Showing 90001 words to 93000 words out of 117786 words
Zan yi da ita?
48
Jikinsa a salu’be ya tura ‘kofar bedroom d’in Mommahn, ya ci sa’a kuwa ya sameta tana zaune ita da Shatu, da ta damawa wani abu a
Cup da alama turketa ta yi sai ta sha, duba da yarda Shatun ta ke ‘bata fuska.
Zuciyarsu gaba d’aya ta buga, musamman Shatu da ta kwana biyu ba ta ganshi, ya yi rama sosai abinda ya tayar mata da hankali kenan har ta ji ‘kwalla na son zubo mata.
Lura da haka da Mommah ta yi yasa ta ja tsaki ta ce “Oya tashi ki kai cup d’in kitchen ki je kuma ki yi Wanka.
Imran ya bita da kallon da yake ayyana shine na ‘karshe, in dai da nufin kallon soyayya ne Insha Allah.
Ganin Mommah ta zuba masa ido ya sa ya zube a gabata “Ina wuni?” Ya furta murya na rawa ji ya ke kamar ya kece da kuka, amma ya yi al’kawari ba zai yi kukannan ba.
“Mun wuni lafiya?”
Yaji amsarta daga sama, murumushin takaici ya saki ganin yarda ta ke amsa shi kamar ba mahaifiyarsa ba, Mommahnsa mai son sa ita ta rikid’e ta koma haka?
“Kiyi ha’kuri da duk abubuwan da na yi miki a rayuwa, kuskurene da kuma ajizanci na d’an adam, amma na yi nadama.” “Allah ya yafe mana gaba d’aya.” Ta fad’a fuskarta a sake “Ni dama ba kayi min komai ba of aure ne da Shatu baka so to tunda an samu mai so na bashi, ba shikkenan ba, na yafe maka Allah ya zaunar daku lafiya gaba d’aya da Matan ku.”
Murya a sha’ke ya ce “Ba ni da mata sai dai ki yi min addu’a Allah ya kawo.”
Mommah ta ware ido “Ita kuma Shaheedahn fa?” “Na saketa” ya amsa mata with confidence dafatan Allah yasa wannan ya zama uzurinsa da zata ba shi matarsa.
Mommah ta ja ajiyar zuciya duk da ta ji dad’in labarin sai bata nuna masa ba Ta ce, “Me ye hujjarka na sakin Shaheedah? Ka yi wauta in dai don nufinka na baka Shatu ne, me ye hujjarka nace?” Kansa a ‘kasa ganin alamar wannan karan ma ba shi da nasara ya ce “Na gayawa Dahda, zai miki bayani, yanzu ma sallama na zo yi miki da neman afuwarki saboda ban
San yarda rayuwa za tayi ba, gobe zan wuce turkey, ubangiji ya huci zuciyarki.”
Jikinta ne ya yi sanyi sosai taji tamkar ta jashi ta rungumeshi, tamkar ta janye ‘kudirinta ta aura masa Shatu amma ina ba zata iya wannan ba. “Saboda ba ka auri Shatu ba shi yasa zaka tafi ka barmu?” Ya d’aga kai “Tabbas haka ne, ba zan juri ganinta ta auri wani ba, zuciya ta tana raya min na aikata koma meye don na sameta, shi yasa zan yi nesa da ita, ubangiji Allah ya basu zaman lafiya.” Ya mi’ke yana rangaji tamkar ya kifa, ko shakka Mommah ba tayi idan tace babu ‘kwayar abinci a cikinsa. Ta runtse ido ina ma zata iya da ta kira shi ta sanar da shi ta janye ‘kudirinta, amma ina sam ba zata iya ba, gwara shima ya je ya d’and’ani takaicin da ya ‘kunsa musu.
Shatu kuwa da take le’be a corridor ta ji duk zancen da suke, tuni ta yi waje da gudu cikin tashin hankali ta na kuka, ban da tana ganin zahirin kamar Mommah da Imran tabbas da ta ‘karyata cewa ita ta haifeshi. Wace irin zuciya ce haka da Mommah?
Ta gabanta yazo ya wuce kuma sarai ya ganta ya kuma ji kukan da take yi, amma ba zai iya tsayawa ba domin shima kukan ya ke tamkar wani ‘karamin yaro, da sauri ta mi’ke ta bi bayansa ji take tamkar ta je ta rungumeshi.
Yana shirin rufe ‘kofar ta saka hannunta ta tura, bai hanata shigowa ba don yana bu’katar hakan shima, ta kulle ‘kofar har da murza key. Zama ya yi a kujera hannayensa dafe da ‘kirjinsa. “Na amince Ya Imran mu gudu muje wani wajen a d’aura mana aure, idan yaso sai mu tafi turkeyn.” D’agowa ya yi yana kallonta bayan ya yi ‘ko’karin tsayar da hawayensa idanunsa sun yi jazur ya mi’ka mata hannu.
Gefensa ta je ta zauna hannayensu sar’ke da na juna. Murya a tausashe ya fara yi mata magana “Ba zan gudu da ke ba, wannan ba hanya bace mai ‘bullewa, na dad’e ina ba’kantawa Mommah rai ya zama dole a wannan karan na ha’kura da ke matu’kar ina son na gama da duniya lafiya, ko da hakan zai zamo ajalina, haka Allah ya ke dama jarrabawa ce ya ke min sai dai fatan Allah yasa naci nasara na
Amsa ta da karsashi, ubangiji yasa na iya jurewa, ki yi ha’kuri ki zauna da mijin ki lafiya, insha Allah shi d’in alherinki ne! Tabbas Ammar ne ya cancanta da ke domin shine ya farantawa Mommah a lokacin da ni na ba’kanta mata, wa ni abin Ayshatu wallahi ban san na yi ba. Alfarma d’aya zan saki ki nemar mini a wajenta please ta amince ta bani su Akram, ko ina can zan nema musu visa. Ki tashi kije kada wani yazo ya ganki zargi ya shiga zu’kata, nagode da kulawarki gareni na san kina sona fin ‘karfinki aka yi.” Wannan karan hawaye ne sosai ya ke fita daga kwarmin idonsa a zahiri yace kullum zance na me zan yi da ita? Ga shi Allah ya jarrabeni da masifar sonta.
Ya fad’a yana kallon bayanta ta na shirin fita ta ji ya ce “Ayshatu!” Cak ta tsaya a ranta tana raya duk duniya ba wanda ya iya furta sunanta correctly kamar Imran idan kuma ya kirata d’in jin kiran take har zuciyarta.
Bata jiyo ba ta dai tsaya cak, don ji take idan ta jiyo d’in zata iya zuwa ta rungumeshi ko ta samu saukin rad’ad’in zuciya da take ji.
Wani akwatin ma’adanar sar’ko’ki ya mi’ko mata, yana furta “A niyyata sai ranar da kika tare a gidana sannan zan baki, sai dai kana taka Allah na tasa, Na tabbata ta Allah is the best, ubangiji ya yi mana jagora ya sanya albarka a cikin auren ki.” Hannunta na rawa ta kar’bi sar’kar ta rungumeta a ‘kitjinta ko bakomai ta maye mata Imran, ta d’ago tana kallonsa murya a dashe ta ce “Nagode ubangiji ya yi ri’ko da hannunka, ya ba mu juriyar rasa Juna.
Da sauri ta fita da gudu, shi kuwa Imran zubewa ya yi cikin matu’kar tashin hankali ya ce “Ya ilahil alameen ka kawo min d’auki”
Ranar dai kam daga shi har Shatu ba wanda ya runtsa,haka nan ya shirya dai-dai lokacin da Dahda ya ke buga masa ‘kofa, ya fito d’auke da suitcase d’insa. Cup d’in tea mai zafi Dahda ya mi’ka masa da sauri ya girgiza kai had’e da cewa “Inni sa’im” Dahda ya ajiye had’e da cewa “Allah ya biya bu’katu mu je ka yi sallama da jama’ar gidan sai na saukeka.” Da sauri ya girgiza kai “A yi min afuwa Dahda, na yi sallama da Mommah da daddare ka sanar da sauran.” Dahda ya girgiza kai “Allah ya yi mana jagora muje to. Na tura maka hoton yarinyar nan fa a waya ka duba?” Da sauri ya girgiza kai “Zan duba insha Allah nagode.” Dahda ya ce “Da kuma digit d’inta sai ka samu lokaci ka kirata mun yanke shawara da Babanta rana d’aya za’a d’aura da nasu Ammar.” “Nagode” kawai ya ce suka tafi to Imran sai muce saduwar alheri.
——————————————-
A zafafe Hameedah ta d’au wayar mijinta tana sake ware idonta akan hoton Shuwa da ta gani a wayar, cikin tashin hankali ta shiga bincikar wayar ta shiga whatsapp taga chatting d’inta dashi, tuni ‘kirjinta ya fara luguden da ka cikin sauri ta fara tura duka sa’konnin zuwa wayarta saboda su zame mata hujja anan gaba.
Ta tuna san da Shuwa ta zo gidan ta kawo mata wani sa’ko a lokacin suka gaisa da mijinnata wato ashe har sun jone cab ai kuwa dole ta jewa da Hajja wannan labarin da dai ta ce ba zata bikin ba amma yanzu ya zama dole taje bikin ayi wacce za’a yi.
Mijinnata yana fitowa daga wanka ta watsa masa wani kallo kafin ta cilla masa wayar cikin tashin hankali Ta ce “Me ye had’inka da wannan mayaudari?” Yana d’aukar wayar yaa saki murmushi kafin ya ce “Ko ba kiyi zancen ta ba ina da shirin gaya miki amma tunda kin lalubowa kan ki ya zama dole yanzu ki sani aurenta zan yi har an saka rana nan da sati uku.” Wani irin ihu ta saka cikin tashin hankali ta ce “Shuwan zaka aura? Ai wallahi ba zan yarda ba, ba gwara ka auro min mata uku lokaci d’aya ba akan kaand auri Shuwa.” Tsaki ya ja ya ce “Kada ki saka min ciwon kai ita na gani kuma ita nake son aure idan kin ga ba zaki iya ba hanya a bud’e take. Bana son maganar banza ke za ki tsara min rayuwa ta.”
Zaman ‘yan bori Hameedah ta yi cikin tashin hankali ta mi’ke ta fara tattara kayanta dole yau ta yi kwanan Abuja ta tasa Zainab a gaba sai ta nemo mata Shuwa. To fa ana wata ga wata ko ya Hajja zata ji idan za’ayi wa autarta kishiya, kishiyar ma da Shuwa idon duniya?
——————-
Gefe d’aya lamarin biki ya fara kankama, yau bridal shower kashegari kuma za’ayi kamu sannan the next day ayi walima sai dinner da za’ayi the following day sai kuma a sada amare da d’akunansu.
Dukkansu a Abuja za su zauna Shatu ce kawai a Kano sai amaryar Imran da zata tafi turkey.
Da aka jewa Babanta da zancen ya amince don dama burinsa ya yi mata aure, kyakykyawa da ita fara tas ga gashi kamar na Shatu duk da dai ita bata da tsaho sosai amma fa akwai dirin jiki mashaAllah.
Zainab da Shaheedah a ranar suka zo har da rakiyar Shuwa, suka kuma taho da tarkacen kayan asiri su, ganin daga Dahda har Imran ba wanda yayi musu magana su ke zaton kamar aikinsu yaci don haka suka zo da sabon shirin su.
Kamar had’in baki itama Hameedah Autar Hajja ranar tazo hankalinta a tashe, ba tare da ta kula da jama’ar da suke wajen ba ta ja hannun Hajja zuwa cikin d’aki.
Hajja cikin tashin hankali take dubanta, ganin yarda tayi wujiga-wujiga “Ke Hameedah lafiya gaya min me ya faru na ganki cikin tashin hankali? Ke dama kika ce ba zaki zo ba me ya kawo ki?” Kuka ta saka ta rungume Hajjan “Na shiga uku Hajja Habib ne zai yi aure, kuma ya rasa wacce zai aura sai Shuwa aminiyar Zainab mai rakata yawan Malamai.” Cikin tashin hankali Hajja ta ce “In ji wane tsinannen? Shi Habibun ne ya gaya miki haka?” Da shashshekar kuka tace “Wallahi shine, bai ji shakka ba ko kunyar sanar dani daga alamu ma ta riga ta gama dashi don cewa ya yi idan ba zan iya zama ba na tafi ga hanya nan, na shiga uku Hajja dole Zainab ta zo ta gaya min inda zan samu shegiyar nan?” Hajja ta saki murmushin da kai tsaye za’a iya cewa na tashin hankali ta ce “Sha kuruminki almurar ai tana nan a gidannan ki bar ni da ita za ta san ta ta’bo min shalele, ba Shuwa ba ko Arab ce yau ta had’u da gamonta.” Ina Hameedah ai da gudu ta mi’ke jin cewa Shuwa tana cikin gidan, yau idan bata raba Shuwa da rayuwarta ba ta haifu a cikin Hajja ba.......
Da sauri Hajja tayi ‘ko’karin ri’keta, sai dai ina ‘kwacewa ta yi kamar mai iskokai a kanta tayear fice a guje, duk wanda ya ganta a lokacin zai iya zargin hauka take sabon Kamu.
A wani parlour kuwa Allah ya taimaketa ta riski Shuwa ai kuwa direct ta sha’kar mata wuya. Shuwa da dama ta san za’a rina sam bata firgita ba, illa ‘ko’karin Ta ‘kwaci kanta cikin matu’kar jarumta ta fisge wuyanta sannan ta zabga mata mari, hakan ya tunzira Hameedah ta samu wani sanda ta rafka mata, Shuwa ta zube ‘kasa da sauri Zainab ta yi kanta tana fad’in “Ke baki da hankaline? Kashe ta za Kiyi?” Wani kallon banza Hameedah ta watsa mata “Ri’kakkiyar munafuka ai na san duk wani ‘kulli dake aka ‘kulla shi, yarda kuka yiwa Dijah shine nima za kuyi min ku yaudare mijina kamar yarda kuka yaudari Yaya Manga to wallahi ni na fi ‘karfinku daga ku har tarkacen asirinku, Hajja yau zan sanar da ke komai wallahi Zainab asiri ta ke makawa Yaya Manga da kebin kan ki shine dalilin da yasa idon ki ya rufe har kika aura mata Yaya Manga, munafuka kuma yanzu ma sun sake ‘kulla wata tsiyar don kuwa farra’ku suka shirya yi miki da d’anki Allah ya toni asirinsu shi da Kansa Yaya Mangan ya ganta tana ha’ka rami zata birne, kuma ita Shuwan ita ta gaya min da bakinta, har haurawa muka so yi da ita da taje gidana akan me yasa za suyi miki haka suka ce so suke da zarar sun mallaki Manga sai su karya asirin lokacin burinsu ya cika an fitar da Dijah daga gidan Manga....” gaba d’aya parlourn salati aka saka cikin mamakin wannan abin aljabi, da takaici Hajja taa dubi Zainab ta ce “Yanzu Zainab abinda za kiyi min kenan duk da ‘kaunar da nabin nuna miki amma ki rasa sakayyar da zakiyi min sai ki yi min farra’ku da d’ana?” Kuka sosai Hajja ta saka yayin da Zainab ta fara ranges-rantsen ‘karya. Nan fa kallo ya koma sama ‘yan biki suka had’u a wajen aka suka su Zainab a gaba ana jifan su da kalamai marasa dad’in ji.
Hargitsewar da gurin yayi nea dangin Mommah na neman tada wata fitinar don kuwa rantsewa suka yi sai sun illata su Zainab, hakan yasa Mommah kiran su Dahda ba shiri don gwara maza su shiga cikin lamarin tunda ana neman illata su.
Da kyar su Dahda, Kawu Sa’idu da Alhaji Baba suka samu shiga gurin, duk da korar da aka dinga yiwa mutane amma kowa fir ya’ki fita, kuma ana mi’kewa za’a fita dasu suke saka musu duka hakan yasa dole aka zauna anan ayi shari’ar.
Kawu Sa’idu ne ya kalli Hameedah yace “Ina jinki me ya Faru?” Nan cikin kuka ta shiga bashi labari turyan-turyan.
Tana gamawa Kawu Sa’idu ya saki Murmushi ya ce “Hukumullahi la ajabun ashe har anzo wajen madallah da sarkin sarakuna mai sakayya yanzu tun a duniya ba sai Anje ‘kiyama ba. yanzu ke me kike so ayi? Abinda fa kuka yiwa Dijah ne ya juya ya dawo kanki, ko kunya ba kiji ba da bakin ki kike cewa an had’u da ke an yiwa jininki asiri shima Imrana ashe asiri kuka yi masa to ba jan magana nake nema ba ta faru ta ‘kare sai kije ki rungumi ha’kuri kamar yarda Dijah ta ha’kura Allah ya ba ku zaman lafiya ke da kishiyarki, ita Shuwa ai gaba ta kaita shashashai kawai duk ‘kawar da ba zata d’ora ka a turbar arziki ba ai kaa gujeta, Allah ya kyauta yanzu ai kun ga ishara da ku da duk mai hali irin naku.”
Har zai mi’ke ya fita don shi ko ganinsu baya son yi. Dahda ya gyara zama ya ce “Kawu ina da magana, dama ina taso Allah ya kawo mu rana irin wannan, ranar da zasu toni asirin junansu da bakinsu, tuni na san da wannan zancen da kuma idona na kama Zainab zata birne laya cikin dare wanda sunana da na Hajja yake zane a jikin layar, kamar yarda shima Imran ya kamasu da matarsa da tulin kayan tsubbace-tsubbace a gabansu, shima ya nuna musu tamkar bai gane ba, sai dai dukkaninmu mun yanke hukunci d’aya domin kamar yarda Imrana ya saki matarsa hakanan nima na saki Zainab...” cece kuce ya tashi a wajen bayan Manga ya zaro waya ya kunna vedio ya yi connecting da T.v a parlourn sai ga kuwa Zainab tana birne birnenta. Gaba d’aya salati da salallami mutane suke a wajen. Cikin tashin hankali Hajja ta ke sake duban tv d’in da gasken dai Zainab ce ai kuwa sai ga Hajja tana kuka riris tana fad’in “Allah ya isa Zainab na bar ki da mai hudowar rana da fad’uwarta shine zai mana sakayya.”
Su Zainab dai ba bakin magana gaba d’aya kunyar kanta ta isheta. Shaheedah kuwa kuka ta ke
Na fitar hankali tabbas ta san rayuwarta ta tawaya tunda ta rasa Imran, ta yi dana sanin bin zugar mahaifiyarta, ta tuna yarda suka cusa masa sonta ta kar’bi da yaji da asiri da rubuce-rubuce, gashi yau rana d’aya ubangiji ya toni asirinsu. Jiki a salu’be suka mi’ke aka basu hanya Hajja fad’i ta ke “Gayyar tsiya ku basu hanya su wuce zan kuma da uwarki in ji ko ita ta saka ki a turbar halaka.”
Ta kuma cigaba da kukanta tana kallon jama’ar da ke wajen fad’i ta ke “ku kuma iyalen saka ido ai sai ayi gaba ko? An samu na kai rahoto idan banda haka abu na gida me ya kawo idonku wajen? Ni bana son munafunci.”
Sum-Sum kuwa suka fice daga wajen, Hajja ta kalli su Mommah kafin ta ce “Dijah don girman zatin ubangiji ki yi ha’kuri ki yafe min, duk da na san girman laifina a gareki wallahi kullum na yi nufin fara ‘kaunarki da yabon kyawawan d’abiunki sai na ji zuciyata ta gaza hakan na tabbata ba haka suka bar ni ba, ni ba kiyi min komai ba wallahi kullum a cikin kyautata min kike?” Alhaji Baba ya ce “Alhamdulillah, hakan da kika yi shine ya dace ke kuma Dijah ki yi ha’kuri ki yafe mata ko bakomai ki saka ta a mizanin uwa don uwar miji uwace matar da ta haifa maka miji ai ba abar wula’kantawa bace macece da ya kamata ka bata daraja ta hudu bayan uwa uba miji ni ana wa hangen sai uwar sa tunda ta yi miki komai da ta haifa miki d’an har kike tin’kaho da shi a matsayin mijin ki. Ke kuma uwar miji duk matar da ta auri d’anki ta gama yi miki komai domin ta so d’anki ta na kuma kula dashi bai kamata ta zama abar tozartawa ko abar