Showing 93001 words to 96000 words out of 117786 words

Chapter 32 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

481

gaba da kishi a wajenki ba, kowa ya ri’ke mutuncinsa ya kuma tsaya a matsayarsa ubangiji yasa ‘karshen lamarin kenan, ya sake dawwamar da zaman lafiya a tsakaninmu.”

Kawu Sa’idu ya ce “Ka gama magana Alhaji Allah ya sa mu dace sai batun Imrana ina ga tunda komai ya bayyana ai sai ayi ha’kuri a mayar masa da matarsa.”

Da sauri Dahda ya ce “Ayi min afuwa Kawu, tunda dai Imran ya ha’kura ya tafi akan zai auri ‘yar gidan aminina har naje musu da maganar yarinyar ta amince musamman da taga hotonsa, to bai kamata a canja d’in ba a barshi a hakan ubangiji yasa hakan ya zame musu alheri.”

Parlourn ya yi tsit saboda duk ba haka suka so ba musamman Hajja da take ganin duk laifinta ne ta share gumin fuskarta ta ce “Manga kayi ha’kuri a mayarwa da Imrana matarsa.” Dahda ya girgiza kai kafin ya ce “Hajja don Allah a bar maganar kada a mayar da hannun agogo baya, ubangiji yasa hakan shine ya fi musu alheri ba mu san abinda Allah ya ‘boye ba.” Kan dole suka amince da abinda Mangan ya ce. Ita kuwa Hameedah a kanta komai ya ‘kare domin dai Kawu Sa’idu ya ce ba ruwansa ba zai yiwa mijinta magana ba dole ta amince ta zauna da Shuwa a matsayin kishiya, hakan ne ya tashi hankalinta ta shiga wani irin kuka na tashin hankali ‘karshe Mommah ce ta shiga lallashinta, ba kunya kuwa Hameedah ta kwanta lamo a cinyar Dijah tana saurarar nasihar da ta ke mata.




————————————


Duk wasu shagulgula da za’a gudanar a bikin sun tafi yarda ya kamata, amare sun sha bidiri don kuwa abin su a nutse su ke yinsa cikin kwanciyar hankali ba harigidon hauka ba, ba wani abu da suka yishi a cakud’e da maza illa dinner itama ‘bangaren maza daban na mata daban, kuma babu rawa balle ace an had’u an cakud’a maza da mata sai dai muce Allah ya sanya alheri.


Kashegari ne d’aurin aure don haka gaba d’aya gidan bikin a safiyar ranar a cakud’e yake,
Duk inda ka juya mutanene dam’kam, duk da ba a gidan za’a d’aura auren ba a babban masallacin Abuja za’a d’aura.



Amare sun sha ado cikin kayan Alfarma, gaba d’ayansu black lace suka saka da adon golden a jiki, hakan yasa suka yi amfani da mayafi da sar’ka duka golden, zo kaga yarda haskensu da kyansu ya ‘kara fitowa musamman Shatu da idan kakin ganta ba zaka ce itace ta dire Ikram da Akram ba. sai dai sam ba ta da walwala, tun safe ‘kirjinta yake dukan uku-uku ga wata fad’uwar gaba da ta riskarta akai-akai ta tabbatar yau zata zama matar Ammar, da ba ta yi masa ko d’igon so illa son ‘yan uwan taka.



Angwayen na shigowa ta ji an rangad’a gud’a “Masha Allah Nahna amaryar Salees, Hafsa ta angwance da angonta Saleem Dukan da ‘kirjinta ya cigaba lokacin da ta jithe ance “Ayshatu ta angwance da mijinta.......”

Tashin hankalin da naga taa shiga ne yasa wayata ta su’bale ta fad’i.




Saduwar alheri

‘Kirjinta ya cigaba da bugu, lokacin da ta ji ance Ayshatu ta angwance da mijinta Ammar......

Sosai zufa ta shiga keto mata ta ko ina bata ta’ba tsammanin Mommah ba zata janye furucinta ba. Wace irin uwace Mommah da ba zata iya yi musu afuwa ba?

Hawaye tuni ya wanke kwalliyar fuskarta tas, ta mi’ke da mugun gudu ta shige bedroom, dai-dai lokacin kuma angwayen suka danno kai, fuskokinsu tamkar auduga musamman fuskar Ammar da yake ta sakar murmushi na zallar farin ciki, tamkar wanda aka yiwa bushara da Aljannah. Zugar abokansu ce a bayansu duka suna baza babbar riga.


Shatu tana shiga d’aki ta yi wurgi da d’ankwalinta da duk wasu abubuwa da aka yi mata kwalliya dasu.

Sosai ta ke jin tsanar Ammar a zuciyarta, ta kuma ha’kkake a ranta ba zancen zaman lafiya tsakaninta da shi, tunda shi ya nace sai ya aureta idan banda haka ai da ya janye da Mommah da ba ta tilasta mata aurensa ba. Kuka ta ke yi sosai tamkar ranta zai fita.


Dai-dai lokacin da Mommah ta turo ‘kofa ta shigo da niyyar ta sanar da ita ta shirya a yi hotuna, turus tayi ganin da tayi duk ta hargitse jikinta harta d’ankwalinta ta yi wurgi dashi, gashin kanta kuwa ta barbaza shi, kana ganinta zaka yi zaton mahaukaciya ce sabon Kamu. Mommah ta saka salati ta ce “Me zan gani haka ni khadijatu?” Jin Maganar Mommah ya sa ta ji zuciyarta ta sake hassala ta ji a ranta ko kallon Mommahn bata so ta yi, zahiri kamar ma Mommahn ta nunawa duniya ta fi son farin cikin Ammar fiye da nasu.

“Ba kya Jine? Ina yi miki magana kika yi kunnen uwar shegu dani?”

Tana hawayen ta d’ago idanunta a runtse ta ce “Bakomai”

Mommah ta ja tsaki “Allah yasa bakomai d’in ya zama bakoman, idan banda shashashanci duk kud’in da aka ‘batar wajen yi miki kwalliya ya tashi a banza kenan ko hoton ba a yi ba kin shigo d’aki kina risgar kuka kamar wacce aka yiwa auren dole”

Da sauri ta runtse idonta, dama da Mommah abokiyar maganarta ce da direct zata ce “Me ye marabar wannan auren da na dole tunda ni dai ba a nemi amincewata ba da an nemi amincewata da direct zance gidan miji na zan koma, amma anzo an had’ani da wannan da ban ta’ba jin d’igon sonsa ba, wallahi sai yayi regretting aurena don duk wasu munanan halaye na sai na sake renew d’insu.”

Mommah da ta gaji da kallonta ta yi tsaki ta ce “Idan ma auren ne ba kya so kin makaro don gobe jirgin asuba za ku bi zuwa Qatar idan kun koma makarantar ya dawo da ke, sai na ga kuma ya zaki yi shashashar banza ba ki san gata na yi miki ba.” Ta fice tana ta mita kamar ta ari baki.

Shatu ta sake zunduma ihu jin wai gobe zasu wuce Qatar, ihun da ya janyo hankalin jama’ar da suke parlour suka bazamo cikin d’akin da tunanin ko ba lafiya ba? Ciki kuwa har da Ammar da ya kasance sahun gaba.


Turus suka yi ganin ta yi buzubuzu da gashinta ga hawaye a fuskarta sai kuka ta ke tana “Na shiga uku, ni ban ta’ba jin irin wannan ba.” Kowa kuma sai ya yi turus jin maganganun da ta ke saki kamar bata cikin hankalinta.


Ammar ne ya ‘karasa tsakiyar d’akin ransa a ‘bace da maganganun da ta ke furtawa ya d’au mayafinta yana yafa mata zuciyarsa cike da tarin haushinta da tausayinta duk a lokaci d’aya ya ji dama yana da iko da ya furta mata abinda take so. Tsaki ta ja ganin mutanen sun cika mata d’aki ta shige toilet ta datse da key, tana furta munafukan banza duk a cikinku aka rasa wanda zai bawa Mommah shawara sai da komai ya lalace sannan zaku dinga jifana da kallon tausayi.”



Mutane duk suka juya suna mamakin me yasa ta aikata hakan wasu ma har sun fara hasashen ko bata da hankali ko kuma tana da jinnu.




————————————-


A ranar aka sada amare da d’akunansu amaryar Imran kuwa nan gidan aka kawota kafin ya zo ya tafi da ita ko yayi mata visa ta tafi da kanta.


Gidajensu kam sun yi kyau sosai sun kuma yi tsari irin tsarin ‘yan boko, sun sha nasiha da fad’a daga bakin ‘yan uwa da
Abokan arxiki kafin su tafi kowacce a barta da halinta.


Mommah ganin Amaryar Imran a ra’be da kanta ta mi’ke ta ce “Taso muje d’akin Shatu ki zauna tunda ita gobe zata tafi? Na ga zaki fi sakewa a can.”

Yarinya mai kunya idanunta cikin laffaya sai da Mommah ta zame mata shi ta ce “bud’e ‘yata ai nan gidanku ne ba shi da maraba da gidanku da kika baro kada ki sake ki d’aukeshi a ba’kon guri, jibi zamu wuce kano kafin Allah ya dawo da mijinki ya tafi dake.”


Sun dad’e suna knocking kafin Shatu ta bud’e idanunta sun kumbura alamar har a lokacin kuka ta ke, ta zuba wa Mommah ido da ta ji tana yi mata bayanin wai su zauna da amaryar Imran ji ta yi kamar ta sha’keta ta mutu. Juyawa kawai ta yi ta zauna a ‘kasa bayan ta ga amaryar ta zauna a gefen gadon.

Mommah ta dubeta “Shatu haka ake kar’bar baki? Ba zaki bata ruwa ba? To tashi maza ki had’o mata wani abin taci don zata fi sakewa anan.” Shatu ji ta yi kamar ta zunduma ihu gashi ba damar tayiwa Mommah musu jikinta a salu’be ta mi’ke ta fita daga d’akin. Mommah ta bi bayanta da kallo tana mamakin hali irin na Shatu da taga Ta d’au zafi lokaci guda.


A kitchen d’in Mommah fad’a ta dinga yi mata “Haba Shatu ance fa ba’konka annabinka sai na ga kamar abinda kika yi bai dace ba. ko kishi ki ke?” Shatu da sauri ta saki cup d’in hannunta ta na ji da gaske kishin na taso mata wai wannan ce matar Imran? Kuma dole duk wata mu’amalar auratayya dole yayi da ita kamar yarda ya yi mata a lokacin first Night d’insu? Tashin hankali duk iya kallon da ta yi mata bata hango wata makusa a jikinta ba, zama ta iya cewa ta fita kyau a nata ganin fa amma fari gashi ido duk itama ta had’a, tana kuma da diri iya diri.

Mommah tsaki ta ja ta ce fice ki bani waje kafin haushinki yasa Na mangareki, maza ki bari ta gane kishinta kike, shashashar banza.” Har ta kai ‘kofa tana ambaliyar hawaye Mommah ta sake kiranta “Goge min hawayen banzan da ke fuskarki, ki kuma d’auki zuma da tsimin da ba ki sha ba ki shanye min su tas, na kuma zuba su a kayan da na had’a miki zaki tafi dasu saura ki ‘ki sha kiga yarda zan sassa’ba miki idan na zo garin.”

Ta runtse idonta tana shan maganin da take jin kamar ta amayoshi ta rasa me yasa kullum Mommah sai ta rutsa ta sha magungunan ga kaza da kullum da kalar da za’a basu. Ta dai gama shanyewa ta ajiye cup d’in had’e da kinkimar tray d’in Abincin amaryar Imran ta fita dashi.




Da fara’a amaryar ta tarbeta, ta mi’ke da sauri tana amsar tray d’in, ita kuma haka kawai ta ji Shatu ta birgeta, Shatu dai fuska a gintse ta shige toilet duk da tayi sallar isha haka ta sake d’auro wata alwalar ta tada nafilfili yi take tana sakewa saboda kawai ba ta son yiwa amaryar Imran magana.



Har amaryar ta gaji ta bud’e akwatinta ta d’ebi kaya, direct toilet ta shiga don watsa ruwa. Wannan damar Shatu ta samu ta yi saurin saka kayan barci ta kwanta had’e da runtse ido, tana addu’ar Allah yasa barci ya d’auketa kafin Amaryar Imran da taji ana kira da mubeenah ta fito.


Sai dai addu’ar ta ba ta ci, domin kuwa akan idonta ta fito ta zauna gaban dressing mirror tana ‘kalailayar fatarta da alama dai ‘yar gayu ce ta bugawa a jarida.

Gaba d’aya d’akin ya bad’e da wani sihirtaccen ‘kamshin humra mai ratsa jiki, Shatu har lumshe ido ta yi tana tunanin idan Imran ya ga matar nan tasa sai ya godewa Allah musamman shi da ya ke d’an gayu mai son ‘kamshi da ado, ga fatar ta daga ganinta za tayi laushi ta tuna sanda ya dinga yaban fatarta ta runtse ido sosai tana tuno sanda yake rad’a mata a kunne “Kina d’auke Ayshatu da irin fatar da nakeso ko da ita kad’ai zaki mallaki zuciyata.” Hawaye ne kawai taji yana zubo mata da sauri ta ja istgfari tunawa da tayi ita yanzu d’in matar wani ce ya haramta ta dinga tuna tsohon mijinta da duk wata muamula da suka mu’amalanta. Ta tabbata Imran ya yi sa’ar mata ta kowane fanni bayan taga ta d’auko kayan sallahrta ta zura da alama saboda sallahr kad’ai aka yisu, don kuwa kaf jikinta a rufe yake idan ka d’auke fuskarta. Tana idar da sallahr kuwa ta-ji tana rera karatun Alkur’ani. Hakan yasa Shatu ta dinga bi itama a zuciyarta har zuwa sanda barci ya d’auketa.
Ta bar amaryar Imran tana ibadarta.



Da Asuba ko da Mommah ta zo tashinsu sai ta tarar har sun tashi suna ta nafilfilinta farinciki ya cika mata zuciyarta, ta tabbatar yanzu ne ‘ya’yanta suka samu mata na gari ko yanzu burinta ya cika ta san zata samu jikokin da mutane za suyi alfahari dasu Insha Allah.


Suna idarwa Amaryar ta dubi Shatu murmushi fal fuskarta tace “Barkanmu da safiya?” Sai kunya ta kama Shatu da sauri ta ce “Ina kwana Amaryarmu?” Mubeenah ta yi murmushi ta ce “Da alama Shatu baki san sunana ba.” Da sauri ta ce “Na sani mana” ta mi’ke tana shigewa toilet don Mommah ta ce mata ta yi ta shirya jirginsu ‘karfe takwas zai tashi, yakamata su kasance a airport zuwa 6:30.



Jikinta a sanyaye ta ke shafa body mist a jikinta, ba tayi wani kwalliya ba ko powder bata saka ba, ta zira doguwar rigarta ta yane fuskarta da mayafin Rigar.


Dai-dai lokacin da Mommah ta shigo hannunta ri’ke da fresh milk a cups biyu ta mi’ka musu “Kullum wannan ce zata kasance abinda za ku fara sha duk Safiya, madara na da matu’kar mahimmanci a rayuwar d’iya mace ku ri’ke wannan sirrin.” Har ‘kasa amaryar Imran ta saka hannu ta kar’ba Mommah ta mi’kar da ita ta ce “Nagode amma ba sai kin dinga dur’kusa min ba Allah ya yi muku albarka ke kuma Shatu maza ki fito yana jiranki ya ce kwa karya a airport.


Hawaye ne ya fara zubo mata ta fad’a jikin Mommah tana sakin wani irin kuka mai karya zuciyar mai sauraro.
Mommah kanta daurewa ta ke ta ja hannunta suka fice ta na rad’a mata a kunne “Ki yi ha’kuri Shatu ki yi ha’kuri da abinda duk nayi miki kinji ki kuma ri’ke nasihun da duk nake miki insha Allah za kici nasara a rayuwa.”

Har gaban su Hajja da iyayensu maza ta kaita suma suka d’ora tasu nasihar.
Shatu ta dinga dubawa ko zata ga su Ikram amma ina basu tashi ba. hannun Mommah cikinnata ba ta saki ba sai da ta kaita har cikin mota ta yi musu fatan alheri sannan Dahda ya ja motar ya tafi Shatu na d’aga ido tana sake duban danginta hawaye na sake kece mata. Sau biyu suna had’a ido da Ammar ta mudubi yana sakar mata murmushi, madadin ta yi farinciki sai ta ke ganinsa tamkar ba’kin kumurci.


A airport Dahda ya dad’e yana yi musu nasiha kafin ya tafi ya barsu bayan ya sake jaddadawa Shatu “ki bi Allah ki ri’ke Al’kur’ani da sunnah kada ki sake ki jefa kan Ki a halakar bin malamai da bokaye ba inda za su kai ki sai tashar nadama, ubangiji yayiwa rayuwar aurenku albarka a kuma dinga ha’kuri da duk yanayin da bawa zai tsinci kansa a rayuwa.” Kuka sosai take yi tana jaddada godiyar ta Dahda da ya maye mata gurbin mahaifin Shakka babu Dahda ya cancanci yabo a ko ina. Fatanta Allah yasa ta saka masa da halacci.



Takwas dai-dai jirginsu ya d’aga, duk maganar da Ammar yake mata Shatu ko ihim ba ta ce masa ba, har suka yi transit suka sake shiga wani jirgin, ba abinda ta ke sai barcin wahala da ‘kuncin zuciya.



Isarsu ‘kasar ke da wuya suka shiga taxi direct ta kaisu har gidan da za su je da ya ke ba sanin garin tayi ba bata wani tsaya tambayar sa ina za suje ba, ta ga dai sun shiga unguwar da ta kasance tsit ba yawan hayaniya mai motar ya tsaya a dai-dai wani ‘karamin gida flat mai kyawun fuska.



Sun kwashe mintuna suna bugu kafin su ji an bud’e ‘kofar wata zabura Shatu tayi ganin wanda ya bud’e ‘kofar sai da ta murza idonta don son ta tabbatar da ba mafarkin da ta saba yi bane kullum, shi kansa tsaye ya yi yana jifansu da kallon mamaki yayin da Ammar ya ke gefe yana sakar musu murmushi zance ko dariya-dariya, yana bud’e hannunsa yace “Surprised!”





Masoya ya kuka ji wannan page d’in? Ko wa su Shatu suka gani? Waye ya bud’e musu ‘kofar?

“Ya naga kamar baka yi farin cikin ganinmu ba? Cewa nayi bari muzo mu kwashi gaisuwa gurin Babban Yaya kafin mu wuce.” Kicin-kicin Imran yayi yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai yi masa don cin fuska ya aure masa mata sannan ya zo da ita gidansa wai sun zo sa albarka, ya juya tamkar ya datse gidansa sai dai ya fasa.


Jikin Shatu a sanyaye ta bi bayan Ammar tana Mamakin rashin mutuncinsa, idan banda neman magana mai ya aikeshi aikata hakan.


Zama suka yi a parlourn kowa fuskarsa babu annuri idan ka d’auke Ammar da ya ke ta sakin murmushi akai-akai. “Bros doguwar tafiya fa muka sha, ba wani d’an abinda za’a bamu mu sha? Ga amarya na tabbatar yunwa ta ke ji.”


Ji Yayi kamar ya tashi ya rufeshi da duka amma sai ya matse ya ce “Ba’kon da ya sanar da zuwansa shi ake tarba da kayan motsa baki, ba wanda ya fad’o bagatatan ba musamman wanda ba gayyatar sa aka yi ba.” Ammar murmushi ya saki kafin ya ce “Idan kuma amarya na kawo fa? Kasan dai akwai tukuicin siyan baki? Don haka ga Amaryarka nan na kawo maka sai ka bani kud’in siyan baki.”


Daga Imran har Shatu wata iriyar zabura suka yi, suna kallon Ammar da ya ke ta sakar musu murmushi ya ce “Zahirin magana kenan, Ayshatu matarka ce da kai aka d’aura mata aure a karo na biyu ba dani ba. Ina fatan ubangiji ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali mai d’orewa.”

Cikin wani irin shock Imran ya mi’ke ya isa wajensa ji kawai ya yi ya rungumeshi yana fad’in “Ba na son wasa Ammar har waya na yiwa su khalil wajen d’aurin auren suka tabbatar min da kai aka d’aura, kuma na ga iv d’in auren.” Murmushi Ammar ya yi “Ba da taka Ayshatun aka d’aura min aure ba da tawa Ayshatun aka d’aura min aure.”

Shatu cikin tsananin mamaki ta ke dubansa tare da wata irin kunyarsa da nadama akan rashin mutuncin da ta aikata akan ance shi ta aura ashe ba shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login