Showing 111001 words to 114000 words out of 117786 words

Chapter 38 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

477

fara aiki take idonsa ya rufe, Shuwa ce ta taimakawa Shaheedah da uwarta suka d’ora Imran akan gado, ta mi’kawa Shaheedah camera kafin ta jinjina mata alamar ta yi aiki mai kyau suka ja mata ‘kofar bedroom d’in suka zauna a parlour.

Dai-dai lokacin da Shatu da police suka bayyana a parlourn. A razane Shuwa da Zainab suka mi’ke hannayensu a bakunansu tamkar su zunduma ihu. Shatu cikin tashin hankali ta ce “Ina ku kai min mijina ba?” Ba tayi wani tunani ba ta afka cikin bedroom d’in cikin tashin hankali ta ‘kwallara ‘kara ganin Shaheedah daga ita sai underwear’s tana ‘ko’karin hayewa ruwan cikin Imran da ta’ballewa kaf ma’ballen rigarsa da gashi sai boxers na maza, da sauri police d’in suka fad’a bedroom d’in. Ba abinda ya damesu da yanayin da Shaheedah take ciki don su sabonsu ne ganin mata a haka, Shatu ta angaje ta tana dudduba Imran ta ke ta tabbatar da baya cikin hayyacinsa ai kuwa ta sake saka kuka ta nayiwa police d’in bayani, Shaheedah kuwa jikinta tamkar mazari sai rawa take saboda razana da tsorata, musamman ganin police d’in sun zaro handcuffed sun ma’kala a hannunta bayan ta zura doguwar riga a jikinta, haka nan su Shuwa ma ba a barsu ba aka datse hannayensu da handcuffs. Shatu kuwa ‘kokari kawai take Imran ya farfad’o ganin yarda ya sandare tamkar gawa. Police d’in ne ya kira doctor ya ce yazo ya duba wani patient suna pera palace hotel. Ya gaya masa room number d’in shi ya tsaya da Shatu, su kuma sauran suka wuce da criminals d’in station d’insu.


Mintuna kad’an Doctor d’in ya d’auka sai ga shi ya bayyana a hotel d’in sabida su sun san kan aikinsu.

Yana dubawa ya tabbatar musu da ‘kwaya ce mai ‘karfi aka bashi ya sha amma yanzu zai bashi allurar da zata saka ‘kwayar ta sake shi in just a minutes.

Ba ayi taking wani time ba kuwa Imran ya farka, duk da yana jin jiri da matsanancin ciwon kai, Shatu ta kamashi ya mi’ke zaune tana shafa masa kansa da ta lura yana sara masa a hankali ya ce mata “muje gida.” Police d’in ya taimaka mata suka kaishi mota da kansa ya kaisu gida sannan ya basu compliment card d’insa ya ce su nemeshi zuwa gobe Idan suna son ganin su Shaheedah. Imran ransa yayi masifar ‘baci musamman da ya ji sunan Shaheedah ko sunan ba ya bu’katar sake ji balle mamallakin sunan.


Suna zuwa gida ruwa kawai Shatu ta taimaka masa ya watsa sannan ya zube a gadon wani nauyayyan barci ya sake d’ibarsa.


A station kuwa a cell aka saka su Shuwa, hankalinsu a tashe yake sosai musamman sun san nan d’in ba Nigeria bace ba sa bu’katar bribe balle su basu su yi bailing Kansu, ko ina ma suka ga kud’in da zasu basun? Hawaye ya shiga kwarara daga Idanun Shuwa tana da Na sanin Zainab, da tunda suka had’u ba ta mori komai a tare da ita ba sai wahala a da tayi tunanin Idan komai ya kankama zata mallake Shaheedah da ita kanta uwar ta Ta, sai yarda tayi dasu, ta kuma mallake duk dukiyoyin mazajensu shi yasa bata jin shakkar kashe ko nawa ne akan matsalarsu don ita bata dangi a Nigeria daga ‘kasar sudan ta gudo tsabar talaucin danginsu a sudan yasa ta barsu ta gudo Nigeria tashin farko ta had’u da Zainab shikkenan suka jone. Tayi tsaki a cell d’innan yafi shurin masa’ki har Zainab ta gaji ta ce “Wai Shuwa tsakin na menene?” A zafafe tace “Na komai ne ma Zainab, Na ba’kin ciki da takaicin had’uwa da ku ne? Duk wani tattalin arziki ne ya kwaranye akan matsalarki da ta ‘yarki sam ba ‘kashin arziki a tare da ku, don haka da zarar an fita cell d’in zan raba jiha da ku kowa ya kama gabansa don ban ga mamora tarayya ta daku ba.” Zainab cikin ‘bacin rai ta ce “Ni kai tarayya ta dake ta zame min masifa, kin d’ora ni a bigiren bin bokaye da malamai wanda hakan ne ya janyo min kwaranyewar tattalin arziki na sabida bawa malamai da bokaye kud’ina, ko da haka kika ganni ina ce da arziki na kika ganni shine Dalilin da yasa kika ma’kale min, sai yanzu saboda butulci kinga bani da komai shine zaki ce kowa ya kama gabansa.” Shuwa a zafafe tace “Na fad’a d’in kowa ya kama gabansa ko ke d’in ‘kanwar uwata ce da zan zauna dake dole daga nan ma da na taho da shiri wallahi ‘kasar mu zan wuce..” nan da nan fad’a ya kacime a tsakaninsu kamar za’a bawa hammata iska. Shaheedah kuwa kuka ta ke sosai ji take kamar ta tashi ta rufe su da duka, tabbas yanzu tana da na sanin hawa turbar da suka d’orata da bata sauketa a ko ina ba sai tashar nadama, yanzu waya san irin hukuncin da hukumar ‘kasar nan zata zartar musu?




—————-

Fuskarsa ta shiga shafawa a hankali, da kyar ya bud’e idonsa. Murmushi ta haske idanunsa da shi kafin ta sakar masa peck a gefen kumatu, a kunne ta rad’a masa “Please ‘kalbeey ka tashi haka wuni fa kayi kana barci ka tashi mu ci Abinci.” Da kyar ya mi’ke ta raka shi har toilet ya yi brush sannan ya watsa ruwa a fuskarsa, yanzu kam ya ji dad’in kansa don kuwa ya yi masa sau’ki Sosai.

Madadin saman dinning akan tattausan carpet ta jere musu kwanukan abincin, ya kuwa ci sosai kasancewar wuni yayi bakomai a cikinsa..


Suna gama ci ta kwashe kwanukan tas sannan ta dawo ta sanya ‘kafafunsa akan cinyarta tana masa massage a ‘kafarsa, dad’in massage d’inne yasa shi lumshe ido take abin ya fara dawo masa kamar a lokacin aka yi shi, bai Ta’ba ganin shashashar uwa irin uwar Shaheedah ba yau kam sun ‘kureshi a malejin mamaki. Shatu da ta lura tunani ya afka ta ce “Gobe ya kamata muje station d’in ayi bailing su, su koma Nigeria na tabbatar dai ba za su sake basu lasisin sake shigo musu ‘kasa ba.” Imran ya bud’e idonsa da suka yi jajur kamar garwashi ya zube su akan Shatu “Ni Zan je nayi bailing su? Ashe kuwa za su tabbata a can, har abada ba zan sake shiga sabgarsu ba.” Shatu shiru tayi masa ganin ya d’au zafi sosai.



—————————

A can kuwa station gwamnatin ‘kasar ta tattara case d'in ta turo Nigeria, sannan aka tarkatasu aka watso jirgi da sharad'in ba zasu sake shigowa turkeyba. hakan ya faranta musu rai tun a airport kuma suka yi baran-baran kowa ya kama gabansa, shikkenan fa amintakar ta watse dama duk abotar da ba tsoron Allah cikinsa baya tasiri. Allah kasa mu fi 'karfin zu'katanmu.


Tun a airport gwamanatin Nigeria tasa aka yi ram dasu dole ne a
tuhumesu dalilin zuwa su aikata wannan aika-aikar a 'kasar da
ba tasu ba, ashe tsuguni
bata 'kareba, domin dai
kotu ta yanka musu tara ko zaman gidan yari na shekara biyu cif....







Nazeefah Nashe

08033748387

Me Zan yi da ita?


Nazeefah Nashe


Wattpad
@Nazeefah381

08033748387




—————————-

Bayan wata hud’u, zuwa lokacin tuni cikin Shatu ya girma ya zama ‘kato masha Allah wata bakwai cif, amma da kyar take iya d’aga ‘kafarta.

Suka fara shirin tafiya Nigeria, Imran tuni ya kammala musu duk wata siyayyarsu ta haihuwa duk da ba wanda ma ya san da cikin ko Mommah bata sani ba, kasancewar ya san matar Ammar ma tana da cikin tare ya siya musu komai domin ko edd d’insu 2 weeks ne kawai banbanci matar Ammar zata riga Shatu kenan.



Ranar wata friday jirginsu ya dirga a Nigeria, suma su Ammar cikin dare zasu sauka dama sun had’a bakin surprising za suyi wa Mommah.


Abokinsa Khalil ya kira ya d’aukesu. Sai ko tsiya yake masa Da yau mun ga abinda zaka yi da ita ko da yake tun akan twins muka san abinnaka cika baki ne dama wa Allah zai bawa wannan kyautar ya banzatar da ita?” Murmushi kawai Imran ya ke yana sosa ‘keya d’aya hannunsa kuma cikin na Shatu yana mammatsa mata shi kasancewar ya kumbura suntum.



Nocking d’in da ake ne yaja hankalin Mommah da take kitchen, faten Accra take dafawa Hajja, da sauri ta fito duk da ta san Hajjan na parlourn ta san ba zata iya mi’kewa ba saboda ciwon ‘kafa da yake damunta, su Akram kuwa suna Islamiyya, Basirah sun gama ayyukan da zasuyi mata sun shige ‘bangarensu guda da Dahda ya ware musu a gidan yayi musu aure da direbobinsa, kowa tana da parlour da d’akuna biyu ga toilet da kitchen duk a parlourn, saboda Mommah tace ba ta son rabuwa dasu, ta riga ta saba dasu tun suna yara.


Turus Mommah tayi da ta bud’e ‘kofar taga ba’kin bazata. Ga Shatu da turtsetsen cikinta. Cikin tsananin farin ciki Shatun ta fad’a jikin Mommah ta rungumeta shima Imran bai yi ‘kasa a gwiwaba ya rungumeta. Mommah ta ce “Ikon Allah to ku kayar dani ku ba ku ga yarda kuka dawo ‘katun-‘katun ba, kamar ana hura ku.” Dariya sosai khalil ya yi ganin yarda Shatu ta turo baki wai ance mata ‘katuwa Mommah ta juya ciki ta ce “To sannu Shatu jaririya zan kiraki kenan kina shirin sake haihuwa ta biyu, don shiririta shine kuka taho ba sanarwa.”


Hajja bud’e baki tayi da tsananin farin ciki tana dubansu “Lallai kun iya dirar bazata, zuwa haka bagatatan.”
Shatu ta zube a gaban Hajja tana murmushi da mamakin ganin Hajjar ba wani had’in rai da ta ke mata da. Hajja ta ja hannunta mi’ke maza ki zauna a kujera, kawai ya wahalar dake ya kwasoki ra’be-ra’be da ciki, madadin ni ya kirani turkeyn na yi miki zaman da’baro” tsaki Mommah ta ja “Shashancin fa Hajja, ai idan Imran bai yi wautar d’an fari ba baya jin dad’i to waye ma ya san da cikin? Allah dai ya kyauta tunda sun zo lafiya.” Shatu ta dinga yi masa dariya ‘kasa-‘kasa ganin yarda yake ta kumbura baki wai ance masa d’an fari. Mommah kuwa masifa ta cigaba da yi “Ni na san da cikin zan barta ta kai wannan lokacin a can? Kai dai Imran Allah ya kyauta maka.” Cikin cunkushewar murya yace “Duk kun sama naji da na sani banzo ba, shima wanda ba d’an farin ba ai yana hanya cikin matarsa ma har yafi na Shatu.” Hajja ta saka salati “Wato duk lalatar da za kuyi mana kenan, kuzo ku had’a uwarku da aiki to duk gidajenku zaku tafi.” Mi’ke ‘kafar Shatu Imran ya yi akan cinyarsa yana matsa mata ita ganin yarda ta kumbura Mommah d’auke kai kamar bata gansu ba, ta shiga kiran su Basirah a waya. Tana sauraran Imran da yake cewa “Ai dama tafiya za muyi.” Tsaki ta ja “Saboda a garin mahaukata ake? Ai ko anan garin take a wannan ‘katon cikin d’aukota gaba na zanyi balle ka kawota da kanka.” Imran bai san sanda ya zaro ido ba ya ce “Mommah... please kada kiyi min haka.”
Wani kallo ta watsa masa tana cewa “To idan baka da kunya ai sai ka d’auketa ku tafi.” Hajja ta ja tsaki ta ce “Shirmen banza to dama wannan wata kunya ce da shi ji yarda fa ya ke lailayar ‘kafarta yana sakin murmushi ko kunyar mu bai ji ba, ai kunya ta yi dama Imrana ya yi hagu, ba su had’a hanya ba ko kad’an gwara ma ki barsu su tarkata su tafi, kafin a gabanki ya dinga abinda zai saki ke kiji kunya, sak halayen ubansa Manga ne a tare dashi yana abu ido wu’ki-wu’ki. To dani kake zancen a d’akina Shatun zata zauna sai naga ko zaka zo ka hai’ke mata a gabana.” Mommah mi’kewa ta yi ta shiga kitchen don kunya zantukan Hajja suka saka ta, Imran yana ganin Mommah ta tashi ya ce bari nayi maganin tsohuwar nan “Hajja rufe idonki.” A zafafe ta ce “Ubanka Manga yazo ya rufe min, maras kunyar banza.” Sosai ya kaiwa Shatu kiss a baki tana gocewa ya buge hannun, salatin Hajja ne yasa Mommah ta fito da sauri daga kitchen dai-dai lokacin da Imran ya ke gyara zamansa yace “Ai sai da nace ki rufe idon ki.” Hajja ta ce “Dijah kada ki sake ki bar Imrana anan gidan wallahi
Nan gaba ma a gabana zai hai’kewa matarsa tana gocewa yana sake tura masa harshenta wai shi tantiri irin abinnan dai da ake nuno yahudu suna yi a t’v.”
Mommah dariya ce ta so ku’buce mata, shigowar su Yaseerah ne yasa ba tayi ba, suna ganin Shatu suka shiga tsalle Yasirah ta ce wasu ‘yan biyun kika ‘kunso? Shatu ta zabga mata harara Mommah ta ce “Zaku fara ko ke Yaseerah da laulayinki bayan son warin tattasai wuce ki gyarawa su Imran d’akunansu don Ammar ma yana hanya, ke kuma Basirah wuce muje kitchen.” Basirah ta turo baki “Wallahi Mommah ‘karya ta ke miki ba wani ba ta san warin tattasai a can’bangarenta wa ke dafawa mijinta abinci?” Shatu ba tayi mamakin aurensu ba don Mommah ta sanar da ita Har ta aiko musu zannuwan gado da flasks. Ta ji dad’i kuma da Mommah ta barsu anan kusa da ita gashi har sun sake gogewa tsaf da su.



Imran ya mi’ke bayan Yasirah ta sanar da su ta gama gyaran ‘bangarennasu ya kama hannun Shatu tashi muje mu huta kafin a gama abincin mu tattara mu wuce gida.” Kicinyar tashi ta fara yi ganin ta na cije baki ya kalli Hajja ya ce “Rufe idon ki.” Hajja ta ce “Ba za’a rufe...” bata rufe bakiba ta ga ya sunkuci matarsa yayi hanyar part d’insu da ita. Wannan karan Hajja kuka ne kawai ba tayi ba Yasirah da take gefe ta ce “Aradu Hajja sun burgeni ko nauyinta bai ji ba sai kace a India.” Hajja ta yi tsaki “Ina zai ji nauyinta yasa jaraba a ransa daga ganin idonsa jaraba ce take cinsa zai je ya sauke akan yarinya, ai indai Dijah ba ta dakatar dashi ba wahalar da yarinyar nan zai je yayi tayi a gidansa shi ysa nan da nan ya ‘kunsa mata ciki.” Sosai Yasirah tayi dariya ta shiga kitchen tana bawa Mommah labari.
Murmushi Mommah tayi don ita hakan dad’i ya ke mata ta tabbata yanzu Shatu tana samun kulawa a wajensa, hakan kuma dama take fata ya kasa ‘boye soyayyarta a ko ina.


Suna shiga bedroom ya kwantar da ita akan bed gaba d’aya ya had’a jikinsu. Murya ‘kasa-‘kasa yace kin san yarda nake missing d’inki kuwa just d’an zaman jirginnan da ban jiki sosai a jikina ba, anya kuwa Shatu Mommah ba mallake miki ni ta yi ba, gani nake ba zan iya rayuwa ba ke ba.” Ya fad’a yana tura kansa ‘kar’kashin wuyanta ya saki wata doguwar ajiyar zuciya kamar sun dad’e basu had’u ba, ko wankar bai bari sun yi ba ya sake sauke mata gajiyarsa a kanta. Idan yaso sa yi wankan mai gaba d’aya.



Tsaf aka shirya musu abinci mai rai da lafiya Yasirah zata kai Mommah ta ce ta bari su fito. Hajja ta ce “Wallahi kuwa kada kije kiga abinda zai saka miki makanta don daga ganin yarda ya jata d’akinnan jaraba zai je ya sauke mata. Dijah ki yiwa kanki fad’a ki barsu su tattara su wuce gidansu.” Mommah ta yi murmushi “Ki k’yaleshi Hajja zan koya masa hankali so nake na ji watannin cikin idan ya kai takwas dama janyeta d’akina zan yi ko naki.” Hajja ta girgiza kai rufa min asiri Imran ba kunya bace dashi ai sai yazo har d’akinnawa ya taushe miki ‘ya.” Mommah murmushi kawai tayi ta mi’ke dai-dai lokacin da suke fitowa daga d’akin, ya wani rirri’kota kamar tana labour sai jera mata sannu ya ke. Momma ta nuna musu dinning “Ku je can ga abinci ku ci.”
Da sauri ya girgiza kai “Bari mu koma ciki, zamu fi sakewa a can.” Kafin Mommah tayi magana har ya juya da matarsa. A ransa ya ke fad’in na fi son na jita a cinyata muna cin abinci, anan ina zan iya duk abinda kayi ace rashin kunya shi malam bahaushe har yanzu ya ‘ki ya waye.
A hankali Shatu tace masa ka bari muci acan d’in. Shima murya a ‘kasa ya ce “Zaki iya zama a cinyata kamar yarda kika sabar min ki dinga d’ura min na bakin ki..” ta waro ido don bata sani ba ko Mommah ta ji. Hajja dai bata ji ba amma sarai Mommah ta ji murmushi kawai ta saki ta tabbata Shatu ta riga ta gogewa Imran hadda, baya gane komai sai karatunta.


A plate d’aya ya zuba musu abincin ya juya cikin part d’insu. Hajja ta ce “‘ya’yan zamani kenan Allah ya kyauta.” Mommah murmushi tayi kamar ta ce “Haka ake so Hajja rayuwar aure mai dad’i kenan abinda nakewa Manga kenan ki ke zata na mallake shi. Wanda ba haka bane tsantsar kulawa ce da madarar soyayya da nake Shayar da shi sai tsananin biyayya wad’annan abubuwa sune jigon mallaka ba boka ba malam, gangar jikinki da kissarki ta isa kad’ai ki mallaki mijinki son ranki.

Hajja ta gyara zama kafin ta ce “Ni kuwa Dijah zuwa yanzu ai ya kamata a nemo dangin uban yarinyar nan don su san tana lafiya a kuma nuna musu kuskuren da suka aikata, sai kuje ko da ke da
Hameeda ne tunda dai ita ga yanayin da ta ke ciki idan ta haihu ta je ta sadu dasu suga juna.”
Mommah ta girgiza kai ta ce hakane Insha Allah zan sanar da Imran d’in da Dahda sai muje da Hameedah da Nahna tunda har yanzu ita ce ba juna biyun sai dai fatan Allah ya kawo.” Hajja ta ce “Ameen ai lokaci ne da aure da haihuwa duka lokaci ne da zarar lokaci ya yi babu haufi sai sunyi.”



———————-



A daren su Ammar suka sauka, su ma dai Mommah a gidan ta ce su zauna kuma Ta tambayi watannin cikin jin basu kai takwas ba tace su tare a d’akunansu da zarar sun kai takwas duk zasu dawo ‘bangarenta kuma a d’aki d’aya zasu zauna suyi jego.


Akram da gudu ya rungume abbinsa sanda ya gan shi, ita kuwa Ikram Mimi ta rungume abinta, don haka kawai bata fiye sakewa da Imran ba, amma sanda ta ga Ammar tuni ta ‘kan’kameshi. Hajja ta ce “

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login