Showing 12001 words to 15000 words out of 117786 words

Chapter 5 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

450

sha mama na bar mata, duk ba ma wannan ba bata raye wa kake so ya rike mata er ta wa take dashi idan bani ba.” Jikin dahda ne yayi sanyi “ maryama ta mutu?” Ya fad’a cikin taushin murya ba kamar yarda ya d’au zafi ba, innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, momma ta ja ajiyar zuciya kafin tace “ maryama ta mutu nima d’azu kira ya ruskeni daga katagum muka tafi a can muka samu ita wannan er tazo ita kuma take sanar damu mahaifiyrta ta mutu.” Allah ya gafarta mata Allah yasa ta huta amma ina mahaifinta?” Momma gyara zama cikin kasa da murya tace” shima Allah yayi masa rasuwa “ Tausayin shatu sosai ya kama Alhaji, ya
Hau girgiza kai yana jaddada lamarin girman ubangiji “ Allah ya gafarta musu Allah kuma ya bamu ikon sauke nauyin ri’kon maraya “. Farin ciki ya ratsa zuciyar mommah sai sannan hankalinta ya kwanta da har ya amsa zai ri’keta “ Nagode dear bari na kawo maka abincin” .

Ta fara zuba masa abincin ya dubeta “ kiyi ‘ko’kari sosai akan yarinyar nan ki koya mata tsafta uwa uba tarbiyya don sosai na lura bata da manner, insha Allah nima I will try my best naga na kula da lamarinta don kamar nauyinta ne Allah ya d’ora mana.” Insha Allah mommah kawai take fad’a zuciyarta cike da farin ciki a take a wajen ya tura mata kud’i a account ya umarceta da kashegari aje ayiwa shatu siyayya. Godiya ta sake masa ta mi’ke don fita shirin barci.




******** kwananta biyar da zuwa gidan amma har ta fara murjewa, jikinta yayi kyau masha Allah duk da haskenta bai fito gaba d’aya ba . Duk wani abin da bata sani ba mommah ta koyar da ita yarda za tayi amfani dashi a gidan.Ta fara kuma ‘ko’karin ganin ta daina rashin kunya duk da har zuwa lokacin da yarinta a tattare da ita.

Abubuwa da dama bata iya cinsu har a lokacin da zarar taci sai tayi aman su saboda rashin sabo sai dai son cin nama shan madara da milo kuwa har dana maza da kauri sosai take damawa ta shanye.Ammar tuni ya fara sakin jikinsa da ita kasancewar yanzu duk ta d’an zubar da rashin kunyar an samo mata malami da zai dinga koyar da ita.Imran ne baya shiga shirginta .


Yauma da wuri ta tashi, tayi saurin yin wanka da brush don kar mommah tayi mata fad’a gashi ne dai bata taje shi ba bata son gyaransa sam bata’ki kuma mommahn Ta aske shi ba kamar yarda tace.


Ganin su mommah tayi suna ta aiki a gidan ta fara tunanin ko mai zai faru ake ta wannan aikin Ta kuma lura zuciyar momma sam ba dad’i don komai a sanyaye take yinsa. Momma ta dubeta tana amsa gaisuwar da take mata cikin nutsuwa” yauwa my baby kin yi wanka maza kije kiyi break fast kizo d’aki ina son ganinki “. Amsawa tayi da sauri tana isa kan dinning , Tayi turus ganin imran a dinning d’in yana break idanunsa ya zuba mata, da sauri ta dur’kusa tana gaisheshi imran ya had’e fuska. “ ke bar nan wajen before I slap you “ kallon ‘kasa-‘kasa tayi masa “ To ba yunwa nake ji ba zaka ce na bar nan.” Harara ya watsa mata sai kuma ya cigaba da abinda yake kafin bakinsa ya furta “ Dirty Girl “ zama tayi ba tare da san abinda yace “ kin san mai nace miki?”kamar doluwa ta hau girgiza kai “ ‘kazama nace miki Alhamdulillah na kusa barin gidan sai kuci’kazantarku ku kad’ai “. Ba tayi masa magana illa kallon plate d’insa da tayi yana shirin kai tsokar nama ta miyar turmeric baki ta saki murmushi kafin tace “ Ga kanan’kazami kana cin miya kamar gudawa.....” Ai da sauri ya furzar da naman bakinsa yayi wajen sink shatu ta tuntsire da dariya a hankali ta furta “ ba’kin mugu in dai ina gidannan ka daina ci ka ‘koshi “ sosai ya kuskure bakinsa ya bita da wani kallo kafin ya wuce shatu ta ja plate taci abinci tayi nak “ Allah gaba ta kaini ba gashima har nayi’kiba ba gobe ma ka sake ce min’kazama Allah mhmmn sai kuma ta girgiza kai.”



Da kyar take nishi sai kuma ta tuna kiran da momma take mata da sauri ta shige sashen mommah a zaune ta ganta ta rakfa tagumi idonta har ja yayi. Jikinta a sanyaye ta ‘karasa ta zauna daf da ita “ Momma mai ya sameki?” Momma ta shafa kanta “ bakomai shatu anjima za’ayi ba’ki babar mai gidan nan zata zo don Allah don’t make any thing da za’a tafi dake a baki bana son kiyi rashin kunya ko wani abu kinji ki daina yawan fitowa kiyi tasa catoon a d’akin ki.” Shatu ta d’aga kai “ Tana da fad’a ne Mommah?” Shatu tace tana kallon ta , mommah ta girgiza kai “ Ba fad’a kad’ai ba zata iya sa daga ni har ke mai gidan nan ya koremu “ “ cabd’i muje ina duk wannan naman mu barhi “ Momma tayi tsaki “ ke kike ta nama Aysha Idan nama ne duk mai sau’ki ne gidanmu ma akwai ina son mijina bana son ta raba ni dashi “
“ Au to hi dahdan sai ya rabu dake “ momma ta d’aka mata duka “ sau nawa na hanaki cewa hi da he a maganarki ? Ba abinda zaki fahimta yanzu sai nan gaba zaki san and wacece hajja tashi kije Na gaya miki ba ruwanki da kowa, kuma ki dinga dur’kusawa har ‘kasa kina gaisuwa kin ji?” Shatu ta girgiza kai kawai daidai lokacin da suka ji dirin motoci a harabar gidan.


Da sauri mommah ta mi’ke cikin rawar jiki ta fice, shatu ta bita da kallo kafin ta fita taga wacece wannan da mommah bata son’bacin ranta. Babban falon ta fita duk mutanen gidan suna zaune gefe d’aya mommah ce dur’kushe tana gaida hajja murya a cunkushe hajjan take amsawa tana yatsine fuska. Ganin yarda su imran suka gurfana suna gaisheta yasa ita ma shatu ta’karasa ta dur’kusa tana gaishe su. Hajja ta zuba mata manyan idonta “ ita kuma wannan daga ina? Sabuwar mai aiki kuka yi da har kuma ta sake ta za’ke take shiga cikin ahalin gida, Ba shakka to mi’ke daga nan kafin Na kai miki mangari.” Shatu ta d’ago ido zata aikata halinnata sai kuma suka had’a ido da mommah sum sum ta mi’ke ta shige “ ina magana an min banza ga a tsohuwar banza ko nace wacece wannan deejah?” Murya can ‘kasa mommah tace “ d’iyar maryama ce’kanwata to ta rasu shine na d’aukota “. “ shine aka ajiyeta ba tare da izini na ba ko? Ni da gidan d’ana ga a baitil mali an samu wacece ma maryama a zuri’arku?” Momma ta sake sunkuyar da kai “ ‘kanwata data bar gida da dadewa “. Hajja salati tasa “ kice min’kanwarki da ta tafi karuwanci shine kika d’auko shegiyar’yarta kika cud’anya cikin tsaftatacciyar zuri’ata, zuriar da aka Haifa ta sunnar manzon Allah to kuwa ba zai yiwu ba kai imran kira min ubanka a waya.” Gaba d’aya suja juya jin takun tafiyar dahda murya a cunkushe ya shigo, shatu da take ra’be a ‘kofa ta shige d’aki wai yau ita ake kira da shegiya ai kuwa tayi al’kawarin sai ta sa matar nan kuka.


Dahda ya dur’kusa a gefenta. Fuskarsa yana d’an sakin murmushi yace “ Hajja ashe kin shigo ? Barka da zuwa ta amsa tana girgiza’kafa “ kai ka bawa shegiya lasisin zama a gidanka ?” Cikin rashin fahimtar zancennata yace “ wacece shegiya?” Kwafa tayi “ baka santa ba kenan d’iyar gantalalliyar’kanwarta maryam da ta bar gida saboda ubanta ya za’ba mata miji ta gwammace ta tafi yawan dadiro.” “ Hajja wanda ya mutu fa ya mutu mai yasa zaki dinga’bata mata gawa ba kuma yawon dadiro ta tafi aure tayi ta haifi er ta don haka wannan zancen don Allah ki daina fad’arsa “. Dada ya fad’a fuskarsa a had’e. Hajja ta sake tsuke fuska “ Ba shakka ubana to ai sai ka bari sai na zama sokuwar uwa sannan in dinga bari kana fad’a ina fad’a shashasha kawai wanda mace ta riga ta gama dashi shi yasa wannan karan da shiri na nazo kaga can to matarka ce ni na bada sadaki aka auro maka ita tunda na bika na bika ka’ki amincewa da auren shi yasa ni na auro maka ita kuma wallahi kace baka amince ba sai dai ka sake wata uwar.” Mommah wani fad’uwar gaba ne ya sameta ganin wacce aka nuna aka ce kishiyarta ce y’ar’kanwar hajjance uwa d’aya uba d’aya da ta dad’e tana zawarci kuma y’arta imran zai aura sannan ace itace kishiyarta tabbas akwai ‘kura. Dahda cikin ‘bacin rai yake kallon ta tana zaune fuskarta sai murumushi take tana rausayar da kai.


Dahda mi’kewa yayi kawai yayi hanyar fita. Hajja ta sake tunzira “ Ba shakka sallamamme ai ban gama magana ba kake shirin fita wannan yarinyar na bada awa ashirin da hud’u t bar gidannan ‘bangaren da nake sauka anan amarya zata tare yanzu ne na san kayi aure da ka auri’yar dangi, Auren imran kuma na saka rana na da wata biyu, ba’kin ciki ya kasheki dijah dama ai na gaya miki ina tafe ga dai abin takaici kishiyarki kuma surukar d’anki sai ki had’iyi zuciya ki mutu, ku matan yanzu baku da buri irin ku mallakewa mutum d’a . Momma mi’kewa kawai tayi
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-9


ELEGANT ONLINE WRITERS........


Tana shiga d’akinta hawaye ya fara zubo mata, Tunani take sosai a zuciyarta so take ta hango laifin da takewa dangin mijinta suka tsaneta har haka, mai tayi musu? Shine abinda take tunani a zuciyarta, har ga Allah bata nufin kowa da sharri rayuwarta take free ba tare da kowa a ranta ba amma sun bi sun tsaneta.

A gefen gadon ta zauna, shatu data gefe jikinta yayi sanyi ganin mommah na hawaye, taji duk duniya ta tsani waccan Almasifatun tsohuwar a hankali ta zauna jikin mommah itama ta saki nata kukayi. Momma dafa kanta kawai tayi alamar rarrashi. Daidai lokacin Ammar da Imran suka shigo d’akin jikinsu a sanyaye suka zauna kan cushion chair d’in da take gefe fuskarsu sam ba walwala musamman ammar, sam baya son abinda zai saka mahaifiyarsa a ‘bacin rai. Ammar yayi’kasa da muryarsa “ Momma kiyi hakuri komai lokacine, kuma wata rana sai labari.” Girgiza kai tayi “ Na kai ma’kura Ammar iya ha’kurin da zan iya kenan kun san iya lokacin da nake’kunsar ba’kin cikin hajja tun ranar da na kwana d’aya a gidannan duk a dalilin mahaifinku bai auri za’binta ba, kuma ba kowa bace za’bin nata sai wannan matar da sai da ta san yarda tayi yanzu ta auro masa ita, to lamarin ya isa zan tattara in tafi amma ba zan zauna ba’kin ciki ya kashe ni ba just like bani da iyaye, gidan ubanku ne ku zauna, bare shi gashi nan zasu aura masa wacce suke so, tun yaushe nake jan kunmensa ya rabu da yarinyarnan ya’ki, saboda kawai kyanta da kwalliyarsa yana rud’arta to yaje ya aureta amma ka san Allah ba hannuna a cikin lamarin aurenka, wanda dama don a gasa min ba’kin ciki aka’kir’kiresa.”
Ta saki ajiyar zuciya bayan ta mi’ke ta shiga had’a kayanta, Ammar ya ri’ke akwatin “ please mommah kada kiyi abinda baki ta’ba yi ba da yarintarki balle da girmanki please ki rabu dasu,ko mu kad’ai zamu iya share miki hawaye, kuma wallahi at this point sunyi na’karshe, kaima yaya Imran don Allah kayi hakuri ka kyale musu’yarsu ko don kwanciyar hankalin Mommah “ wani kallo Imran ya zuba masa “ meye laifin shaheeda da zan rabu da ita, ko kana tunanin a bayansu take? To kullum maganar ta tana jin haushin abinda suke wa mommah.” Wani kallo momma ta wurga masa sai kuma tayi kwafa “ mhmn ba dai shaheeda bace Imran ka aureta ban hanaka ba, tunda lokacin da na hanakan ai baka ji ba, sai dai bahaushe yace wanda bai ji bari ba.... kai kuma Ammar kada ka sake masa magana idan ta nice ma barin gidan zanyi ba sai na zauna zanga kayan takaici ba .” Imran shiru yayi yana sake zabgawa Ammar harara sai kuma yayi kwafa ya fice. Mommah tabi bayansa da kallo tana masa addu’ar shiriya a zuciyarta ji take kamar ta rusa kuka gaba d’aya sun cusawa Imran soyayyar shaheeda ta ‘karfi da yaji da yaudara da komai. “ ka rabu dashi Ammar tsakaninka dashi Addu’a ya riga yayi nisa a soyayyar shaheeda ba zai ta’ba ganin aibunta ba.” Ammar ji yayi ransa ya sake’baci idan dai da shine ko da gold aka’kera shahida sai ya ha’kura aurenta balle shi dai ban da kyan fuska bai ga mai ya gani tare da shahidan ba tana tafiya kamar sillan kara,sai iyayi da kwainane. Shatu dai tana gefe tana kallon ikon Allah, takaicin Imran kuwa ya gama cikata. Har so take taga wacece wannan da ya fi sonta akan’bacin ran mahaifiyarsa. Ammar ya cigaba da bawa mommah ha’kuri ganin ta’ki ha’kura yasa ya fita wajen bayan ya danna kiran hajiya mama mahaifiyar mommah a cikin wayarsa. Basu san me yace ba sun ga dai ya dawo da sauri ya mi’kawa mommahn wayar, ya wurga masa harara don ta san’kara ya kai ta wajen hajiya maman. Tana sallama hajiya mama ta shiga fad’a tuni mommah ta sa kuka ta fara bata labari. Hajiya mama cikin zafi ta katseta “ kishiya saboda kishiya zaki bar gidanki akan ki aka fara kishiya?da girman ki da komai kike neman zubar da mutuncin ki to ahir ki kiyayeni kina shirin auren da’kanne da ‘ya’ya, nan gaba su kuma idan sunyi wa zai musu fad’a? To ki saurareni da kyau ki mayar da akwatinnan kafin ma su gani su ji dad’i gobe insha Allah’kannenki sun zo hutu daga turkey zasu zo kanon suyi miki hutu hisham ma dama yana ta son zuwa wajen mutuminsa Ammar. Ina shatu?” Momma ta mi’kawa shatu wayar “ maza ki masa hajia mama ce “. Shatu ta kar’bi wayar cikin rashin sabo ta fara gaisheta “ lafiya lau shatu ya ba’kunta? Gobe zaki ga aunties d’inki suna ta son ganinki.” Murmushi shatu kawai tayi saboda ba ‘yan hayaniyar a kanta. Hajiya mama ta sake cewa “ Ba dai matsala dai ko?” Shatu ta girgiza kai “ Bakomai mama” To masha Allah sai kin ga sa’ko “ hajiya mama ta fad’a tana kshe wayar. A hankali shatu ta mi’ka wa Ammar waya, ganin yarda jikinta yayi sanyi yasa Ammar ya shiga janta da wasa” shatun mommah’kalau kuwa yau na ganki jiki ya mutu? Ko don ki had’u da Babarki a masifa “ harararsa shatu tayi “ Ai wallahi ba tsoronta naji ba, don dai kawai mommah ta hana ne amma wallahi da tuni ta d’ebi kashinta a hannu yo Allah na tuba wannan ‘karamar alhakin, ka san Allah da ‘kauyenmu ne yau sai na saka yara sun mata kid’an Atire.” Ammar mai zaiyi banda dariya mommah kuwa bud’e ido tayi tana kallon shatu yarda take yi da baki “ To shatu ba ‘kauyenku bane kuma anan idan kayi wa wanda ya girme ka rashin kunya kulleka ake a gidan yara don haka be careful.” Ammar ya fad’a fuskarsa d’auke da alamar tsoratarwa. Shatu ta kya’be baki “ Ai in dai ba kayi a fili ba sai mutum yayi ta bayan fage yarda za ‘a gane ba.” Ammar girgiza kai kawai yayi yace “Allah ya shiryeki shatu.” “ Tashi maza kije kiyi sallah Ayshata ai Na san kina jin maganata ba zaki jawo min abin fad’a ba “.murmushi tayi tana mi’kewa dad’in yabon da momma tayi mata da sauri ta shige toilet ta bar momma da ta zuba tagumi tunani yyi mata katutu.



Dahda da daddare da kansa ya shigo d’akin mommah ganin ko nemansa ba tayi ba. A zaune ya sameta kan sallaya da alama lazimi takeyi, jikinsa a sanyaye yake dubanta yana son matarsa shi kad’ai kuma ya san irin son da yake mata, ba don komai ba sai don yarda bata tsallake umarninsa kuma iya iyawarta take kyautata masa ba ta son ‘bacin ransa sam.
Tana ganinsa ta d’an d’auke kai idanunta yana kawo hawaye. A gefenta ya zauna had’e da ri’ko hannunta tayi’ko’karin zamewa ya matse hannun murya a ‘kasa yace”Deejah yau mantawa aka yi da abincinka?” Wani kallo tayi masa kafin hawayen idonta su zubo. Hawayen ya dinga bi da ido “ kukan na menene?” Murya can’kasa tace “ abincinka yana wajen amaryarka” fuska ya sake tamkewa kafin yace “ wace irin magana ce wannan? Kema kin san sarai ba da amincewata aka yi aurennan ba, to me yasa zaki damu kanki yarda ta shigo haka zata koma, bani da tsarin ajiye mata biyu a gidana, ba ra’ayina bane tashi muje ki bani abinci kada ki sake’bata min rai” Ya jata ya mi’kar tsaye suka fita. Hanyar part d’insa direct suka nufa. Dai-Dai lokacin hafsa’yar hajjan ta ganosu itace auta a d’akinsu da sauri taje ta sanar da hajjan. Hajja kuwa tayi saurin fitowa fad’i take muje ba dani za’a yi wannan iskancin ba muje da kaina in kai masa amaryar in kuma nuna masa ni Na haifeshi ba shi ya haifeni ba...


A bakin ‘kofar part d’in nasa ta tsaya tana buga ‘kofar da ‘karfi kamar zata ‘balle ‘kofar. Dahda ransa a ‘bace ya bud’e ‘kofar, murya a sar’ke yace “Hajja lafiya?” Kallon sama da ‘kasa ta jefa masa “ sannu isashshe har kana da bakin tambayata lafiya to ita lafiyar tana gidan ubanka wuce muje ka taho da amaryarka ita ta cancanta ta kwana a d’akinnan sai an mata kwananta uku rus da bazawara ta bata, kuma ban amince da ko bakin’kofar nan naga sillan’kafafunta ba wuce muje ka taho da matarka.” Mommah da take cikin parlourn tana jiyo duk abinda yake wakana ta mi’ke zaune zauciyrta na tafarfasa ta fice daga palrlourn.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login