Showing 102001 words to 105000 words out of 117786 words

Chapter 35 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

465

saukar su a zuciyarsa, cikin wani yanayi ya ce “Amma dai kin san soyayya ce ta ke kawo ka ji ka na sha’awar mutum ko? Please Shatu kada ki sa na fara dana sanin rabuwa da Shaheedah wallahi ba haka ta ke min ba duk tsananin fad’an da muka yi da ita tana bari na kusanceta.” Wani kishine ya taso ya tokare mata ‘kirji, har gumi ke tsatstsafo mata ta ji duk wani tausayinsa da ta ke ji ya kau, haushi da takaicin furucinsa suka bi suka goge wancan ‘bur’bushin tausayinnasa, kan ta tsaye ta ce “Me zai hana ka dawo da ita ta baka abinda ni na hana ka.... kuma ka jawowa kanka da niyyata na zo na baka abinda kake so amma wallahi wannan furucin yasa sai na tabbatar da sharad’ina idan yaso bayan Shaheedah ka ‘karo uku ma.”

Daga haka ta rufe ‘kofar da ‘karfi zuciyarta na sake bugawa kamar zata tsaga ‘kirjinta ta fito.

Imran kuwa runtse idanunsa ya yi yana da na sanin furucinsa madadin gyara gashi ya sake hassala zuciyarta har yana hango tsananin fushin da bai ta’ba gani ba akan fuskarta.

Da kyar ya rarrafa ya mi’ke ya na bin bango ya isa kitchen lemon tsami mai yawa ya matse a cup ya zuba gishiri kad’an ya runtse ido ya sha. Sannan ya dawo parlour ya sake kwanciya ya runtse idanunsa.

Shatu kuwa hawaye ne ya ‘balle mata a cikin bedroom na zallar kishi da takaicin d’a namiji ko ita ta saka ya rabu da matar tasa. Duk tsananin yunwar da ta ke ji tuni ta nemeta ta rasa ta zauna gefen gado tana lalubar numberr Mommah a sabuwar wayar da ya had’a mata yau da safe. Amma wayar sam ta ‘ki tafiya hakan yasa ta sake sakin kuka. Kukan da yasa Imran saurin nufar bedroom d’in, tana ganinsa ta hau cillinshi da pillow tana furta ka fita ka fita! Bana son ganinka ai ba yau ka fara fifita Shaheedah a kaina ba, ni dama mecece banda baroro mai warin baki.

Da sauri ya nufeta amma ina ta mi’ke a sukane ta shige toilet ta murza lock. Imran ya yi turus yana mamakin tsananin kishi na Shatu wannan da kishiyar za’a yi mata ya zata yi. Ya saki murmushi yana had’ata da Allah ta bud’e Shatu ta yi mursisi ta ce ba zata bud’e ba, haka Imran ya fice daga d’akin ya nufi samo musu abincin da za su ci.

———————-

Gefe d’aya Shuwa ce a gidansu mahaifiyar Zainab wato ‘kanwar Hajja da suke uwa d’aya uba d’aya.

Takanas suka taho da ita da shaheedah da zainab d’in suka tasa Yaganah a gaba suna bata labarin ‘karya da gaskiya. Ran Yagana ya ‘baci ta hau sababi har tana fad’in ba tun yau na lura Hajja ba son aurenki ta ke da Manga ba ke kuma ki ka nace sai shi, ga shinan daga ke har ‘yar ki sun mayar da ku zawarawa, yanzu wa gari ya waya? Shuwa ta saki murmushi Na tsananin ‘bacin rai tana tuno wula’kancin da aka yi musu a fili ta furta “Wallahi ki rabu da su Umma ba su ci bulus ba, yanzu ne ma za mu d’aura d’amara tsakanin mu da su shege ka fasa kin ga wula’kancin da suka yi mana kuma auren Habeeb mijin Hameedah yanzu na d’aura d’amara sai na mayar da ita abin kwatance, ita dai Zainab ta ha’kura tunda shika uku sun cika cif da Manga ya yi mata na farko an yi d’aya yanzu kuwa ya cike biyu cif, amma Shaheedah kam tamkar ta koma gidanta kafin iddarta ma ta cika zamu je har turkeyn bayan an gama shirya ta tsaf ta yarda in dai ya ganta ba zai iya d’auke idanunsa a kanta ba da kansa zai furta ya mayar da ita d’akinta.” Zainab da uwarta su ka saki ajiyar zuciya har Shaheedah ma sun tabbatar Shuwa zata iya aikata hakan tunda ta furta, don haka hankalinsu ya sake kwanciya kamar tsumma a randa. To fa! Tur’kashi! In ji malam bahaushe.

————————

Ammar yana isa gida Kano direct ya wuce bayan Hisham ya sanar da shi Mommah sun wuce Kano har da Mubeenah, don haka ya wuce can kawai don burinsa ya ga Mubeenah.

Da kyar ya bud’e idanunsa ya zube su cikin nata kafin ya furta “Please Hayateey ki taimaka min wallahi zan iya mutuwa a condition d’in da nake.” Da kyar muryarsa ta ke fita yayin da yake maganar da alama iya gaskiyarsa ya ke furtawa har ‘kasan zuciyarsa. Hannunsa ta kama tana matsawa cikin nata kamar zata amince da bu’katarsa sai dai tuni wata zuciyar ta sake ce mata da sauran lokaci.

Yana ‘ko’karin janyota ta yi saurin mi’kewa bai tsince ta a koina ba sai bakin ‘kofa hakan ya tunzira zuciyarsa ya ji ransa ya matu’kar ‘baci a zafafe ya ce “Na wa kike bu’kata in baki in dai zaki amince na samu sau’kin abinda na ke ji zan baki.” Turus ta ja ta tsaya zuciyarta ta karye da tausayinsa duk da tsoron Allah ya shigeta ta fara nadamar abinda ta aikata ko ma ta ke kan aikatawa sai dai tuni shaid’an ya rinjayi zuciyarta ta juyo tana masa wani irin duba “Bana bu’katar ko kwabo kafin na sallama maka gangar jikina, sai dai tabbas ina bu’katar na sani so na kake ko kuwa sha’awata, kuma da kanka ka ce ka amince da sharad’ina sabida haka sai ka jira lokaci. Maganganunnata tamkar d’igar dalma ne a ciwo yanayin yarda ya ke jin saukar su a zuciyarsa, cikin wani yanayi ya ce “Amma dai kin san soyayya ce ta ke kawo ka ji ka na sha’awar mutum ko? Please Shatu kada ki sa na fara dana sanin rabuwa da Shaheedah wallahi ba haka ta ke min ba duk tsananin fad’an da muka yi da ita tana bari na kusanceta.” Wani kishine ya taso ya tokare mata ‘kirji, har gumi ke tsatstsafo mata ta ji duk wani tausayinsa da ta ke ji ya kau, haushi da takaicin furucinsa suka bi suka goge wancan ‘bur’bushin tausayinnasa, kan ta tsaye ta ce “Me zai hana ka dawo da ita ta baka abinda ni na hana ka.... kuma ka jawowa kanka da niyyata na zo na baka abinda kake so amma wallahi wannan furucin yasa sai na tabbatar da sharad’ina idan yaso bayan Shaheedah ka ‘karo uku ma.”

Daga haka ta rufe ‘kofar da ‘karfi zuciyarta na sake bugawa kamar zata tsaga ‘kirjinta ta fito.

Imran kuwa runtse idanunsa ya yi yana da na sanin furucinsa madadin gyara gashi ya sake hassala zuciyarta har yana hango tsananin fushin da bai ta’ba gani ba akan fuskarta.

Da kyar ya rarrafa ya mi’ke ya na bin bango ya isa kitchen lemon tsami mai yawa ya matse a cup ya zuba gishiri kad’an ya runtse ido ya sha. Sannan ya dawo parlour ya sake kwanciya ya runtse idanunsa.

Shatu kuwa hawaye ne ya ‘balle mata a cikin bedroom na zallar kishi da takaicin d’a namiji ko ita ta saka ya rabu da matar tasa. Duk tsananin yunwar da ta ke ji tuni ta nemeta ta rasa ta zauna gefen gado tana lalubar numberr Mommah a sabuwar wayar da ya had’a mata yau da safe. Amma wayar sam ta ‘ki tafiya hakan yasa ta sake sakin kuka. Kukan da yasa Imran saurin nufar bedroom d’in, tana ganinsa ta hau cillinshi da pillow tana furta ka fita ka fita! Bana son ganinka ai ba yau ka fara fifita Shaheedah a kaina ba, ni dama mecece banda baroro mai warin baki.

Da sauri ya nufeta amma ina ta mi’ke a sukane ta shige toilet ta murza lock. Imran ya yi turus yana mamakin tsananin kishi na Shatu wannan da kishiyar za’a yi mata ya zata yi. Ya saki murmushi yana had’ata da Allah ta bud’e Shatu ta yi mursisi ta ce ba zata bud’e ba, haka Imran ya fice daga d’akin ya nufi samo musu abincin da za su ci.

———————-

Gefe d’aya Shuwa ce a gidansu mahaifiyar Zainab wato ‘kanwar Hajja da suke uwa d’aya uba d’aya.

Takanas suka taho da ita da shaheedah da zainab d’in suka tasa Yaganah a gaba suna bata labarin ‘karya da gaskiya. Ran Yagana ya ‘baci ta hau sababi har tana fad’in ba tun yau na lura Hajja ba son aurenki ta ke da Manga ba ke kuma ki ka nace sai shi, ga shinan daga ke har ‘yar ki sun mayar da ku zawarawa, yanzu wa gari ya waya? Shuwa ta saki murmushi Na tsananin ‘bacin rai tana tuno wula’kancin da aka yi musu a fili ta furta “Wallahi ki rabu da su Umma ba su ci bulus ba, yanzu ne ma za mu d’aura d’amara tsakanin mu da su shege ka fasa kin ga wula’kancin da suka yi mana kuma auren Habeeb mijin Hameedah yanzu na d’aura d’amara sai na mayar da ita abin kwatance, ita dai Zainab ta ha’kura tunda shika uku sun cika cif da Manga ya yi mata na farko an yi d’aya yanzu kuwa ya cike biyu cif, amma Shaheedah kam tamkar ta koma gidanta kafin iddarta ma ta cika zamu je har turkeyn bayan an gama shirya ta tsaf ta yarda in dai ya ganta ba zai iya d’auke idanunsa a kanta ba da kansa zai furta ya mayar da ita d’akinta.” Zainab da uwarta su ka saki ajiyar zuciya har Shaheedah ma sun tabbatar Shuwa zata iya aikata hakan tunda ta furta, don haka hankalinsu ya sake kwanciya kamar tsumma a randa. To fa! Tur’kashi! In ji malam bahaushe.

————————

Ammar yana isa gida Kano direct ya wuce bayan Hisham ya sanar da shi Mommah sun wuce Kano har da Mubeenah, don haka ya wuce can kawai don burinsa ya ga Mubeenah.

A kitchen ya tarar dasu da Mommah a kunyace Mubeenah ta dinga kallonsa tana sakin murmushi. Suka zube anan parlourn Mommah yana ba su labarin yarda Imran ya yi da ya gansu. Mommah ta saki murmushi ta ce “‘Dan nema ai kaga yanzu zai san mahimmancinta ba zai sake gigin sakinta ba, kai dai Allah ya saka maka da aljanna yarda ka yi ri’ko da zumunci ubangiji ya yi ri’ko da hannayenku ya saku a tuba madaidaiciya, Really proud of you my Son.” Murmushi kawai ya saki idanunsa a kan Mubeenah da ta kasa sakin jikinta dashi sai sunkuyar da kai ta ke, hakan da Mommah ta gani ya sata mi’kewa ta shige bedroom wannan damar Ammar ya samu ya ri’ko hannunta ya manna mata kiss had’e da cewa “Maza ki tattaro shirginki mu gudu gidanmu, nima yau na tabbata a ango.” Murmushi kawai ta saki tana zame hannunta.

A daren ranar Mommah da wasu ‘kawayenta suka raka Mubeenah har gidan ta Mommah tayi mata kyautar turarukan wuta da magungunan mata masu tsananin kyau. Mubeenah da Ammar muna yi muku fatan alheri don dai yau na san Ammar ba d’aga ‘kafa.

——————————

Ko da ya dawo daga siyo musu abincin ya tarar har a lokacin bata parlorn alamar har yanzu bata huce ba, shakka babu ya ‘ballowa kansa ruwa. Ya saki ajiyar zuciya kafin jikinsa a sanyaye ya nufi bedroom d’in.

Tana zaune gefen gado ta ci black jeans da red hug shirt a jikinta, gashinta zube a gadon bayanta, wani sihirtaccen kyau ta yi masa duk da Ba makeup a fuskarta, shi dama ya fison ya dinga ganinta ba makeup. Ciki-ciki ta amsa masa sallamar idanunta akan t.v tana kallon wani series indian film da ake yi a zee t.v. ‘Kamshi da sanyin a’cn ya had’u da na damina ya bada wani sanyayyen ‘kamshi, Imran ya lumshe ido kafin ya ‘karasa gabanta ya zube akan gwiwoyinsa gaba d’aya hannayensa akan cinyoyinta ya d’ora kansa akan su yana sha’ka daddad’an turaren dorot da tayi tsuguno da shi, ji tayi kamar ta cusa hannayenta cikin lausassar sumarsa sai dai ta ‘ki aikata hakan, ta fara ‘ko’karin janye jikinta, amma ya ‘ki bata dama muryarsa a dashe ya ce “Yi min duk hukuncin da kike so matu’kar za ki janye wannan fushin da nake ganin yana ‘bata min fuskarki.” Ya d’ago yana lalubar ‘kwayar idanunta da suka nuna zallar wutar kishin da suke masa. “Please Hayateey.” Ya fad’a yana tura hannu cikin d’amammen cikinta “Yunwa ko?” Shirun dai still ta yi masa hakan yasa shi cicci’barta yana fad’in “Ni da nake da kyakykyawa kamar ki ina ni ina sake tunanin wata mace ko kyauta aka bani zance bana so, daga yau ma suna na mijin kan tace.” Ya fad’a yana kaiwa bakinta sumbata kamar yarda dai ake yiwa jarirai idan an d’aukesu. A ‘kasan carpet ya zaunar da ita yana janyo ledar abincin ya juye a plate “Oya maza ki ci ko na d’ura miki.” ‘Kamshin abincin ya tasiranci yunwar da ta ke ji hakan yasa ta fara cin abincin don tilas ba don ta daina fushin ba. Imran gefe ya ja ya zuba mata ido yarda ta ke komai a nutse. Sai da ta ‘koshi sannan ta mi’ke ta shige d’aki.

Imran ya saki ajiyar zuciya dole yau ya samo mafitar da zata amince dashi. Tunanin da yayi ne yasa ya ce “Good Idea!” Hakan yasa ya ci abincinsa sosai, sannan ya mi’ke ya d’au key ya fice.

——————————

Da daddare tana shiga wanka ya shiga d’akin ya cilla micijin robar kan gadonta, ya fice da sauri.

Tana fitowa tayi shirin ta tsaf da shafe-shafe ta, ta d’auko wata shegiyar rigar barci fara tas da undies d’inta farare tas ta saka ta kama gashinta bayan ta turareshi ta d’aura masa wani tafkeken ribbon fari ta yi kyau sosai tamkar ‘yar tsana, ta kalli kanta a mudubi tana da tabbacin yau Imran sai ya kusa hauka idan ya ganta hakan tana jin kunyar fita amma tana tuno hud’ubar su Hafsa da suka tabbatar mata da haka zata siye zuciyarsa domin ba kunya tsakanin miji da mata.

Ta murd’a ‘kofar bedroom d’innata ta fice, tana ‘yar wa’karta, gaba d’aya jikinta kamar shaking ya ke, ta dusashshen hasken dim light d’in da ya ke parlourn ya hangota ji ya yi numfashinsa na shirin season ya tabbata Shatu so ta ke ta kasheshi in dai yau bata amince dashi ba, ta gabansa ta zo ta wuce don neman magana ya sha’ki ‘kamshin sihirtacciyar Humran da sauri ya runtse idonsa, ba wani abu zata d’auka a kitchen ba dama neman magana ne hakan yasa ta d’au ruwa ta fito, murmushin mugunta ya saki a zuciyarsa ya ce zaki kawo kan ki da ‘kafarki Shatu na shiryawa wannan daren na gaji da dankwaliliya.

Murmushi ta yi bayan shigar ta d’aki, don sarai taji dafin idanunsa suna kewayawa a jikinta, tana
Zama a saman gadon micijin robar na motsawa kamar na gaske har tafiya ya ke idanunta ya kai kansa, kan kace me ta daka tsalle sai bakin ‘kofa tana ‘kwalla ‘kara........

Masu tambayar Wattpad user name d’ina ga shi nan

@Nazeefah381

Jikinta na ‘bari ta ke kallonsa tana nuna masa d’akin da bakinta, kamar bai san komai ba ya ri’kota jikinsa yana fad’in “Lafiya?” A rud’en ta dinga gaya masa miciji miciji ne a bedroom. Ya gintse dariyar da take shirin tona asirinsa tare da ware ido ya ce “What? Miciji kuma? Yau mun shiga uku don micizan garinnnan ba su da mutunci tsaf suke hallaka mutum har lahira.” Tuni ta sake ‘kan’kameshi tamkar zata koma cikinsa. Ya zaunar da su kan kujera don ya ji ‘kafafunsa na son gaza d’aukarsa saboda shaking da suka fara. Da gaske ta rud’e sosai a razane ta ke. “Please ‘kalbeey ka fitar min da shi?” Da sauri ya dafe ‘kirjinsa “Wa? Ni? Ta ina zan iya fita da shi Ai sai dai da safe a kira masu fita dashi, ni yanzu tsoro nama kar ya fito parlour d’innan, Cikin sauri ta mi’ke bai iske ta ko ina ba sai a bakin bedroom d’insa ya danne dariyarsa ya bi bayanta zuciyarsa fal farin ciki.

A gefen gado ya tarar da ita a takure ta kalleshi har zata kwanta ta ‘kudunduna sai kuma ta tuna ba tayi sallah ba da sauri ta mi’ke ta hau dube-dube.
Yana cute smilling alamar kinzo hannu ya ce “Me ki ke nema?” A ‘kuntace ta ce “Ban yi sallah ba kuma ba kayan sallah ta anan.” Yana so ya ce mata akwai kayan Shaheedah a d’akin tunda ba tazo ta kwasa ba bari ya d’auko mata Hijab d’in yana tsoron ba’kin kishinta. Ya ja ajiyar zuciya “Bari na lalla’ba na d’auko miki a ina suke?” “Suna nan saman resting chair”
Da sauri ya fice har da d’an tsallensa a bakin corridor a zuciyarsa ya ce “Yaro man kaza!”

Yana dawowa ya ganta ta mi’ke tsaye wai ta ji motsi a toilet d’in, ya dudduba bai ga komai ba sannan ta yarda ta shiga shima don yana tsaye bakin ‘kofar ta yi brush da alwala ta fito, har zata tayar ya ce ta jira shi shima bai yi sallahr ba.

Tare suka yi sallahr ya jasu nafila sannan kuma suka yi shafa’i da wutiri ya d’an dafa kanta ta ji yana kwararo addu’oi bud’e idonta tayi tana tuhumarsa addu’ar menene ya sakar mata murmushi ya ce “Ta neman zaman lafiya ai tunda aka kawo ki ba muyi ba ko?” Ta d’aga kanta “oya tashi kije ki kwanta.” “Kai a ina zaka kwana na ga ma bedroom d’in naka ba kujera.” Murmushi ya saki ya ce “Kada ki damu dani ni ina iya kwana a zaune ma banda ina tsoron micijin da sai Na koma parlour ma.” Tausayinsa ta d’an ji ta ce “Ai kuma da sanyi ka dai kwanta daga gefen bed d’in ni kuma sai na kwanta a can side d’in.” Yana murmushi ya ce shikkenan ma.”

Har zata kwanta ya mi’ka mata fresh milk mai sanyi da ya riga ya had’ata da desire tablet, ba ta kawo komai a ranta ba ta kwankwad’e sannan ta zame ta kwanta.

Imran hankalinsa kwance ya shiga wankansa har da ‘yar wa’karsa cikin tsananin farinciki ya tabbatar a irin halittar shatu mai saurin amsa kira da ko kiss aka yi mata sai idonta ya canja, da zarar maganin nan ya fara aiki da kanta zata kawo ‘kafarta. Ya dad’e yana wanka da kayan wankansa masu matu’kar ‘kamshi na companyn makari,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login