Showing 3001 words to 6000 words out of 117786 words

Chapter 2 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

449

suke jin labarin mutuwar muji mahaifin shatu. Ashe da ya taho hatsari yayi a garin yola hakan yasa ya bada address din family house d’insu na nan kafin a kawo shi kuma rai yayi halinsa. Su kuma basu san inda zasu samesu ba. hankalin shatu ya tashi ta zube wajen har iskokanta suka ziyarceta, kowa a wajen ya tausaya mata musamman da suka ji labarin rasuwar maryamu ma. Moddibo kuwa innalillahi wa inna ilaihir raji’una yake ja kansa yana juyawa sai gani a kayi shima luuuuu ya kifa. Ai ko ana d’ago shi aka ga rai yayi halinsa. Nan kuwa koke- koke ya ‘karu shatu kuwa kuka take aljannun Na sake bugeta. Gwaggoji kuwa kasa magana tayi tana taajjabin lamarin Ubangiji ashe haka mutuwa take lokaci d’aya taji mutuwar d’anta ‘kwaya guda da rage bata dawo daga razanin ba shima mijin ya mutu, ai ji tayi ina ma ita ma ubangiji ya d’au ranta.


Moddibo kam ya dace ya mutu ranar juma’a aka sadashi da gidansa Na gaskiya. Haka rayuwa take Allah yasa mu cika da imani .




Gwaggoji daga ranar bata sake samun lafiya ba. sai dai a kwantar a tayar, hankalin shatu ya matu’kar tashi duk ta sake firgai firgai ko wanka batayi, bata so ta rasa gwaggoji a karo na hud’u Ta san idan ta rasa gwaggoji gatanta ya gama zubewa warwas. Mutanen nan taga basu da zumunci ko a yanzu haka ita take yiwa gwaggojin komai hatta da gyara jiki idan ta’bata. Iyakacinsu da su abinci shima ko yaro’karami zai iya cinyeshi.



Ranar wata juma’a da yayi dai-dai da rasuwar malam sati takwas, suna kwance gwaggoji na nishi sans-sama tace “ shatu ko bayan raina kada ki zauna ana tunda kince maryamu ta gaya miki inda magaifiyarki take kiyi tafiyarki can, wadannan mutanen kowa kansa ya sani, ga ‘yan ubanci da suka a kansu ba zasu ri’ke ki da gaskiya ba , ina jin tsoron in mutu in barki anan don haka na dad’e da tanada miki kud’in mota.” Ta fad’a tana lalube a cikin bujenta dubu goma cif ta ciro ta mi’ka mata. “Ki’boye shatu ki adana su Allah yayiwa rayuwarki albarka ya kareki daga sharrin dukkan abin ‘ki, baki da wani gata sai dangin mahaifiyarki saboda haka ki tafi can ni na san lokaci na yayi, mutanennan mugaye ne duk ‘yan uba suke da malam dalilin gallazawar da suke mana da saran ‘boye yasa muka gudu muka barsu yaranmu ta dalilin azabarsu su uku muka rasa don haka kema ba zasu barki ba....” tari ne ya fara sar’keta tuni ta fara aman jini, zuciyar shatu ta bushe Ta riga ta saba da mutuwa ta san ita d’inma mutuwar zata yi.

A Jikinta kuwa gwaggoji ta saki kalmat shahada ta mutu, ko alamar hawaye babu a idon shatu sai zuciyarta data ke wani tu’ku’kin ba’kin ciki. Ta ja mayafi ta rufe mata fuska taja gefe tana jan wani numfashi mai huci ta tabbata yanzu bata da wani gata........


Sai asuba ta sanar da mutanen gidan mutuwar gwaggoji. Ba tare da wani nuna jimami ba su kayi jana’izarta aka kaita gidanta na gaskiya.


Bayan kwana bakwai rayuwa ta canjawa shatu zancen gwaggoji ya fara tabbata, ko abinci basa bata sai tayi musu aikatau. Karshe suka ce zata fara fita tallan nono bayan ga ‘ya’yansu mata basu d’ora musu ba.


Cikin dare taji jatau suna shawara da d’an uwansa wai su had’a ta aure da liti yaron da kowa ya shaida d’an Ta’addane, ai kuwa shatu a daren ta mi’ke Ta hau shiri tabbas lokacin barinta garin yayi a yau zata tafi dangin uwarta.


Cikin duhun daren ta fito sai dai kafin ta kai ga d’arewa’karamar katangar jatau ya hasketa. Waye nan.......


*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-
3



“Waye nan” jatau ya sake fad’a da sauri shatu ta juya tayi kamar zata shiga bayan gida, murya can ‘kasa tace “nice zan zaga ne “ tsaki yayi ya shige yana bambamin fad’an “iskancin banza da wofi kawai ki nemi frigita ni cikin tsohon dare zan yi maganinki mai kama da ifritan aljannu” shatu dai bata ce komai ba tabi bayansa da harara tana sakin ‘kananan tsaki “ aradu Allah zai kaimu lokacin da zanyi maganinku “ yana shigewa sad’af- sad’af Ta shige bayan gidan ta kuma haure’karamar katangar ta bar gidan a guje.


Shatu duk da kasancewarta yarinya da ba zata gaza shekara sha biyu tana da wayo da kaifin basira, hakan yasa bata sha wuyar kai kanta tasha ba, ta hau motar da zata kaita har cikin gari sannan aka saka ta a motar garin bauchi.



*************

Tafiyar awowi ce ta kaisu bauchi ko daga nan ta tambayi motar katagum, yaran tasha yasa ta a motar da zata kaita tafawa balewa daga can ne zata samu motar katagum.

Suna isa kuwa kasancewar gidan babban gidane bata sha wuyar nemansa ba a kasadata da family house din nasu. Duk inda ta wuce sai an bita da kallo kasancewar tayi kama da mutanennan da ake kira bararoji, jikinta dukun-dukun hakanan kanta she looks very dirty.
Sam bata damu da rufe gashin kanta ba haka take tafe wurjanjan da silifas wari da wari a ‘kafarta.


Gidane babba irin ginin mutanen da , mai dauke da d’akuna birjik a kowacce shiyya, kasancewar nan ne ainahin gidan sarauta na garin, yasha gyara sosai da paint kana gani dai kasan ba wahala a tattare da ahalin gidan. Fili ne fetal ga manyan bishiyu ko ta ina. Rashin sanin inda zata yasa ta nufar wasu yara da taga suna wasan’kwallo a harabar gidan, ganinta a gurin yasa suka arce da gudu don su tabbas zatonsu aljannahce. Tsaki shatu taja had’e da komawa can gefe da ‘kullin kayanta ta zauna.

Iface-Ifacen yaranne ya fito da ahalin gidan a rud’e suna duban yaran da suke fad’in “Aljannah Aljannah “ shatu ta girgiza kai tana juyosu daga waje a zuciyarta tace “ai kuwa sai kunci ‘kwal uwarku akan iyayenku zan huce a aljannar zan zo musu kafin na bayyana kaina “ da sauri ta hargitse sumar kanta tsaf ta mi’ke ta hau zare ido ta shagid’e hannu d’aya, Ta dumfari babbar shiyyar da taga yaran sun nufa.

Ba zato ba tsammani suka ganta a tsakiyar filin kan kace meye iyayen yara sunyi hanyar neman tsira sai tsohuwa dada da aka bari jikinta yana’bari tana fad’in innahu min sulaimanu kuyi min aikin gafara wallahi ba laifina “ shatu ta cusgune fuska ta dumfari dada ai kafin kace mai dada ta saki gudawa da fitsari a wando ganin tana shirin fad’uwa shatu ta tintsire da dariya “ ke tsohuwa dakata kada ki sume min ni ba aljannah bace kamar yarda kuka d’auka mutum ce ni d’iyar maryama ‘ya wajen d’anki Lamid’o “. Dada ta zaro ido tana kallonta kafin tace “ki rantse da Allah “ shatu taja tsaki “ kwarankwatsa ni ba aljannah bace ko kinga kofato a ‘kafata “ sai sannan dada taja dogon numfashi tana zamewa a jikin bango zata zauna. Shatu ta kalli gudawar tace tana toshe hanci. Sai sannan dada ta lura ta saka salati da sauri ta rarrafa tashiga bayan gida shatu kuwa sai tuntsira dariya take.


Sai dada ta kimtsa ta dubeta bayan ta kaita rumfarta taje ta kira matan gidan “ to duk ku fito ku ji min bayani wai wannan d’iyar maryama ce maryaman da tuni lamid’o ya sallamata ga d’iyarta mai kama da jinnu ta bayyana “ shatu ta girgiza kai a hankali ta furta “zaki bayanin wannan ma “.

Sai sannan kowa ya fito cikin tsananin ta’ajjibi ana kallon shatu wai wannan jinin lamid’o ce yarinya kamar fulanin daji ita kuwa maryama mai yayi mata zafi ta za’bi rayuwar daji akan rayuwarta cikin gata da mutuncinta “. ‘Daya daga cikin matan ta fad’a shatu ta watsa mata wani kallo had’e da cewa “ yo haka ‘kaddarar Allah ta za’ba mata kuma kada a sake a zagi uwata don kuwa bata raye aradu raine zai ‘baci “ Ta fad’a cikin karyayyiyar hausarta ta fulanin usli. Gaba d’aya suka zaro ido dada ta saka kuka “yanzu’yar nan kika ce maryama ta mutu? Innalillahi yau ya lamid’o da liman zasuji da wannan ba’kin labarin kullum zancen su na maryama ne “
Ta fad’a tana jan majina hawaye sha’be-sha’be, kafin ta share hawayenta tsaf ta mayar da kallonta kan shatu tana mata kallon ‘kurilla “ wace shaida zaki bamu mu yarda ke d’in jininmu ce d’iyar maryama daso?” Shatu ta mata wani kallon she’ke’ke aradun Allah babu shaidar da zan baku sai na cika cikina tunda ku kam baku san zuru ba kun san wahalar da na hya kafin nazo nan amma ba wanda yace min ga ko ruwa Na hya “ dada tace “kwarai da gaskiyarki ke harira kawo mata abinci ke kuma furera ki kira matar lamid’o kice ko mai suke su biyo jirgi daga habuja suzo hukuncin ubangiji ya tabbata.”

Ana kawo mata abincin ta fara ci hannu baka hannu kwarya dad’in abincin har tsakar kanta ga nama zu’ku-zuku wanda rabonta da cin nama tun sallahr layya ta bara idan har bata manta ba. Taci tayi nak ta sha zo’bo sai sannan ta fara washe baki tana dariya ta kalli dada “to ko ki yarda ko kada ki yarda ni d’in diyar maryama ce ga hotunan da ta bani kafin rai yayi halinsa” ta fad’a tana zaro hotunan daga bujen da yake jikinta. Wanda suka san maryama da wanda sai a hoto suka santa duk suka zaro ido dada girgiza kai “ ba shakka hukumullahi la ajabun innalillahi wa inna ilaihirrajiuna wato maryama daso sallama tayi damu “ hawaye shabe shabe dada ta saki tana sake rushewa da kuka , sai kuma ta dubi shatu tana fyace majina “ ikon Allah wato shi ubannaki bararo ne?” Shatu ta zaro ido “ kan bala’i inji uban wa?” Ta fad’a tana cizon yatsa

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-4
ELEGANT ONLINE WRITERS****



Dada ta zuba mata idanun tsofaffinta , cikin gatse tace “inji ubanki muji da ya sace mana’ya ya gudu da ita” shatu ta girgiza kai had’e da mi’kewa a katifa tayi kwanciyarta. Ba a d’au dogon lokaci ba barci yayi awon gaba da ita. Dada ta bita da harara “ wannan yarinyar daga gani ‘yar daru ce bari kakannin naki suzo ni za’a barwa ke sai na koya miki hankali tukun, ke fure kira min su lamid’on kiji sun taho “ furere ta amsa daya bayan d’aya suna ficewa daga d’akin. Koda furere ta kira wayar taji shiru ta tabbatar sun taho kenan tunda ta san ba sajin kud’in jirgi kullum a tafe suke.



Dada tana zaune tana lazimi ita kuwa shatu barci takeyi sosai abinta cikin kwanciyar hankali.

Liman na dawowa dada ta sake bashi labari, cikin farin ciki yake kallon shatu da ba abinda ta d’auko na uwarta da alama can dangin ubanta ta d’auko don ban ga kamanni ba “ ya fada yana kallon dada, dada ta ta’be baki “ yo kaima dai ka fad’a yarinya kamar bararo ko fulanin daji anyi magana tace inji ubanwa? Bari su su lamid’on suzo sa tantance idan jininsu ce ko Ba tasu ba sa san yarda zasuyi da ita, ni wallahi tulin sumar kanta ne ma da idanunta suke ban tsoro yarinya kamar d’iyar jinnu don kyau “. Malami dariyar su ta manya kawai yayi gani n shatu ta mi’ke ba tare da sanin dadar ba tana ta harararta “ yo ki fito kice min kawai baki yarda dani ba mana Allah na tuba na me zan zauna ina muku’karya “

Sallamar su lamid’o ce yasa dada yin shiru bata tanka ta bata Allah ya sani tsoro yarinyar ke bata “ maraba lale da iyayen maryama kuzo yau dai kuga jikarku d’iyar maryama “ da sauri suka ‘karasa d’akin suna watsa idonsa akanta ta kuwa ‘kuri tana kallonsu.maman maryama tace “dada kada kice min wannan jinin maryama ce?” Dada ta ta’be baki “babu wai itace maryama ta haifo muku bararoji mai kama da ubanta. Ai mama bata’karasa jin abinda zata ceba ta ‘karasa da sauri ta kamata ta rungume “ Alhamdulillah ashe zan sake ganin maryama?” Shatu ta zame jikinta “ ai kuwa ba zaki sake ganin maryama idan dai ba yau kema zaki bita yarda ta tafi ba ashe kuna sonta ku ka kasa bata burin ranta akan haka ta gudu ta bar gida ta bar gatanta ta gwammace rayuwa cikin daji “. Lamid’o zama yayi yana kallon yarinyar mai cike da tsiwa da surutu mama kuwa sake janta jikinta tayi “ mun dade muna neman inda zamu ga maryama sai yau Allah ya nufa “ cewar lamido dada ta girgiza kai “ yau ai kaga dalilin da yasa ba zaku ga maryama ba tana can ‘kungurmin dajin da ba wuta balle a samu tv ta ina zata ji cigiyarta da ake ba’kin cikina d’aya ne Allah ya dauke maryama ba tare da mun sake ganawa ba sai bararon ‘yarta da ta bar mana” dada ta fad’a tana fashewa da kuka, mama ma zama tayi da’bas a kujera tana juya maganar dada lamid’on kuwa salati kawai yake ja , yanzu maryama ta mutu maryaman da ya dad’e yana nema ya nuna mata gata dama tuni ya yafe mata , mama kuka ta saka sosai tana rungume shatu a cinyarta cikin tsananin’kaunarta sam bata damu da daud’ar da take jikinta ba. Shatu taji zuciyarta ta karye da tausayin kakanninta mutuwar innaji ta dawo mata sabuwa kar itama ta rungume mama tana sake sakin kuka mai ratsa zuciya mama ta sake rungumeta tana shafa himilin gashinta.

Tsawon lokaci suna cikin jimami kafin lamid’o ya kalli shatu yace ya sunanki?” Murya a dashe tace “ shatu “ lamid’o ya jinjina kai “ to ya akayi kika gane nan kika zo ina so naji labarinki da garin da kuka zauna da labarin rayuwar maryama a garin....... shatu ta gyara zama daidai lokacin da wani daddad’an’kamshi ya ziryaci hancinta tana d’aga ido ta hango mai sallamar da sauri ta mi’ke tana wara ido tana fad’in “innaji “ mama ta kama hannunta “ zauna aysha ba mamanki bace yayarta ce da take bi ana ce mata mammah “ mammah da take tsaye ta waro ido tace “ mama kada kice min y’ar maryama ce ina maryaman ina ‘yar uwata alhamdulillah yau burina ya cika “. Mama hawaye ya ziraro mata don Ta san za’ayi haka Ta sani sarai deejah bata da buri irin taga maryama kullum zancenta kenan. Shigowar samarin yaran deejan yayi daidai da lokacin da mama tace “ Addu’a ‘yar uwarki take bu’kata yanzu Allah yayi mata rasuwa wannan y’arta ce Aysha da ta bari “. Gani su kayi mammah kawai ta zube numfashinta na ‘kokarin d’aukewa da sauri y’ay’anta su kayi kanta suna jijjigata had’e da kiran sunanta amma shiru. Dada ce ta d’ebo ruwa ta watsa mata sai kuwa ta kawo ajiyar zuciya “mama don Allah kice min wasa kike ko mafarki nake ba maryama ta bace ta mutu “ Lamid’o ya mi’kar da ita zaune Kafin yace “ Allahn da ya fi mu son maryama ya amsheta addua tafi bu’kata yanzu sai kuma d’iyarta da ya bar mana mu dinga kallo muna jin dad’i Alhamdulillah da wannan hikima ta ubangjji “. Da sauri mammah taja shatu jikinta ba tare da ‘kyankyaminta ta rungumta tana bata sumba a gefen kumatu cikin nuna mata tsananin ‘kauna take share mata hawaye tana kallonta with so much caring , saurayin d’anta da yake gefe imran ya hau ‘bata fuska cikin tsananin mamakin mammahn da bata’kyankyamin wannan yarinyar da Daud’a ta samu wajen zama a jikinta. Zuciyarsa har tashi ta fara yi saboda mutum ne shi mai tsananin’kyankyami da tsafta har da ta siyarwa. Runtse idonsa yayi kawai ba ya ma son sake kallon wannan kwamacalar. Ya bud’e kujerarsa wata karama da ya shigo da ita daga motarsa ya zauna. Sai a lokacin dada ta kula dashi duk da’kamshinsa ya sanar da duk ahalin gidan zuwansa’kamshin turarensa na amouage interlude 53 ya karad’e gidan sanye yake cikin black jeans da white long sleeve shirt ta Ralph lauren polo ya gyara glass dinsa da yayiwa idonsa kyau ba’a ganin ‘kwayar idonsa gashin kansa a kwance luf, murya a dashe yake gaida lamid’o da dada. Dada cikin mamakin halinsa na ko da yaushe tace” jakadan turawa yaushe ka bayyana a ‘kasar.” Cije lips dinsa yayi bai bata amsa ba sai ammar kaninsa ne yace “ yau kwanansa biyu “ dada ta kyabe fuska “ ai dama shi ba zaka ganshi ba Sai a dangin uwarsa saboda sun fimu farcen susa ammar kaine namu Allah yayi maka albarka yo wannan dama fuska kamar hadarin kaji wake maraba dashi ga shegen tsurfar tsaftar tsiya da ‘kakale aikin banza ko mu har a gaya mana tsafta “ . Ammar dariya kawai yake shi kuwa imran ya’kare tsuke fuska shi yasa sam baya son zuwa gurin tsohuwar nan mai shegiyar maganar tsiya. Lamid’o ya gyara murya kafin ya dubi Aysha “ ina jinki ayshatu bamu labarin “ ai kuwa ta sake gyara zama ta jingina kanta a jikin mommah ganinta take kamar innaji wallahi. Mommahn ta kara janta jikinta duk da warin da bakinta da jikinta yake bata’kayamaceta ba tana sauraran yarda take basu labari tiryan-tiryan.


Kafin ta gama bada labarin gaba d’aya gurin kowa kuka yake har ammar banda imran da ya d’auke kai gaba d’aya haushin yarinyar yake ji ga shegen surutu kamar kanya ba mamaki ma ‘karya take ba jininsu bace idan banda haka mai ya had’a su da bararoji. Yanzu haka had’a baki a kayi da ita tazo ta cucesu mutanen duniya da basu da gaskiya musamman su d’in da an sansu a gari . “ ya kamata ku bincika kafin ku tabbatar da gaskiyarta “ hakan kawai yace yaja baki yayi shiru kamar bashi yayi magana. Momma ta d’ago a fusace zata yi magana lamid’o ya d’aga mata hannu ita kuwa shatu wata harara ta zuba masa da ya sashi ware ido yana kallonta cikin mamakin rainin da ta nuna masa sai kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login