Showing 105001 words to 108000 words out of 117786 words

Chapter 36 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

739

ya fito d’aure da towel a jikinsa sai ‘karami a hannunsa yana goge sumar kansa yana sane ya ‘ki sako bathrobe so ya ke Shatu ta ganshi a haka ya sake cilla mata wani assignment d’in.

Shatu ta ware ido daga kwancen tana kallon Imran ashe dai da gaske ingarman namiji ta ke aure jikinsa a murje ya ke da alama yana shan training. Wata kunya ce ta kamata kasancewar bata ta’ba ganin namiji a haka, take kuma wasu irin abubuwa suka fara mintsilin jikinta da alama maganin ya fara aikinsa. Ta runtse ido tana kiran sunan Allah “Ya rabb kada ka bani kunya.” Imran kuwa ya cigaba da shafa mai a gashinsa da cinyoyinsa sannan ya zira gajeran wando ya nufi gadon bayan ya rage hasken d’akin da sauri Shatu ta mi’ke tana kallonsa daga shi sai gajeran wandon da ko gwiwa baizo masa ba a fisge ta furta “A haka za ka kwanta ba ka jin kunya?” Ya dubi jikinsa menene? Ni dama can bana iya barci da riga damuna suke wai ma ba wannan ba naga kema rigar jikinki da ita da babu duk d’aya.” Cikin tashin hankali Shatu ta juya a zuciyarta ta ce “Na shiga uku wallahi Imran mugu ne yana sane ya ke jefa ni a wannan halin.” Ita kad’ai ta san mai ta gani ta fad’i hakan. Imran gani bata kallonsa murmushi ya saki sosai ya kwanta abinsa yana sake ware air condition d’in d’akin duk da sanyin da ake tsilalawa a waje. Shatu sassan jikinta ya sake d’aukan ‘bari ta rutse hannunta a cinyoyinta dafatan Allah yasa ta samu sau’kin lamarin da take ji. Imran ya kwanta yana sakin ajiyar zuciya ya kunna wa’kar westlife a wayarsa kasancewar sa masoyin westlife d’in tun lokutan baya.


Wa’ko’kin ba abinda suke ‘kara mata idan banda wutar soyayyarsa da wata irin sha’awa da sam bata san ta kai mizanin haka ba a fannin.

Murya a dashe kamar zata yi masa kuka ta ce “Please Ya Imran ka kashe ba fa kyau jin wa’ka da daddare.” Ya juyo yana mata wani irin kallo “Nima ba na ji da daddaren yau ne dai nace bari na kunna tunda ga ni ga hayateey ta a cikin duvet d’aya sanyi ma na ke ji please ki amince mu samu body contact yau dai d’aya ko ma rage jin sanyin.” Ta runtse idonta saboda yarda ya ke mata magana da wani salo bata jin ko bai fad’a ba ita da kanta ba zata kai kanta garesa ba, saboda ta samu sau’kin abinda ta ke ji. Matsawa yayi sosai jikinta su ka samu body contact wanda dukkaninsu sai da suka saki ajiyar zuciya a haka kuma labarin ya sauya salo.

Lamarin da yazo musu a wani irin yanayi kowa burinsa ya nunawa d’anuwansa yarda ya ke matu’kar ‘kaunarsa, Shatu tuni ta manta da wani batun shekara guda ta mi’ka kai Imran ya yi yarda ya ke so da ita, ta sha tsananin azaba fiye da darenta na farko sosai zata iya cewa budurwa ta koma sabida azabar da ta sha, Yau Mommah ta sha kira kai har da su Innaji da Babaji Ikram da Akram kuwa an kira su yafi shurin masa’ki.




————-

Da Asuba da kyar ya bud’e idanunsa ya mi’ke bayan ya zameta a jikinsa da kyar, ya zuba mata ido tana barcinta peacefully beauty face d’inta ta sake fitowa, wani farinciki yake ji yana ratsa shi fiye da farincikin da yaji a first Night d’insu. Da gaske yana tsananin son Shatu Son da shi kansa ba zai iya misalta shi ba, ya sha zumarta da madarar ‘kaunarta wanda Allah yayi mata baiwa da su tabbas su Shatu ne maza suke kiran su da suna matan baiwa. Don kuwa dai komai da komai ta had’a har fiye ma da tsammanin yarda ya zaceta. Rungumar da ya yi mata ne ya farkar da ita cikin tsananin ciwon jiki ta turo baki ta ce “Haka muka yi da kai me yasa ka yi breaking promise d’inmu?” Wata dariya ce ta kufce masa a fili ya ce “Shatu Danger! Da amincewarki fa aka yi komai.. in tuna miki abinda kika ce da shau’ki ya d’ebeki?” Bai yi auneba ya ganta a bakin toilet t shige ta gar’kame.


Wanka take a cikin bathtub amma murmushi ta ke saki ita kad’ai tana tunano da sunayen da ya dinga sumbatu yana kiranta da su amma shine shi zai tsokaneta don tace “‘kalbeey please banda kishiya ba zan iya sharing d’inka da wata banza can ba.” Ta runtse ido tana sake tuno wasu al’amura masu girma da suka waka na a tsakaninsu, murmushi ya su’buce mata tabbas ta yi dace da samun ingattacen namiji mai cikakkiyar lafiya wanda indai ya cigaba da abinda ya ke mata tabbas zai mulketa son ransa don sai abinda ya ke so zata aikata.


Akan Sallaya ta sameshi idanunta ya sauka akan kayan da ya ajiye mata da ya d’auko a bedroom tana cono baki ta ce “Wai baka ji tsoro ba don Allah ka sake shiga d’akinnan?” Yana murmushi ya d’aga mata kai “kuma micijin yana nan?” Ta sake jifansa da tambaya shima murmushin ya yi ya d’aga mata kai Shatu ta fara tunanin ko dai dama wayo ya yi mata amma kuwa In dai micijin wasa ne ta tabbatar da hakan, sai ta rama ita ma. Da sauri ta zura rigarta suka tada sallah ganin lokaci zai ‘kure musu. Tare suka yi azkar bayan sun karanta matayyassar minal ‘kur’an Shatu ta dubeshi “Ina kwana?” Janyota yayi jikinsa ya ce “Sai kace wani a ‘kauye wannan ce gaisuwar da nake so every morning.” Ya fad’a yana kaiwa bakinta sumba ta. Lumshe ido ta yi a zuciyarsa ya ce ka Shatu akwai kar’bar sa’ko hakan yana nuna ita d’in lafiyayyiyar mace ce.

Ta mi’ke tsaye bayan zame jikinta da tayi, shima mi’kewar yayi yana fad’in ina zaki? Murya a dake ta ce “Zan je na tabbatar da micijinnan na gaske ne ko na ‘karya ne? Idan na tabbatar na ‘karya ne kana sane ka sani na yi breaking promise d’ina ina tabbatar maka sai na rama.” Dariyarsa ya guntse hakan Yasa Shatu fita a hanzarce don son ganewa idonta. Imran ya ri’ke kansa ya ce “Shatu Danger! Ko wannan karan kuma da me zata rama oho ni dai ba na kwashi ganima ba.” Ya furta a fili yana bin ta a baya........


08033748387

08033748387


Wattpad user name

@Nazeefah381


Turus Shatu tayi tana kallon micijin robar, ita kanta bata san sanda ta tuntsire da dariyaba tabbas ta tabbata wawuya, da har Imran ya yi fooling d’inta ba tare da ta ganeba. Dai-dai lokacin Imran ya shigo shima da murmushi d’auke a fuskarsa. Shatu tana ganin sa ta kai masa dukan wasa bayan ta cukuikuye shi, shima dariyar ya ke yana kai mata cakulkulu daga haka wasan ya canja.





—————————-

Shuwa ta sake gyara zamanta idanunta akan malami zance ko bokan da ya ke sake rattabo mata bayani, “Idan har ta jajirce tayi yarda akace d’in bana haufi maganin nan zai yi tasiri mai girman gaske, abin bu’kata kawai kada a kuskure ‘ka’idojin amfani da maganin, sannan sai ta tabbatar shine mutumin da zata fara had’uwa da shi idan kun je gidan sannan zata saka kwallin, ta kuma runtse idonta kafin ta bud’e sai ta tabbatar shine a gabanta.” Shuwa tana murmushi ta ce “Don dai wannan ai ba wani abin wahala bane za’a aikata yarda kace.” Ya girgiza kai “Haka ake so kuskuren yi kamar yarda aka ce shine zai sa lamarin ya juye madadin zazzafar soyayya sai a koma zazzafar ‘kiyayya.”
Shuwa ta mi’ke tana zube masa kud’in da ya bu’kata ko d’ar ba taji ba ta san zata samu fiye da su, a lokacin da Shaheedah ta koma gidan Imran.


Daga nan direct gidan su suka wuce ita da Zainab d’in suka fara ‘kulle-‘kullen yarda zasu samu visar turkey. Bazawarin Shuwa mijin Hameedah suka yi wa magana.
Ba ‘bata lokaci Habeeb d’in ya tabbatar musu za’a samu a cikin sati d’aya insha Allah.


Nan fa aka fara shirya Shaheedah da magungunan mata iri-iri saboda sun tabbatar da zata koma d’in basa tantama da al’amarin mutumin da ya basu maganin don kuwa an tabbatar musu aikinsa kamar yankan wu’ka ne.

Duk wani tattalin arzikinsu ya tafi akan samarwa Shaheedah magungunan gyaran jiki da na mallaka, duk da har yanzu jikin nata ya’ki kar’bar magani don kuwa tana nan jiya i yau a bushen dai babu kyan gani.


—————————-

Shatu kanta bisa cinyar mijinta bayan sun dawo daga yawon da ya kaita na guraren sha’katawa da suke turkeyn. Gaba d’aya jikinta ciwo ya ke mata saboda Imran ya ‘ki barinta ta huta gurzar amarcinsa ya ke sosai da sosai, tun tana hanashi har ta ‘kyaleshi saboda itama hakan abin alfaharinta ne ta tabbata dad’inta da ya ke ji ne yasa ya ma’kale mata.

Fatarta ta sake fresh sai wani shining ta ke, wasa ya ke yi da gashin kanta wai shi yana mata kitso wanda tana da tabbacin daga nan labarin zai canja salo.

Wayarta ta zara ta fara kiran Mommah rabonta da waya da ita tun yammacin jiya, Akram ne ya d’au wayar da gwarincinsa ya ce “A ne?” Shatu ta tuntsire da dariya kafin ta ce “Ai bakinka ne A ne d’in ina Mommah bata kace Mimi ce.” Cikin murna ya ce “Hi Mimi auce ja ki jo?” Ta ce “Soon Insha Allah Akram d’ina.” Mommah ta kar’bi wayar da farin ciki ta ce “Ya aka yi Shatun Mommah?” Gaisheta ta yi sannan ta ce dama na kira ne mu gaisa” “Masha Allah nagode ‘yar albarka ina Imran?” Ta kalli Imran da ya shagala gefe d’aya yana abinda ya ke so da jikinta, da sauri ta kashe wayar ganin yana neman ya sata ta saki ihu cikin wayar, ta mi’ke da gudu shima ya rufa mata baya yana mamakin yarda
Sam baya iya d’agawa Shatu ‘kafa ba kamar Shaheedah ba da ko da tana amarya bai damu da ita ba sai ya kwana uku ma a lokacin bai kulata ba, banda Shatu da ya mayar kamar abincinsa kullum suna cikin ruwa kamar agwagi tabbas ya yarda da aka ce mata suna suka tara......



Suna fitowa daga wanka Shatu ta saka wata riga ‘yar ‘bigila armless da bum short ba ta yi drying gashinta ba don ta san ba mamaki da ta gama drying d’in a sake komawa ruwa shi yasa sam basa rabo da mura.

Tuni ta saba da saka ire-iren kayan don Imran ya ce ya fi sonsu ya yi ta ganin cinyoyinta a fili suna tafiya da imaninsa. Tana kwancen a jikinsa suka jiyo nocking mamaki ya kamasu don su basa ba’ki ko ma’kota ba huld’a suke da su ba, Imran ya zame ta daga jikinsa yana mi’kewa, zai bud’e da sauri Shatu ta ri’keshi “Haba ‘kalbeey ji fa kayan da suke jikinka idan kuma mata ne fa, bari ga rigar da nayi sallah.” Ta zura rigar ta nufi bud’e ‘kofar shi kuma ya shige bedroom.

Tana zuwa ba tare da ta tambayaba kawai Ta bud’e ‘kofar.

Turus ta yi ganin Shaheedah da iyayenta, Shaheedah ta ji kamar ta yi hauka shikkenan aikinsu ya ‘baci ita kanta Shuwa jikinta har rawa ya fara yi sabida tashin hankali amma sai ta maze ta dake tana zabgawa Shatu da duk jikinta ya yi sanyi harara. “Wuce ki bamu guri gidan mijinta ta dawo.” Shatu cikin ‘bacin rai ta tuntsire da wata irin dariya ta ce “Ashe ya dawo da ita? Ai ban sani ba.”
Zainab da ta ji tamkar ta sha’kota ta ce “To matsiyaciya jikar bararoji tun yaushe ya yi waya yana neman biko ki matsa nace kafin na mangare ki.”
Shatu ta ji wani abu ya tokare mata numfashi bata tantama kishi ne,
Ita Imran zai yaudara har yaje biko ba tare da saninta ba sai gani kawai ta yi mata ta dawo? Cikin ‘bacin rai ta juya ta shige ciki.

Sabida gumin da ta ji yana bin jikinta ta ma manta da kayan da ya ke jikinta ko tsananin kishi ne oho, ta cire after dress d’in ta wurgar, nan fa idonsu ya yi kyakykyawan gani diri iya diri, bata bi ta kansu ba ta shige bedroom d’in Imran cikin masifaffen tashin hankali.


A kuma lokacin ne Shuwa da bata sare ba tace Shaheedah ta sake fito da kwallin ta gwagud’a a Idonta. Shaheedah kuwa tana rawar jiki ta fito da kwallin duk da ita jikinta ya yi sanyi ta tabbatar mai zu’ke’kiyar mace kamar Shatu ba abinda zai yi da ‘kemasashshiya kamarta, amma haka nan ta bi umarnin Shuwa ta sake ranbad’a kallon.



Sosai jikinta ya ke jijjiga yana rawa da kumbura baki cikin matu’kar masifa take kallonsa, shi kuwa gaba d’aya idanunsa yawo suke a jikinta musamman da take shaking d’in komai nata na girgiza sai ya ga kamar dama don ta tsokaneshi ta ke yi, ya mi’ke tsaye da nufin kamata. Da sauri ta sa hannu ta dakatar da shi “Ka da ka fara yaudarar kanka wajen rungumata hakimar taka na parlour tana jiranka, ni zaka yaudara ashe har ka yi bikon matar ka ka dawo da ita ban sani ba, shine zaka yaudareni.” Kallonta kawai ya ke yana murmushi kafin ya ce “Wacece mata ta kuma ina da wata matarne bayan ke Hayateey?” A zafafe ta ce ka fita ka gansu mana gata can da iyayenta sun kawota ni zaka mayar sha ka tafi wallahi b zan zauna ba dole ka mayar dani gun Mommah duk masifa ka zauna ta baka abinda ni ba na baka...” kuka sosai ta fashe da shi da hakan har ya tashi hankalin Imran saboda ba ya san kukan Shatu ya kai mata kyakkyawar runguma, yana aikin lallashi wanda daga haka komai ya canja, dama dai Shatu in dai zata jita a jikin Imran shikkenan duk nutsuwarta sai ta kau, saboda tsananin soyayyar mijinta, hakan yasa mata sha’awarsa mai zafi tabbas ta yarda gangar jikin Imran itace mahad’in tata gangar jikin.




A parlour kuwa Shaheedah ce ta kasa zaune ta kasa tsaye Shuwa ta sake ambula mata sihirtattun turarukan da ta tabbatar idan wani bai yi aiki ba tabbas wani zai yi, cikin masifa bayan sun gaji da jiransu Shuwa ta ce ki tashi ki bishi uwar d’akin ki tabbatar kuma ‘kwayar idonki ta gwauraya cikin tasan idan kin ga da dama ma ki kai masa kyakkyawar runguma ya sha’ki sihirtattun turarukan nan idan ya so ya kusanceki ko a gaban shegiyar bararojin ne kinga daga nan babu haufi aurenku ya mayu.”


Shaheedah jiki a salu’be ta mi’ke ta nufi bedroom d’in, tana ayyana matu’kar burinta ya cika sai ta mayar da Shatu abar kwatance don da gaske sai ta wula’kanta rayuwarta. Dai-dai lokacin da ta saki dariyar mugunta a kuma lokacin ta tura ‘kofar bedroom d’in, idanunta suka gane mata abinda ya sa wani abu ya tokare mata a ‘kirji Imran ya yi sak bayan idanunsa sun sauka cikin na Shaheedah......



Jikar Nashe.....
Follow me on my Wattpad

@Nazeefah381


Yanayin da ta riskesu ya fi gaban na rubuta, cikin zafin zuciya ta juya ta fice daga d’akin, Imran ya saki tsaki yana mamakin dabbanci irin na Shaheedah, ashe da gaske Shatu ta ke su d’inne suka zo? Ya shiga tunanin me ma ya kawo su? Mai kuma suka zo yi masa?.


‘Ko’kari sosai yayi wajen daidaita nutsuwarsa ya mi’ke had’e da fad’awa toilet da kansa ya had’a musu ruwan wanka ya fito mata da wata riga da da kad’an ta wuce cinya mai yankakken hannu, za tayi musun sawa ya ce “Ita nake so ki saka ina son nunawa mutanennan yanzu ni ba sa’an aurensu ‘yarsu bane, ina da matar da direct zan iya kiran ta fi kowa kyau a wajen diri kyan fuska kai everything ma.” Ya fad’a yana gyara mata gashin da yayi mata drying d’inshi a lokacin.


A gefen jikinsa ya rungumeta (side hug) suka fice daga bedroom d’in cikin murmushi yana rad’a mata special words a kunne da ya sata sakin dariyar da bata shirya ba.
Dariyar da ta ja hankalin su Shaheedah da take zaune tana kuka, d’if gaba d’aya ji da ganinsu ya d’auke cikin matu’kar tashin hankali, su da kansu sun san Shatu ta riga ta zarce Shaheedah da komai ma. Idanunsa ‘kasa-‘kasa bayan sun zauna Shatu na jikinsa ya ce “Barkanku da sauka, me yake tafe da ku?” Zainab da taji tamkar ta tashi ta rufe shi da duka ta runtse idanunta kawai, Shuwa ce tayi ‘karfin halin kawar da kanta ta ce “Imran alfarma muka zo nema duk da dai munzo ba shiri, amma kayi ha’kuri ka mayar da Shaheedah d’akinta tunda dai akwai sauran igiyar aure abinda yasa kenan muka yi tattaki takanas muka zo.” Wani kallo ya bisu da shi kafin ya ce “Ki yi ha’kuri tun ina ganin sauran mutuncinku, ku fice min daga nan, Alhamdulillah a yanzu Allah ya tsamoni daga halakar da kuka cillani, ta ‘kin bin umarnin mahaifiyata ku ka saka na dinga bijire mata shine yanzu kuke son ku sake mayar dani halaka, ba zan mayar da ita har abada kuma na haramtawa kaina aurenta, ko da ace ban auri Shatu ba balle Aysha ta fiye min duk wata mace in dai da sunan aurena a rayuwata, tana da Qualities da zan iya zama da ita ita kad’ai ba tare da kishiya ba, ta kuma tattare ni’imomi da yawa da ni kad’ai na san sirrinsu, ko na had’ata da wata macen ba zan iya koda kwatanta adalci a tsakaninsu ba balle na aikata adalcin. Kun bani mamaki ma da har kuka yi tunanin zan iya cigaba da zama da ita bayan kamata da nayi da aikata shirka ‘kiri-‘kiri, godiyata ma ga Allah da bamu had’a zuri’a da ita ba da abin sai ya fi min ciwo da wani ido zan kalli d’an a lokacin da ya tuhumeni me yasa ban samar masa uwa ta gari ba, Am sorry to say ba zan ta’ba sake mayar da aurenmu ba har gaban abada Allah ya bata miji wani kamar ni ko ma mafiyi na.”

Ji suka yi gaba d’aya kawunan su sunyi nauyi, zu’katansu na na hank’oron ‘bacin rai wato duk ku’din da suka kashe ya tafi a banza kenan? Gaba ‘daya kuma ku’dinna su suka kwashe a hidimar Shaheedah da niyyar ubangiji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login