Showing 99001 words to 102000 words out of 117786 words
ta san ba su kad’ai bane a gidan tabbas yau da sai ya gane kurensa da a hakan zata fita kuma duk nacinsa ba zata bari ko ra’bar jikinta ya yi ba.
Shima ya yi wanka, ya sha wasu ‘kananan kaya na companyn Gucci wandon ash rigar ba’ka sai p cap da yasa a kansa Ash mai ratsin black a kansa, ya yi kyau sosai ba d’an kad’an ba. A bakin mirror d’in da take veilling kanta ya tsaya, ya ziro kansa ta saman wuyanta yana shinshinar ‘kamshin turarenta, gugar da jikinsa ya ke mata ya sa ta feeling wani iri hakan yasa ta saurin janye jikinta tana masa kallon ‘kasa-‘kasa ta ce “Ni fa bana so ka dinga yawan had’a jiki da ni har sai lokacin da shekara ta yi ka tara mutane ka sanar dasu irin son da ka ke min, sannan ka yi min lefena.” Murmushi kawai ya ke yana d’aga mata gira “Wani abi ki ke ji idan na had’a jikin da ke?” Turo baki ta yi kafin ta fice tana cewa “Ni ba wani abu da nake ji ni dai kawai ba naso.” Jawota ya yi ta baya ya ce “Gangan kenan in dai ba wani abu ki ke ji ba to ki barni na sha sharafina sauran abin kuma ki ri’ke kayanki har sai shekarar ta yi in dai kin yarda nima na yarda.” Bata amsa masa ba ta janye jikinta ta fice daga bedroom d’in a zuciyarta ta na cewa “Gangan kenan in dai zan amince da
Haka ai gwara kawai na yarda da wancan d’in.”
Tana zama ya shige inda Ammar ya ke yana kwance yana zabga waya da mubeenah yana ganin Irman ya yi masa alamar menene da hannu? Imran ya ce “Ka fito mu tafi eatery ko?” Ya girgiza kai “Ba dani ba naje naga abinda yafi ‘karfina kamar yarda kace ka taho min da take away.” Imran ya fice yana yi masa da’kuwa da cewa sai kasa matarka ta raina ni na san tana ji ta waya.
Tunda suka fita yake janta da tsokana iri-iri sai dai bata tanka shi ba tayi kicin-kicin da Fuska. Shopping ya fara kaita wani babban mall, ta dinga jidar kayan girke-girke duk da ba yanzu zata nuna masa ta iya girkin ba sai ta gama wajiga shi da kwa’ba da shirme kala-kala ta ga da gaske zai iya zama da ita a kowane hali, ko kuwa don ya ga ta goge ne ya damu ya dawo da ita.
‘Bangaren English Wears da kansa ya dinga jidar mata haka nan sleeping dress ya fiso ya yi ta ganinta da irin kayan da turawa suke sakawa a t.v su da ba wani body shape ne da su mai kyau ba.
Shatu bata hana shi ba sai dai a zuciyarta ta ce “Zaka yi dana sanin siyan kayan nan da kanka.” Ta dinga smilling wanda daga ganinsa na mungunta ne.
Daga nan direct eatery suka wuce suna tsayawa ya ce “Take away zamu yi ko me madam?” Fuska a murtuke tace “Take away.”
Girgiza kai ya yi ya shige ciki. Ita kuma ta bi bayansa da kallo tana sakin ajiyar zuciya.
Tana gama cin abinci ta shige bedroom ta gar’kame da key, tana sakin dariyar mugunta.
Bai kawo komai a ransa ba ya zata duk abinda take fad’a iya bakinta ne, don haka yaje ya she’ka wankansa ya saka wasu kayan barci masu shegen kyau, da taushi. Sai murmushi yake da alama yana tunanin yarda zai gwangwaji amarci.
Sai dai me yana murza ‘kofar d’akin ya jita a gar’kame da alama password d’in lock d’in ta canja tunaninsa bai ta’ba bashi zata iya canja password d’in ba. Knocking d’in da ya dinga yi bai sa ta bud’e ba sai dariya ta ke tana cewa ka tafi da wajen Shaheedah cele mai zaka yi da ni Shatu mai kama da baroro.
Ji yayi tamkar ya kurma ihu, ya juya cikin wani irin yanayi ya tafi bedroom d’insa ranar dai kam da kyar ya yi barci.
———————————————-
Da sassafe ta shiga kitchen kamar abin arziki, ta shiga jagwalgwala girki, musamman sanin cewa Ammar ya tafi bare ya toni asirinta yace ta iya girki, tsaf ta jagwalgwale abincinta ta zabga yaji da gishiri ga d’anyen kwai ko albasa bata saka masa ba ta saka d’anyan dankali a ciki ta soya kwa’ba dai zalla ta ding yi.
Ta kuma shirya su a dinning kamar wani had’add’en abinci, ta gyara gidan tsaf sai ‘kamshin turaren ruwa da ta zuba a humidifier ya ke yi.
Har zuwa lokacin da ta yi wanka ta shirye cikin wani wata matsatstsiyar riga iya gwiwa maroum colour, ta futar da duk wani shape d’inta.
Zama ta yi a parlour har zuwa sanda ta ji motsin bud’e ‘kofarsa da sauri ta juya idanunta suka sar’ke da nasa da alamu ya nuna bai samu isashshen barci ba........
Da sauri ya iso inda take yana sakar mata murmushi duk da da fushinta ya kwana a ransa bai nuna mata haka ba, kuma tun a daren ya nema mata gafarar Allah shi dama don tashi ya yafe mata don ba ya son a kamata da irin laifin da aka ce ana kama masu gudun miji ranar Al’kiyama musamman tsinuwar mala’iku.
Sunkuyar da kai ta yi tama kasa had’a ido da shi don ta san abinda tayi bata kyauta ba. Musamman Mommah ta zaunar da ita taja kunnenta akan cewa duk laifin da mijinta zai yi mata kada ta sake ta gujeshi domin hakan haramun ne sannan yana ragewa mace ‘kima a wajen mijinta.
Murya a sanyaye ta ce “Ina kwana.” Yana murmushin ya ja hannunta ya mi’kar da ita tsaye ya had’e jikinsu guri d’aya tare da zuba mata kyakykyawar sumbatar da ta kusa sata rasa numfashinta
na sakwanni. Da gaske ta amshi sa’konsa, ya tabbatar da hakan har cikin zuciyarsa ganin yarda ‘kafarta ta ke shaking ta ma kasa tsayuwa. Imran ya saki murmushi a zuciyarsa ya ce “Mu je zuwa a hakan za’a kai shekarar da ta ke zance da common kiss ya sata a wani yanayi ina ga ya aikata mata wasu abubuwan da suka zarce kiss, ya tabbatar indai suna gida d’aya sai ya sata karya al’kawarinta da kanta don shi ma’abocin romancing ne.
Cak ya d’auketa duk da yaji nauyinta, kasancewarta akwai cikar hips da mazaunai. A kujerar dinning ya zaunar da ita yana sakin ajiyar zuciya da nishi ya ce “Cab nan gaba ashe ‘kiba za kiyi ba ta wasa ba.” Had’e rai tayi kafin ta ce “Idan na yi ‘kibar ai sai ka sakeni tunda ba ka son ‘kibar.” ‘Dal ya d’alle bakinta “Allah ya sa na sake jin wannan bakin mai kama da
Gidan tsutsa ya ambaci kalmar saki ba ki san ba kyau ba? Ni da ke ai mutu ka raba ne takalmin kaza, mutuwar ma ina fata ta d’auke mu rana d’aya mu shige aljannah tare ko my life.” Murmushi ta saki ta sar’ke hannunta waje d’aya ta na nuna masa abinci “Break fast is ready ka yi sauri ka ci kada ya yi sanyi.” Direct ya kalli cikin ‘kwayar idonta ya ce “Ke fa?” Ta girgiza kai tana shafa cikin ta ce “Bana break fast da wuri saboda kada na yi ‘kiba ka yi min kishiya.” Dariya sosai ya saki har ta shagala da kallonsa ganin yarda dariyar ta yi masa kyau sosai, ta shiga godiya ga ubangiji da ya mallaka mata shi a matsayin miji ta tabbata ko kallonsa kad’ai ta ke ya wadace Samun farin ciki.
Ya bud’e warmers d’in yana bin abincin da kallo da ido ya ke ganin kamar zai yi dad’I hakan ya sa ya fara had’iyar yawu, tun Karin ya ci.
Tea flask ya nuna mata “Zuba min
Coffee ki samu lada mana My life.” Ta mi’ke ta fara had’a masa coffee d’in shi kuwa ya shagala da kallonta musamman yarda rigar ta yi mata kyau ta kwanta ta fito kuma da duk wata sura Ta jikinta, tudun ‘kirjinta ya bayyana sosai ksancewarta mai fuller breast.
Tana juyowa ya saki ajiyar zuciya ya d’auke idonsa da sauri yana murza goshinsa.
Spoon d’aya yayi na abincin yayi saurin rintse ido da
Farko dankalin bai dahuba ga uban gishiri da ta lafta ga ‘karnin
‘Kwai, da ‘kyar ya had’iye lomar bakinsa shima don ta tsareshi da idanunta ne ga shi ta ‘bata fuska “Ba dad’i ne? Ai dama na san cewa zaka yi ba dad’i duk wahalar da na yi Na dafa saboda ka saba cin Na matarka mai dad’i.” Ta fad’a tana bubbuga ‘kafafunta a ‘kasa da gaske kuka ta ke kamar ba plan ta shirya ba. Imran ya mi’ke da sauri ya ri’kota, zaunar da ita ya yi kan cinyarsa da dukkaninsu jikkunnansu suka amsa wannan had’uwar, cikin canjawar murya da bugun numfashi ya rad’a mata “Ban fa ce miki ba dad’i ba, It is
So delicious na manta ne ban gaya miki doctor ya hana ni cin gishiri da mai ba.”
Wani kukan ta sake fashe masa da shi tana mutsu-mutsu a jikinsa da shi kansa bai san lokacin da
Ya shiga aika mata wani zafaffen romance da ya ke yinsa a gigice cikin wani irin zazzafen yana yi da gaske ne sosai jikinsa ya samu mahad’insa bai ‘ki komai ma ya faru a parlourn ba, ita kanta mai cika bakin tuni ta lula wata duniyar don bata san ma a inda kanta ya ke ba. ta tabbatat Imran ya haddace iya romance,
Wani abu da ya yi mata da zai sani wuyat rubatawa ne ya sata saurin janye jikinta tana maida numfashi idanunta duk sun birkice ta mi’ke tana tattare yamutsatstsen gashinta da aka bi aka hargitsa mata shi, shi kansa gashin ya ji kisses balle ‘kirjinta da har rad’ad’i ta ji yana yi mata.
Da gudu-gudu ta shige bedroom d’inta kasancewar rigar tata ya yaga ita kuwa kunyar tsayawa ta ke a haka.
Imran ya bita da kallo cikin tashin hankali ji ya ke kamar ya janyo ta ko fyad’e ya yi mata. Ya dad’e a kwance a wajen cikin wani yanayi da ko ranar da ya santa a d’iya mace bai shige shi ba ko don yanzu ta sake cika ne ta ko ina, ga shi ba ta bar shi ma ya kusanceta ba ta ‘kwace jikinta ta gudu. Ya runtse idonsa yana tunanin anya kuwa zai iya amince wa da shirmen Shatu Na cewa sai an shekara da aure zai kusanceta suna gida d’aya ashe kuwa tabbas wata rana za’a tsinci gawarsa.
Da kyar ya mi’ke hannunsa dafe da ‘kasan cikinsa ya shige bedroom d’insa, direct toilet ya shige ya sakarwa kansa shower yana fatan samun nutsuwa amma ina
A duk sanda ya runtse ido surorin Shatu ke yi masa gizo. Haka ya lalla’ba ya fito ya zube a saman gado bayan yasa gajeran wando da vest,
Sosai ya ware a.c d’in d’akin yana fatan samun sau’kin abinda ya ke ji.
Shatu wanka ta yi sosai don kuwa wankan tsarki ya kamata, ta yi drying gashinta kafin ta sake saka man gashi ta turara shi duk da ta tabbatar turaren da ta ke masa shi ya jawo masa yau shima sai da aka sid’eshi Tas, murmushi ya su’buce mata tuno sumbatun da ya dinga yi mata a kunne tun ma ba aje ‘kololuwar ba Kenan, ta tabbata soyayyarta ta gama yi wa Imran dabaibayi ko yanzu ta bashi kanta ta san ba zata yi da Na sani ba amma ina ai sai ta ja masa ajin da sai ya wahala sannan zata amince masa.
Ta yi tsalle a gado ta na godiya ga Allah da ya bata miji tamkar da
Dubu a fagen romances da soyayya ta tabbata ya cigaba da
Aikata mata irin na yau to tabbas zai mallaketa sai abinda ya ce zata dinga Aikatawa.
Wannan karan atamfa ta saka duk da shima d’inkin fam d’arinka tsirara ne domin duk d’inkunannata ba na arziki haka Mommah ta sa a kayi mata su zubin karuwai so dai ta ke d’iyar tata ta zama karuwar cikin gida.
Kanta ba d’ankwali ta fito sai gashin da ya kwanta a bayanta. Ta dad’e a parlourn tana dakon fitowar sa sai dai shiru ku san 2 hours ba shi ba kamar sa ga yunwa da ta ke sasa’kar cikinta, tunani ta fara yi ko fita ya yi zuciyar ta ta hasasho mata shi yana can ya nemi wata macen a waje ya samu ya sauke mata jarabar da ta ke Cinsa.
Ai da hanzari ta mi’ke don bata san sanda ta kai kanta bedroom d’insa ba saboda tsananin kishi da ya ke cinta.
Turus ta yi ganinsa a kwance ruf da ciki ya dafe cikinsa, yana jinta ya sake runtse idonsa baya san ganin ta saboda kallonta zai sa ke sabinta masa mikin ciwon mararsa.
Jikinta a sanyaye ta zauna a gefen gadon bata san sanda ta zuba hannunta cikin sumar gashinsa ba cikin tashin hankali bayan ta ji zazzafan zazza’bi a jikinsa ta ce “‘kalbeey mai ya Sameka?” Da sauri ya runtse idonsa da sunan da ta kirashi da muryar da ta ambata wajen kiran hannun da tattausan hannunta da suka dam’ki gashinsa suka haifar masa da wata zazzafar sha’awa da gaske Shatu so take ta tarwatsa shi...........
(Ku yi ha’kuri jiya wayata ce ta samu matsala shi yasa ku ka jini Shiru)
Da kyar ya bud’e idanunsa ya zube su cikin nata kafin ya furta “Please Hayateey ki taimaka min wallahi zan iya mutuwa a condition d’in da nake.” Da kyar muryarsa ta ke fita yayin da yake maganar da alama iya gaskiyarsa ya ke furtawa har ‘kasan zuciyarsa. Hannunsa ta kama tana matsawa cikin nata kamar zata amince da bu’katarsa sai dai tuni wata zuciyar ta sake ce mata da sauran lokaci.
Yana ‘ko’karin janyota ta yi saurin mi’kewa bai tsince ta a koina ba sai bakin ‘kofa hakan ya tunzira zuciyarsa ya ji ransa ya matu’kar ‘baci a zafafe ya ce “Na wa kike bu’kata in baki in dai zaki amince na samu sau’kin abinda na ke ji zan baki.” Turus ta ja ta tsaya zuciyarta ta karye da tausayinsa duk da tsoron Allah ya shigeta ta fara nadamar abinda ta aikata ko ma ta ke kan aikatawa sai dai tuni shaid’an ya rinjayi zuciyarta ta juyo tana masa wani irin duba “Bana bu’katar ko kwabo kafin na sallama maka gangar jikina, sai dai tabbas ina bu’katar na sani so na kake ko kuwa sha’awata, kuma da kanka ka ce ka amince da sharad’ina sabida haka sai ka jira lokaci. Maganganunnata tamkar d’igar dalma ne a ciwo yanayin yarda ya ke jin saukar su a zuciyarsa, cikin wani yanayi ya ce “Amma dai kin san soyayya ce ta ke kawo ka ji ka na sha’awar mutum ko? Please Shatu kada ki sa na fara dana sanin rabuwa da Shaheedah wallahi ba haka ta ke min ba duk tsananin fad’an da muka yi da ita tana bari na kusanceta.” Wani kishine ya taso ya tokare mata ‘kirji, har gumi ke tsatstsafo mata ta ji duk wani tausayinsa da ta ke ji ya kau, haushi da takaicin furucinsa suka bi suka goge wancan ‘bur’bushin tausayinnasa, kan ta tsaye ta ce “Me zai hana ka dawo da ita ta baka abinda ni na hana ka.... kuma ka jawowa kanka da niyyata na zo na baka abinda kake so amma wallahi wannan furucin yasa sai na tabbatar da sharad’ina idan yaso bayan Shaheedah ka ‘karo uku ma.”
Daga haka ta rufe ‘kofar da ‘karfi zuciyarta na sake bugawa kamar zata tsaga ‘kirjinta ta fito.
Imran kuwa runtse idanunsa ya yi yana da na sanin furucinsa madadin gyara gashi ya sake hassala zuciyarta har yana hango tsananin fushin da bai ta’ba gani ba akan fuskarta.
Da kyar ya rarrafa ya mi’ke ya na bin bango ya isa kitchen lemon tsami mai yawa ya matse a cup ya zuba gishiri kad’an ya runtse ido ya sha. Sannan ya dawo parlour ya sake kwanciya ya runtse idanunsa.
Shatu kuwa hawaye ne ya ‘balle mata a cikin bedroom na zallar kishi da takaicin d’a namiji ko ita ta saka ya rabu da matar tasa. Duk tsananin yunwar da ta ke ji tuni ta nemeta ta rasa ta zauna gefen gado tana lalubar numberr Mommah a sabuwar wayar da ya had’a mata yau da safe. Amma wayar sam ta ‘ki tafiya hakan yasa ta sake sakin kuka. Kukan da yasa Imran saurin nufar bedroom d’in, tana ganinsa ta hau cillinshi da pillow tana furta ka fita ka fita! Bana son ganinka ai ba yau ka fara fifita Shaheedah a kaina ba, ni dama mecece banda baroro mai warin baki.
Da sauri ya nufeta amma ina ta mi’ke a sukane ta shige toilet ta murza lock. Imran ya yi turus yana mamakin tsananin kishi na Shatu wannan da kishiyar za’a yi mata ya zata yi. Ya saki murmushi yana had’ata da Allah ta bud’e Shatu ta yi mursisi ta ce ba zata bud’e ba, haka Imran ya fice daga d’akin ya nufi samo musu abincin da za su ci.
Da kyar ya bud’e idanunsa ya zube su cikin nata kafin ya furta “Please Hayateey ki taimaka min wallahi zan iya mutuwa a condition d’in da nake.” Da kyar muryarsa ta ke fita yayin da yake maganar da alama iya gaskiyarsa ya ke furtawa har ‘kasan zuciyarsa. Hannunsa ta kama tana matsawa cikin nata kamar zata amince da bu’katarsa sai dai tuni wata zuciyar ta sake ce mata da sauran lokaci.
Yana ‘ko’karin janyota ta yi saurin mi’kewa bai tsince ta a koina ba sai bakin ‘kofa hakan ya tunzira zuciyarsa ya ji ransa ya matu’kar ‘baci a zafafe ya ce “Na wa kike bu’kata in baki in dai zaki amince na samu sau’kin abinda na ke ji zan baki.” Turus ta ja ta tsaya zuciyarta ta karye da tausayinsa duk da tsoron Allah ya shigeta ta fara nadamar abinda ta aikata ko ma ta ke kan aikatawa sai dai tuni shaid’an ya rinjayi zuciyarta ta juyo tana masa wani irin duba “Bana bu’katar ko kwabo kafin na sallama maka gangar jikina, sai dai tabbas ina bu’katar na sani so na kake ko kuwa sha’awata, kuma da kanka ka ce ka amince da sharad’ina sabida haka sai ka jira lokaci. Maganganunnata tamkar d’igar dalma ne a ciwo yanayin yarda ya ke jin