Showing 33001 words to 36000 words out of 117786 words

Chapter 12 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

459

yana ganinta ya d’an saki murmushi tare da mi’kewa zaune ya jawo ta yayi mata kyakykyawar runguma ita ma ‘kan’kameshi tayi kawai ta saki kuka kasa ce mata komai yayi shima yana sakin ajiyar zuciyar suka lula wata duniyar ranar da yake jira ga shi ta zo masa a baibai ranar da shaheedah zata zama mallakinsa. Sun dad’e a wani yanayi na romancing juna kafin ta janye jikinta a hankali bata shirya kar’barsa a wannan lokacin ba kamar yarda antyn ta ta ja mata kunne sai komai ya kammala sannan zata amince dashi akwai aikin da tasa malaminta yayi mata.wani kallo yayi mata “why shaheedah?” Murmushi ta sakar masa “ka tashi kayi shirin dinner mu tafi wani dalili can ba zai ruguza mana farin cikin da muka dad’e muna arranging ba,an dai riga an gama cutar mu kuma wallahi bana jin zan iya zaman kishi da kowacce mace akan ka don haka kayi shirin rabuwa da ita wallahi ta kowani hali ma” murmushi ya sakar mata yana shafa kumatunta “ki sha kuruminki my lovely wife ni na san abinda nake shirya mana bana son ki ‘kara d’aga hankalinki aure dai an d’aura amma ba wanda zai saka ni dole nayi acecpting d’inta as a wife kallon arziki ma ba yi mata zanyi ba.”
Murmushi ta saki murna fal ran ta tace “yauwa tnx so much dearie ai ko cewa aka yi ta tare ka amince sai ta zame mana house girl ko?” ‘Daga kai yayi yana shafa kanta murya can ‘kasa tace “Amma don Allah kada tace dinner yau bana son ganinta wallahi raina ‘baci yake.” “Tohm shikkenan ba zata ba zan san yarda zan yi da ita yanzu jeki a fara shirya min ke ki fito kamar ‘yar tsana.” Tana dariya ta mi’ke Ta fice daga d’akin. Gaba d’aya suka zuba mata ido barin Ammar da Hisham da basu san tana ciki ba. ko kallonsu ba tayi ba ta fice da Sauri.

Ali ya kalli Ammar yana dariya “kun ga abin mamaki ko? Amaren yanzu basu da ta ido they are shameless yanzu fa ita ta kawo kanta wajen mijin ko da yake dama ya fi son irinsu matured in ji shi da fad’a” gaba d’aya suka tuntsire da dariya. Ammar yace “Da kun ga wacce aka aura masa da kun san ba ‘karamin gata aka yi masa ba.” Ali yace “yauwa wa aka aura masa please?” Hisham yace “shatu ce fa.” Gaba d’aya suka zaro ido Ali ya tuntsire da dariya “wai wannan yarinyar mai kama da larabawa ita ce yake tuejewar baya so?cab ni fa nan har ina cewa ina ciki to ai shi ba ‘karamin gata aka yi masa ba.” fitowar Imran daga d’aki ce yasa su kayi tsit suna kallonsa fuskarsa a tamke kamar tunda aka halicceshi bai ta’ba dariya ba. harararsu yayi ya fice daga d’akin yana jin suna tuntsira masa dariya.


Mutane ne ‘yan biki a zaune a parlourn haushi ya kama shi hakan yasa yace saratu mai aiki ta kira masa shatu, ta amsa tana ‘kunshe dariyar da take cin ta don duk sun san labarin, ta shige a d’akin mommah ta samu shatu tana dariya tace “shatun momma kizo in ji Babban yaya.” Sak shatu tayi tana kallon jama’ar d’akin..

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-21


ELEGANT ONLINE WRITERS......


Mommah ta kalli saratu “mai za tayi masa da yake nemanta?je ki ce ba zata zo ba idan ya matsu da son ganin ta shi ya shigo ya ganta a gaba na.” “Auzubillahi Wannan wace maganar wauta ce mutum da matar sa kice ba zai ganta ba wani yace ki d’aura musu Auren ?a’a ni ba za’a yi wannan d’iban albarkar dani ba tashi maza kije kafin in kai miki mangara da ido ‘kwala-‘kwala a wajen.” Shatu ta mi’ke tana duban dada da tace sai taje kanta ko d’ankwali babu ga rigar tata armless ce sai wani skinny jeans. Bayan saratu ta bi tana ta mita da zuciyarta wallahi ya gaya min ba’ka sai na gaya masa ‘kirin ai nima ba son auren nake ba.corridor d’in da ke hanyar kitchen saratu ta nuna mata ta wuce tana dariya ‘kasa-‘kasa. Shatu ta girgiza kai alamar zamu gamu. Tana shiga ta gan shi zaune a kan kujerar da take gaban working space na kitchen d’in mommah. Ya had’e rai sosai yayi folding hannayensa a ‘kirji kayan da suke jikinsa sun amsheshi sosai three quater black jeans da white T.shirt Kansa ya cukurkud’e kamar Na buzaye alamar bai samu gyara ba. tsaye tayi a gefe tana ta’be baki duk da ta san bai yi wanka ba amma gaba d’aya mayen ‘Kamshin turrensa ya game kitchen d’in.Ganin yayi mata banza yana mata kallon up and down yasa ta juya zata fice.murya a cunkushe yace “wallahi kika fita ba tare da na gama abinda Yasa nace ki zo ba zaki gane baki da wayo” juyowar tayi itama tana masa irin kallon da yake mata “to ka fad’i abinda zaka fad’a I have something to do.” Tsaki yayi yace “bar d’an guntun english d’inki ki je kiyiwa wad’anda basu sanki ba ba su san yarda kika zo ba burga dashi wai ni ban ga dalilin da yasa mommah ta ma’kala min ke ba ban ga komai tare dake ba banda ‘kwala-‘kwalan idonki kamar me”
Waro ido tayi tana dubansa dariya take sosai har ya ‘kulu kafin tace “exactly like your’s”bud’e idanunsa yayi sai kuma yayi tsaki “Ba wannan yasa na kira ki ba warning d’inki zanyi dama kada ki sake naga ‘kafafunki wajen dinner wallahi kika kika saka ran habibteey ya ‘baci zaki gane baki da wayo a wajen zanyi disgracing d’inki kina ji ai? Kuma ki san yarda kika yi ki ka sa mommah ta raba wannan auren ko ta yaya ma kuwa idan ba haka ba duk wula’kancin da kika tarar a gida na ke kika siya na gaya miki.” Sake kallonsa tayi ta turo baki “To ni ina ruwa na na gaya maka nima ina sonka ne kawai biyayya zan yiwa mommah idan kai kaga ba zaka yi musu biyayya kaje ka gaya mata baka so na sai me? Kuma wajen dinner sai naje sai dai kai da matarka muciya da zani ku ha’kura.” A zafafe ya taso zai kai mata cafka ta san kuma mai zai faru idan ta bari ya cafketa don haka tayi saurin fita a guje tana tuntsira dariya ta lura baya son ace muciya da zani ita kuwa ta samu nayi. Babu wanda tayi wa maganar ya hana ta dinner tana komawa d’aki Hafsa ta fara mata make up don ta iya make up sosai,kafin su tafi turkey karatu ma tana yin na kud’i a Abuja don haka ta fara tsantsara mata.
Shi kuwa Imran yana can yana ta faman kiran mommah ta’ki receiving so yake ya gaya mata bai amince shatu taje dinner ba tunda shaheedah bata so kuma yaga dai dinnerr ta Shaheeda ce.yayi mata missed calls ya kai goma bata d’aga ba,ita kuwa mommah tana ganin kiransa ta’ki d’agawa tana gaban Dahda da yake sanar da ita kawu sa’idu yace lallai-lallai shatu ta tare a gidanta ta zaro ido “amma why Dahda she is too young fa ba zata iya facinga marriage issue ba wallahi don Allah ka bashi ha’kuri bayan haka ma ga karatunta abin zai yi mata yawa.” Dahda ya ja ajiyar zuciya “kin san dai halin kawu sa’idu wallahi ba zan iya fuskantar fad’ansa ba,ki bar ta tare d’in idan yaso shi sai ya kula da harkar karatunta a kuma ja masa kunne kada ya sake yayi wata mu’amalar auratayya da ita.
Gaba d’aya mommah jikinta ne yayi sanyi, har sai da Dahda ya ri’ko hannunta yana matsawa a hankali “Don’t worry ba fa abinda
Zai faru insha Allah sai yanzu nake ganin wautar mu daga nia har ke da muka had’a aurennan zuwa nextweek ayi mata kamu da walima kawai a kaita Allah ya basu zaman lafiya zan tura miki 10million a account a siya mata komai da zata bu’kata a kaita d’akin mijinta haka Allah ya tsara kuma zanyi warning d’in Imran d’in dama ya barta tayi karatunta. Tashi kije ana ta kiranki.”
A sanyaye ta mi’ke kamar jira ake wayar Imran ta sake shugowa, a zafafe ta danna “wai Imran meye haka ne tunda ka kira kaji ban d’aga ba ai ka san a busy nake amma ka wani dameni da kira. Nace menene kayi shiru wallahi zan cutting wayar.”
Sakin ajiyar zuciya yayi murya a ciki yace “Am sorry mommah wai me nayi miki da zafi haka kullum kike min fad’a?” Tausayinsa ya kamata amma madadin ta nuna masa sai tayi tsaki “ina jin ka menene nace?” “Mommah favour d’aya zaki yi min don Allah yarinyar nan kada taje dinner.” Tsaki mommah tayi jin ko sunan ta baya iya fad’a saboda tsana “wacece yarinyar nan?” Shiru Imran yayi har mommah ta ‘kulu tace “duk sanda ka tuno sunanta ka kira ni muyi magana.” Ta kashe wayar.Imran ya dafe kai yana tsaki shi wallahi ko sunanta baya son furtawa. Amma ya zaiyi dole ya sake kira.tana d’agawa ya runtse idonsa “please mommah Aysha nake nufi.” “Oho saboda kada shatu villager ta ‘bata maka taro ko kuma a dinga nuna ta ana ga second wife d’inka ko to sai taje idan yaso idan tace ka tashi a gaban mutane da mic kace baka sonta shashasha kawai. ‘Dif tayi switching phone d’in off gaba d’aya ma. Imran ya cillar da wayar yana tunanin wata mafitar ran sa duk a ‘bace.Samu mafita ya saka shi sakin murmushi idan an san wata ai ba’a san wata ba shi yasan tsiyar da zaiyi mata.


Tsaf shatu ta fito tayi masifar kyau cikin makeup d’in da dressing d’in da aka yi mata pink lace ne da touches d’in maroum a jiki hakn yasa aka saka mata head maroum dinkin ya zaunu daram a jikinta duk da dai ‘kwailace inji Imran amma fa
Komai yaji don tafi waccen matar tasa muciya da zani 😂. Tafiyar da za tayi ma sai da Nahna ta koya mata sai zabga’kamshin turare take. Suka fita da su Hafsa don mommah da Hajiya mama dama ba zuwa za suyi ba. Ta windown bedroom d’insa ya hangosu, don haka da sauri ya ajiye babbar rigarsa da hularsa a saman gado ya fice da key d’in mota a hannunsa. A tsaye ya tarar dasu murmushin dole yayi yana duban Hafsa don ya san Nahna bala’i ce da wayonta sarai ba zata yarda da rainin hankalinsa ba. “small mom mu d’anyi magana ma na” bin sa tayi tana murmushi ganin yarda yake kallon shatu ita tunaninta mamakin kyan da tayi yake. “Waye zai kaiku ne?” Ya fad’a yana kallon Hafsa “wallahi Ammar muke jira wai ya tafi shiryawa” “okey ita wannan ku bani aronta zan kawo ta da kaina” Hafsa ta kalleshi “mhmn mhnn faof Big son kada ka jefa ni a trouble don Na sanka trouble maker ne”. Dariya yayi sosai “nothing will happen insha Allah kada kiji komai wannan jaririyar ma kawai dai kin sanni da kishi apart from that ma yanzu duka responsibility d’inta yana kaina tunda an shafa ko ba haka ba?” Hafsa ta ta’be baki “ni dai da ka barta” zuwa yayi yaja hannun shatu yana murmushi “muje ke” shatu tayi ‘ko’karin janye hannunta ta kasa ya matse shi gam ya kuma yi mamakin jin wani irin taushi a hannun kamar audiga. “Alhamdulillah” ya furta bayan ya shiga part d’insa ya tarar gayyar abokansa sun fita, turjewa shatu ta fara yi ya jata da sauri har suna had’e jikinsu ya tura ta bedroom dinsa jin ana bud’e bedroom d’in Ammar.suna shiga ya tura ta saman kujera yana murmushi “ba dai nace ba zaki ba ance sai kin je yanzu ai sai naga ta yarda zaki.” Turo baki tayi alamar zata yi shagwa’bar da ta saba, ya matsa kusa daf da daf da ita yana mata kallon cikin ido “wallahi kika fara min kuka anan sai kin gane kurenki ba dai ba kya jin magana ba? Sai in ga mai fita dake ai har da wani zuwa ayi miki shafe-shafe kayan haushi kawai in dai don ni kika yi to ba kiyi kyau ba look at your mouth kamar gidan tsutsa.” Shiru tayi masa zuciyarta Na ‘kuna yanzu duk wannan kwalliyar a banza aka yi kenan? Nocking d’in da ake ne Yasa shi saurin zira rigarsa don ya san shaheedah ce ya gyara hula yana fesa turare Ta mudubi yake yi mata dariyar mugunta ganin yarda ta ‘bata fuska ‘kiris take jira ta fashe amma taurin kai ba zai bari tayi kuka ba. Tana kallo ya bud’e bedroom d’in ya zare key d’in da sauri ya fita ya kulle ya rufe ta baya da key yana murmushin mugunta. Shaheedah da take tsaye ta zata ita yakewa murmushin ganin kyan da ta zuba.
Tayi kyau sosai cikin black dressing ya kama hannunta suka fita.to su shatu za’ayi dinner a d’aki kenan,yana fita shatu tasa kuka ta tuge d’an kwalin da sar’kar kuka take sosai kamar me gashi tana ta buga ‘kofa amma ba wanda ya jita hakan yasa ta zauna gefen gado,ga mararta ta fara ciwo ta kuma san period ne tunda tun last month dama ta fara,Allah yasa dama da pant d’inta da pad a jaka don mommah ta gaya mata in dai ta ga date d’inta yazo to ta dinga fita da shirinta,tana ji mararta na ta motsi ta zuba tagumi kawai.


Gurin dinner ya had’u an cika kamar me kowa yayi kyau an ci kuma an sha ana ta spray d’in kud’i, Hafsa da Nahna kuwa sai neman shatu suke ba ita ba labarinta, haka yasa hafsa taje kusa da Imran tana tambayarsa,murmushi yayi yace tace fa ba zata iya zuwa ba bata jin dad’i tana d’aki na.” Hafsa bata kawo komai ba ta juya jikinta a sanyaye tana tantamar zancen Imran a zuciyarta.

Ita kuwa shatu tana can ri’ke da mara ba tayi aune ba ta fara bleeding tana mi’kewq taga tayi masa staining bed sheet waro ido tayi a hankali tace “Na shiga uku” sai kuma ta ‘kyal’kyale da dariya “Allah ya ‘kara ni nace ya kulleni kuma wallahi ba zan wanke ba” kuma sosai yayi staining. Ta shiga toilet ta zame pant da under skirt d’inta ta yar a wajen sannan ta wanke jikinta a toilet seat d’in shima ko flurshing ba tayi ba ta gyara jikinta tsaf Ta fito tana dariyar mugunta.”Alhamdulillah nagode maka period da kazo yanzu.”
Ta koma saman bed d’in tayi kwanciyar ta daga d’ayan side d’in ‘kamshin turarensa da sanyin a.c ya gauraye ta lumshe ido barci tuni ya fara fisgarta.



Mommah sai da ta ga kowa ya fice Dada ma ta shiga d’akin da suka sauka tayi shiri

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-22


Mommah sai da ta ga kowa ya fice Dada ma ta shige masaukinta,tayi shirin barci ta kwanta sannan Ta samu Hajiya mama da zancen tariyar shatu kamar yarda su kawu sa’idu suka bu’kata “Hajiya mama kin ji bu’katar da suka zo da ita na son shatu ta tare nan da one week.” Hajiya mama da sauri ta kalleta “wani irin zance ne wannan ina ce dake mu kayi zancen nan,kika tabbatar min baki saka nan da sahekara biyar ma zata tare ba,su waye suka zo da wannan batun nifa bana son mutane su ga muna tauyewa yarinyar nan ha’kkinta a fara zaton don marainiyace don haka ni ban amince ba na tabbata kuma Babanku ma ba zai amince ba.” mommah tayi ‘kasa da kai tace “wallahi Hajiya mama nima yanzu na fiki da na sanin aurennan ji nake kamar na warwareshi,ban da kawu sa’idu ne ma yazo da maganar da tuni na gama solving d’in problem d’in to shi mutum ne kaifi d’aya da baya canja magana, shi ya gayawa Dahda yace a gaya min a bisa umarninsa yarinya ta tare ko nan da one week ne ba na son yaga kamar na nuna masa bai isa da yarinyar ba.” Hajiya mama ta girgiza kai kafin taja ajiyar numfashi tace “Tir’kashi!ana wata ga wata yanzu shatu mai zata je ta aiwatar a gidan auren shekara sha hud’u da watanni?ai an daina yayin wannan auren,wallahi dama da kinyi shawara dani tun a farkon fari ma ba za’a yi wannan auren ba yanzu mai gari ya waya? Kin san dai babu dalilin da zamu bad’awa wannan dattijon arzikin ‘kasa a ido dole mu amince da abinda yace tunda dai kina gani ranar shi yazo ya siya miki ‘yanci a gidannan,dole mu amince Allah yasa haka shi yafi zama alheri a gareta,ikon Allah kenan idan banda haka ga iyayenta nan su hafsa ko maganar aurar dasu ba’a fara ba sai ita jaririya a kansu,to Allah ne kad’ai ya san lamarin da ya ‘boye a bayan hakan sai mu bita da fatan alheri,amma ko nan gaba idan zaki aiwatar da abu ki dinga neman shawara don aikin mai shawara baya ‘baci,kuma ko bakomai ba za’a zo ana dana sani ba Allah ya shige musu gaba yasa ace gwara da aka yi.” Murya can ‘kasa mommah tace “ameen ai insha Allahu ma zan ja kunnensa kada ya sake ya d’ora mata nauyin auratayya har zuwa san da za ta gama ko da secondary ne” murmushi mama tayi a zuciyarta tace “kayya ban da yaran zamani duk da dai aure ne aka yi shi ba da son junansu ba.” momma ta gyara zama tace”kuma da dada zan had’a ta su tare har zuwa san da
Zamu ga kamun ludayin zamannasu,Sannan ga babansu ya bada ten million yace a siya mata kayan d’aki suna cikin account d’ina.” “Kash ai da bai wahalar da kansa ba addarsu,kuma tabbas Na san Babanku fad’a zaiyi,amma shikkenan kiyi masa godiya ai hannun ba zai ‘ki dad’i ba,mu ma za muyi namu ‘ko’karin don Babanku yace kallon shatu yake kamar maryam gatan da maryam ba ta samu ba shi zai mayar kan shatu, zan kira shi nima da safe nayi masa godiya gobe sai ku fara shiga kasuwa da ‘yan uwanki ku siya mata kaya Na gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login