Showing 36001 words to 39000 words out of 117786 words

Chapter 13 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

471

Na fad’a kayan da ko gidan waye za’a kai ba’a ji kunya ba zan wa Babanku waya anjima kad’an shima ya bada abin da zai bayar.” Momma tayi godiya ta mi’ke ta tafi wajen dahda don shima bai je dinner ba yace ba zai iya wannan rashin kunyar ta ‘ya’yan zamani ba. Hajiya mama kuwa d’an kwanciya tayi da niyyar cikin dare za ta tashi tayi nafiloli Ta sake ro’ka musu zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba don ita macece mai ibada kuma kullum addu’arta akan zuri’arta take.

Sai ‘karfe d’ayan dare dinner ta tashi duk da ango ya gaji amma kasancewar amarya tana ta girgizar rawa yasa dole ba’a tashi ba.rawa ce ta rashin kunya take ta yinta kamar yarda amaren zamani suke yi abin har mamaki ya dinga bawa jama’a musamman ango da abokansa. Da ya gaji ne ma ya mi’ke ransa a ‘bace ya fisgi Hannunta suka fice daga hall d’in dinnerr.zuciyarsa a cunkunshe da ba’kin ciki kasancewarsa mutum mai kishi, bai san ba abinda mutane suke kallo a jikinta ba.
Tun a mota kuwa ya dire mata kwandon masifa kamar zaici babu. Ita dai tayi shiru don ta san ta ‘bata masa rai. Yana parking kuma kallonta bai yi ba,ya bud’e motar ya fita.jikinta a salu’be ita ma ta fito daga motar tana kallo ya shige part d’insu ta san ko ta bishi ba zai saurareta ba don haka ta wuce cikin gida da niyyar ta kira shi a waya ta bashi ha’kuri,tunda dai ta lura har lokacin aikin su bai kammalu ba.


Shi kuwa sauri kawai yake ya isa part d’insu ya fitar da shatu kafin friends d’insa suzo su same ta. Yana bud’e d’akin mamaki ya kamashi ganinta tana barcinta peacefully ya zata zai zo ya sameta tana kuka. Gashinta a baje a saman pillow. Ya tsaya yana kallonta kafin ya daddage ya d’aka mata duka. Da sauri ta tashi da addu’ar farkawa daga barci a bakinta kamar yarda mommah ta koya mata. Ta tsaya tana kallonsa ranta a ‘bace. Tsaki yayi “da halla mi’ke ki fice Min a d’aki kafin wani yazo ya ganki kin wani baje min a bed kina barci salon ki saka min virus,saura kuma Idan kin shiga ki gayawa mommah ni na hanaki zuwa wallahi sai na miki rashin mutunci dama tana tambayrki kice barci ne ya kwasheki kuma kanki Na ciwo shi yasa ba kije ba.” ta’be baki tayi kafin tayi magana ya ja hannunta cikin mita yake cewa “wuce muje na lura so kike sarakan maganar nan su ganki anan to ta Allah ba taki.....” sak yayi yana kallon abokansa da suke zaune a parlourn idanunsu a kansa a zuciyarsa yayi tsaki yace mayu kawai ya juya d’akinsa ya rufe gam da key. Dariya suka tuntsire da ita Ali da Abdul suka bi bayansa don tsokana sai dai suna zuwa suka tarar ya rufe bedroom d’in gam.Ali ya tuntsire da dariya “Bar magulmaci dama wa zai ce baya son wannan zu’ke’kiyar da gaba ma ba’a son kyan da za tayi ba.


Shi kuwa Imran dama ya san idan ya bar ‘kofa a bud’e yaga ta kansa don haka ya rufe. ‘Ko’karin cire kayan sa yake yana cire babbar rigar zai d’aura akan gado idonsa yayi masa kyakykyawan gamo da sauri ya ware ido yana kallon stain d’in da yake gadon sa da d’an ‘karfi yace “what?”lallai ma yarinyar nan ta gama raina ni ‘bata gurin nan tayi?haka Allah yaso wani bai shigo ya gani ba, balle a zata disvirgining d’inta yayi.ya dafa kan sa zuciyarsa na tashi “wallahi yau shatu kin gama dani ina zan kai wannan kayan ‘kazantar ko masu aiki na bawa fassarar da zasu yi min kenan kai ya Allah wace irin yarinya ce wannan?” Tsaki ya sake ja ya fara ‘ko’karin yaye dubet d’in da bed cover d’in ya d’aga can dole yaje toilet ko idonsa ne ya rufe ya wanke ga shi bashi da hand gloves.iya gurin ya kama yana runtse idonsa, bud’e toilet d’in ke da wuya ya sake yin wani gamon da sauri yayi cilli da bed sheet d’in cikin sink amai na taso masa wannan wace irin ‘kazama ce yanzu kuma ita aka aura masa? Wallahi ba zai iya wannan ‘kazantar ba, idonsa a runtse yay flurshing toilet d’in yana yi yana ja
Mata Allah ya isa kamar wani ya sa shi. Ya saka harpic, yana sakin ajiyar zuciya a zatonsa ya gama amma ina juyawar sa ke da wuya ya ga undies d’inta zube a ‘kasa da sauri ya ja baya,kamar ba zai yi ba sai kuma yayi tsaki ba dolena nayi ba duk wanda na kira kamar na tarawa kaina jama’a ne kowa kuma da fassarar da zai yi masa.idanunsa a runtse shima undies d’in ya d’auke shi ya saka a toilet bin kafin da safe ya kira ta wallahi sai ta wanke masa toilet tsaf duk dama gobe zai bar gidan sai ta ci kanta ita kad’ai, da kyar ya wanke bed sheet d’in kawai don baya son yin wani cikin friends d’insa by mistake ya shiga ya gani wallahi da shima barin sa zai yi ta zo ta wanke to yana gudun ‘bacin rana kada ayi zaton wani abu yayi da ita shi kuwa Allah kada ya nuna masa wannan ranar da wani ido zai kalli jama’a bayan tarin cika bakin da yayi akan cewa MAI ZAI YI DA ITA? Yana gama wankewa ya cilla shi cikin washing machine sai sannan zuciyarsa ta dinga tashi ai kuwa ba ji ba gani ya dinga kwara amai sai da ya gama aman yayi brush yana gamawa ya fice da sauri murya a cunkushe yace wallahi ban yafe ba banza ‘kazama.😂 ya gyara gadonsa tsaf ya bad’e bedroom da turaren wuta da room freshner. Sannan ya fice parlour baya tunanin zai iya wanka a toilet d’in wallahi dole key ya d’auka a daren gwara yaje gidansa yayi wanka. Yana had’e rai ya fito, ai kuwa suna ganinsa Ali da shegantaka ya taso”wai ya aka yi ne yalla’bai mai amarya tazo yi part d’inka ko dai har ka fara sonta ne?”harara ya zabga masa “matseni in gaya maka” Abdul yace “ai abin bai kai na matsewa ba in dai wannan ne ai baya ‘buya abinda zamu gani ‘kunshe a mahaifarta muzo mu sha suna.” “Mtsww God forbid wallahi sai kace irin ku ai ni tunda nace muku ba abinda zanyi da yarinyar nan to kuwa zaku sha mamaki ba ku san waye Imran ba.” Dariya su kayi sosai suna kallo ya fice Ali yace “mhmn a dai juri zuwa rafi yalla’bai wata rana tulun zai fashe” Abdul ta tuntsire da dariya yace “d’an iska ranar mayar da martani ba.” Yana jin su murmushi kawai yayi ko don tanadin iskanci da suka yi masa ai ba zai kusanci yarinyar nan ba haka zai saketa wallahi da zarar shirinsa ya kammala. (To kowane shiri ne wannan mhmmn wani abin sai d’an gidan manga)



Ita kuwa tana bedroom d’inta bayan tayi wanka Night gown a jikinta da cup d’in tea a hannunta tana sipping a hankali so take ciwon marar da yake d’an damunta ya lafa mata. Hafsa ta shigo d’akin idanunta a kanta ta zauna a gefen gadon “wai ina kika shiga ne? Ban ganki wajen dinner ba?” Hafsa ta fad’a tana shafa kanta.
Murmushi shatu ta saki a karo na farko taji tana son rufa masa asiri saboda sam bata son haushinsa da mommah take ji tace “wallahi period pain ya hanani fita d’azu fa kamar na mutu dole kuwa nayi kwanciyata side d’in su Ya Imran.” Hafsa ta girgiza kai “ashe da gaske yake wallahi na zata ‘karya yake har na had’a shi da mommah sai kije ki wanke sa a wajen mommah don wallahi ta kunnu da yawa cewa take zai zo ya sameta don ma Hajiya mama tana hanata tace ba huruminta bane da tuni ta kira shi ta sulle shi sai kije ki wankeshi.” Shatu ta mi’ke ta tafi wajen mommah. Tsaf ta wanke shi kuwa mommah ta jata jikinta “oh am sorry daughter to da kika yi zamanki a can hope ba abinda yayi miki kuma kin sha magani?” Daga kai tayi tana kwanciya a cinyar mommah da take feeling d’inta kamar Innaji she really love mommahnta to the extent.



Da safe Dahda ya shiga wajen hajja gaishe ta da kyar take amsa gaisuwar. Sister’s d’insa ma duk suka gaisheshi anan yake sanar da Hajja tariyar shatu ita ma kamar yarda kawu sa’idu ya tsara sati mai zuwa Hajja ta ta’be baki”To ni yanzu ina ruwa na nayi magana kaje ka yayata ni a bakin duniya ai ba abinda zance maka manga aje Allah yayi albarka gobe-gobe ma zamu tattara komatsanmu muyi gaba ba kuma zamu sake dawowa ba kamar yarda ka bu’kata kuma ina son ka jini da kyau dama ka samu fili ka siya ka fara yi min gini anan kano duk san da na tashi zuwa na dinga zuwa can na sauka na san mallakina ne. Shashasha ana yi maka gata baka san gata ake maka ba duk an mallakeka da
Surkullen fulani.” Murya can ‘kasa Dahda yake amsa mata “Insha Allah Hajja za’a Gina,amma tafiyar da kun bari wani satin idan shatun ta tare.” Hameedah mai son ganin ‘kwaf ta gaban Hajiya ta saka baki “eeh Hajiya mu bar shi wani satin idan ta tare sai mu tafi cab amma za’a ga ‘kwailar amarya ai ni na zata ba yanzu zata tareba. Dahda ya zabga mata harara don sam basa shiri da hameedah baya son halayenta gaba d’aya.ya mi’ke yana yiwa Hajiya godiya bayan ya ajiye mata ma’kudan kud’i da niyyar yi mata toshiyar baki. Bakin Hajja kam yana mutuwa tsaf saboda kud’i.nan ta shiga jera masa albarka. Yana fita hameedah ta shige part din zainab ta bata labarin tariyar. Hankalin zainab ya tashi don basu kawo tariyar nan kusa ba sun zata sai ‘yar su ta riga ta mallake gida tukunna sai ga sabon labari ya bayyana a zuciyarta tace ashe kuwa sai na tashi tsaye kafin kwa’bata tayi ruwa.


Tsaf yayi wankansa ya shirya cikin shigarsa ta musamma farin filtex d’insa da hula damanga takalmi bartozzi ya d’ora agogon rolex d’insa a damtsen hannunsa kana ganinsa kamar ka sureshi ka sace. Sai zabga ‘kamshin turarensa da yake mix yake different colours ‘kamshinsa daban yake.
Direct part d’in mommah ya nufa cikin tafiyar izza kamar Kuma ‘kasaita kamar yarda ya saba yi kullum. So yake yaje ya dam’ki ‘yar gidan mommah ta wanke masa toilet duk da yasa an wanke amma sai ya wahalar da ita.

Cak tayi da tea cup a hannunta tana ‘kare masa kallo cikin shigar doguwar rigar ta ta shadda as usual yanzu ma kanta ba d’ankwali. Sarai yaji idonta a kansa yayi mata banza yana dur’kushe a gefe yana gaida su dada da Hajiya mama da momma. Dada ta dubi shatu tsaki tayi “kiji min ‘yar banzar yarinya ba zaki gaida mijinnaki ba.” Da sauri yace “ta bar gaisuwarta jeki bedrroom d’ina da toilet ki gyara min” ya fad’a yana tsareta da ido tsaki momma tayi “akan me duk ina house helpers d’in gidan da sai ita zata gyara maka don wani sabon iyayi gidan ma da yau zaka barshi.” Dada ta zabura tace “Auzubillahi kuji min mata tana neman jawo mana masifa da ranar nan ruguzu ta fad’o mana aikin mijinnata ne ba za tayi ba to kuma idan bu’katar ta yake fa ba iya sharar za tayi ba tashi ki fice kafin na kai miki mangara a’a wallahi ba ruwana idan rashin kunya zaki saka ta dinga yi masa ba kuwa zanje zaman d’akin nan ba ki hana a raya sunnahr muhammaduna rasulillahi d’an Abdullahi. Kai tashi ka bi matarka kaji.” Mommah gaba d’aya ran ta ya ‘baci har ya mi’ke a zafafe tabi bayansa suna zuwa corridor tace “kai ji mana kuma wallahi ko hannu ka ri’ke mata ban
Yafe ba.” Tana fad’a ta juya Imran shi dariya ma ta bashi ya juya kawai a zuciyarsa yace “kin san kina tsoron hakan kika yi mata aure kash ina ma bana gudun ayi min dariya da ayau zan mayar miki da shalelen taki cikakkiyar mace.”

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-23


ELEGANT ONLINE WRITERS........


Suna shiga bed room d’in ya ja ‘kofa ya rufe, fuska a d’aure yake kallonta,ya tsareta da ido sosai kafin yace,”sakonki na jiya ya isar min, wai ke ki nuna min kin cika mace ko?har kin fara period, amma ban san ke wawuya bace sai yanzu,wa yace miki mace tana bari ma a gane tana period? Baki san abin kunya bane hakan?” Turo baki tayi kawai tana kallonsa,sai kuma a lokacin wata shahararriyar kunyarsa ta kamata,ta ji sam bata kyauta ba yanzu shikkenan ya gane mata sirrin ta? Sirrin da mommah tayi ta jan kunnenta akan kada ta bari a gani, da sauri ta runtse idonta.
Tsaki ya ja “Dama kafin na dawo ki tabbata kin fitar da ‘kazantarki daga toilet d’in ki kuma wanke min bin d’ina,and then lastly ki tabbatar kin wanke anything dake toilet d’in ya dawo kamar sabo, wawuyan yarinya kawai.” Ya fad’a yana kai mata ran’kwashi, daga haka ya fice ya kuma kulleta da key ta baya.

Sai sannan shatu ta bud’e idonta, tana sakin ajiyar zuciya, a hankali tace “Wai ni Shatu mai na aikata mutuminnan yanzu zai sake min kallon ‘kazama.” Tsaki ta ja ta shige toilet d’in, very neat ta samu toilet d’in,amma haka nan ta ‘kara wankeshi.


Momma jin shirun yayi yawa, da sauri ta danna kiransa a waya don hankalinta sam ya gaza kwanciya. Tsawon lokaci wayar tana ringing shi kuwa yana kallo yana driving ya’ki receiving call d’in sai murmushi yake, ya san mai take yiwa bata san ko bindiga aka saka masa ba zai iya aikata abinda take tunani ba.

Ji yayi text message ya shigo, ya bud’e yana murmushi had’e da ware ido kamar yarda hakan ya zame masa jiki. “Wallahi ka aikatawa yarinyar nan wani abin sai ka sani.” Dariya yayi sosai har da dukan sitiyari. A zuciyarsa yace “Ai kuwa yanzu wasan zai fara Mommah.”


********************************

Cikin kuka da tashin hankali take kallon mahaifiyrta, “Yanzu Anty duk burin da naci ya tafi a banza kenan? Yarinyar nan tarewa za tayi? Kuma ana nufin itama Imran mallakinta ne kamar yarda yake mallakina? Tana da right da komai a kansa, zata had’a jiki dashi? Komai da zaiyi min zai mata?” Cikin tashin hankali ta sake rintse ido. “Na shiga uku Anty pls kiyi wani abu mana, wallahi ji nake kamar zuciyata zata buga.” Tsaki Zainab tayi kafin tace “Ke bana son shashancin banza ki tsaya ki saurari abinda zan ce miki,ko jiya munyi waya da shuwa ta tabbatar min da ta koma gurin mutuminnan abinda ya sake ce mata kenan dole ki san yarda kika yi kika bashi maganinnan yaci a nama, a kuma ranar da yaci ake so lallai ya had’a shimfid’a da ita, yace min wallahi da zarar anyi haka kashegari zai sake ta kuma ba zai sake waiwayarta ba.” Kukan ta sake saki “Ni fa anty a sake wata shawarar wallahi ba zan amince ya shafi jikinta ba,balle har su had’a shimfid’a Imran nawa ne ni kad’ai.” Tsaki Anty tayi ta mi’ke a zuciye tace “Sai ki shirya zama da ita din-din-din a matsayin kishiya,ni dai abinda naga zan iya yi kenan shashasha ko meye abin damuwa?abin rana d’aya lokaci d’aya, kuma wallahi kika sa nayi asarar kud’ina ranki ne idan yayi dubu zai ‘baci,kin san nawa na kashe? Ban da tafiya cikin jeji da shuwa ta kwana tana yi a garinsu, to kije kiyi yarda kike so, ki bari suyi surkullensu na fulani su su mallakeshi,kin san dai yarinyar nan ta fiki komai da komai.” Runtse idonta shaheeda tayi murya na rawa tace “zan gwada Anty Allah ya bani iko.” Antyn ta dafa ta yauwa “ko ke fa idan kika yi hakan shine zaki samu kansa,ki ci karanki babu babbaka.” Shaheedah ta saki ajiyar zuciya tana dafa hannun mamanta tace “Amma Anty ta yaya zai amince ya kusanceta bayan kin san ba son auren yake ba.” Anty tayi murmushi “Yaro-Yaro ne ai ba yanzu zakiyi ba sai lokacin da muka so ta bar gidan,a lokacin dama kin tsara tafiya Abuja sai ki bashi a nama yaci,to kafin ki tafi ki tabbatar kin bashi desire tablet a cikin tea da safe mai ‘karfin gaske,idan ya bu’kace ki kice period kike ko kuma kafin maganin ya fara aiki kiyi sauri ki tafi shikkenan fa fa’kat, burinmu na farko zai cika.” Dariya shaheedah tayi ta rungume Antyn ta cikin tsananin farin ciki,hankalinta kam yanzu hundred percent ya kwanta.



Da yamma kafin a kai amarya Momma ta kira Imran, ba ‘bata lokaci yazo, tana kallonsa su biyu a
Parlourn tace “Nasiha zan maka Imran a matsayina na mahaifiyarka duk runtsi duk wuya ka kula da iyalinka,amana ce ubangiji ya dan’ka maka a hannunka, kayi adalci a tsakaninsu Imran kada kaga ita wannan yarinya ce ka cuceta ko ka zalunceta,zata tare nan da kwana shidda....” da sauri Imran ya zaro ido yace “kwana shidda Mommah ai naga tayi ‘karama.” Mommah tsaki tayi”Ni kaina ba’a son raina hakan zata faru ba ba yarda zanyi ne, sai dai ina son in ja kunnenka hakan ba yana nufin na baka lasisin kula ta bane, wallahi ban amince ba kada wata mu’amala ta had’aku,
Ka bar ta tayi karatunta please Imran.”

Ransa a ‘bace ya saki ajiyar zuciya yana tunanin mai zai kaishi kusantarta ko shi ya kawo maita duniya, gaskiya bai ji dad’in lamarin tariyar nan ba, har hakan ya gaza ‘boyuwa a
Fuskarsa,sai dai bai ce komai ba ya mi’ke ya tafi bayan ya zaro key d’in part d’in shatu na gidansa ya mi’kawa mommah kamar yarda ta bu’kata.


Tunda ya koma bedroom d’insa ya zubawa kayan da abokansa suka had’a masa na komawa gidansa kallo,idan ka ganshi zaka yi zaton kayan yake kallo,Sai dai tuni zuciyarsa ta tafi tunanin neman mafitar yarda zaiyi da auren Shatu, tunani iri-iri ya shigeshi wata zuciyar tace kawai ya saketa ya gudu da matarsa su bar ‘kasar, a duk shawarwarin wannan ce tafi tsaya masa.




Tsaf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login