Showing 72001 words to 75000 words out of 117786 words
bari ya huce shi yake kawo rabon wani, zan tafi Qatar yau jirgin dare zan bi, mai kika ce kin Amince?” Da sauri ta ‘daga kai bayan ta runtse idanunta tana ji zuciyarta na wani irin bugu. Hawaye yana son zubo mata tayi saurin mayar dasu. Ya zama dole duk soyayyar da take yiwa Imran ta mayar dashi akan Ammar ko don ta saka halacci da halacci. Murmushi ya saki a hankali yace “Alhamdulillah nagode sosai, yau kuma na san zanyi kwanan farin cikin samun amsarki, buri na ya cika.” Ya zaro waya a aljihunsa sabuwa ‘kal ‘kirar Iphone 12 ya fara nuna mata yarda za tayi amfani da ita. Sannan ya ciro atm card ya bata “Na saka miki ku’di a ciki ina yi miki addu’ar samun nasara a karatunki and I really love you.” Da sauri ta rufe idanunta tana sake jaddada masa kalaman godiya.
Tana gani ya fice suna waving juna, ji yake tamkar ya dawo ya rungumeta. Yana tunanin yarda zai jure tsawon lokaci bai ganta ba.
———After One year( Bayan shekara ‘daya.......)
Cikin shekarar al’amura da dama sun faru wasu masu da’di wasu akasin haka.
Cikin masu da’din har da fara karatun Shatu a jami’a, da gogewarta sosai ta zama ‘yar gayu ta bugawa a jarida, duk inda ta wuce dole idanuwa su bi kanta. Fatarta ta murje sosai kamar larabawan Habasha ga diri cikakken hips da tsukakken ciki, uwa uba cikowar mamanta da suke cas dasu a cikin Riga. Hatta da idanunsa sun ‘kara haske tamkar madara.
Har wannan lokacin Imran bai zo ba, saboda al’amura sun caku’de masa, yana yawan kiran Wayoyinsu baya samunsu. Sai dai ya kira maigadi ya ce ya kaiwa Mommah. Sosai take receiving sai dai ko sau ‘daya bai ta’ba tambayar ‘ya’yansa da bai san da su ba. Haka nan ita ma bata ta’ba cewa mai yasa bai tambayesu ba. Addu’a ce dai bata fasa yin ta ba.
Sosai tunanin Shatu ya bun’kasa a zuciyarsa, wata irin soyayyarta ce mai zafi take huda dukka sassan jikinsa, burinsa ya gan ta, sai dai yana jin kunyar tunkarar Mommah da zancen, ya san abin da kunya. Don haka yake dauriyar shanye abin a cikin ransa. Yana niyyar ya samu hutu yaje yayi ya’ki a bashi matarsa.
Tuni asirin ya fara barin jikin sa an kai tajallin da yake zama ya dinga tuna moment ‘dinsu da Shatu.
Wani al’amari da Ba zai iya mantawa da shi ba. Zuciyarsa tana jin zafin sakin da yayi mata, ashe zai zo yayi da na sani, ashe da wannan halin da yake ciki har gwara ace ya zauna da ita yaji kunyar abokannasa, da duk wanda ma zai masa dariya.
——————-
Gabatowar bikin su Hafsa da Nahna ne ya sa Ammar dawowa Nigeria, don ya ro’ki alfarmar a ha’da da na shi da na Shatu.
Ranar da ya iso ya samu Mommah da maganar, tayi na’am da maganar sai dai tana tsoron zartar da hukunci kai tsaye tace ya bari zata samu Dahda da umarninsa zata yi aiki.
Da daddare kuwa ta Samu Dahda da zancen, ya dubi kyawawan jikokinsa da suke gefensa suna wasa tamkar ba ‘yan shekara ‘daya Ba, sun yi girma na ban mamaki kamar Akram ta sake bayyana sosai da mahaifinsa, haka nan macen da Shatu take kama sak da sak. Dudubniyarsu suke akan kakannasu da ‘ko’karin son ‘kwace alawar da yake ba su. Tunani ya shiga yi sosai kusan duk burin Shatu yanzu ya cika yarannan kuma dama bata saba dasu ba Mommah ce take hidima da su, ko anyi auren kuma Ba bata su za’ayi ba. Ga shi ta fara karatunta, tunda bikin su Hafsan sai nan da wata biyu zai iya amincewa ayi. Musamman da na Hisham za’a ha’da, shi yin wancan da yake ta dakon dawowarsa bai dawo ba balle ayi tunanin kome. Don haka direct yace “Shikkenan yayi shirye-shiryennasa ayi bikin dashi amma anan zai barta sai ta gama school.”
Farin ciki ya cika zuciyar Mommah burinta a karo na biyu zai cika. Da murna ta fita ta sanar da Ammar amincewar Dahdan.
Ammar yayi murna da farin cikin da har ba zan iya fasalta muku shi Ba. Yayi sujudusshukur ha’de da sake godiya ga Mommah sannan da sauri ya nufi ‘dakin Shatu.
—————————
Jirgin ‘karfe 8:00 na dare ne ya sauke su Hisham a airport. Ya kira wayar Imran ya sanar masa ya zo ya ‘dauke shi.
Farin ciki ya cika zuciyar Imran na ganin Hisham ya san ba mamaki ‘karshen matsalolinsa sun zo.
Tun a hanya Hisham yake son tambayar sa ko ya san da haihuwar yaransa amma ya kasa zuwa ya gansu tsawon shekara guda? Sai dai yaja bakinsa yayi shiru tunda Mommah ta garga’desu da yi masa zancen. Sai dai ya kalleshi yayi masa magana ta hanyar lislama “Ni kuwa Imran mai ya hanaka zuwa gida tsawon shekara da wani abin?” Imran jim yayi kafin yace “Ina son zuwa amma dai akwai dalilin da yasa ban je ‘din ba.” Hisham yayi tsaki “Wani dalili ne zai hanaka zuwa ganin iyayenka? Amma shikkenan ka san da cewa saura 2 months bikin mu da su Hafsa?” Da sauri Imran yace “Kai masha Allah, a kace zuwa Nigeria ya kama ni, ni I don’t know why? Duk wanda na kira daga family baya shiga, ko kaima ka san sai a dubai na Sameka? Wa ka samo mana?” Hisham cikin murmushi yace masa fine girl idan kaje zaka ganta.”
Suna isa gida suka tarar da Shaheedah zaune ta sake ramewa kamar mai cutar ‘kanjamau, don tsananin rama, ‘kirjinnan ya shafe kamar na tsofaffi. Cikin wani irin kallo Hisham yace “Lafiya Shaheedah me ya sameki haka?” Tsaki tayi ta ma ‘dauke kai kamar ba da ita yake ba. Imran yana dariya yace “Kai ma dai ka fa’da ance family planning ‘din da tayi ne ya sata wannan uwar ramar, kuma ta cire fa amma har yanzu bata ciko ba ji don Allah ni kaina bana son ko kallonta wallahi saboda ramar tayi yawa.” Cikin masifa Shaheedah ta kalleshi “Kaji da munafurcinka ina ce kai da kan ka kace baka son ‘kiba amma yanzu da kinibibi kace wani wai baka son kallona saboda rama.” Cikin bala’i shima ya kalleta “Da nace miki bana son ‘kiba ce miki nayi ki ‘kanjame ji be kifa bakomai a jikinki sai ‘kashi......” ai kuwa ta mi’ke “amma dai kasan ko lalacewar nayi a gidanka na lalace don ba haka ka aure ni Ba.” A zafafe shima yace “A ya na aureki?dama can duk ciko ne kada ki manta a daren farko na gane komai ciko kike yi, komai na jikin ki Ba ki da ‘kirar mace ko ka’dan komai ciko...” hawaye ne kawai ya fara zubar wa Shaheedah ganin cin mutuncin da yayi mata a gaban Hisham taji kamar ta ‘dora hannu a kai ta saka ihu....
Saduwar alheri ku yiwa ‘kanwata addu’a An yi mata c.s ta samu ‘karuwa Baby Boy. Nagode
Hajja ae gidan kamsh
Turaren wuta
Turaren gashi
Turaren kaya
Turaren wanka
Kulaccan
Kurkur oil
Humran
Kabbasa
and more
Whatsapp number 09120958937
In dai turare mai nagarta kuke nema to kun dace, ku nemeta domin ku kwashi gara’basa.
Me Zan Yi Da Ita?
Kai Alhamdulillah Masha Allah jiya sister ta ta sha addu’a am really appreciated wallahi. Jazakumullah bil jannatil Aaliyah.
ME ZAN YI DA ITA?
40....
Da wata irin zabura ta mi’ke cikin matsanancin ‘bacin rai tace “Wallahi Imran ka yi da ‘yar halak you will pay for it.” Daga haka ta shige ‘dakin ta cikin tashin hankali, tabbas dole ta kira Antyn ta ta gaya mata kalar iskancin da Imran ya tsiro da shi. Alamar duk wani shiri na su ya ruguje ko yana daf da rugujewa.
Imran tsaki yayi yana kaolin Hisham da duk ransa ya ‘baci, da abinda ya aikata. Zai yi magana Hisham ya dakatar dashi. “Am highly disappointed wallahi au Imran gaskiya ban ji da’din abinda ka aikata ba da alama yarinyar nan ba ta jin da’din zama da Kai, me yasa ka canja ne completely kamar ba Imran ‘din da na sani ba?” Tsaki Imran yaja yana zama saman kujera kansa kawai ya dafe yana murza goshinsa, kafin ya ‘dago idanunsa sun burkice sunyi jajur “Ba zaka gane ba Hisham gaba ‘daya yarinyar nan ta fice min a Zuciya, ga takaici da dana sani da nake na sakin waccen Yarinyar.” Da sauri Hisham ya ware ido “What! Tsaya wai wa kake nufi? Kada kace min Shatun Mommah?” Direct Imran ya amsa masa “Yes exactly ko ina da wacce na saka ne bayanta?” Wata dariya ce ta ‘kwacewa Hisham “Ashe kuwa ka sha giyar wake in dai Shatu ce, kada ka manta Shatu fa Fulanin Daji da kace ko an ‘daura maka ita a ‘kafa sai ka kunce, yarinyar da Mommah ta za’ba maka ka saketa within three days da aure ita kake gaya min kana da na sanin sakinta? To me zaka yi da ita? Kada kace min dawo da ita zaka yi domin kuwa tayi maka nisa tuni ta yi aure ta haifi twins.” Wata irin zabura Imran yayi hankalinsa a tashe ya mi’ke yana kallon Hisham, kafin ya ji wani jiri na ‘dibansa “Kace min wasa kake Hisham? Please!” Hisham yayi tsaki akan me zan yi mk ‘karya gaskiya na gaya maka.”
Daga haka ya zauna yana kallonsa “Ba abinci ne a Gidannan? Naga tun da na shigo ko ruwa baka bani ba..” Imran bai ko kalleshi ba ya zauna dafe da kansa. Zuciyarsa take wani irin tu’ku’ki tamkar ya mutu, da gaske ne Shatu tayi aure? Shatun da yake da niyyar mayar da aurensu, Shatun da ta mamaye duk wani gurbi da tunani na zuciyarsa, Shatunsa da yake tuno da duk wasu ni’imominta da Allah ya bata a lokacin da ya tara da ita, itace wani banza can ya aureta har ya ‘dan’dani ni’imarta yaji taushi da santsin fatarta, yaji za’kin ba’kinta ya ‘dan’dani da’di da gar’dinta har da albarkar zuria a tsakaninsu. Da sauri ya hau yamutsa sumar kansa yana fa’din No No No! Da ‘karfin sa. Hisham tsayawa yayi cak yana kallonsa tsananin mamakin lamarin yake yi. Kafin ya ja tsaki yace “Tunda baka yarda ba kaje Nigeria ‘din ka gani. Ai gani ya kori ji, kuma idan babu Abinci a gidannan ni zan kama gaba na.” Mi’kewa kawai Imran yayi hannayensa zube a aljihu ya hau struggling a parlourn kafin ya juyo cikin kyakykyawan kallo ya tsare Hisham da idanunsa cikin zafin rai yace “Wani mai gangancin ne ya aure min mata?” Tsaki Hisham ya ja kfin yace “Kayi Istigfari ka daina kiran matar wani da sunan matarka, mutumin da ya aureta har da albarkacin zuri’a tashi guda twins ta haifo masa alamar an sha soyayya kafin a haifo su don sosai yaron yayi kama da ubansa..” flower verse ‘din dake gefensa yayi cilli da ita ji kake wani taratsatsa bai damu ba ya tashi ya bi ta cikin glasses ‘din ya isa inda Hisham yake. Wuyansa ya da’kuma a wani irin yanayi ya furta “Don’t tell me rubbish, ya ishe ni Hisham, ka gaya min sunansa nace kawai!” Hisham ya ta’be baki ha’de da mi’kewa yace “Sunansa Muhammad, malam zaka bani abinci ko na kama gabana na gaji da wa’dannan silly Questions ‘din naka kana nufin don ka saketa sai a rasa mai aurenta duk da tsananin kyan ta?” Idanunsa akan jinin ya ke masa magana “Idan ban da hauka ji yarda ka jiwa kanka ciwuka tun ma ba kayi arba da yarda ta goge ta zama kyakykyawa ba, da kuma santala-santalan yaranta ina ji da sai zuciyarka ta buga don tsananin takaici, ga shi wanda ta aura ‘din yana tsananin sonta ya kuma fi ka komai ku’di kyau uwa uba dukiya......” da ‘karfi Imran yace “Hisham! I’m tired of you nonsense zo ka fice min a gida kuma bikin naku ma ba zan zo ba, sai me don tayi aure ina ce dai ba gwauro ka ganni ba da matata.” Hisham yana dariya yace “Fankon? Ko ba kai da bakinka kace duk ciko bane yanzu ne zaka kirata mata? Gida kuma kar kazo amma ka sani ko yanzu ka mutu, da kyar rahmar ubangiji ta sameka saboda rashin biyayya ga iyaye, Na barka lafiya dama sada zumunci nazo muyi tunda kuwa kayi min korar kare sai nace saduwar alheri.” Daga haka yayi saurin ficewa daga gidan saboda dariyar da take shirin fallasa shi. Sai da ya bar harabar gidan sannan ya shiga tuntsira dariya tamkar mahaukaci sabon Kamu.
———————————-
Tana kuka sosai ta shiga kiran mahaifiyarta, zuciyarta tamkar ta tsinke don tsananin ‘bacin rai. Da kyar ta samu kiran yayi connecting, Antyn ta ta ta ‘daga wayar “Shaheedah ya aka yi?” Fashewa da kuka Shaheedah tayi kuka mai cin rai da saka tashin hankali a zuciyar mai sauraro “Anty wallahi na mutu, yanzu Imran ya tsane ni ya tsani surar jikina tsana mafi muni....” Tsaki zainab tayi kafin tace “To ba dole ya juya miki baya ba Shaheedah, kin zauna kin ‘kanjame ke ‘yan magungunannan na ‘karin ‘kiba da hips ba shan su kike ba balle ki ciko ki yi dumimi irin na ‘ya’ya mata, me nace miki rannan da kika turo min pic ‘dinki ban ce miki ki nemi magani ba kin zauna kin ‘kanjame kin bushe kin lalace wai ke miji baya son ‘kiba, sai ranar da ya auro mai ‘kibar sannan zaki san dama yaudararki yake.” Kuka ta sake fashewa, sam bata son jin kalmar kishiya. “Ba zaki min shiru ba ki saurari abinda zance miki? Ko kin ji nace kishiyar za’a yi miki? Ki san yarda kika yi kika dawo Nigeria zan baki supplement Na ‘karin ‘kiba kuma ki saki jiki ki dinga cin fats ko kya tayar da koma’dar da ta kwanta, duk namijin da kika ji yace baya son mace mai ‘kiba ‘karya yake bai samu bane, sai kin murje jikinki sannan za mu san abin yi.” Tayi shiru tana jinjina lamarin komawa gidan a zuciyarta, ba don komai ba sai don bata son ha’duwar Imran da Shatu, don haka tace “To amma Anty kina ganin dawowa gidan ba matsala? Bana son Habibi ya ha’du da Shatu wallahi.” Antyn ta zabga tsaki “Ke kike ta wata Shatu tun taushe muka yi musu farra’ku ko kin ga ko zancenta yana yi? Ina ji ma Ammar ne zai aureta haka dai Manga yace ban ce kuma ki sanar da Imran ba kin ji na gaya miki. Kuma kin je kin cire abin hannunnan ko yana nan ma’kale a hannunki?” Ta ja ajiyar zuciya kafin tace “Tun yaushe na cire nima yanzu buri na ai na haihun, tun da naga kamar yana son yara, har yanzu fa bai sanma ta haihu ba fa.” Anty ta tuntsire da dariya “Ai dabararki tayi Shaheedah ban ta’ba zata ni kika biyo ba sai da kika aikata hakan naji da’di sosai, ko da takaicin wannan aka barsu ai ya ishe su, ka haihu uban yara ya’ki zuwa ganinsu kuma ko hoto bai ce a tura masa ba, ai kin sha’ka musu aikinki yayi kyau wallahi.” Haka dai suka yi sallama suna sake ha’da ‘kulle-‘kullensu da makircin su ubangiji ka raba mu da sharrin zuciya.
—————————-
‘Kwala kiran da Mommah take mata ne ya sata fitowa da mugun sauri, hannunta ‘dauke da Spoon da take aiki dashi a kitchen. A hanzarce ta isa ‘dakin Mommah don jin kiran kamar ba na lafiya ba.
A tsaye ta samu Mommah Ikram a bayanta da alama barci takeyi don ta tashi da ‘dan Zazza’bi. Hawayen da ta gani a fuskar Mommahn yasa gabanta matu’kar fa’duwa ta isa da sauri tana tambayar “Lafiya?” Mommah ta runtse ido tace “Shatu sai dai muyi ha’kuri Dada tazo sa’i lokaci yayi yanzu Hajiya Mama take gaya min.” Hawaye ne sosai ya mamaye fuskar Shatu tace “Innalillahi wa innailaihirrajiuna! Ashe ha’duwarmu da ita ta ‘karshe kenan da muka je kai mata yara.” Mommah ta saki ajiyar zuciya tace “Eeh, Baiwar Allah kenan Dada mai matu’kar ri’ko da addini, mai son zumunci da fa’dar gaskiya komai ‘dacinta Ubangiji Allah ya gafarta miki Dada.” Hawaye ya sake wanke idanunta tana tuna drammerr da suka sha lokacin da suka kai mata su Ikeey, ta dinga rungumesu tana cewa “Ubanku yayi asara yana ma kan yi ‘dan banza mai idon gwal ai zai zo ya sameni ne, shine ya ‘dirkawa ‘yar ciki har cikin ‘yan biyu sannan ya saketa duk don kada ayi masa dariya bayan ga abin dariyar nan ya bari tun da gashi nan wannan mai faskareren kan shi ya ‘dauko, da an yi magana sai yace me zai yi da ita? Yau dai ga abinda zai yi da ita nan ya fito ‘dan jakar Uba.”
Hawaye ya sake zubowa Mommah ta share su, tace “Allahumma gafir zunubiha jami’an. Maza Shatu kije ki duba girkin ki, ba mu da lokaci jirgin asuba zamu bi insha Allah,idan mun sauka a
Bauchi sai wani ya tare mu a mota.
Da sauri Shatu ta juya dai-dai lokacin da taji Knocking tana bu’dewa taga mai gadi, waya ya mi’ka mata yace “Don Allah kaiwa Hajiya Chairman ne ke magana.” Ta shige da sauri takaiwa Mommah.
Mommah ta san wayar waye, don haka ta ‘daga bayan gaisuwa ta sanar dashi mutuwar Dada. Salati ya saka da wayar a kunnensa, kafin ya dawo daga shock ‘din Mommah ta katse wayar.
Yana ta Hello! Yaji ‘dif hakan yasa ya ri’ke wayar zuciyarsa cike da wani irin tsoro ya shiga kwararowa Dada addu’oi a zuciyarsa. Kafin da azama ya fara booking flight ta internet. Ya shiga kiran wayar Hisham da kamar ba zai ‘dauka ba sai kuma ya ‘dauka a zafafe yace “Ka gama kora ta daga gidanka meye kuma na kira Na?” Imran yace “Allah ya baka ha’kuri ni mutuwar Dada na bugo na sanar maka.” Hisham ya ja salati shima kafin ya ri’ke kansa ba ‘dan ka’danba yaji mutuwar Dada kakarsa. Imran ne ya gaji da shirun yace “Kana ina ne?” “Ina ruwanka da inda nake? Ina airport gida zan koma yanzu haka ina cikin flight.” Imran yace “Shikkenan ma ha’du gobe a Nigeria nima na yi booking gobe zamu taho, and thanks for the visit kayi ha’kuri da rashin kyauta ta maka da ban yi ba temper tace ta hau da yawa. Ni kaina I don’t know what