Showing 60001 words to 63000 words out of 117786 words
tafi. Don ita zainab sune ‘kirjin biki tuni na ta tafi.
Dahda yana da gida a maiduguri don haka a can suka sauka, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta tafi gidan Hajjan. Mota cike da kayan gudumawa.
Gidan dan’kam da jama’a ta samu. Babu mai yi mata kallon arziki kowa wani irin duba yake mata, ‘kalilan ne masu murmushin da bai kai ciki ba. Gefe ta samu ta zauna ita da Basirah mai aikinta kasancewar Hajjan na cikin bedroom d’inta, kuma bata bata fuskar shigar mata d’aki ba. Tsawon lokaci tana zaune Hajja bata fito ba, jama’ar wajen kuwa ba wanda yake ta tata, hakan yasa ta zauna tana dannan wayarta.
Tafi Awa d’aya da zuwa kafin Hajja ta fito daga d’akin ‘yan koranta na bayanta alamar an san da zuwanta, don duk fuska ba walwala suka fito. Mommah na ganinta ta dur’kusa har ‘kasa ta gaisheta, tamkar ba zata amsa sai kuma ta amsa cikin ginshira.
Basirah ta jawo babbar ghana must go ta kayan da suka kawo ta dire a gaban Hajjan, daga haka ta fice daga parlourn ranta a ‘bace da kallon rainin da ake yiwa uwar d’akinta, matar da take mata kallon mahaifiya don kuwa Mommah tayi musu ri’ko na fisabilillah da ko a gidajen iyayensu ba zasu samu irn kular da take ba su ba.
She’ke’ke Hajja ta dubi kayan, ba Ta kuma ko bud’e ba tace “An Gode.” “Hajja ai ba ita zaki godewa ba Ya manga za’a godewa don na tabbatar shi ya bada kud’in.” Mommah ta zuba mata hameedah da tayi maganar ido saboda yarda ranta ya ‘baci don kosun ficikar Dahda babu a cikin kayannan, amma da yake ba sa sonta balle ace tayi alheri dole suce Haka, wannan ta guda tace ba zata zo bikin ba gashinan tunda ga yanzu ta fara riskar takaici. Hajja ta gyara zama “Alhamdulillah dama ina ta son ganinki, ya kika ji da ‘bacin ran sakamakonki tun yanzu kuma ashe kin fara girbar abinda kika shuka, Imran kuma ya saki ‘yar taki, ko bakomai ya nuna miki baki isa ba, ina isar taki da kike tin’kaho da ita? Ai dama Na san ko mu dad’e ko mu jima sai tarihi ya maimaita kansa, yarda kika hana d’ana yi min biyayya kema sai kin riski sakamakonki gashi nan kuwa dahir kin gani. Kwana uku da aure ya sako miki ita.” Gaba d’aya gurin suka saka dariya Idanun Mommah suka kawo ‘kwalla, har zata tanka musu sai kuma taa tuna umarnin Hajiya Mama, don haka dole tayi shiru tana jan addu’oi a zuciyarta, ko bakomai Imran ne ya jawo mata, mi’kewa kawai tayi ta fice daga gidan don bata son zubar da hawaye a gabansu. Hannun Basirah ta ja suka bar gidan tana sake jiyo sanda Hameedah tace “Aikin banza gayyar tsiya kawai ta bi ta mallake mana d’an uwa.”
Ko da ta shiga motarr driving d’in kawai take ba cikin nutsuwa ba, yarda zuciyarta take tafarfasa tamkar ta fasa ‘kirjinta ta fito hakan yasa ta samu gefen titi tayi parking hannunta dafe da ‘kirjinta ta shiga kiran layin Dahda don ba zata iya cigaba da driving d’in ba, da kyar ta sameshi ta gaya masa halin da take ciki. Basirah kuwa hankali tashe take tofa mata duk addu’ar da tazo bakin Ta.
Cikin mintuna ‘kalilan Dahda ya bayyana a wajen cikin tashin hankali ya d’aukota cak daga cikin motar numfashinta yana fisga da ‘karfi, da sauri ya sata a seat d’in baya kanta saman cinyar Basirah yaja motar da wani irin mahaukacin speed. Suna isa asibitin dama tuni yayi waya don haka suka tarar da wheel bed aka yi saurin d’orata akai aka turata a guje don numfashinnata gaba d’aya yana shirin d’aukewa.
—————
Wani irin mugun mafarki da Shatu tayi sakamakon kwanciyar da tayi barcin rana shi ya farkar da ita a razane, cikin firgita take kiran “please Mommah kada ki mutu bana son na rasa uwa a karo na
Biyu.” Da sauri Hajiya Mama ta kamata don itama tun safe gabanta yake fad’uwa ba wai tana jin dad’in jikinta bane. Idan kuwa ta shiga irin wannan yanayin zahiran mutuwa ce babu tantama. “Kiyi addu’a ba’a son tashin hankalin mai ciki.” Hajiya Mama ta fad’a cikin ‘karfin hali da dauriya. Da sauri Shatu ta rungumeta “Hajiya Mama don Allah ki kaini wajen Mommah. Mafarki nayi ta mutu.” Wani irin tashin hankali ya riski Hajiya Mama don bata san sanda ta dafe ‘kirjinta da yake bugawa ba ta kama Shatu ta rungume kawai ba tare da tayi magana ba, ‘kirjinta yana bugu fat-fat.
———————
Dai-dai wannan lokacin shi kuma Imran suna gaban Doctor shi da Shaheedah. Bayan rattabawa Doctor bu’katar su ta zubda ciki da kuma son tsarin iyali Doctor ya tabbatar musu ba wata matsala. Har ya sake ‘karfafa musu gwiwa abinda ya dace kenan it’s too early ace sunyi aure ko shekara ba ayi ba su haihu, zai zubar mata da cikin tunda bai wuce 3months ba tablet kawai zai bata, cikin zai fice. Maganin tsarin iyali kuwa zai d’orata akan methoe d’in da zaiyi dai-dai da tsarin jikinta, har zuwa sanda zasu bu’kaci haihuwar, idan ma bata son d’aukar ciki da haihuwa zasu iya yi mata dashen kwalba ko a samu wata macen a dasa mata cikin ta haihu ta yarda halittarta ba zata canja ba, tunda bata so. Hakan yayiwa Shaheedah sosai ta kuma raya a ranta idan time d’in yayi abinda zata yi kenan.
———————-
Doctors sosai suke ‘ko’karin ceto ran Mommah, duk da hankalinsu suma a tashe yake don har zuwa lokacin numfahsinta gaba d’aya ya d’auke sunyi-sunyi ya’ki ya dawo.
Dahda hankalinsa a tashe yake zirga-zirga yake kawai bakin emergency d’in zuwa lokacin da
Yaga fitowar Doctor d’in daga d’akin. Yanayin yarda yaga fuskar Doctor d’in yasa zuciyarsa matu’kar bugawa da ‘karfi.....
ME ZANYI DA ITA?
34
Dahda yayi saurin dafe ‘kirjinsa yana ambaton addu’oin da duk suka zo bakinsa, a zahirin gaskiya shi kansa bai san abinda bakinsa yake furtawa ba.
Har zuwa sanda likitan ya iso wajensa. Ya dubeshi kafin yace sai dai kuyi ha’kuri mun yi ‘ko’karin ganin ta dawo hayyacinta, sai dai still she is unconscious, amma dai muna saka rai za’a samu nasara insha Allah. Dahda ya saki wata wawuyar ajiyar zuciya, ji yake a rayuwarsa bai ta’ba samun kyakykyawan labarin da ya zarce wannan ba. Alhamdulillah ya furta a hankali har yana sakin d’an guntun murmushi yace “Doctor Allah ya baku nasara, ni kuma nayi al’kawarin yi muku kwaskwarimar asibitin nan cikinsa da bai. Amma Doctor kana ganin meye musabbabin ciwon nan?” Doctor yace “Gaskiya ba zan ‘boye maka ba,musabbabinsa ‘bacin raine mai tsananin gaske da ya cunkushe zuciyarta ya hanata functioning yarda ya kamata.” Dahda yace “Na san za’a rina, Dijah da na sani ban amince da zuwanki bikinnan ba, amma wallahi sunyi na farko sunyi na ‘karshe yau zan nuna musu bad side d’ina da za suyi mamaki, in dai na tabbatar su d’inne silar ciwon Dijah.” Duka wannan zancen Dahda a zuciyarsa yake yinsa, sam bai san ma Doctor d’in tuni ya wuce da sauri ba ya koma ‘dakin da Mommah take dama abu yazo ‘dauka.
Basirah ya kalla ransa a ‘bace ya shiga rattabo mata tambayoyi, tamkar dai ‘dan jarida.
Basirah kuwa bata ‘boye masa ba, ta bashi labarin zahirin abinda ta sani. Dahda ransa ya shiga ‘kunci da tunanin anya Hajja tana sonsa kuwa? Tabbas da tana sonsa, da ta so farin cikinsa Dijah, su ba su san Dijah zai iya fad’a kansa tsaye itace rayuwarsa ba. Uwa-Uwa ce dole ya ‘daga mata ‘kafa, amma Hameedah kam tabbas yau zata san waye shi, zai je mata a zahirinsa na Ahmad ba Mangan Hajja da suka sani ba.
———————
Hajiya Mama hankalinta a tashe, ta shiga kiran wayar Manga, bayan ta gwada ta Mommah sau shurin masa’ki ana sanar mata is switch off. Bugu biyu ta ci nasarar Mangan ya ‘dau wayar. Bayan gasiheta cikin girmamawa, ta tambayeshi isarsu lafiya sannan ta d’ora da tambayar Dijah. “Na kira Addar tasu ya fi sau nawa bana samunta, Allah dai yasa lafiya?” Manga ya saki ajiyar zuciya Uwa kenan, ita ce mafi kusanci da zuciyar ‘ya’yanta, gashi dai har taji a jikinta Dijan ba lallai ta zama tana lafiya ba. “Bakomai Hajiya Mama, sai dai tana bu’katar addu’a don tana kwance anyi admitting d’inta a hospital, amma dai Alhamdulillah cikin hukuncin ubangiji da sauki.” Maimakon ta shiga ru’dani kamar yarda Manga ya yi hasashe sai yaji tace “Ubangiji Allah ya bata lafiya, yasa kaffara ne, zuwa gobe idan yanayin jikinnata ba afuwa insha Allah zan biyo flight, a kuma cigaba da addu’a ba’a ja da hukuncin ubangiji, cuta da mutuwa duka lamarin ubangiji ne, shi ya saukar da cuta ya kuma samar da maganinta.” Manga ya saki ajiyar zuciya yana gasgata ‘karfin Imani na surikar tasa a zuciyarsa, shi yake ganin girmanta a ko da yaushe. A hankali yace “Nagode Hajiya Mama, idan ta farka zan ha’daku a wayar.” “Allah ya farkar da ita lafiya yasa muji alheri. Allah yayi muku albarka gaba ‘daya.” “Ameen” Manga ya furta. Yana disconnecting wayar.
Sai da ta kashe wayar sannan ta dubi Shatu da duk nutsuwarta ta tattara ta akan Hajiya Maman tana jiran ‘karin bayani. “Ki kwantar da hankalinki, Mommah ba mutuwa tayi ba, tana dai kwance bata da lafiya, mafarkinki kuma insha Allah ba zai zama gaskiya ba.” Shatu hawayene ya sake zubo mata gaba ‘daya hankalinta yafi ‘dazu tashi tunda taji Mommah ba lafiya hankalinta ba zai ta’ba kwanciya ba har sai Mommah ta samu lafiya.
Hajiya Mama cikin zafi ta katseta “Bana son sakarci kin ji ko? Menene abin kuka wa yace miki a yanzu kukanki take bu’kata? Idan kika cigaba da yi min kuka tafiyata zanyi wajenta Na barki, dama dalilinki zan zauna ban tafi ba sai Na ji yarda ta kaya gobe tukunna.
Kuma ki tashi ki je ki nemi abinci ki ci, kafin kisa mu wani tashin hakalin, ayi haihuwar guzuma ‘ya kwance uwa kwance.”
——————————-
Tablet ‘din abortion ‘din da ta sha, bai tashi yi mata aiki ba sai cikin dare. A mugun razane ta farka hannunta dam’ke da mararta da take jin tamkar zata dare. Cikin tashin hankali ta fara dukansa tana kiran sunansa. Shima a ‘dimauce
ya farka yana duban yarda take mur’kususu. “Imran help please!” Ta fad’a da ‘karaji, yayi saurin mi’kewa yana tayar da ita, ganin shegiyar rigar barcin da take jikinta ya sashi sauri zaunar da ita, ta mi’ke da sauri don ta ma kasa zaman, shi kuwa ‘ko’kari yake ya suturce mata jikinta, ganin duk ta ru’de ya sa shi zira mata hijabi kawai ya sunkuceta cak a guje suka fita compound ‘din gidan.
An sha gwagwarmaya sosai a asibitin kafin cikin ya fita, sannan aka yi mata wankin ciki aka bata hospital Gown tasa, don rigarta tayi kaca-kaca da jini.
Tana kwance akan gadon ya shiga ‘dakin, idanunsa akanta, yana mamakin yarda ta zabge lokaci ‘daya, sai ga shi yau dai yaga zallar muninta, don bai ta’ba ganinta ba makeup ba sai sau ‘daya shima bata kai haka lalalcewa ba.” Ya zauna a gefenta, yana kallon asalin gashinta, ashe wanda da yake gani duk gashin doki ne, sai yau yaga nata na ainahi wanda ba zai fi nasa da kad’an ba. Ya dai ta’be baki yana zama a gefe yace “Ya jikin?” Cikin kunyar kanta da yanayin da ya sameta yanzun na bayyanar ainahin halittarta ta shiga kau da kai. “Mu tafi gida Habibi wallahi ina son hutawa.” Ya girgiza kai “sun ce ba yau ba, ba ma wannan ba za suyi miki planning d’in da kike so sunce a tambayeki za’bin wanda kike so.” Zura masa ido tayi kafin a zuciyarta tace “Ina? Ai wallahi gida zan tafi ba zan zauna ka dinga ‘kare min kallo ba a haka har sai ka hango muni na.” Murya a sar’ke tace “planning daga baya ai sai muzo ayi ni nafi son su saka min inplan.” Ya ta’be bakinsa. Ta lura sosai da wani irin kallo da yake jifanta dashi, abinda yake dake ‘daga mata hankali.
——————————————-
Cikin Iko da izzar khali’ku, Mommah ta farka, idanunta akan dandazon likitocin da suke tsaye a kanta su kusan goma. Tana ganin sanda suka fara fa’din Alhamdulillah, suna mamakin yarda suka samu nasara haka, don da har sun cire rai. Ni kuwa nace Allah ai maji ro’kon bawa ne Hajiya Mama da Shatu da duk wani da yake da kyakkyawar ala’ka da Mommah ranar baiyi barci ba, addu’a suka kwana suna yiwa Mommah da fatan samun lafiya. Tabbas naga tasirin addua da girman ubangiji.
Bayan an gama kimtsata, sannan suka tura ta zuwa ‘dakin da zata huta. Sai lokacin Manga da Basirah suka san ta farka. Da sauri Manga ya ‘karasa wajen idanunsa cikin na Mommah da take sakar masa kyakkyawan murmushi, wanda kana ganinsa ka san na tsagwaron ‘karfin hali ne. Kawai likitoci da malaman jinya sai gani su kayi Manga ya dur’kushe ya kai goshinsa ‘kasa yayi sujjada. Gaba ‘daya wurin sun gasgata da girman soyayyar Manga da Matarsa. Dariya kawai ake masa, musamman ganin yarda yake hawaye hannayensa a sama ya mi’ka godiyarsa ga Jalla wa Azza.
A Amenity aka ajiyeta, hannayenta cikin na mijinta, nurses suka zo zasu ‘da gata, da sauri ya tsayar dasu da kansa ya zaunar da ita ya jinginar da ita a jikinsa, yana shafa bayanta. Ita kuwa tayi lamo a jikinsa cikin shau’ki da tsananin son Mijinta. Suna fita Basirah itama Ta bisu bayan ya mi’ka mata key d’in gidansa na maiduguri “Kije ki yiyo break-fast, sannan ki ha’do mata kayan da zata bu’kata.” A kunyace ta amshi key ‘din ganin yarda ya rungume Mommah da tsam tamkar wani zai ‘kwace masa ita. Suna fita ya ra’da mata a kunnenta “I love you Dija na, tabbas da wani abu ya sameki, ban san ya rayuwata zata kasance ba, dole nayi azimi uku na godiya ga rabbil izzah.” Murmushi tayi tana wasa da fingers ‘dinsa, shi kuma ya ciro waya yana kiran layin Hajiya Mama. Bugu ‘daya ta ‘dauka alamar dama a ‘kage take ya kira ta. Ba tare da yayi magana ba ya kangawa Mommah wayar a kunne, cikin kasalalliyar muryar ta tace “Assalamu Alaikum.” Hajiya Mama bata san sanda murmushi ya su’buce mata ba tace “Alhamdulillah ala ni’imatihi tatummussalihati Addarsu ya jikinnaki?” Mommah tayi murmushi cikin kasalalliyar murya tace “Alhamdulillah, wallahi naji sau’ki Mama, ina Shatu?” Hajiya Mama ta mi’kawa Shatu wayar da take jin tamkar ta fisge. Tana sawa a kunne cikin dariya tace “Mommah kin warke?” Dariya tayi tace “Insha Allah Shatu, Allah yasa dai baki saka damuwa a ranki ba kin san...” sai kuma tayi saurin katse maganar ganin idanun Dahda a kanta. Ta ‘karasa da “komai na Allah ne.” Shatu tace “To Mommah na har naji da’di Allah ya baki lafiya idan Hajiya Mama zasu taho anjima zan biyosu.” Da sauri Mommah tace “A’a kada ma ki fara, kin manta abinda nace miki?” Kamar tayi kuka taji Mommah tace “Mi’kawa Hajiya Mama wayar, tana bata Shatu ta fice tana hawaye ita haka kawai dalilin wani ciki a hanata ganin Mommah, cikin jin haushi ta kaiwa cikin duka “ladan janyowa da kai ka hanani ganin uwata, da ‘katon kanka kamar na Babanka.” Sai kuma ta ri’ke baki Oh kuji shashanci na ko a ina naga kanna sa?” Ta saki murmushi kawai tana shigewa kitchen jin zaburar da cikin yayi “Acici na san yunwa yake ji, ko kuma don na masa ‘dan wannan dukan ne, yaro baka sha duka ba sai kazo duniya tukun in rama duk abinda ubanka yayi min a kanka.”
————
Tana gani su Hajiya Mama suka tafi, ita kuma aka barta da Iya shugabar ma’aikatan cikin gidan, Haushi ne ya kama Shatu ta le’ka ta windown motar tace “kuma wallahi Hajiya Mama kafin ki dawo sai na shanye duka kayan za’kin gidannan ba dai kin hanani ba.” Hajiya Mama ta ware ido kafin tace “Au ta’bargazar da zakiyi kenan! To na san maganinki muje cikin gidan.” Shatu ya wuce tana tura ciki, da har mamaki girman cikin yake bawa Hajiya Mama kamar ba cikin fari ba, yayi girma sosai ga Shatun ta sake bud’ewa. Hajiya Mama tace “Allah ya raba lafiya.” Sai da ta kwashe kaf kayan za’kin gidan tas, ta kuma kira masu aiki ta basu dokar kada wanda yaba Shatu kayan za’ki, sannan ta tafi. Alhaji Babba Babnsu Mommahn da zasu tafi tare sai dariya yake mata ita da Shatun da take ta sake tunzira Hajiya Maman. Kuka ta zauna ta dinga yi a parlourn kamar yarinya sai watsi take da throw pillow d’in parlourn. Masu aiki sai dariya suke mata suna fad’in SHATU DANGER kamar yarda suka ji Hisham yana gaya mata.
Isar su Airport ‘din ke da wuya suka tari taxi suka nufi asibitn bayan sun gayawa drivern sunan Hospital ‘din.
Dahda ne ya fito harabar Hospital ‘din bayan sun sanar da isowarsu ta cikin waya.
Sun tarar jikin nata da sau’ki, sai dai har yanzu numfashinta bai koma normal ba, tana yi tana hutawa. Hajiya Mama da Alhaji Baba sun tausayawa ‘diyar tasu sosai, musamman ganin duk juriyarta an wayi gari zuciyarta ta kasa, dama duk cikin ‘ya’yansu ta fi kowa ha’kuri. Alhaji Baba ya dubi Manga bayan sun fita yace “ina son ganin Doctors d’in nata domin naji ainahin abinda yake damunta, idan kuma ba matsala zan fitar da ita waje ko egypt haka ko Germany.” Dahda ya girgiza kai “ Bakomai Alhaji Baba amma kamar hakan nauyi nane kuma ko baka fa’da ba nayi niyyar aikata hakan. Sannan matsalar dangina ce musabbabin wannan ciwo nata ba zan ‘boye maka ba.” Nan ya shiga bawa Alhaji Baba labari.
Kafin a gama bashi labarin gaba ‘daya ransa ya ‘baci cikin wani yanayi yace “Ashe har yanzu jahilcin nan ba zai kau daga zuciyar malam bahaushe ba, me ye laifin yarinyar da ta auri ‘danki ko ‘dan uwanki? Sannan kuma mai yake jawo wannan muguwar tsanar da gaba ta dangin miji? Da suke tsangwamar mutum bai ji ba bai gani ba a nawa tunanin jahilci ne da hassada, da kuma jayayya da lamarin ubangiji, haka ne mana kina ganin Allah bai iya ba da ya bawa ‘danki mata wance, ko kuma bai iya