Showing 1 words to 3000 words out of 117786 words

Chapter 1 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

448

*♡ME ZAN YI DA ITA?♡*


NAZEEFAH SABO
NASHE

FREE📚
08033748387


Da sanyin safiya ta fito daga rugar fulanin cikin wata bukka dake daga gefen rugar sanye take da kayan fulani irin usul din fulanin nan fuskarta a cunkushe da mabayyanin ‘bacin rai. Tana tafe tana kunkuni alamar ba dan son ranta ya fito ba.

Kwarya ce a kanta da nono a ciki a tsakar gidan ta tarar da mahaifiyarta zaune da turtsesten ciki a gabanta ta had’a kai da gwiwa . Har zata wuce sai kuma ta dawo ta tsaya mata’kerere a ka, bakinta a zun’bure tace “innaji zan tafi” innaji ta saki ajiyar zuciya kafin ta furta “idan kinje ki gaida modibbon saura kuma idan kin fita ki tsaya dukan d’iyoyin jama’a ko tumakinsu “ “ aradu duk yaran da ya higa gonata nima sai na higa ta uwarshi “ cikin takaici innaji ya watsa mata harara “ ina magana shatu kina cewa aradu sai kinyi to ai shikkenan kije kiyi Allah ya shiryeki ni dai ina gaya miki ki kula da kanki kina sani ba kowa ne damu a garinnan ba idan mune yau fa anjima gawa muke bana son ace har yanzu kina wannan halinnaki kowa unguwar nan yasan halinki ba mai fad’ar alherinki sai aibunki shatu don Allah ki shiryu kada kizo nan gaba kina wahala a lokacin da ‘kasa ta rufe min ido “ . Duk da jikinta yayi sanyi bata fasa cewa “yo innaji sai na bari yara suna tsokanata suna ce min mai idon mujiya kamar ubansu ya rad’a min “ innaji ta mi’ke da kyar da alama cikin yayi mata nauyi murya can ‘kasa ya kama hannunta “ suyi ta fad’a miki mana kyau idanun suke musu masha Allah zaki dinga cewa idan suka fad’a miki yi sauri ki tafi kinga hadari na hadowa ki gaidar min da modibbo ki kar’bo min rubutun idan ya rubuta “. Da sauri ta fice kamar zata tashi sama tana ayyana “ wallahi innaji ba zan kyalesu ba jibgar d’iya ni kayi idan ya shiga gonata’yan kwal uba masu kan faranti “.
Da tsallanta take tafe da wa’karta duk da ‘kwaryar nonon da take kanta har da cilla sanda duk yaran da ta wuce’kus suke da bakinsu kada suyi magana suci Na jaki sai dai tana wucewa suke tuntsira dariya murya ‘kasa’kasa suke cewa “mujiya idonki a loko “ sai su taka da gudu. Shatu ‘kwafa take tana haddacesu d’aya bayan d’aya ta kuma tabbatar wallahi sai sunyi bayani.

A saman buzu ta tarar da kakanta Na gurin uba moddibo wanda ya kasance gawurtaccen malami a garin nutsuwa tayi sosai don shi kad’ai take tsoro a garin , ta ra’be gefensa ta tsuguna sai da ya kai aya sannan ya d’ago ya kalleta fuskarsa ba yabo ba fallasa yake amsa gaisuwar da take masa “ Gashi inji innaji tace tana gaidaka “ moddibo ya girgiza kai had’e da jan’kwaryar yana girgiza kai “ ‘yar nema ai Na zata yau ma kinyi halinnaki kin zubar dashi wallahi da yau ma sai na zaneki dan na lura sam ke baki tausayin innarki idonki a tsakar ka yake d’auki ki kaiwa salame Ta adana shi a ciki” mi’kewa tayi zuciyarta a tunzire kamar ta kai masa mari ita fa ta tsaneshi bata ‘ki ya she’ka barzahu ba don ya takura mata baki kamar shantu ta fad’a a zuciyarta zanyi maganinka aradu gobe. A tsakar turken tumaki ta tarar da ita salame ta amsa gaisuwarta tana kar’bar’kwaryar nonon fuska a sake tace “ya jikin innar taki?” “ ba sauki sai na Allah yo wannan uban ciki yayi mata turtsitsi ta ina zata samu sau’ki Idan ba haifeshi tayi ba aradu duk ranar da Ta haife abin da yake cikinta sai na jibgeshi “ salame ta zaro ido tana kallon shatu da take zaro zance “ashe kuwa dai shatu da ake cewa baki da kai zancen ya kusa tabbata jaririn zaki jibga?” Ta ta’be baki “ yo idan ban jibgehi ba ai aradu ban haifu ba a cikin innaji ko sallah fa a zaune take yi gashi tun a ciki shegen karanbani garai yayi ta kwarafniya jiya fa ina kallon cikin yana wutsilniya wallahi tana cin abinci kika ji d’if tun kan yazo duniya ma ya nuna halinsa” salame ta girgiza kai tana katse’kwaryar ta mi’ka mata daidai lokacin da modibbo ya shigo yana dogara sanda “ to uwar shashashanci kina nan kina zuba kamar ‘ya’yan kanya zo ki wuce ki kai mata rubutun Allah ya raba lafiya” “ ameen “ ta furta murya can ‘kasa “ ai kai na gado a kwakwazo duk gari an sani” mai kika ce “? A guje ta arce tana fad’in cewa nayi Allah ya tashe mu lafiya salame kuwa girgiza kai tayi don ita taji abinda tace sarai don dai shi ma kunnensa yana da matsala ne.

Tun a hanya take Allah-Allah taga d’aya daga cikin yarannan sai dai bata gansu ba haka ta koma gida ranta a ‘bace da rashin cikar burinta.

Tana shiga innaji ta kar’bi rubutun had’e da nuna mata buta ta san nufin innaji tunda lazimi take ta sunkuci butar ta fara alwalar. A nutse ta tada sallah duk da rashin jinta innaji Ta tsaya sosai wajen bata ilimin addini don masaniyace sosai Na boko ne dai sai taga dama take zuwa ko idan an tura ta ta shige gonakin jama’a tayi’barna.

Suna idar da sallah innaji ta ri’ke hannunta murya a raunane tace “ shatu jikina yana bani kamar rayuwata tazo gangara don haka ya zama dole yanzu Na sanar dake labarina ko da nan gaba zaki bu’kaci haka a lokacin da ‘kasa ta rufe min ido ga mahaifinki tsawon wata biyar da tafiyarsa har yau ba amo ba labari daga tafiya fatauci ina son ganinsa ban san ina ya tafi ba.” Hawayene ya ciko a idanun shatu sam bata son taji innaji tayi mata zancen mutuwa ta lura kuma kwana biyu kullum zancenta kenan. “ innaji don Allah ki daina min zancen mutuwa idan kika mutu an higa uku “ baki shiga uku ba shatu Allah yana tare dake kuma kina da gata tunda moddibo yana raye balle nasan mahaifinki komai dad’ewa Zai dawo ki share hawayenki burina kawai ki nutsu “ fad’awa jikinta tayi “don Allah ki daina cewa zaki mutu ni kece gatana “ innaji murmushi tayi tana kallon zallar yarinta a idon shatu da Ba zata gaza shekara sha daya ba. “ To ki dinga addu’a Allah ya rabamu da cikinnan lafiya naga aurenki shatu “. Da sauri ta furta ameen “


Har dare tana son jin labarin da innaji zata bata amma kuma tana tsoron zancen mutuwa don haka tayi mu’kus.

Cikin dare ta kasa ha’kuri ta mi’ke zaune “Innaji baki bani labarin ba “ murmushi innaji tayi don tasan shatu da son jin zance ta mi’ke zaune da ‘kyar ta jingina da bango.


*********. **********
Asalina haifaffiyar garin liman katagum agarin bauchin yakubu sai dai mahaifiyata yar asalin mambilace a jihar taraba acan mahaifina ya ganota ya aura shi yasa zaki ganmu da asalin kyau na fulanin usuli.

Mahaifina d’an bokone mu biyu iyayena suka haifa daga ni sai yaya ta dijama. Kasancewar mahaifina lecturer hakan yasa ya dage akan harkar iliminmu. Muka taso cikin tarbiyya da ‘kaunar juna ni da yayata mai tsananin kama dani ta girme ni da shekara hud’u. Yayata tana gama secondary samari su kayi mata ca hakan yasa babanmu yace dole ta fitar da miji duk da kasancewarsa d’an boko baya take ilimin addini yana bashi ha’kkinsa sosai. A lokacin ina ss 1 yayata ta fitar da miji a kayi mata aure da wani matashin mai kud’i ahmad manga inda suka tare cikin garin bauchi a unguwar gwallaga.


Lokacin da na shiga ss2 a lokacin muka fara soyayya da wani ma aikacin makarantar atbu inda gidanmu yake kasancwar a staff houses muke shara yake da gyaran compound d’in gidanmu soyayyarsa ta d’ibeni don kyakykyawa ne sosai . Ba wanda ya sani a gidanmu a ‘boye muke komai duk da bama keta iyakar ubangiji amma fa soyayya tayi zurfi a tsakaninmu ta yarda tabbas a lokacin idan aka hanamu aure zamu iya rasa rayuwarmu. Duk da bashi da ilimi haka nake son shi tunda yana da ilimin addini bokon ma a hankali nake koya masa a ba ca da. Ina ss 3 tashin hankalin ya fara zuwa don kuwa wani d’an abokin babanmu yace yana so na babanmu kuma yace ya bashi gashi bababnmu irin masu kafiyar nan ne sam baya juyuwa mai juyashi dama babansa ne kuma ya rasu. Hankalina ya tashi sosai nayi kuka kamar raina zai fita na gaya wa mamanmu bana sonsa ta fad’awa baba yace ban isa ba bai haifi dan da zai ce yes yace no ba. Haka mamanmu tayi ta rarrashina ita da yayata amma zuciyata Ta kasa ha’kura.
Hakan ya tunzira zuciyar Baba yace ya fasa barin sai na gama jarrabawar na ‘karasa a gidan mijina aure zai yi min.

Aka fara shirin biki hankalinmu a tashe ni da miji wannan yasa ana gobe d’aurin auren muka gudu ni da miji. Da sassafe muka wayi gari a wata ruga ya bani kayan fulani na saka sai da muka zo gidan ya sanar dani gidansu ne nan ya shiryawa mahaifinsa ‘karya akan cewa iyayena sun rasu a hanya kuma fulanin tashi ne hakan yasa suka rungumeni a gidan bayan wata biyu aka d’aura mana aure da miji duk da kullum zuciyata na bani shawarar na koma gida amma ina tsoron mahaifina. Shakararmu goma da aure kafin Allah ya kawo cikinki. Har yau a garin nnan ba wanda yasan ina da ‘yan uwa sai yanzu da nake gaya miki kina zuwa liman katagum kika tambayi gidan sarkin fulani nan ne main house na familyn babanmu koda ta Allah zata kasance. Ya fad’a hawaye na ziraro mata na tuno iyayenta.

Shatu ma hawayen take “yanzu innaji da gatanki muke ta yawo bama nan garin bama can mune har nan niger 🇳🇪 ashe asalinmu yan nigeria 🇳🇬 ne “. Innaji ta dafa kanta tace “kaddarar haihuwarki ne shatu da ta wannan cikin fatana idan kin sadu da dangina kice su yafe min na mutu ina tsananin kewarsu “. Share hawayenta tayi tace “insha Allah innaji ba zaki mutu ba da ‘kafarki zaki ga danginki “.

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-
2

Sumul suka farka innaji ranar ta d’an ji sau’ki, har yamma shatu na tare da ita Ta kasa motsawa ko nan da can ranar kam jikinta a sanyaye yake duk tsiwar da masifat ta zubar tana gefen innaji a zaune kan tabarmar karauni. Innajin Ta tsefe mata kanta Ta wanke tas da kanwa da karkashi sai ‘kyalli gashin yake yasha man kwakwa kasancewar shatu mai gashi na ban mamaki tamkar mutanen ‘kasar hindu don ma bata son gyarashi da ‘kyar take barin innajin ta ta’ba mata kai shima sai tayi mata jan ido.
Har aka gama tana kwance lamo ba mai magana tsakaninsu ita innaji tana karatun suratu maryama ita kuwa shatu ta lula duniyar tunani gaba d’aya ta rasa sukuni.har la’asar tayi kafin ta mi’ke tayi alwala ta kuma zubawa innajin ruwan alwala innaji ta kar’ba tana murmushi “ Allah yayi miki albarka shatu yasa ki cimma duk burin da nake miki fata a rayuwarki “. “Ameen “ shatu ta fad’a murya a sha’ke. Suna idarwa innajin ta aiketa gidan modibbo kar’bo rubutu.

Duk tsokanar da yara suke mata a hanya ranar banza tayi dasu burinta taje ta dawo ta iske innaji lafiya sumul, don haka take ta sauri kamar zata tashi sama.

Ko mintuna biyu bata yi ba a gidan moddibon ta juyo a sukwane ko saurarar gwaggoji ( salame) da take ‘kwala mata kira ba tayi ba.

Kamar an cillota haka ta afka tsakargidan da sauri ta saki ajiyar zuciya had’e da cewa Alhamdulillah Allah innaji na d’auka kafin na dawo kin mutu” murmushi innaji tayi kafin ta furta “mutuwa ai sai lokaci yayi ayshatu” da sauri ta dubeta jin sunan da ta kira ta dashi innaji ta waro ido tace “lafiya “ ta hau girgiza kai “ ji nayi kin kira ni da sunan da baki Ta’ba kira na ba “ dariya kawai tayi tana shan rubutun ta had’e da kallon shatu kallo mai nuna tsananin ‘kaunar da take mata.


Cikin dare innaji ta fara jin ciwon na’kuda tun tana daurewa har abin yaci ‘karfinta ta mi’ke da ‘kyar ta bud’e wata adaka ta zaro wasu hotuna da biro ta rubuta address din family house d’insu ta nad’e a takarda ko bakomai bata san ya ta Allah zata kasance ba.


Da ‘karfi ciwon yazo mata har bata san lokacin data fara tashin shatu ba a razane shatu ta tashi saboda wani mummunan mafarki da take a wannan lokacin, ganin innaji cikin wani mawuyacin hali bata san sanda ta zunduma ihu ba tana ru’kun’kumeta “ bana so innaaji bana son mafarkin da nayi ya tabbata “. Da kyar innaji ta’ka’kalo wani murmushi tana mi’ka mata takarda “ ayshatu ban san ya ta Allah zata kasance ba amma koma dai yayane bayan raina ki nemi dangi na idan mahaifana suna raye ki basu wannan takardar da wannan hoton suna gani sun san ke jini nace Ayshatu idan babanki ya dawo kice masa ya yafe ni Allah ya yanke ganawarmu “. Hawaye take yi sosai na tsananin azabar na’kuda. Ayshatu kuwa ta zama kamar mutum mutumi ta rasa ma mai zatayi abinka da’kan’kantar shekaru. Sai jijjiga innaji take ba bakin magana har zuwa sanda taji innajin ta saki kalmar shahada jikinta gaba d’aya ya saki ji kake d’if lamarin Alhakamu ya tabbata. Ita kuwa a nata tunanin barci innaji tayi bata san mutuwa ba bata san ya ake mutuwa ba gashi ana fad’a musu zafin fitar rai a yanda kuwa ake kwatantawa tabbas wannan ba mutuwa bace barcine ta ayyana hakan a ranta, don haka hankalinta kwance ita ma ta kwanta a gefen innajin barci ya kwasheta barcin da shine ya kaita har’karfe goma na safe.

Tana farkawa ta tashi a razane tana kallon hasken d’akin tare da tunanin me yasa innaji yau bata tashesu sallahr asuba ba. dubanta ta kai inda innajin take da sauri ta zare ido ganin idonta a kakkafe ya kalli sama ai bata san sanda ta hau jijjigata ba jin bata motsi yasa ta runtuma waje a guje tana Kiran jama’a “kuzo ku duba min innata tayi barcin zomo na tasheta ta’ki tashi “ ma’kota suka shiga gidan sai gani tayi suna fitowa jiki a salu’be ga kallon tausayi suna mata . Kalmar da taji wata ta fad’a ne Allah yaji’kanki maryamu halinki na gari ya biki yasa ta farka daga tunanin da take na cewa innaji barci take.aiko zuba hannu aka ta ‘kwalla’kara sai ganinta a kayi a zube ba numfashi.
Allahu akbar kabeeran Ubangiji kenan mai yin yarda yaso a lokacin da yaga dama Allah yaji’kan iyayenmu.


A safiyar juma’ar misalin ‘karfe sha d’aya na safe aka sada innaji zuwa gidanta na gaskiya hawaye sai zarya yake a fuskar abokan arziki kowa ya shaida innaji bata da abokin rigima to ita maganar ma bata dameta ba balle har ta samu abokin rigima. Shatu zube a cinyar gwaggoji sai mayar da ajiyar zuciya take da razana har sai da moddibo ya sake mata rubutu aka bata. To haka dama rayuwa take.



A hankali shatu ta fara sabawa da rashin innaji kullum kuwa ma’kale da takarda da hotunannan take kwana tayi al’kawarin sai ta sadu da dangin mahaifinta. Gidansu gwaggoji ta koma ta daina wanka ta daina komai wai ita ta gama jin dad’in duniya tunda innaji ta tafi ta barta. Yaran mutane kuwa a lokacin ta ‘kara takura musu musammam masu uwa raye shatu bata da ‘kiba sam amma sai ‘karfi ta gallabi mutanen garin tun ana d’aga mata’kafa saboda rashin uwa har tausayin ya kau aka fara kawo ‘kararta wajen gwaggoji. Gwaggoji bata da fad’a sam don haka shatu take’kara sangarcewa kullum da rashin jin da zata rakito ta kai yanzu har manya shiga shirginsu take musamman masu gonaki da suke kuka da ita.

Makaranta kuwa tuni tayi sallama da ita ta allo kawai take yi itama don moddibo yana cin gidansu ne da batayi ba. Gashi yanzu shi bashi da cikakkiyar lafiya yau fari gobe tsumma.



BAYAN WATA SHIDDA

Da rasuwar innaji jikin moddibo ya ‘kara tsananta, hakan yasa shi fara had’a komatsansa baya so ya mutu anan ya fito ya mutu cikin ahalinsa da suke garin yola. Itama gwaggoji hankalinta yafi kwanciya su tafi musamman saboda shatu ko bakomai a can dangi da yawa za’a samu mai tayasu kula da ita.


Safiyar wata asabar suka fito da ‘yan ‘kullin kayansu suka fara sallama da mutanen garin da suka yi dandazo a ‘kofar gida, duk jikinsu yayi sanyi musamman yara da suke kallon shatu Idanunsu fal ‘kwalla. Shatun ma kuka take ta kalli yaran tana murmushi “kuyi min tsokanar’karshe don Allah ko bakomai zan dinga tuna ku.” Shiru su kayi mata, murya na rawa ta fara binsu d’aya bayan d’aya tana cewa “ku fad’a mujiya mai idonta a loko....” Ai kuwa yara suka fara har ita suna kuka kuka, dariya- dariya a haka suka rakasu har inda mai amalanke yazo ya d’ebesu tana d’aga musu hannu suna bin amalanke , rayuwa kenan ba mamaki shikkenan tayi sallama da garin nijar. Amma ta’kudirce insha Allah zata dawo.



Kwanansu kusan biyu suna tafiya, kafin Allah ya kawo su garin yola nan suka hau motar garinsu demsa, daga demsa suka shiga wata’kur’kura ta isar dasu cikin ‘kauyensu gwamba. Ai kuwa mutanen garin suna ganinsu suka shiga fitowa ana murnar ganinsu.
Bayan sun shiga cikin gidan mai girman gaske ginin’kasa suka fara yiwa juna gaisuwa anan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login