayan mahaifin Tajuddeen. Ita kaɗai suka taɓa rasawa a cikinsu........✍️

         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥



*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗



           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻


𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣6️⃣



........Kuka ne sosai ya kufce mata, dan matuƙa tana so da begen mahaifiyarta. (Dan Lulu ta kasance irin yaran nan ne masu ƙulafucin uwa, sai kuma gashi ALLAH bai ƙaddara zata rayu da ita ba) kukan nata ya sake karya zuciyar iyayen nata, haka ma Baba duk da dauriyarsa sai da yaji ƙwalla sun cika masa ido. Hannunta ya kama ya zaunar a kusa da shi tare da ɗora kanta a kafaɗarsa ta dama yana ɗan bubbuga bayanta alamar lallashi. Sai da suka samu taɗan tsagaita kukan sai ajiyar zuciya da take faman saki sannan baba ya fara mata nasiha. Bayan ya gama kowa a falon yay tasa. Kakarta da suke kira Dada ma dai ta danne abinda ke ƙasan ranta na ƙiyayyar auren tai mata nasiha sama-sama, dan ta ɗauki alwashin sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen raba wannan auren ƙaddarar. Komai da suke faɗa yana shiga kunnen Lulu, sai dai zuciyarta na fassara komai da gargajiyanci da kuma tsauri da yawa saboda ita tunaninta daban da nasu kasancewar babu ilimin addini a tare da ita. Kuka ma da sukaga tanayi na tuna mahaifiyarta ne kawai babu na aure dan a wawtarta auren nan dai na wata ɗaya ne kacal. Duk wata ƙyauta da iyayen nata suka shirya bata anan wajen suka bata ita kamar yanda tsarin family ɗin yake. Bayan an gama Uncle Khamil da Uncle Shu'aib suka ɗauke ta suka maida gidan Daddy dan Uncle Yousuf yana ajiyeta ya juya. Acan ɗin ma dai bayan sallar azhar Daddy da Uncle Yousuf, Mommy aunty Saliha da gayyar iyaye ƴan jiƙamshi suka zagayeta da tasu nasihar, duk da dai Daddy baice komai ba, sakamakon gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, jikinsa duk a sanyaye yake alamar damuwar rabuwa da ƴar tashi. Sai dai yana ƙoƙarin dannewa amma hakan ya gagara. Bayan tashi da ga wannan zaman aka cigaba da kimtse-kimtsen tafiya da amarya, yayinda Aunty Saliha ta sake ɗaukar Lulu ta kaima matan nan masu gyarata suka sake murjeta tas da kayan gyaransu na musamman da tarin ƙamshi kala-kala. Ba kuma a maidata gidan Daddy ba sai huɗu na yamma cikin shirin miƙata gidan iyayen mijinta. Tayi ƙyau matuƙa cikin atamfar da Aunty Saliha ta bata ta saka. Aka kuma ɗora mata alƙyabba ƴar ubansu baƙa mai kwalliyar golden da fari kaɗan, sai stones da suka sake ƙawatata. Shara-shara alƙyabbar take. Takalmanta yau ma flat ne baƙaƙe. Babu kwalliya ko ɗis a fuskarta dan tace bata so. Sai dai hakan bai hanata zama mai cika ido da kwarjini irin na amare ba, ga gyara tasha na fitar hankali dama fatar nan ta sake wani irin ƙyau kamar madara a sabuwar ƙwarya (Dangin Smart ban son jealous 🥱😉) Hankalin Lulu bai tashi ba sai da taga Daddy na hawaye sanda aka fito da ita yana riƙe da hannunta zai sakata a motar da Hassan zai ja, dan sune zasu mata rakkiya shi da Hussain da Mubeen. Sai motar ƴan rakkiyar amaryar su biyosu a baya. Duk da abokan ango sunzo kasancewar amaryar ƴar dangi ce akwai zugar motoci da ga family ɗin biyu na Jiƙamshi da Garko da zasu bisu da nasu motocin. Ba Daddy kawai ba Uncle Yousuf kansa yana can falon Daddyn yana sharce hawaye yamaƙi fitowa shi. Lulu da duk taji karaya tamkar ba ita ɗin nan ba ta rungume Daddy ta saki kuka mai ban tausayi. Itafa auren nan baisa taji komai, amma wasu abubuwa da ga zuri'ar tata kansa zuciyarta ta motsu. Da ƙyar Uncle Khamil ya janye Lulu a jikin Daddy aka sanyata a mota, Hussain da Mubeen suka sata a tsakkiya, gaba kuma Amrah da Afrah ne sai Hassan da zaija motar.
      Masha ALLAH motocin rakkiyar Lulu sun ratsa kwaryar Kano ne tamkar wata gwamna zata gitta dan gatan da zuri'arta suka nuna mata. Duk inda suka ratsa sai anso jin wanene haka? Koda babu mai bada amsa. A haka suka iso anguwar fagge layin su Smart. Yanda aka jera motocin tun daga ƙofar gidansu har kusan ƙarshen titin ya sake ɗaukar hankali matuƙa, hatta mata dake cikin gidaje fitowa suke leƙen wannan sabon lamari, lallai an sake shaida Smart kam dai ya ɗakko ƴar gidan madara.
      Smart da ƴan uwansa mazan gidansu suna falon Abba daya tarasu su duka amaryar ta iso. Daga ɗakin suna iya jin surutai da gidan ya ɗauka da kambama yawan motocin da suka rako amarya. Balle ma motar da aka kawota ciki ta musamman ce da Daddy ya saya mata matsayin gift na aure. Tasha adon ribbon kuwa da balun masha ALLAH. A hankali Smart da ke kusa da Rufa'i mai bi masa babban ɗan Mama ya lumshe idanunsa yana jin wani irin yanayi mai wahalar fassara na saukar masa. Addu'a ya shiga karantowa game da wannan aure nasa mai cike da rikici takowane ɓangare. Ita kanta amaryar da nata.. Addu'ar Smart kamar an saita dai-dai da fitowar Lulu amaryar ƙamshi da ga mota Mubeen riƙe da hannunta. Fuskarta rufe take ruff da hular alƙyabbar dan haka ba'a iya ganinta tako ina sai hannunta mai ƙawace da adon zanen lalle ja da baƙi. Da wani sirrintaccen ƙamshi na musamman mai ratsa ɓargo da jijiya. Har cikin gida Hassan da Hussain da Mubeen da su Afrah sukai mata rakkiya, hakan ya matuƙar sake burge mutane da kallon al'amarin matsayin shaƙuwa ce ta kawo hakan tsakaninsu. Sun kaita har ƙofar falon Ammah da ke cike da ƴan uwanta itama, da ga nan Aunty Saliha da Aunty Naja'atu suka kama hannunta suka ƙarasa da ita cikin falon Ammah. Da ga haka su Hussain suka juya cikin sanyin jiki da basu taɓa tunanin zasu iya ji akan Mawaddat da sukai ƙololuwar tsana a cikinsu ba dalilin fifitata da mahaifinsu yay sama da su da mahaifiyarsu. Mubeen ma sai kawai ya kama hawaye....

     Sauran ƴan rakkiyar amarya sun ɗura ciki suma. Wasu farin ciki ya kawosu wasu ko gulma da jinjina inda ALLAH ya kawo Lulun. Duk irin yanga da jin kai da izza irin tata ta ƙare da aure a getto eria irin haka? Kai lallai da mamaki koda yake tarihine ya maimaita kansa tunda haka itama mahaifiyarta tayi, sai dai akwai banbanci sosai a yanayin tsarin auren. Wasu ma harda dariyar mugunta wasu ko tausayinta suke ji a nasu ganin taci baya gaskiya. Wasu ko tayata farin ciki suke ALLAH ya kawota matakin da ko wacce ɗiya mace ke jin alfahari da ɗaukaka. Abu mafi ɗaukar hankali tarbar mutuntawa da suka samu daga ahalin ango duk da yawansu. Ammah kam da ga ciki su Aunty Nasara na shiga da Lulu ta taso ta rungumeta a jikinta. Haka ma ƴan uwanta sai faman musu lale marhabun akeyi. Ajiyar zuciya Lulu ta dinga saki da sake lafewa aikin Ammah, dan wata irin nutsuwa taji tana ratsa mata sassan jiki da ɓargo batare data san dalili ba. Duk da bata san wacece ita ba, ba kuma ta gani fuskarta abinda matar tai mata ya sata jin ƙaunarta. Bayan kakarta Dada Ammah ce mace ta biyu datai mata runguma irin ta mahaifiya, a hankali hawaye suka shiga ziraro mata daga cikin hular alƙyabbar tsigar jikinta na wani irin tashi. Adda Fati babbar yayar su Ammah da suke uba ɗaya ce tazo ta kama hannun Lulu aka shiga da ita ƙuryar ɗakin Ammah da aka gyara dama dan tarbar amaryar, shiyyasa kowa ya fito aka dawo falo da ɗayan ɗakin dan kowance a gidan dama ɗakuna uku ne a falonta.
        Gida ya sake amsar harami tako ina, dan ƴan kawo Lulu basu wuce ba sai kusan biyar da rabi na yamma. Lulu na can ƙuryar ɗakin Ammah tare da su Amrah dan ita dai fa babu ƙawa, dama da lafiya-lafiya ne da Nadiya ce zata kasance da ita. Sai dai ta riga ta jingine tarayyarsu a matsayin tarihi ita kuma idan ta ɗana tarkon tafiya bata waiwaye. An tara musu abinci da abin sha kala-kala har da su fura mai ƙyau da tsafta. Aiki su Amrah suka shiga cin nama da furar nan dan sun musu da ɗi. Da farko dai Afrah zata fara wani iyayi Amrah tai mata gargaɗi da tuna mata kashedin da Mommy tai musu. Hakan yasa ta dawo hankalinta, sai da suka buɗe abincin kuma taji ɗanɗano sai ta ware ta hau ci. Duk abinda suke Lulu na kwance lamo a gadon Ammah tana kallonsu kawai. Kanta ke mata wani irin masifar ciwo, dan tana cikin matsanancin buƙatar kayan shaye-shayen ta matuƙa. Kwana bakwai fa kenan bata sha komai ba, kai ai tayi ƙoƙari matuƙa. Har ji take ana mata mutsu-mutsu a brain, ga hayaniyar bikin nan na matuƙar caja mata kai itama. Dan ma nan ɗin da aka kawosu su kaɗai ya mata daɗi, duk da sunajin hayaniyar amma da sauƙi ba kamar suna a wajen ba. Su Aunty Saliha basu wuce ba sai bayan magriba su, ƙin shigowa sukai mata sallama dan karsu takalo ta, bayan wucewarsu ma cikin gidan ta fara lafawa da mutane, dan dj da su Mubarak suka sa ya kwashi mata duk anyi waje. Tuni su Amrah ma da ke jiyo sautin kiɗa suka gudu suka barta ita kaɗai a ɗakin. Batace musu komai ba sai lumshe idanunta da tai barci ya kwasheta, cikin mintina ƙalilan zazzaɓi mai zafi ya rufeta ruf ta hau rawar sanyi, ga fanka na juyawa a ɗakin ta kasa tashi ta kashe ta. Barcin take a wahale ga mafarkin mahaifiyarta........✍️
       
         




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070


VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login