Showing 48001 words to 51000 words out of 117786 words

Chapter 17 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

466

masa ita.”


——————-
Shaheedah kasa runtsawa tayi cikin daren, kuka kuwa ita kanta ba zata iya irga adadin da tayi shi ba, kukan take ba ‘ka’k’kautawa tana dana sanin bata zuba masa maganin ba. Bayan ya gama buga ‘kofar tana le’kensa ta ga kuma san da ya fito daga bedroon d’insa ya shiga d’akin Shatu. Hankalinta tashe ta shiga buga kanta a jikin wardrobe tana kuka, ga numberr Antynta ta ‘ki shiga. A zuciyarta ta dinga ayyana shikkenan yau Imran ya d’and’ana wata macen duk da dai ta san i gobe aure ya mutu murus. Tunaninta ne ya tsaya cak lokacin da ta tuna iya zallar maganin na zubawa a shayi ta bashi ya sha bata bashi na naman ba. Ta zaro ido da sauri tana mi’kewa bata son a samu matsala, zuciyarta ta shiga harbawa ya akayi ta manta? Bayan mutumin ya ja kunnenta akan kada tayi kuskure yanzu tsoronta d’aya akan mai zai faru? Bata son lamarin ya juye kanta. Da sauri ta sake buga wayar Antynta cikin sa’a a lokacin ta shiga. Hankali tashe ba tare da gaisuwa ba tace “Na shiga uku Anty.” Da sauri Antyn tace “Da aka yi me? Kin kuwa duba time Shaheedah past 3:00am fa.” Cikin kuka ta shiga bata labari. Antyn ta zabga salati “lallai kuwa Shaheedah dole kice kin shiga uku ba ke kad’ai ba ma har ni. Wace irin wauta ce wannan? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna sai fa da na ja kunnenki akan kada ki bada maganin ba tare da mahad’insa ba saboda shiriritarki yasa nace duk sanda zaki bayar ki nemi shawarata saboda in tuna miki yanzu ga shi kinje kin ji’ka mana aiki. Sai ki jira zuwa wayewar gari muga abinda zai faru. Yanzu na san ko na kira Shuwa wayarta ba shiga zata yi ba tana can tana yawon banza.” Kuka Shaheedah ta saka kalmar Na shiga uku kuwa ba ta bar bakinta ba.

Ai kuwa Shaheedah yarda ta ga rana haka ta ga dare gashi taje ta ga Imran bai dawo d’akinsa ba. Ta tabbatar har a lokacin yana tare da Shatu, hakan ya dad’a d’imauta zuciyarta, ta tabbatar da maganin yayi aiki da yanzu wani zancen ake ba da ba wannan ba.

Har Asuba tana jiran wayar Antynta. Sai da aka idar da sallah sannan Antyn ta kira, duk da ita Shaheedahn ko sallahr ta gagara yi. Da azama ta d’aga wayar cikin murmushi Antyn tace “ki kwantar da hankalinki boka yace wa Shuwa bakomai tunda har ya sha na shayin, sakin zai yiwu ‘kiyayyar ce nan gaba zata iya gushewa amma kafin lokacin za’a san abin yi in dai sakin ya yiyu za’a yi musu farra’ku. Yace na tsananin tsanar a cikin naman yake.” Shaheedah da sauri ta saki dariya cikin zakwad’i tace “Har naji dad’i da wallahi hankalina a tashe yake. Ina godiya Anty na samun kamarki sai an tona really proud of you yanzu shegiya yau zata je musu da black news.” Ta she’ke da dariya Allah dai ya bar mana Anty shuwa” Anty tace ameen ai ta cika aminiyar ‘kwarai.”



(Masoya na kuyi ha’kuri da jinkirin da aka samu yau biki muke wallahi shi yasa ma zaku ga typing d’in kad’an ba haka na so ba. Sannan gobe insha Allah ba typing ina da babban uzurin da zai ri’keni zuwa jibi dai insha Allah zaku ga typing mai yawa. Wallahi ina sonku sosai kamar yarda kuke son books d’ina domin da bazarku nake taka rawa💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿)

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-28

Elegant Online Writers.


Cikin daren ya farka yaji kansa yayi nauyi yana wani irin sara masa tamkar zai rabe gida biyu. Zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai ta’ba jin kwatankwacin wannan ciwon kan ba. Idanunsa har dishi-dishi suke ga ni. Da kyar ya mi’ke yana ture Shatu daga jikinsa ‘ko’kari yayi sosai ya kai kansa bakin ‘kofa, zuciyarsa na hassala da bugawa da ‘karfi ya fice daga d’akin, burinsa dama ya fita don sam baya son ganin Shatu da take kwance a gefensa, tsanarta sosai ta d’arsu cikin zuciyarsa, fiye da
Kwanakin baya. Da azama ya isa part d’insa. Turus ya zauna a gefen resting chair da take bedroom d’in nasa Kansa yana cigaba da sara masa. Duk ‘ko’karinsa na son furta addu’a sai dai harshensa ya ‘ki ba shi had’in Kai. Tsawon lokacin da shi kansa ba zai iya ‘kayyadewa ba yana zaune a bakin gadon sai d’aga kai yayi ya ga gari ya fara haske. Da kyar ya mi’ke ya shige toilet. Sai da ya fara sakar kan sa shower ko zaiji sau’kin rad’ad’in da kansa da zuciyarsa ta ke yi, kafin ya d’auro alwala ya fito.
Sallahr ma yayi tane kawai ba tare da nutsuwa ba al’amarin da zai tabbatar maka tabbas da sihiri. Imran mai ‘ko’karin Ibada musamman Azkar na bayan sallahr Asuba, yau shine da mi’kewa da sauri bayan ya idar da sallah. Burin sa kawai ya aiwatar da abinda zuciyarsa take so na sakin Shatu, yana ji tabbas idan ba hakan ya aikata ba zai samu lislama cikin ‘kirjinsa da kwanyar kan sa ba.

Biro kawai ya d’auko da jotter ya kuma rubuta abinda zuciyarsa ke son ya aiwatar. Ya nad’e takardar had’e da mi’kewa. Direct part d’in Shatu ya nufa.


Shatu tun da Imran ya farka itama ta farka sai dai rad’ad’in da take ji a ‘kasanta shi ya hana ta mi’kewa, har zuwa san da ya fice daga bedroom d’innata tana jinsa.
Ba ta jima sosai ba ta mi’ke da
‘Kyar don duk jikinta ya d’au tsami, sai dai ta dake ta shiga toilet d’in a hankali. Yarda ta ga yayi mata da daddaren haka itama ta had’a ruwan ta zauna a ciki. Tsawon
Mintuna sannnan tayi wanka Ta d’aura Alwala ta fito.

Tana zaune saman daddumar da carbi a hannunta kan ta akam gwiwarta. Idanununta a lumshe da alama barci take ji, amma da yake ta saba sai tayi azkar d’in dole haka ta zauna tana son ta ‘karashe ta kwanta, don bata jin ko school zata iya zuwa yau.

Motsin bud’e ‘kofar ne yasa ta d’ago idanunta suka sauka cikin nasa, Gabanta ya fad’i ganin yarda idanunsa suka nuna tsananin ‘bacin rai haka nan fuskarsa babu annuri ko mis’kala zarratin, tamkar dai fuskar mutumin da aka yiwa mutuwa mai tsananin d’aga hankali, mutuwar iyaye d’a ko miji haka fuskarsa ta nuna. Da sauri ta d’auke kai don kuwa ba zata juri kallon da taga yana antaya mata ba, sai ya tuna mata da kallon da yake mata lokutan baya da ya shud’e sai dai wannan har ya fishi muni. Zuciyarta ta shiga sa’ke-sa’ke da son hasasho mata ma’anar kallon tambayoyi barkatai ta shiga yiwa kanta ita da zuciyarta. Laifin mai nayi masa? Ko dai ya taraddani ba budurci? Da sauri ta kawar da wannan tunanin don ba zata mance zafafan kalmomi da yabo da godiya da ya dinga mata da ya sameta a cikakkiyar budurwa da ta kai mutuncinta d’akin miji. Ba wannan bane zuciyarta ta bata amsa. Bai bari ta sar’ke da wani tunanin ba ya mi’ka mata takarda, ba tare da ya jira ta bud’e ba yayi azamar barin d’akin.

Hannunta na rawa ta shiga bud’e takardar, fatan ta taga yabo da godiya kamar yarda take karantawa a littafi sai dai tuni idanunta suka ga sa’banin haka kan kace kwabo hawaye sun ji’kar takardar sharkaf, ta sake ware idanunta akan rubutun da suka koma mata dishi-dishi “Ni Imran na saki mata ta Shatu.....
Daga haka ta yarda takardar ta fara gurshe’ken kuka “Tabbas nayi ganganci Imran da na mallaka maka kaina na manta ma’kiyi baya ta’ba zama masoyi, abinda kake sha’awa a jiki na kenan kuma ka same shi, dole ka sake ni don ka sha fad’a dama abin kunya ne a ganni tare da kai ace matarka ce mai zaka yi dani? Ni Shatu ‘yar ‘kauye Shatu da na taso a daji.” Hawayen ya cigaba da gangaro mata. Tana ji zuciyarta na bugawa na tsananin ‘bacin rai da ‘kuncin zuciya.

Da kyar ta mi’ke ta koma bakin Gado ta zauna, tana sake saka maza a layin mutane marasa tabbas dubi dai kalaman da ya dinga gaya mata jiya dubi sakayyar kuma da yayi mata yau, sakin aure a ranar da ta kwana uku da tarewa a gidan miji ya mayar da ita ‘karamar bazawara a shekarunta da ko shekaru sha shidda bata rufa ba. Wallahi ya cuce ta kuma ba zata ta’ba yafe masa ba har gaban abada ta kuma tsane shi tsana mafi muni, da bata ta’ba yiwa wani mahaluki ba.



Shi kuwa yana komawa d’akin sa ya ji duk wani ‘bacin rai da ‘kuncin zuciya sun kau daga ransa ya lumshe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya. Shi dama ya san ba zai ta’ba son Shatu bada jiyan ma bai san me yasa har yaje ya kusanceta ba yana kuma dana sani da ba’kin cikin aikata hakan, ya tabbatar yanzu raini zai shiga tsakaninsu ba zai kuma bar ‘kofar rainin ba. Don ko dariya ba zai yi mata ba balle ta raina shi. Mommah da ya tuna shine gaban sa ya fad’i ya sani sarai a wannan ga’bar ba zata yi masa sassauci ba, yayi zugum yana tunani zuwa lokacin da wayarsa taand hauand ringing.
Da sauri ya d’auka ganin mai nemarwa Shaheedah visar zama a turkey ne, nan yake sanar masa visa ta kammala kuma ko gobe suke so zasu iya tafiya akwai jirgi da zai tashi daga Abuja. Cikin farin ciki da son gujewa fad’an Mommah Imran yace yayi masa booking. Da sauri ya mi’ke ya shiga shirya kayansa, yau zasu wuce Abuja idan yaso gobe jirginsu ya d’aga zuwa turkey shikkenan ba shi ba fad’an Mommah.


Ita kuwa Shaheedah tana can zaune jiran tsammani tun asuba take saka ran ganin Imran sai dai bai shigo ba, hankalinta a tashe yake bata da tabbacin maganin yayi aiki ko baiyi ba. Duk da dai bata haufi game da shu’umancin Shuwa. Ko sleeping dress bata cire ba balle aje ga babin wanka, idanunnnan yayi ‘kozai-‘kozai tunda ranar ba makeup gashi na kwana ana kuka. Tana cikin wannan yanayin Imran ya shigo. Gabanta ya fad’i ganin fuskarsa a had’e ba dai abu bai tafi yarda suke so suke fata ba. Ba kamar yarda hasashenta yake ba shi Imran haushinta yake ji tunaninsa duk ita taja masa yaje ya saukewa ‘karamar yarinya bu’katarsa ta jawo masa raini, da bata kulle ‘kofa ba ai da duk hakan bata faru ba. Fuskar nan a had’e yake dubanta, ya ja tsaki ganin duk tayi Jeme-jeme da ita zai iya cewa tunda yake bai ta’ba ganinta ba makeup ba, don haka yau yaga fuskarta ta kamar an tsamo kaza a
Salu’be daga ruwan zafi. “Ki tattara duk wani komatsanki.....” da sauri ya kalleta ba tare da ya ‘karasa ba ganin ta d’ora hannu a ka tana shirin runtuma ihu ido a waje take cewa “Don Allah kayi ha’kuri.” Tsaki ya ja “meye haka? Ai ba kiga hukuncin da zan miki ba sai nan gaba kad’an wallahi don na lura kin raina ni sosai. Kiyi sauri malama kada mu rasa jirgin tafiya Abuja gobe zamu wuce turkey sai kiyi waya ki sallama da duk wanda ya dace nan da 30mint jirgin Abuja zai tashi.” Daga haka ya juya ya fice Shaheedah ta saki wata wawuyar ajiyar zuciya, idanu a lumshe take fad’in Alhamdulillah wallahi har na tsorata. Na zata saki na zai yi. Sai kuma ta fara taka rawa jin turkey zasu wuce. Murnar ta ta tsaya cak tana tunanin ina labarin sakin Shatu? Ko har ya sake tan bata sani ba? Ture zancen tayi a gefe ta tashi da azama tana tattara kayan da zata tafi dasu. Tana yi tana danna kiran Antyn ta, sai dai bata d’aga ba da alama tana can tana hidimar Dahda.


Shatu ta dad’e a zaune ta rasa abin yi ita ba waya ba balle ta kira Mommah. Gaba d’aya jin ta take kamar mara lafiya, da kuma zata iya dama da fita zata yi tada shiga motar haya to sam ba zata iya tafiya ba. A hakan dai ta lalla’ba ta tattare iya abinda zata iya zuciyarta na tururi, ta fara tunanin ashe haka mata suke ji idan aka ce an sake su. Tabbas abin da ciwo ba kad’an ba wallahi ta tausaya musu ta kuma tausayawa kan ta.
Tana ganin takwas tayi ta shige toilet don tayi alwalar sallahr walaha kamar yarda Mommah ta koyar da ita.


Dai-dai lokacin shi kuma Imran ya fito daga part d’insa d’auke da trolley d’insa guda biyu. Cikin shigarsa ta kullum ta yard d’inkin African Attire. Da sauri ya isa sashen Shaheedah ta gama shirinta tsaf sai zanga ‘kamshi take, tayi kyau kuma sosai kamar ba ita ya tarar wata iri d’azun ba. Murmushi ta sakar masa tana bashi side hug “Haba my Habibi afuwa mana kada mu shiga flight kana had’e min rai a zata auren dole aka yi mana.” Bai yi mata magana ba yaja trolley d’inta d’aya ya fice. Don haka dole ta bi bayansa da sauri tana kulle part d’inta. Har ya wuce part d’in Shatu sai ya jiyo ya kalli ‘kofar sai kuma ya saki tsaki, ya juya da sauri, yaa jin tsanarta na sake shiga zuciyarsa.


Sun shiga mota kenan ya gaya kiran Mommah ya sake shigowa wayarsa a karo na biyar, gaban sa ya sake fad’uwa duk da ya tabbatar har zuwa lokacin bata san da sakin ba, don ya san Shatun ba ta da waya. Hakan yasa dole ya d’aga kiran, murya ‘kasa yada gaisheta “Sannu isashshe kaga damar d’aga wayar kenan? Allah yasa dai ka kai min yarinya makaranta.” Da sauri yace “ Bata je ba.” Mommah cikin zafin rai tace “Saboda me?” Imran ya d’an ‘bata fuska kafin yace “Ba ta da lafiya ni kuma tafiya ta kama ni, dama ina shirin bugowa na sanar miki mun wuce da Shaheedah ita kuma a tura driver ya d’aukota kiyi ha’kuri Mommah.” Ya fad’a murya a sanyaye had’e da sauri switching wayar off, yaja motar da sauri. Da motar zai wuce airport sai ya yiwa Ammar waya yazo ya d’auki motar.

Mommah sakar baki tayi tana kallon wayar cikin tsananin takaicin Imran d’in Shatu bata da lafiya shi kuma shi da matar sa ta Gold tafiya ta kama su, bai kuma yi hankalin yada kawo min Shatu gida
ba saboda bai damu da ita ba cabd’i ai kuwa ido na idon Imran wallahi sai ya gane kuren sa.” (Allah sarki Mommah baki san ma mai gaba d’ayan Imran yayi ba.)


Ran ta a ‘bace ta ‘kwalawa Nahna kira, su suna nan basu tafi ba sai wani satin. Da sauri Nahna ta shiga. Key kawai Mommah ta mi’ka mata “kije gidan Imran ki taho da Shatu bata da lafiya.” Ganin ranta a ‘bace yasa Nahna bata ce komai ba taand kar’ba ta wuce.



Tana isa mai gadi yawas bud’e mata, ta ci sa’a ‘kofar main entrance d’in gidan ba a rufe take ba da Shatu ba zata ji bugun ba. A ‘kuryar d’aki tais sameta tana karatun suratul mulk da alamar sallahr walaha ta idar. Don sun mayar da ita kamar compulsory in dai kai jinin Hajiya Mama ne. Shatu ta sakar mata murmushin da zamu iya kiransa na ya’ke kafin tace sannu da zuwa Anty Nahna, idanunta na zubar da hawaye duk da ‘ko’karin ‘boyesu da take. Nahna cikin tausayinta ta zauna a gefenta tana dafa ta “wani ciwo nea yasa idanunki suka yi haka Shatu kin gasan idon ki kuwa?” Shatu ta lumshe idanunta tana jin azabar suyar da zuciyarta take kafin tace.....

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-29


Elegant Online Writers.....
“Wani ciwo ne yasa idanunki suka yi haka Shatu? Kin ga kuwa idanunki?” Nahna ta sake maimaita mata tambayar a karo na biyu, ganin Shatun ta runtse idanunta tana kwararar hawaye Ta ‘ki magana. Hankalin Nahna a tashe ta dafa ta “kiyi magana nace mai ya same ki?” “Wani abu yayi miki?” Girgiza kai tayi ta mi’ke, gaban dressing mirror taje ta d’auko ba’kar takardar sakin ta mi’ka mata, sannan ta sake zubewa a gabanta tana kuka.
Hankalin Nahna ne yayi bala’in tashi, a wani irin yanayi na fad’uwar gaba ta bud’e takardar, idanunta suka hasasho mata abinda zuciyarta take hange, ta san tabbas ba zai wuce hakan ba. “Na saki Mata ta Shatu saki d’aya.” Rintse takardar tayi a hannunta, ita kanta zuciyarta suya take hawaye na zuba a kwarmin idon ta. Tabbas Imran bai kyauta ba, ya bar musu abin fad’a a cikin dangi bata san kuma ya mutane za su kalli abin ba. Tausayin Mommah ya kama ta,mace mai son zumunci Allah ya bata d’a da ya taso da soyayyarta da son zumunci,sai dai gaba d’aya rashin tsoron Allah yasa an birkita mata shi. Kamar ba Imran d’in ta Na da ba,da ba ta saka kara ya tsallake. Ganin kukan da Shatu take, hakan yasa tayi saurin share hawayenta ta rungumeta “Kiyi ha’kuri Shatu Na san mutuwar aure da ciwo amma ina son ki d’auki hakan a matsayin ‘kaddara, haka dama Allah ya tsara I ya ‘kayyadaddun kwanakin da za kiyi da auren Imran kenan, wani mahalu’ki bai isa ya juya hakan ba, hakan kuma ba yana nufin gushewar farin cikinkiba
insha Allah soon Allah zai kawo miki madadinsa ai ba shine autan maza ba. yanzu ki tashi mu tafi kuma don Allah bana son ki nunawa Mommah damuwa balle ki ‘kara sanya ta a wani yanayi, ki daure ki ‘karfafa mata gwiwa. Ko kina son wani ciwon ya kama ta?” Da sauri Shatu ta girgiza kai “Yauwa to ki nuna mata bakomai bana son ganin hawayennan a fuskarki.” Da sauri ta goge ta mi’ke ta bi bayan Nahna da sauri, tana jin abinda ya cunkushe mata a ‘kirji yana raguwa kad’an-kad’an.

Har suka shiga Mota Nahna bata sake cewa komai ba, da alama bata ta’ba shiga ‘bacin rai kamar irin na yanzu ba.
Shatu ta juya ta yiwa gidan kallon ‘karshe a matsayinta na matar aure a gidan,tuni zuciyarta ta sake karyewa ko bakomai wallahi ta tabbatarwa zuciyarta tana son Imran, amma ko son sa zai yi ajalinta a yanzu kam ta cire

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login