Showing 117001 words to 117786 words out of 117786 words

Chapter 40 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

476

murna.


Maigari da kansa ya ce “Su shiga gidansa, Shatu tana mi’kewa ta sake kallon yara da mutanen gurin tace “Ku tsokaneni mana, Mai idonta a loko mujiya...” dariya suka saka ana sake tuno balain Shatu a duk lokacin da akayi mata wannan wa’kar.


Sai da suka huta a gidan maigari sannan suka d’unguma gidansu Shatu. Ranar kam kaf su Mommah ba wanda bai yi kuka ba har Imran kowa yana mamakin yarda suka iya rayuwa wa wannan gidan, kayan Innaji suna nan ba abinda aka ta’ba duk wannan tsawon shekarun kasancewr mutanen ‘kauye akwai amana.

Bayan gama koke-koken suka tafi kabarin Innaji suka dingayi mata addu’a Hajiya Mama kuka take sosai tana sake tuno Maryamanta yarinya mai sanyin hali da biyayya, tabbas ta yarda ‘kaddarar Maryamace tazo a haka. A hankali ta dinga shafa ‘kasar kabarin tana fad’in Allah yaji ‘kanki Maryama.

Sai dare suka bar gidan Innaji bayan sun tattara kayayyakinta masu mahimmanci, gidan Imran yayi Sha’awar gina masallachi da shi mai girma, shi kuma gidan su Moddibo da yake yana da girma za suyi makaranta da asibiti ko da ‘karamine. Alhaji Baba da su Hisham su kuma suka ce za suyi wannan.

Kashegari mutanen garin suna samun labarin suka dinga zuwa suna yi musu godiya don gaskiya sunji dad’i sosai don kuwa ba su da duk wad’annan abubuwan a garin sai kame-Kame. Har inda motar da abokin Ammar yayi parking ya kawosu kasancewarsa mazaunin Nigerr yasa da suka sauka a airport suka kira shi. Shi yazo yayi musu jagora har cikin ‘kauyen bayan Shatu ta
Gaya masa sunan garin. Suka raka su suna mata wa’kar tana murmushi don ita tace su yi mata tana so. Suka tafi tana d’aga musu hannu idanunta fal hawaye tana tuna ranar da suka bar garin da Gwaggoji.


———————-

Wannan karan cikinta tun yana wata biyar aka sanar da ita twins ne kuma duk maza murna wajen ahalinnnan ba magana, amma Imran ya ce sam ba Za’a yi mata aiki a Nigeria ba don haka direct suka wuce Egypt da Mommah sai Hajja da zata ga Doctor da su Ikram da Ayda kasancewar ana hutu.


Suna zuwa da two weeks aka yi mata cs yaranta kyawawa duk maza, a take Imran ya d’aga su yana murmushi yace an samu Alhaji Baba da Dahda, Aalim da Aarif yayi musu la’kabi. Yana murmushi ya kalli Shatu Allah yayi miki albarka yasa nexe year by now ki haifo min twins mata.... Shatu ta zaro ido kafin ta turo baki tana kallon Mommah ta ce “Kiyi masa magana ni a gidan Momma ma zan tare sai na yi shekara...” Mommah murmushi tayi ta ce “Ba dani ba salon ki dinga bin dare kina tafiya wajen mijinki, ku je can gidanku ku ci soyayyar ku.” Hajja ta harari Imran ta ce “Rasa kunya ba ai gashi nan sai d’ura mata cikin ‘yan biyu yake sabida ba’kar jarabarsa...” Shatu ji tayi kamar ta lume cikin ‘kasa duk kunya ta isheta. Imran kuwa ba abinda ya dameshi ya kai mata peck a kumatu had’e da fad’in “Ba su san sirrin da ni’ima da yake jikin matata bane da ba suga laifina ba da na zama superglue.” Da sauri ta kalli su Mommah taji ko hankalinsu na wajen, tayi saurin runtse ido bayan taga murmushi a fuskar Mommahn alamar kaf zancen Imran ya shiga kunnenta.

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************



Alhamdulillah anan na kawo ‘karshen littafinnan na Me Zan yi da ita? Ina ro’kon afuwa ga duk wanda ba sa’bawa a cikin rubutuna bisa kuskure ko ajizanci na d’an adam.


Godiya ta gareku masoya da kuka yi jumurin karanta littafinnan har ‘karshensa musamman ‘yan group d’in Nashe Vip group da suka yi ho’b’basa wajen biyan kud’insu don karanta littafina, bani da bakin da zan gode muku sai dai nace Allah ya saka da mafificiyar Aljannah.



Godiyata ga jinjina ga ‘yan ‘kungiyar Elegant gaba d’ayanta ina alfahari da kasancewata a cikin su, ina godiya Nimcyluv da jajircewa da kika yi wajen dawo dani rubutu online thanks so much....


Sai mun had’u a sabon littafina insha Allah.


Taku Nazeefah Nashe ‘yar mutan makwarari.


Mai ta’kama da ikon Allah.



08033748387


—————————-

Suna samun hutu suka



Compiled by Deejasmah❤🦋




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login