Showing 96001 words to 99000 words out of 117786 words
bane yanzu da wani ido zata dubeshi.
“How comes? Komai ya juye haka don Allah bani labari ya aka yi Mommah ta janye furucinta. Ta kuma ha’kura ta yafe min?” Imran ya fad’a hannayensa cikin na Ammar, da ya gyara zama yana kallonsa ya ce labarin da tsawo amma dole in gaya maka ko ka barni na huta jibi na ke son juyawa in d’auke amaryata zuwa Qatar nima.
——————————————————
Tun bayan da ka saki Shatu hankalina ya tashi musamman da naga Mommah a cikin wani yanayi, hakan ya sa dole na amince da shawarar da zuciyata ta ke bani na son sharewa Mommah hawaye daga takaicin da ka cusa mata, direct na furta mata ina son auren Shatu idan ta gama idda, duk da ina da tawa Ayshan da na ke masifar so ba kuma wata bace illa wannan Ayshan da na aura wato Mubeena. Na amince a raina zan had’asu su biyu na aura lokaci guda. Duk da dai ban ta’ba son Shatu soyayyar aure ba.
Na lura hakan yasa Mommah cikin farinciki sosai da har ta gaza ‘boyewa sai da ta bayyana.
Kwatsam muna shirin Shatu ta gama idda a fara shirin aure, sai ga Shatu da ciki, hakan yasa direct lokaci guda na sanar da Mommah na janye maganar auran Shatu don ba zan iya auren uwar yaranka ba alhali kana raye mai zan ce da yaranka idan suka girma suka tuhumemu da wannan kwamacalar? Mommah ta amince da uzurina don ita da kanta ta san hakan ba mai yiwuwa bace kuma tana tsoron haddasa gaba a tsakaninmu. Tun a lokacin muka fara neman hanyar da zamu daidaita ku koma, sai dai mun fahimci matsala ta wajenka saboda baka zo ba, sannan da ta haihu ma ka ‘ki zuwa, ni na ro’ki Mommah kada ta yi fushi da kai ta saka a Addu’a nima kuma zan dage da yi maka addu’a don tabbas na lura lamarinka da saka hannu.
Lokacin da ka dawo na hango soyayyar Shatu sosai a ranka a take na ro’ki Mommah ta amince a mayar muku da aurenku.
Mommah ta ce Ammar ban ‘ki ta taka ba amma ba yanzu zan mayar da aurensu ba har sai Imran ya shiga taitayinsa ka cigaba kuma da nunawa kana sonta kada ka bari kowa ya fahimci ba soyayya kuke ba. A take na amince da shawarar Mommah, ban gayawa kowa ba har sai lokacin da naga Dahda ya birkice akan lallai sai an mayar da aurenku, sannan na gaya masa na kuma tsara masa plan d’in yace zai nema maka auren ‘yar abokinsa wacce ba kowa bace illa Ayshatu na. To kaji abinda ya faru, duk da na ta’kaita maka, yanzu dai a bani abinci don kuwa yunwa na ke ji.”
Imran da hawayen farin ciki ya gauraye fuskarsa tuni ya sake rungumw Ammar yana sakin kuka, kukan cikar burinsa a lokacin da gwiwarsa ta karye ya d’ebe haso da samuwar rabin rayuwarsa wato Shatu, yaji tamkar ya mi’ke ya rungumeta tsam a jikinsa amma ba Zai iya ba a gaban idon Ammar sai dai tabbas yau shi kad’ai ya san kalar soyayyar da zai nuna mata.
Da sauri ya mi’ke yana kallon Ammar “Ta shi muje eatery ka ci abinci sai muyiwa madam take away.”
Ya fad’a yana jifan Shatu da wani sihirtaccen kallo da murmushi a bakinsa. Kunya ce ta kamata ta yi saurin sunkuyar da kai. Hakan da ta yi shi yasa ya ji ba zai iya tafiya ba ba tare da ya sata a jikinsa bugun zuciyarsu ya had’u waje d’aya don haka ya kalli Ammar da ya mi’ke ya ce “Please ina zuwa bari na raka ta d’akinta tukun ta samu ko wanka ta yi kafin mu dawo naga kamar she looks so tired” Ammar dai murmushi ya saki yana d’aga kansa.
Shatu ta mi’ke ta bi bayan Imran wani farinciki yana huda duka sassan jikinta, da zuciyarta kai har ma da ‘bargo.
Suna shiga d’akin ya juyo yana kallonta idanunsa na lullumshewa na zallar fitina hakan da ta gani ya tuna mata first night d’insu da sauri ta sunkuyar da kai, shi kuwa saurin jawota ya yi ya had’e jikinsu yana sakin wata ajiyar zuciya da ta tafiyar masa da duk wani ‘bacin rai da ya taru ya dun’kule masa a ma’koshi, ashe da gaske ne ba’kin ciki na taruwa a zuciya.
Ita kanta Shatu sakin ajiyar zuciyar take ya d’ago idanunta yana ‘karewa cikin ‘kwayar idanunta kallo da wani kyakykyawan smile da ni kaina ban ta’ba ganin Imran yayi shi ba. Murya can ‘kasa ya ce “Ji na ke fa tamkar na had’iye ki? Ban ta’ba tunanin zuwan wannan ranar ba, ke fa ya kika ji?” Ya fad’a yana jan karan hancinta. Murmushi kawai ta saki ta ce “Kaje Yaya Ammar fa jiranka ya ke.” Ya ri’ke kansa cikin fad’in “Ouch ni na manta dashi ma, ya zama dole na kuma yau na faranta masa, kamar yarda ya faranta min da abinda tunda na ke a rayuwata ban ta’ba ganin abinda na so sama dashi ba. Sauri zan yi in sallameshi in dawo yau kwana zan yi muna hira bayan mun yi addu’ar godiya ga Allah.” Yana fad’in haka ya fita da sauri har yanayi kamar zai fad’in garin juyowa yana kallonta.
Murmushi ta saki cikin tarin farin ciki ta isa mudubi tana ‘karewa kanta kallo ta tabbata dai MATAR IMRAN. Samun kanta kawai ta yi da dur’kusawa ta kai goshinta a ‘kasa. Ta dad’e tana addu’a. Sannan ta d’ago tana dariya a hankali ta furta yanzu wasan zai fara kada ka yi tunanin ka sameni a ‘bagas bayan tarin wula’kancin da ka yi min duka sai na fanshe kafin na sakar maka jikina ka yi yarda kake so dashi, sai ka amsa laifinka sai na jigata ka son raina sai kuma na nuna maka Shatun yanzu Aysha ce Ba Shatun Mommah ba........
Saduwar alheri!
Love you lodi-lodi
Jikar Nashe.
Tsam ta mi’ke ta shige toilet, wanka ta yi sosai mai sunan wanka, sannan ta hau wanke duk wani lungu da sa’ko na ha’koranta, ta sake binsu ta kuskure da mouth wash.
Tana fitowa ta bud’e jakar kayan da Mommah ta had’o mata, murmushi ta saki ganin duk masu kyau ne, tana bud’esu kuwa zallar ‘kamshin turaruka ne ya bad’e hancinta, take ta lumshe idonta tana sake jaddada ‘kaunar Mommah a zuciyarta tabbas Mommah Uwace abar alfaharin ‘ya’ya, kunta ta kamata kamar tana gaban Mommahn na abinda ta dinga aikatawa ashe Mommahn duk gwada su take.
Lace ta ciro peach colour mai tsananin kyau ga taushi an yi mata d’inkin doguwar riga da tayi mugun fito da duk wata sura ta jikinta, kasancewar lace d’in mai matu’kar tsada na Hkg company ne yasa bata wani ji nauyinsa a jikinta ba. ta taje tulin sumar kanta kafin ta kawa ‘karamin band ta kalmasa gashin a ciki sai yayi mata kamar gammo tabbas Shatu akwai suma.
A cikin kayan dai ta gano wasu chewingum masu ‘kamshin tsiya hakan yasa ta wurga a bakinta. Yau dai su Shatu har lip stick a kasa akan d’an mitsilin le’ben sai gashi ya fito ras dashi ya bada shape d’in heart, ba ta ja jagira ban sai dai ta taje gashin giran, ta kuma saka masacara a Zara-zaran gashin idonta. Ni kaina sai da
Na ware ido Na sake kallonta tamkar ba Shatu ba musamman da ta kalmasa d’ankwalinta ta yi d’aurin Zahra buhari ga gold ya ji a wuyanta da hannuta tsaf ta fito a zaratan Mata tamkar ba Shatun Mommah ba.
Zamanta ta yi a gefen gado da
Mayafinta a side jira take ta ji motsin shigowarsu ta yafe mayafin don tayi al’kawarin sai an mata siyan baki kamar yarda ake yiwa kowace amarya.
Tana jin motsin kuwa taja mayafin ta rufe kanta ruf, tana cigaba da danna waya, tuni d’akin ya baje da wani ‘kamshin zallar turarikan Wuta da humra da aka had’o mata. Na Hajja A’i gidan ‘kamshi duk mai son turarenta ya duba page 40 akwai numberrta ta iya turare sosai tabbas ba ‘karya musamman na jiki da dorot.
Har wani part Na daban ya kai Ammar bayan sun dawo bedroom ne da parlour yana murmushi ya dubi Ammar d’in “Ka sha zamanka anan kada ka fito sai na zo da kaina na fito da Kai.” Ammar ya zaro ido cikin mamakin furucin Imran d’in sai kuma ya yi murmushi ya ce “Allah sarki ni na baro tawa amaryar na zo inda za’a kulleni ace kada na fito ai shikkenan, da zan samu jirgi ma yau zan koma don hankalina yana kan Mubeenaty.” Imran ya hau sosa ‘keya kafin cikin dariya ya ce “Kai yaro ne bana son kaga abinda hankalinka ba zai iya d’auka ba ko na jefaka a wani hali gashi madam d’in taka bata kusa.” Ammar ya sake ware ido ya ce “Lallai Bros nine ma yaro da Aurena fa?” “Ka san meye auren? Ai da ka tare da ita ina tabbatar maka ba zaka iya tahowa ka barta da tare zaku ta ho honey moon amma ka taho ka barta acan. Ka yi zamanka kawai ka saka a kawo maka ita ku gurji amarci wallahi zan kai ku guraren sha’katawa da yawa.” Ammar ya grigiza kai “Ma dawo nan gaba, idan Mommah zata zo, saboda akwai tarin ayyuka da Na bari a Qatar.” Imran ya fice yana cewa “Kai ka cika ni da surutu Na bar madam a can.”
Ya dinga ‘ko’karin kiran Mommah, amma bata d’agawa tun d’azu ya ke nemanta ya zabga mata uban godiya. Duk da dai ya samu Dahda amma Mommah fa? Da ita ya kamata yayi sharing duk happiness d’in nan don haka ya ‘kudirce cewa ‘karshen wata suma zasu tafi ya sake jaddada gidiyarsa garesu sannan shi da Shatu da su Akram su je wajen dangin Baban Shatun.
Wannan karan ya sameta, da wani irin farin ciki da karsashi ya ce My heart. Sunane da ya ke Kiranta dashi rabonta da ta ji sunan a bakinsa har ta mance. Murmushi ta saki tace “Burinka ya cika ko? Yanzun ka daina fushi Dani? Kuma zaka yi min al’kawarin Imran d’ina Na da ya dawo mai jin maganata.”
Ji ya yi kawai hawaye ya fara zubo masa. Bana komai ba sai Na zallar farinciki da takaicin ba’kantawa Mommah da ya dinga yi, ba tare da ya san dalili ba, cikin muryar kuka ya ce “Please My heart ki yafe min, na yi nadama.” Ya fad’a yana danne gefen lips d’insa tamkar ya ciresu sosai yake jin zafin zuciya. Mommah ajiyar zuciya ta saki ta ce “Na yafe maka Imran dama can ban ri’ke ka da komai ba Na san ba yin kanka bane ina Shatu sun sauka Lafiya? Ka yi ‘kokari ka had’a mata layin nan ‘kasar don a dinga samunta a waya, ka kuma bi da ita a hankali she is still young.” Daga haka ya ji ta katse wayar. Murmushi ya saki a zuciyarsa ya ce “Haba Mommah ai ba wannan maganar don tsahon lokacin da kuka tsaya kuna jan raina yau sai na fanshe a jikin Shatu, yarinyar da tunda na kusanceta ban sake barci mai dad’i ba yau dole duk mafarkan da nakeyi su tabbatar zahiran Na d’and’anesu a zahiri.
Wanka ya shiga, tsaf ya fito yana zabga ‘kamshin sabulan wanka na makari, Wando ya saka three Quater black da white armless riga ya gyara kwantacciyar sumarsa da sajen da yake gefen fuskarsa ba ‘karamin kyau ya yi ba. sannan ya d’au ledojin take away d’in da yayi musu.
Kitchen ya shiga ya yi warming abincin ya kuma dafa madara fresh mai d’umi ya zuba a flask, ya yayyanka mata fruits duk ‘ko’kari yake Na son faranta mata.
A dinning ya jere komai sannan yasa kai ya shiga bedroom d’in da take. Yana bud’e ‘kofa daddad’an ‘kamshin da ya cakud’e da sanyin a.c ya dakar masa fuska take wata kasala ta lullu’beshi.
Ya kai dubansa a saman bed d’in inda ta takure kanta murmushi ya saki yana taku zuwa wajenta. A gefe ya zauna ya ra’ba jikinsa da nata ya yi mata kyakykywar runguma ta gefenta yana sakin ajiyar zuciya ya yi nufin unveiling d’inta da sauri ta ri’ke hannunsa, da ya saka shi lumshe ido sabida taushin hannunsa, murya a sar’ke ta ce “Siyan Baki?” Imran ya shige jikinta sosai yana shinshinar ‘kamshinta ya ce “Akwai siyan bakin da ya fice wannan ni cinye bakin ma zan yi, please Shatu ki bud’e min fuskarki I wanna kiss your lips.” Cikin muryar ‘bacin rai kamar gaske ta ce “Bakin da yake warin? Har ka daina ‘kyamarsa?” Kunya ce gaba d’aya ta dabaibayeshi a kunne ya rad’a mata ban da tuna da ta shi muje ki ci abinci tunda rowar fuskar za kiyi min zan nemo abin siyan bakin.” Ya fad’a cikin wata voice da ta toni asirin halin da ya ke ciki. Tana mi’kewa tsaye ta ji ya kai mata wata kyakykyawar runguma ya kuma cire mayafin da sauri ta bud’e ido tana kallonsa ranta a ‘bace ta ce “Wallahi sai ka ba ni kud’in siyan baki na, kuma million biyar na ke so cif, sannan kada ka saka ran nan kusa zan amince ka kusanceni sai nan da shekara guda, sai na yarda da gaske ba sha’awa ta ka ke ba soyayyar zahiri ka ke min, sai ka kuma sanar da
Abokanka yarda ka ke tsananin so na domin sai an yi Walima ko anan ko a Nigeria ka fad’awa mutane yarda ka ke tsananin so na, sai ka yi min lefe sannan zan amince ka kusanceni shima after one year.
Da sauri Imran ya dinga jifanta da wani irin kallo ganin da gaske ta ke maganar da take, surarta kawai ya ke kallo da le’benta da ya ke fisgar hankalinsa. Ya ja gwauron ajiyar zuciya kafin cikin wata irin murya ya ce “One year fa kika ce?” Cikin sake tabbatar masa da furuncinta ta ce “Tabbas!”
Ayi manage da wannan zaman makoki muke don ma kada kujini shiru ne nagode
"Kallon cikin idonta ya sake yi cikin bu’katar ‘karin bayani, yanayin kallonnasa yasa ta yi saurin ‘kasa da idonta. Sam ba zata jurewa kallon ‘kwayar idonsa ba, murmushi kawai Imran ya saki yana mamakin ƙarfin hali irinnata.
Cikin slow Voice ya ce “zan yarda da sharad’inki but on one condition duk runtsi ba zamu raba makwanci ba, ina nufin Ɗaki ɗaya zamu dinga kwana, ban kuma amince da raba cin abinci ba idan kin yarda sai na ce miki Imran ma ya yarda da dokarki tunda kece ki ke aurena."
Taɓe bakinta ta yi kafin ta ce "Zan amince da komai amma banda kwana makwanci Ɗaya am serious fa, ko ba ni ke aurenka ya zama lallai abi sharaɗina kuma ni ban iya girki ba don ba shi na zo yi ba ko da ya ke me ma za kayi da abincin Shatu ƙazama bagidajiya." shiru ya yi mata ya lura dangerrtace ta motsa. Bari ya bida its yarda take so zuwa kwana biyu ya tabbatar idan ya biye mata yanzu ɓata masa rai za tayi ta kuma dinga tuno da maganar da ta wuce, shi a karan kansa haushin kansa ya keji idan ya tuna kaf furucinsa na.baya da ya dinga jifan Shatu da su.
Jikinsa a sanyaye ya ri’ke hannunta, duk da Ƙoƙarin ƙwacewa da ta dinga yi, amma ta gagara dole ta bishi a haka.
Da kansa ya ja mata kujera ta zauna tana duban abincin tana yatsine baki don abincin duk ƙamshin spices ɗin garin suke yi don ma a haka wai yayi ƙoƙarin samo masa cinnamon rice da salad ga gasashshiyar kaza da ta ji yaji sosai. Ta dinga cin abincin tamkar ba taso ba wai abincin bane bata so duk salon ta ɓata masa rai sai dai ba ta ci nasara ba domin zuciyar Imran yau cike ta ke taf da farinciki bai ga kuma wani dalili da zai ɓata masa shi ba.
Lemon Shani ya tsiyaya mata a cup ya kai mata bakinta “Ha” ya faɗa kamar yarda ake yiwa yara, ta bud’e bakin tana basar dashi.
Ya ajiye cup ɗin ganin ta miƙe ya bi bayanta, yana sake mamakin ganin yarda hips ɗinta ya cika sosai duk inda ta juya shima sai ya juya.
Tana zama ya hau yi mata tausa, cikin wani irin salo da son ya isar da sa’konsa ai kuwa sa’kon ya je inda ake son ya je don haka da sauri ta janye ‘kafarta. “Bar shi bana so” Imran da dariya taso kamashi ya ce “Why?” “Ni dai kawai bana so” ta fad’a tana cono
Baki. “To ni zo kiyi min.” Wani kallo ta yi masa kafin ta furta “Ba abinda na zo yi ba kenan.” Wannan karan dariya ya yi sosai ya ce “Ai shikkenan bari ki gama hutawa sai
Mu yi abinda kika zo yi ko an samu ‘kanin su Ikram, kin san yarinyar nan ko kallona ba tayi amma na san laifinki ne ke kika cusa mata tsanata.” Had’e rai ta yi ta ce “Kawai kuma sai na cusa mata tsanarka alhali kaine mahaifinta.” Zamewa ya yi ya kwanta had’e da d’ora kansa a cinyarta yana sha’kar daddad’an turaren da aka turara kayanta tun a gida, tun tana ‘ko’karin ‘kwacewa har ta saduda ta ‘kyaleshi ganin barci mai nauyi da gaske ya sure shi, ita kanta barcin ta ke ji, ta tabbatar yarda bata samun barci shima baya samu throw pillow d’in kujerar ta ja ita ma ta kwanta barcin ne sosai ya yi awan gaba da ita.
Shi kansa Ammar a gajiye ya ke sosai don haka bayan gama wayarsa da mubeenah kwanciya kawai ya yi barci mai nauyi ya yi awan gaba da shi.
Sai da gari ya yi duhu sannan ta farka, da kyar ta zame cinyarta da ya bi ya kanainaye da hannunsa, hakan ne ya farkar da shi ya zuba mata ido alamar “Menene?” Murya a dashe alamar barci ya yi nauyi ta ce “Lokacin sallah fa ya wuce.”
Cikin tsananin mamakin barcin da yayi ya mi’ke don rabonsa da irin wannan barcin har ya manta, tana ganin ya shige bedroom dinsa ita ma ta mi’ke ta shige.
Sai da ta idar da sallahr sannan ta sake shiga wanka.
Wannan karan shigar wasu rantsatstsun English wears ta yi ta kawo after dress ta saka kasancewar