Showing 24001 words to 27000 words out of 117786 words

Chapter 9 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

457

min da magana baka neman albarkata baka damu da farincikina ba ko da yaushe sai ‘bacin raina nagode kaje ka yi aurenka kaje mutanen da kake tunanin zasu baka farin ciki su baka fiye da wanda ni zan baka Allah ya sanya albarka a aurennaka but put this in your mind bani ba ‘yan uwana a bikinka ba zamu zauna muga ‘baci rai ba.” Daga haka ta mi’ke ta shige d’aki jikin Imran ne yayi sanyi ji yake kamar yace ya fasa baya son ‘bacin ran mahifiyarsa bai san me yasa zuciyarsa ta kasa ha’kura da shaheedah ba, tsawon lokaci yana zaune kafin shatu ta fito tana ‘yar wa’karta ta “uwa tana da girma mahaifiya tai mini komai” da sauri ya kalleta gani yake kamar da shi take da shi d’in kuwa shatu take amma ya kasa ta’buka komai yana juya kalaman wa’kar shatu a zuciyarsa.


Ko da ta fita bata zame ko ina ba sai wajen mai gadi, da murmushi y tareta don yana son shatu musamman yarda take girmamashi ga kyauta akai akai “uwata ta kaina ya aka yi?” Ya fad’a yana mata murumushi shatu tayi ‘kasa da muryarta “Baba taimako zaka yi mi please amma bana son kowa ya sani” ya girgiza kai “ shatu danger yau kuma wa ya takaloki?” Dariya tayi kafin murya can ‘kasa tace “wasu ‘kadangarun bariki zanyi magani ga dubu biyu ‘kai’kayi zaka siyo min don Allah” Baba ya ware ido “Aa fa shatu’kai’kayi kuma mai zaki yi dashi?” Ta had’e rai idan ba zaka taimakeni ba shikkenan bara na tafi” ganin tayi fushi yasa yace “zo uwata zan taimakeki ai ba zan’ki mai taimakona ba” ta mi’ka masa kud’in tana dariya.
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-16


ELEGANT ONLINE WRITERS.....


Baba murmushi ya saki “ko waye ya shiga gonar uwata? Ko ma dai waye ya jawowa kansa yau” Baba mai gadi ya furta a hankali yana jinjina girman al’amarin shatun.


Tun yamma ta dinga zagaye gidan har ta tabbatar da windown ko wane d’aki sannan hankalinta ya kwanta taje ta ‘boye ‘kai’kayinta a ma’ajiyar da ta tabbatar babu mai ganinsa,sannan ta cigaba da harkokinta tamkar babu komai a zuciyarta.


Tana general kitchen ita da masu aikin gidan amaryar Imran ta shigo sai wani iyayi take da rawar ‘kafa.shatu ta zabgawa harara kafin ta bud’e fridge tana duban masu aiki “Imran yace kuyi masa abinci ne?” Ta tambayesu cikin kallon raini. Saratu ta girgiza kai “ai dama bamu muke masa abinci ba daniel ne kuma tun wancan satin ma ya dakatar da daniel ko ruwan tea zai sha naga a kitchen d’in mommah yake dafawa da kansa.” Kallon one by one tayi musu tana yatsine fuska “Ba dole ba,ba dole ya daina cin abincin gidannan ba gida duk an tara gayyar ‘kazamai dama zuwa nayi inyi warning d’inku kada wacce ta sake yi masa abinci ni da kaina zan dinga yiwa mijina abinci bana son ya dinga cin na kowani ‘kazami.” Shatu tsayawa tayi tana kallonta sai kuma ta tuntsire da dariya ta kalli saratu tace “saratu bani aron muciyarku akwai abinda zan gwada da ita” ta fad’a tana yiwa shaheedah kallon sama da ‘kasa ita bata ga abinda Imran ya gani a jikin wannan ba ‘kafafu kamar sillan kara. Shaheedah ranta yayi ‘kololuwar ‘baci da sauri ta cafko shatu ta fara wanketa da mari shatu ta daka tsalle ta rama sannan ta shiga ‘kar’kashinta ta tad’eta ta fad’i hakan yasa shaheedah ‘kwalla ‘kara ina shatu bata saurara mata ba ta hau kanta ta shiga lugude a ruwan cikinta. Masu aiki suna gefe sai dariya suke sun ‘ki rabawa saratu a zuciyarta fad’i take dai-dai kenan shegiya mai girman kan tsiya. Ihun shaheedah ne ya karad’e gidan hakan yasa duk mutanen gidan suka yiyo general kitchen d’in ban da mommah da take wanka. Da sauri su kayi kan shatu suka fara jibgarta tun tana ihu har muryarta ta dashe gefen bakinta da goshinta ya kumbura suntum. Ihun shatu ne ya fito da momma daga toilet riga kawai ta zira ta fito a guje dai-dai lokacin Imran ya dawo kenan shima ya juyo ihun yayi yo cikin gidan da sauri yabi bayan mommah. Momma ta tarar dasu har a lokacin dukanta suke sun mata jina-jina su saratu sai ihu suke suna fad’in zasu kasheta. Da sauri momma tayi kukan kura ta ‘kwaceta bayan ta dubesu ranta a ‘bace tace “mai tayi muku? Mai tayi muku zaku yi mata wannan hukuncin?””an daketa d’in ko zaki rama mata ne ita har ta isa ta doki shaheedah ta kwana lafiya wacece ita a gidan?”muryar tsagera hameedah ce mai wannan tsaurin idon tana fad’a tana yiwa mommahn wani banzan kallo. Imran kansa sai da yayi mamaki Ammar kuwa da ya shigo yanzu yaji furucin hameedah akan mahaifiyarsa bai san sanda ya waska mata mari ba. baki bud’e kowa yake kallonsa babbarsu falmata tace “kana hauka ne Ammar ‘kanwar ubanka ka Mara?” Ita dinma wani kallon banza yayi mata yace “‘kanwar ubana tafi uwata ne?nawa hameedan take ina ce shakara biyu ta bani shekara nawa tawa uwar ta bata da zata gaya mata magana?” Yana fad’in haka yaja hannun shatu da mommah suka fice daga kitchen d’in bayan yayiwa Imran kallon banza,yana tsaye ana zagin mahaifiyarsa ya kasa d’aukan mataki.

A bakin gado ya zaunar da mommah idanunta kawai yana zubar da hawaye, hakan ya ‘kara tunzira zuciyarsa ya mi’ke a zuciye zai fita mommah tayi saurin ri’ke hannunsa tana girgiza kai tace “kada kaje Ammar hakan ma da kayi nagode maka ko bakomai yau na san na haihu ka ‘kwatar min ‘yancina Allah yayi maka albarka d’auki shatu ka kaita clinic ayi mata dressing ciwukannan.” Kallonsa ya mayar kan shatun dai-dai lokacin da Imran ya turo ‘kofar ya shigo, murya can ‘kasa yayi sallama, Ammar jan hannun shatu kawai yayi suka fita sam baya son ma ganin d’an uwannasa gani yake kamar an canja musu shi Imran mai zuciya Imran mai tsananin son mommah mai gudun ‘bacin ranta, yau shine ya zama haka a gabansa ake cin mutuncin uwarsa ya kasa magana ya kasa kata’bus.Yana kallo suka fice ya bisu da kallo da ajiyar zuciya, sannan ya samu gefen mommah ya zauna, kansa ya d’ora a kafad’arsa wasu ‘kwalla da bai san na menene ba suna ‘ko’karin zubo masa, ya kama hannun mommah murya can ‘kasa furucin “Am sorry mommah” ya fito daga bakinsa, bata kalleshi ba illa d’auke kai da tayi “kiyi ha’kuri ita ma yarinyar bata kyauta ba na tambayi masu aiki sun gaya min duk yarda aka yi ita ta kwatantata da muciya saboda raini ita kuma tayi saurin hannu ta mareta bata san wannan yarinyar ba ‘kyaleta za tayi ba, ko ta’kyaleta a lokacin sai ta nemo abinda zata rama gaba kad’an please momma kiyi ha’kuri amma kiyi mata fad’a” wani kallo mommah tayi masa sannan ta zare hannunta “wacece yarinyar sunanta ne baka sani ba ko kuwa canja mata suna kayi Imran anya kuwa jininka ce fa ita,duk duniya ku ya kamata ku nuna mata gata tunda bata da wasu sha’ki’kan y’an uwa kazo kana ce min wani bata kyauta ba, rashin kyautawar mai tayi? ‘Dirka-d’irkan mata su zauna suyi mata jina-jina sannan ace wani bata kyauta ba to ba ha’kura nayi ba wallahi wannan karan sunyi da y’ar halak ni kad’ai kuma Na san abinda zan musu tashi ka bani wuri mai kayan haushi kawai ka zo ka cika ni da wani zancen banza da wofi zanyi maganinku ne gaba d’aya daga kai har dangin ubannaka sai na shayar daku mamaki.” Imran zuba mata ido kawai yayi ya ma kasa magana sam ba ya son hayaniya d’abi’ar dahda tsaf ya d’auko shi yasa yaji har kansa ya fara ciwo. Jan pillow yayi kawai ya kwanta a gadon mommahn ya ri’ke kansa da yake d’an sara masa.
Mommah ta dubeshi kawai tayi tsaki ta mi’ke ta bar masa bedroom d’in tana cigaba da ‘kananan maganganunta.



Koda dahda ya dawo duk da girkinta ne ranar ko ‘keyarta bai gani ba, tana part d’inta ta tasa shatu a gaba tana lalla’bata ta sha peppe soup ko kad’an ne kafin tayi barci. Amma shatu fir ta’ki yau zuciyarta a hassale take da ‘bacin rai sun riga sun kai zuciyarta ‘kololuwa a ‘bacin rai duk ‘ko’karin mommah da Ammar haka suka gaji suka ‘kyaleta suka zuba mata ido sai ajiyar zuciya take saukewa tana hura hanci.



Gefe d’aya kuwa amaryar dahda zainab ta saka shi a gaba tana gaya masa ‘karya da gaskiya a gaban y’an uwansa ta tattara lefin gaba d’aya ta d’orashi kan baiwar Allah mommah, Dahda kawai jinsu yake yana girgiza kai ya san abinda matarsa zata yi ya san wanda kuma ko da kuskure ba zata aikata ba.Da ya gaji da ji mi’kewa yayi ya shige part d’insa ransa a ‘bace shi yasa ko da wasa baya son danginsa su ziyarceshi. Sai da yayi wanka sannan ya fara jera kiran mommah a waya amma ta’ki picking,gaba d’aya jinsa yake kamar maraya ta riga ta’bata shi ta sangarta shi baya iya ta’buka komai ba tare da taimakonta shi wannan auren matsala babba Hajja ta gangamo masa sam a tsarinsa bashi da niyyar ‘kara aure. Ganin ta’ki picking calls d’insa hakan ya sashi mi’kewa ya dangana ga part d’inta.


A zaune ya sameta kan sallaya ta d’ora kanta a saman gado tana jan carbi fuskarta da alamar ‘bacin rai sosai. A hankali ya taka wajenta ya zauna a gefen gadon, motsinsa ne ya sata saurin d’ago da kai su kayi four eyes lallausan murmushi ya sakar mata yana dafa kanta yace “Haba Dija na me ya faru? Yau ko ‘yar sannu da zuwan ma babu.” Still fuskarta a d’aure ta mi’ke ta fara nad’e sallay sai kuma hawaye sharr ya biyo fuskarta ta dur’kushe a gabansa ta kife fuskarta a cinyarsa ta saki kuka, kuka mai cin rai da tunda yake bai ta’ba ganin dijansa nayi ba. hankalinsa ne ya tashi da sauri ya dafa kanta sannan ya mi’ke tsaye ya d’agata rungume ta yayi sosai yana fad’in “yi shiru ki gaya min menene me suka yi miki?” A hankali yake fad’a mata cikin cool voice. Dijah kukan take sosai kafin ya fara wiping tears d’inta a cikin wani salo na matu’kar soyayya da son cooling zuciyarta. Shi kad’ai yasan yarda kukan dijan yake d’aga masa hankali “Don Allah Dija kiyi shiru ki fad’a min wai menene? Bana son kanki yayi ciwo please.” Ganin damuwa ‘karara a fuskarsa ya sa ta tsagaita kukan nata ta fara bashi labari, tana gamawa ta d’ora da fad’in “don haka dahda na gaji a wannan karan dole ne a san abin yi ko Imran ya fasa auren can da aka ‘kir’kireshi don a wula’kanta ni ko kuma ya had’a da za’bina ko kuma wallahi na bar gidannan don ba zan zauna ba’kin ciki ya kamani ba zuciya ta ta buga Allah ne kad’ai yarda nake jin ciwo a zuciyata kullum matsalata dangin miji sun saka kayi aure ka auri ‘yar uwarsu ban ce komai ba ko bakomai hajja tana da iko da kai to nima a barni nayi iko da nawa d’an idan kuma ba haka ba na bar maka gidan ka zauna da duk wacce suke so ka aura,amma dole wannan karan nima Imran yabi umarnina a matsayina na uwarsa da ta kawosho duniya.” ‘Kuri manga yayi mata da ido ganin yarda take masifa wai dijan sa ce haka dijan sa mai ha’kuri mai sanyin hali ita masifar danginsa yasa ta juye ta koma masa mai fad’a, sam bai ga lefinta ba ya tabbata an kaita ma’kura dama ance shi mai ha’kuri bai iya fushi ba a duk sanda aka ‘kureshi dole yayi mata abinda take so ko don ya faranta mata zuciyarta ta sauka daga fushin da take idan ba haka ba yana tsoron yana tsoron ranar da zata fara mayar da martani ga hajja, ya san tabbas abin ba zai yi kyau ba.Hannunta ya kama yana matsawa a hankali,murya ‘kasa-‘kasa yace “It’s enough ‘yan mata na dijan manga gaya min mai kike so ayi?” Murmushi ta saki zuciyarta na rage zafin da take mata, ta haka manga yake samo lagonta a duk sanda tayi fushi shi yasa basa dogon fad’a suke shiryawa. Ta gyara zamanta a jikinsa tana masa kallon cikin ido “in dai manga na yana son ganin farin cikina to ya amince da ‘kudirina ta haka zaka’kwato min ‘yancina a wajen ‘yan uwanka so nake ka aurawa Imran shatu ya had’asu su biyu ta haka kawai zan nuna musu power ta nima na dasa musu ba’kin cikin da suka dasa min ba dai shatu bace ba sa so to ita zata zama kishiyar d’iyar tasu ‘yar so.” Kallonta yake cikin nazarin anya tana cikin sense d’inta idan ban da haka wacce shatun? Wannan ‘yar ‘kwailar bayan haka ta san ko sama da ‘kasa zata had’e Imran ba zai kar’bi shatu matsayin mata ba amma bari ya tambayeta wacce shatun take nufi? “Wai wacce shatun kike nufi dijah?” Ya fad’a yana sake ‘kure ta da kallo, dariya ta saki tace”au muna da wata shatun ne bayan ta gidan nan shatu na nake nufi shatu da suka yiwa duka saboda ta ta’ba d’iyar gold to ita nake nufi” girgiza kai manga yayi shima yana murmushin yace “amma dai wasa kike ko? Idan ban da haka wannan yarinyar da bata wuce 14 ba za’a yiwa aure banda haka ma kin san halin d’anki ba yarda za’ayi ya amince da wannan batun.” Momma ta marairaice fuska tana kwanciya a kafad’arsa tace “please dahda don’t say No kai kad’ai ne last hope d’ina kaga dai da kayi aure ban ce maka komai nayi ha’kuri duk da zuciyata na hurting sosai kullum a haka nake kwana amma na san dole ne kabi umarnin hajja indai kana son ganin daidai please ka cika min burina don Allah ka amince.” Tausayinta ne ya kamashi ya fara shafa bayanta amma shifa yana tsoron lamarinnan ya san halin Imran da ba’kar zuciya ban da haka ma yarinyar is too young “
Dijah ba fa wai na’ki bane ‘kan’kantar shatu nake dubawa bana son ayi abin da za’a tauye mata ha’k’ki matsayinta na marainiya kada mu cuceta ta yama zata iya kishi da shaheedah apart from that ma ta ya kike zaton Imran zai amince da auran shatu?” Murya can ‘kasa tace “shi yasa bana so ka fad’a masa ya zama sirri tsakanina da kai so nake sai dai suji an d’aura da shatu kawai ko bakomai nima power ta ta uwa ta fito Ba kuma tarewa za tayi ba har sai ta gama school, shi kuma Imran ka barni dashi na san ta yarda zan ‘bullo masa shekaru kuwa ba abin ji bane duk da ba tarewa za tayi ba mutanen da ma a shekarunta tuni sun jima a d’aki. Ni dai abinda nake so da kai kawai ya sirri tsakanina da kai nima anan ko ‘yan uwana ba zan gayawa ba insha Allah sai dai suji” d’aga mata kai yayi “zan cika miki burinki dija na ko don ki cigaba da kasance min sanyin idaniya ta yanzu tashi muje ki bani abinci I have gists for you” ya fad’a yana kashe mata ido d’aya. Shi yasa kullum manga yake narka mata da zuciyarta take kuma kishinsa don ya san salo salo na kama zuciyar mace.






To fa masu karatu ya zata kaya ne kun amince ayi auren ko a barshi tabbas dai akwai rigima kwantacciya.😂Imran mijin shatu ko ya zata kasance? Ku biyo ni next month insha Allah na tafi hutu typing wahala

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-17


ELEGANT ONLINE WRITERS.....



Cikin daren kamar an mintsineta ta mi’ke duk da jikinta da yake ciwo hakan ba zai hanata aiwatar da ‘kudirinta ba a karo na barkatai ta sake kaiwa dogon mudubinnata ziyara,shatu ta sake ‘karewa ciwuwwukan da suka ji mata kallo cikin matsanancin ‘bacin rai ta girgiza kai muryarta a dashe tace wallahi ba zaku kwana lafiya ba ayau yarda kuka saka ni ‘bacin rai sai na hanawa idanunku barci. Ta isa inda ta ajiye ‘kullin ‘kai’kayinta tana murmushi “yau akwai rawar asosa casss a gidannan” sai kuma ta tuntsire da dariya murya a ciki tace “mu zuba ni daku shege ka fasa” ko takalmi bata saka ba don kada mommah taji takunta ta fice daga part d’in mommahn cikin sand’a.

Duk windows d’in bedrooms d’insu ta dinga zugewa a hankali tana hura musu sai kuma aka ci sa’a duka gadajennasu a jikin windows suke sai da ta taka abu sannan tsawonta ya kai.tana gama hura musu tayi saurin juyawa ta shige general parlour karaf suka ci karo da Imran zai shiga sashensa bayan ya gama aiyukan da zaiyi a system d’insa a parlourn,da sauri ya kai dubansa kanta har zaiyi magana sai kuma ya ta’be baki ya shige part d’insu, shi yanzu tsoronta yake ji sosai ba ya son ya fad’a tarkonta. Shatu tayi murmushi kawai ta shige part d’in mommah tana jira a fara rawar asosa.
Tana zaune kuwa a gefen gadonta ta fara jiyo iface-iface a general parlour ihu sosai Ta jiyo hakan ya sata fitowa daga d’akinta sai taga mommah ma da dahda sun fito daga d’akin mommah. Momma da sauri tace “koma ciki shatu ke da baki da lafiya bari muje muga menene” bata so hakan ba amma hakan ta zauna kan kujera.bayan dahda ya kalleta yayi mata alamar t zauna.
A parlour suka samesu gaba d’aya sai ihu suke har da masu ludaya da
Cokula suna sosawa. Shaheeda kuwa daga ita sai guntuwar vest sai ihu take tana kiran Imran ya taimaka mata shi kuwa yana tsaye yana mamakin mai ya samesu tabbas ya tabbata shatu ce tayi musu ramuwar gayya saura ‘kiris ya saki dariya a karo na farko da lamarin yarinyar ya daina bashi haushi sai dariya, yarinya sai shed’ananci kamar zuriar shaid’anu.Dahda da mommah fad’i suke “subhanallahi mai ya faru?” ‘Kannen dahda sai cewa suke ya taimaka musu jikinsu kuwa yayi rud’u-rud’u salati dahda yasa yace suje su suturce jikinsu su tafi asibiti.amma ina lamarin ya girmama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login