Showing 114001 words to 117000 words out of 117786 words

Chapter 39 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

479

‘yar nema wato ke shine ubannaki, Ai shikkenan kun raba.” Manga da yake ta dariya ganinsa cikin iyalinsa cikin farin ciki ya ce “Ban da twins ai su dai kam mu aka haifawa su ri’ke wad’anda suke cikin Allah ya saukesu lafiya.” Mommah ta ce “Tabbas don ni naci kashinsu na ci fitsarinsu.” Su dai ba wanda ya yanka a cikin su sai murmushi suke.




—————————————-

Bayan kai Shatu da Mubeenah asibiti Doctor ya tabbatarwa da Mommah Mubeenah ‘kalau zata haife cikinta cikin hukuncin ubangiji, amma Shatu still wannan karan ma cs za’ayi mata saboda bakin mahifarta ba ya bud’ewa, Shatu ta d’an tashi hankalinta amma ta kwantar mata da hankali tace “Kowa da jarrabwarsa rayuwa bata tafiyarwa bawa successfully dole a jarrabaka a gwada imaninka.” Hakanne ya kwnatarwa da Shatu hankali.

Aka yanke da zarar Mubeenah ta fara labour ita kuma za’a yi mata c.s saboda a samu su haihu rana
D’aya. A kuma ranar Mommah tace ta basu kwana uku kowa ta yi sallama da mijinta kafin su tattara su dawo d’akinta. Duk da iyayen Mubeenah sun so d’aukarta amma Mommah ta ro’kesu su barta, basu ji ko d’ar ba suka barta don sun tabbata zata samu kular da ko su ba zasu bata ba.

A kashegarin ranar ita da Hameedah da Ammar sai Nahna da Hisham suka d’unguma asalin ‘kauyensu Shatu. ‘Kememe Imran ya ‘ki binsu yace idan ta haihu zamu je a zuciyarsa ya ce dole na zauna na more kwana ukunnan don na san idan Mommah ta d’auke min mata sai na yabawa aya za’kinta da zarar ya tuna hakan ‘kirjinsa yake luguden daka tsawon wata biyu fa zai yi ba Shatu anya kuwa zai iya?

Me zan yi da ita?


Littafin

Nazeefah Nashe


Elegant Verified Online Writers......


08033748387


https://www.wattpad.com/user/Nazeefah381?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_profile&utm_campaign=invitefriends&wp_page=home&wp_uname=Nazeefah381&wp_originator=GHG3oXDuy%2FyzvnGIdOQobZD6X5lwLSdr1D2fuHcQ2YaWzGdHWjyTkcuCrRetsuFuOhOOST8i92DU1zHjm6baftBk6FpQLITawz9m%2F5qBhp2oUpPmsvRwZiKU4cLCvC8Q


**********************************

Sun samu tarba a ‘kauyen sosai duk da ba su san da wacce su Momman suka zo ba, sai da suka huta sannan Mommah cikin son tsoratar dasu Ta ce “Mu dangin Shatu ne wato ‘yar wajen innaji maryamu ni d’in ‘yaruwarta ce yayarta ciki d’aya mun samu labarin Shatu tana garinnan shine muka zo tafiya da ita.


Kaf wajen ba wanda zufa bata karyo masa ba, musamman ganin Ammar da Hisham da shigar suit ba’ka’ke sai kace ‘yan sanda.

Nan take tsoffin suka shiga rantse-rantse rashin sanin inda Shatun take Sadau ya ce “Aradu kakarta tana rasuwa ta arce ta bar garin nan. Sai da Mommah taga sun razana sosai musamman da suka ji ance za’a kamasu sannan ta sanar dasu gaskiyar lamari ta kuma yi musu nasiha sosai musamman akan wula’kanta maraya bayan a al’kura’ani mai girma ubangiji ya tsoratar akan Hakan, ya kuma yi umarnin a kyautata musu jikinsu ya yi sanyi sosai musamman da ta kwatanta musu da rasuwar d’aya daga cikinsu ya bar yaransa shin zai so a wula’kanta su. Kaf is wajen ba wanda bai yi hawaye ba, suka dinga yiwa Mommah godiya da ta sanar da su abinda ba su sani ba ashe al’amarin maraya mai girma ne a wajen ubangiji, al’kawari suka d’auka sosai don gane kuskurensu, kuma zasu je har birnin suka Shatu su bata ha’kuri da izinin ubangiji. Mommah ta ji dad’i sosai ta ce “Haka ne ya kamata.”

Kwanansu d’aya cur kashegari da safe suka d’unguma suka tafi har da sadau da Iroro don suje su ga waje idan sun tashi zuwa ba sai sun nemi d’an rakiya ba. Mommah ta zube musu alheri sosai da kud’ad’e ta raba musu jari take suka dinga murna suna fad’in “Ahe shatu alherinsu ce amma suka wula’kantata.” To dama haka lamarin ubangiji shi yasa ba’a so a karan farko ka wula’kanta mutum alhali baka san tarin baiwar da khali’ku ya yi masa ba, ba mamaki wata rana shine zai taimakeka to da wani idon zaka kalleshi bayan tarin wula’kancin da kayi masa.


Shatu sosai ta ji dad’in had’uwa da tayi da dangin babanta, murnarta ta gaza ‘boyuwa akan fuskarta, sai murmushi take saki ko bakomai dangin uba da su ake ado, Hajja ma da farin cikinta ta dinga gaisawa da su ba tare da ta nuna musu ‘kyama ba ko kad’an.


———————————-

Kwana ukun da Mommah ta basu Na cika ta tattara su Shatu suka koma sashenta Imran kamar yayi kuka gwara ma Ammar ya dake bai nuna rashin kunyarsa ba. duk da dai shi tasa matar daman raguwa ce bata fiya jurar fitinarsa ba tunda ta samu ciki kuma sai ta ‘kara langa’bewa.

Imran da kyar ya gama sallama da Shatu har da hawayensa sosai yake jin zafin rabuwa da Hayateey d’insa, a kunne ya rad’a mata “Please ki dinga satar hanya idan ba so kike na kusa zarewa ba, wallahi da gaske ba zan iya juriyar wannan abin ba, Gaskiya banda uwa uwa ce da na nuna mata ban amince ba.”Ya fad’a yana saka idanunsa da suke she’kin ‘kwalla cikin na Shatu, mamaki ya kamata da taga da gaske Imran hawayen yake. Hannunsa ta ja tana matsawa a hankali ita kanta ba wai tana son rabuwarsu bane amma bata son ta yiwa Mommah da take wa kallon mahaifiya tawaye. Matse hannunnasa tayi da ‘karfi alamar ta rasa abin cewa, sai kuma can murya a cunkushe ta ce “Please kada kaci amanata, kada ka kai bu’katarka wajen kowa duk sanda kake son kusantata ka tura min text ni kuma zan biyo dare Nazo.” Kyakykywar runguma ya kai mata ya ce “Na sani ke kanki zaki wahalar rashina kusa da ke saboda jikinmu ya zama tamkar d’aya, dole zamu ha’kura da abinda Mommah ta ce, amma hakan ba zai saka mu jefa kanmu a halaka ba, ki cire kunya please ki dinga zuwa muna gaisawa ko da sau d’aya a rana.” Yatsa ta sa ta lakaci gefen hancinsa ta ce “Insha Allah.” “Ban yarda ba promise?” Hannunsa ta kama ta dun’kule cikinnata a hankali ta d’aga Kai. Ya rugumeta tsam a jikinsa, sannan ya taya ta jan trolley zuwa sabon d’akin da Mommah ta basu ita da Mubeenah a ‘bangarenta.


Sun sha matu’kar wahala kafin su saba da rashin juna, musamman Imran da yake kwana birgima a gado don ma dai ya ‘dauko Akram yana taya shi kwana. Ita kuwa Mubeenah ba abinda yake damunta, ita hakan ma gaba ta kaita akan ‘kwazzabar da Ammar yake mata. Shatu dai kam sai a hankali don ma kullum idan ya dawo tana ture kunyarta ta bishi cikin d’akinsa ta rage masa zafi, saboda ta san mijinta yana da ‘karfin sha’awa musamman a kanta.




—————————

Labour mai zafi ne yazo wa Mubeenah, hakan yasa aka tafi asibiti har Shatu da za’a yiwa c.s

Suna zuwa kuwa aka shige da Shatu theatre room hankalin Imran yayi masifar tashi gani yake kamar Shatun ba zata fito ba, shi yasa ya koma bakin ‘kofar ya kasa ya tsare. Jira kawai yake a fito masa da albishir mai da’di.


Mubeenah kuwa bata d’au dogon lokaci tana na’kuda ba ta haihu ta sankato yarinyarta fara tas da ita tamkar ‘yar larabawa ko da yake mahaifiyarta ta had’a jinsi da larabawan.

Murna sosai ya karad’e dangin Manga a asibitin kamar ha’din baki lokaci ‘daya aka fito da Babyn Shatu itama mace fara tas da ita masha Allah ba dan kar kuce ‘karya nake ba da na ce muku jariran kamarsu ‘daya don har sai da Mommah ta ce ayi musu shaida gudun kada a kasa banbancesu.


Shi Imran ba ta Babyn yake ba zuciyarsa na wajen Shatu da har lokacin ba ‘a fito da ita ba, sai da yaga an fito da ita har tana sakar masa murmushi sannan hankalinsa ya kwanta, da har ya fara dana sanin amincewa da yayi aka yi mata aiki a Nigeria.

‘Daki ‘daya aka kwantar da su kuma Mommah ce da kanta zata zauna da su, duk da Hameedah tazo daga maiduguri kasancewar mijinta ya tafi China, to ita zata koma da Mubeenah ta taya ta zama kafin a sallami Shatun a asibiti.

Dahda dai bai amince da shawarar Mommah ba ya ce ta tafi gida Hameedah ta zauna da Shatu a asibiti ita da Yasirah, tunda ita cikinta bai tsufa ba kamar na Basirah. Dole Mommah ta amince don ko bakomai ma ba za’a bar Hajja a gida ba bai ma kula da ita ba kuma ita kad’ai tasan kan abincin Ta da magungunanta.

Hakan ya yiwa Imran da’di, don tabbas in dai ta Hameedah ce to kuwa da shi za’a yi jinyar Shatu a asibiti ba inda zaije nan kwana nan wuni sai dai yaje ya ‘dan huta ya dawo.

Kwanannan uku da Shatu tayi a hospital kamar wasa da Imran aka yi shi ya kasa ya tsare ga jaririyar kullum a hannunsa, lamarin sosai yake bawa likitocin da ma’Ikatan jinyar asibitin sha’awa. Zahiran Imran yake nunawa Shatu matsananciyar ‘kauna da kulawa tare da soyayyar da ba gwauraye a cikinta.




————————————-

Sati uku aka ‘kara kafin ayi sunan zuwa lokacin tuni Shatu ta warware gaba d’aya masu jegon sunyi ras dasu tamkar ba su bane suka kumbura suka yi ba’ki, Mommah tuni ta gyarasu da kayan gyaran jiki masu kyan gaske, da mayuka masu kyau sai gasu farar fatarsu ta sake fitowa sai she’ki take. Tamkar an sake ‘kara musu kyau tabbas sun had’u da jarumar surika da ta san mutuncinsu take kuma kula dasu ko don samun walwala da nisha’din ‘ya’yanta.



Shirin suna suke ba na wasa ba, aka kama babban event centre mafi tsada a garin kano, an kuma samo masu abinci da za suyi girke-girke iri-iri. Imran dai sakar Naira yake kamar bayaso so yake ya burge matarsa ko don isarsa da tayi ita duka aurenta ba a yi biki da ango ba, kaya yayi mata sosai na gani a fad’a bayan lefen da ya bawa Mommah ta ha’da mata. Haka nan Ammar shima yayi tasa bajintar sosai ma kuwa.

Mommah babbar motar Bus ta companyn Dahda ta bayar aka je har ‘kauyen dangin Baban Shatu aka ‘daukosu kaf ‘dinsu manya da suke ‘yan uwan mahaifinta.

Suna zuwa ‘bangare guda aka basu suka dinga zugar kaji suna sake godewa mahaifin Shatu da ya auri Marayamu har suka samu tagomashin arzikin nan.



——————-

Gurin suna yayi kyau sosai ya ‘dau harami tamkar a ‘kasar turai Shatu da Mubeenah kaya iri ‘daya suka saka wani black lace mai adon peach yayi masifar yi musu Kyau. Suma su Imran black shadda suka saka anko komai nasu iri ‘daya tamkar amaren jegon.

Imran bai ji shakkar bayyana tsananin ‘kaunar da yakewa Shatu ba, musamman yasa aka bashi mic ya shiga bayyana mata matsananciya ‘kaunar da yake mata ta hanyar mic ‘din, gaba ‘daya wajen ya yi tsit muryar Imran kawai ke tashi a hall ‘din yana fad’ar baitukan idanunsa a lumshe hawaye na ziraro masa, alamar abinda ya fad’a d’in d gaske yake from the bottom of his heart. Yana gamawa wajen aka saki tafi raf-raf.

Khalil cikin dariya ya kar’bi mic d’in yace “Alhamdulillah! Malam Imran yau mun ga abinda za kayi da Shatu, tabbas hukumullahi la ajabun. Abokansa da suka san mafarin zancen suka dinga sakin dariyar sha’kiyanci. Shi dai Imran rungumo Shatu yayi yana sakar mata wasu zantuka a kunne da ya saka ta murmusawa dole, hakan ya sake burge jama’ar da ke wajen.



——————————

Gajiya da Mommah Tayi da rashin kunyar Imran, har Ammar d’inma duk ha’kurinsa ya fara nuna gazawarsa. Hakan yasa suna kwana hamsin ta tattara su ta ce “Su koma gidansu lada ya isa Haka, bayan tayi musu gyara Na musamman da ta tabbatar duk wata martaba ta jikinsu ta dawo sannan ta mayar dasu gidajensu.


Imran ranar kamar ya zuba ruwa a ‘kasa ya sha musamman da ya samu Shatu zam-zam, don ko bari ta ga gidan bai yi ba, sai da ya fara gurzar angwancinsa, sannan suka zaga gidan da ya lashi ma’kudan nairori wajen ginashi. D’aki Guda aka warewa Baby aka zuba mata duk wani abin bu’akatar Ta....


https://www.wattpad.com/user/Nazeefah381?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_profile&utm_campaign=invitefriends&wp_page=home&wp_uname=Nazeefah381&wp_originator=GHG3oXDuy%2FyzvnGIdOQobZD6X5lwLSdr1D2fuHcQ2YaWzGdHWjyTkcuCrRetsuFuOhOOST8i92DU1zHjm6baftBk6FpQLITawz9m%2F5qBhp2oUpPmsvRwZiKU4cLCvC8Q



Me zan yi da ita.....



Gida kam yayi kyau sosai tamkar a ‘kasar turawa parlour komai anyi shi bisa tsari. Shatu ta dinga zagaye gidan cikin tsananin murmushi da murnar cikar burinta, tabbas rayuwa tazo mata da d’imbun nasarori wanda ba ta Ta’ba mafarkin kasancewarta a cikinsu, Gida mai kyau Miji Nagari ga arzikin haihuwa da Allah yayi mata musamman twins da ta haifa, tabbas Allah ya cika mata ni’imominta na duniya, abinda ya rage mata kawai yau ta ganta ta zama cikakkiyar lawyer. Shikkenan ita kam sai tace tazo duniya a sa’a. Addu’arta kullum Allah yaji ‘kan Innaji da Babaji har da Gwaggoji da Moddibo. Hawaye ya zubo mata, da ta tuna dasu sune kad’ai basu mori arzikin nata ba, Ta so ace suna raye sun ga yarda Shatu mai idon ta a loko ta koma. Imran ne da sauri yasa hannayensa yana wiping tears d’in da take fitarwa. Da murmushi a fuskarsa ya ce “Me ya saka a wannan hawayen zubowa?” Itama murmushin tayi a hankali ta furta “Na tuna iyaye na, shine dalilin zubar hawaye na, Innaji da gatanta ashe ta bar mu mu kayi rayuwar jeji a can Niger, insha Allah kuwa zan kai musu ziyara, zan sa a gina musu makarantar Boko da ta Islamiyya har da masallachi duka sada’katul jariya ga iyaye Na, in dai Na zama lawyer Na fara tara ku’din salary na.” Murmushi Imran ya saki yana jan hancinta ya ce “Ba sai kin zama lawyer ba, Hayateey dole na cika miki burinki Insha Allah.” Tsananin murna yasa ta doka tsalle ta rungumeshi tana furta “Thankyou so much ‘kalbeey.” Dariyar ta bashi ganin har yanzu ta’barar Shatu tana nan da yarintarta. A zuciyarsa ya furta auren irinku Shatu rahma ne da Allah yake bawa ‘kayyadaddun bayinsa, ciki da waje kinyi min ba gi’bi.



Bayan wata biyu kusan ince gaba d’aya familyn d’in suka tafi umara Iyayen Mommah da su Nahna Hisham da matarsa har da hafsa da ta haihu kwana Arba’in da suka wuce, Hajja da Ammar da Matarsa Mommah da Dahda Imran da Shatu, Akram da Ikram, masha Allah haka suka d’unguma umara cikin tsananin farin ciki da walwala.


Hameedah ma ta so zuwa sai dai laulayin da take yasa mijinta ya hanata zuwa, don tun bayar nadamarta da addu’oin da aka yi tayi ya fito ya sanar da ita gaskiya dama duk shiri suka had’a da Imran ba wani asirin Shuwa da ya cishi sun dai yine don su ganar da ita sharrin dake cikin tarayya da irin su Shuwa. Tuni Ayda da Amna sun ‘kara girma kamanninsu sun ‘kara fitowa sosai zahiran da Mommah suke kama.


Sati uku cif suka d’auka a saudiya suna ibada sannan suka dawo zuciyarsu cike da ya’kinin ubangiji ya amsa musu duka addu’oinsu.



Shatu dai suna dawowa ta koma makaranta gadan-gadan ta kama karatu, Mommah take kaiwa Aidah da masu aikinta guda biyu, idan ta dawo sai ta biya ta ‘daukosu. Don ta iya driving sosai.


Imran ya tattara ya dawo Nigeria don ba zai iya nisa da Shatu ba, ya dai ‘dora duk d’awainiyar ayyukansa Na can akan wani d’an turkiya da ya tabbatar yana da ri’kon Amana. Shi kuma ya bud’e wani companyn anan kano, zai iya cewa Auren Shatu ya zamo masa da alhairai masu tarin yawa don ta ko ina bud’i yake samu.

Ba kuma ruwansa da kowacce mace don tabbas Shatu kullum sai ta d’auke masa sha’awar kowace mace, yana da ya’kinin ko kyauta aka bashi mace zai ce ya yafe don ya san Shatu number one ce a fagen kishi. Shi yasa ma yaji a zuciyarsa sam ba shi da muradin ‘kara aure.


—————-

‘Bangaren su Zainab kuwa tuni suka yi baran-baran da Shuwa kowa ya kama gabansa, Shaheeda kuwa da kyar ta samu wani ‘karamin ma’aikacin gwamnati ta aura don ya fi mata zama ba auren don sam ba zata iya kame kanta ba. Duk da rashin mutuncin mijin haka ta ha’kura ta aureshi tayi matu’kar da na sanin biyewa Sharrin zuciya da turbar da suka ‘dorata akai. Haka dai dama abin yake duk burin Zainab yabi ruwa, ‘karshe dai ba arzikin ba mallakar mazajen wad’anda basa so su zauna gidan mijinsu kuwa gasu nan suna zaune abinsu lafiya, cikin kiyayewar ubangiji su kuma sai Allah ya barsu da iyawarsu, da malamansu da bokayensu.




——————————

Wani hutu da aka yi su Shatu suka nufi ainahin mahaifar babanta ta kai musu ziyara ita da Mijinta da yaranta, suka kai musu kayan abinci na bajinta sannan Imran suma ya samu fili ya bada kwangilar gina musu masallaci makaranta, da kuma asibiti. Ai kuwa ya sha addu’a. Shatu ma taji dad’i sosai.

Don haka a daren ranar da suka dawo tayi shiri na musamman ta sake nuna masa ita d’in yanzu Hakimar mace take amsa suna. Sosai ya gigice ya d’imauce da har ya fara tunanin anya Shatunsa ce, don kaf ta sake canja masa na tabbata kuma a wannan daren da kyar idan bata ‘kunshi ciki ba, don ya’ki yarda da tsarin iyali, yace so yake ta cika masa gida da yara musamman ganin nasu familyn basu da yawa don Allah bai bawa iyayensu haihuwa da yawa ba.



———————

Ai kuwa wata guda a tsakani Shatu ta sake tabbatar wa da ciki ne da ita don ta ji canji a jikinta sosai hakan yasa dole ta yaye Ayda, da dama ba wani damuwa tayi da nonon sosai ba, shekararta guda cif aka yayeta.

A satin kuma ya cika mata al’kawarinta suka nufi Nigerr ta jirgi da shi da yaransu har da Mommah don tace tana so taje kabarin ‘yar uwarta da su Hajiya Mama da kaf zuri’arsu Hajja ce kawai bata jeba saboda ‘kafa da ta matsa mata.




Sam yaran garin basu ganeta ba, kuma garin yana yarda yake bai canja ba, canji d’aya ya samu yawancin mutanen cikinsa sun sake lallacewa, idan kaga sa’annin Shatu sai ka zata sun bawa shekaru talatin baya. Ganin har suka je gidan mai gari basu ganeta ba, yasa suna zama ta dubi tulin mutanen da suka biyosu, sun ga ‘yan birni. Maigari ya ce “Ina jinku bayin Allah bamu Shaide ku ba?” Shatu ta tintsire da dariya kafin ta ce “Nice fa Shatu mai ido a loko..” gaba d’aya wajen cikin al’ajabi suke kallonta, wata ‘kawarta Halime da sauri ta rungumeta tane cewa tun d’azu nake cewa Aradu wannan kamar Shatu.. murmushi Shatu tayi ba tare da taji ‘kyamarta ba itama ta rungumeta. Nan fa guri aka shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login