Showing 30001 words to 33000 words out of 117786 words
abokansa sai kuma suka ji an sake d’aura auren Imran da Aysha mujittafa....... gaba d’aya abokansa suka waro ido suna kallonsa shi d’in ma kallonsu yake....
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-19
ELEGANT ONLINE WRITERS....
Ina mi’ka d’umbin godiyata ga masu karatun littafinnan nagode ‘kwarai da gaske da soyayyar da kuka nuna min da littafin me zan yi da ita?burina dama saka nishad’i a zuciyarku. Ina alfahari daku I Really appreciated wallahi, da zan iya da na mayar dashi 2pages kamar yarda kuka bu’kata, to hakan ba zai yiwuba ina da scheduled da yawa so am sorry kuyi ha’kuri dani a hakan har muje inda zamu. Nagode sosai.
**********************************
Aliyu ne ya dafa Imran yana dariya “Amma lallai guy d’in nan ka raina mana hankali yanzu dama mutum biyu zaka aura baka gaya mana ba” Abdul ya girgiza kai yana murmushi yace “wonderful ni bama wannan ba how comes kai da baka son hayaniya ka auri mata biyu ina cika bakin da kake mana na cewa mace d’aya ta isheka?” Yana jinsu duk suna surutunsu ya kasa furta komai zallar tunani da zuciyarsa ta tafi,sai zufa yake tunani yake wacece ita wacece ma wata Aysha da aka d’aura masa aure bai sani ba, tabbas ashe kuwa tayi shirin zama bazawara don sam bai ga dalilin da zai sa ya amince da mace har biyu ba. Koma waye ya bawa dahda wannan gurguwar shawarar. Tsawon lokaci zuciyarsa ta kasa hasasho masa shatu ce yarinyar gaba d’aya zuciyarsa ma bata hasasho masa shatu ba tunani yake a cikin ‘ya’yan abokan dahda da suka mayance masa cewa suna sonsa aka d’auki d’aya aka bashi. Bai cewa abokansa komai ba duk da surutan da suke masa, burinsa yaga dahda ko Ammar amma ba d’aya da ya gani,hakan yasa dole suka shiga motocinsu suka tafi masauki.Imran dai ya zama tamkar mutum mutumi.
Amarya shaheedah kuwa a bakin yayyenta maza da suka dawo dga d’aurin aure ta samu labari.shaheed da ya shigo a rud’e ne ya dafa ta murya can ‘kasa yace “How comes shaheedah duk cika bakin da kike yi ba zaki zauna da kishiya ba sai gashi ko tarewa ba kiyi ba angonki ya auri wata zai had’a ta dake.” Shaheedah da bata d’au zancen serious ba ta zabga masa harara “God forbid don Allah shaheed ka daina wannan wasan bana son sa as per as am alive ko kallon ‘yan mata ba zan bar habibi yayi ba balle kishiya over my death body” shaheed murmushi yayi kafin khalil ‘kaninta yace “ai kuwa kin makaro don kuwa mata biyu aka d’aurawa aure da habibinnaki ke da wata Aysha.” Da sauri shaheedah ta mi’ke tana kallonsu “please don Allah kuce min wasa kuke?what a nonsense?” Khalil da shaheed suka sake tabbatar mata haka nan sauran mutane da suka je d’aurin aurenma suka tabbatar mata,dalilin da yasa ta yanke jiki ta fad’i, tuni nmufashinta ya d’auke,hakan yasa da sauri aka rufu akanta ana ‘ko’karin ceto ranta.
‘Yan kano kuwa tuni labari ya riski zainab ta hanyar mutane masu sanar da ita fad’uwar shaheedan da dalilin fad’uwarta ta.cikin tsananin mamaki take cewa “mata biyu a haba dai ba kuji da kyau ba idan kuwa hakan ya tabbata tabbas duk wacce tayi ‘ko’karin zama kishiyar shaheedah tayi shirin riskar ba’kin cikin da zai zama ajalinta wallahi.” Da sauri ta mi’ke ta nufi General parlour inda Hajja take.tun kafin ta furta komai hajja ta tabbatar da ba lafiya ba don yanayinta ya nuna ‘karara. Da sauri Hajja ta mi’ke da niyyar ta jata su samu sirri don ganin dada a zaune da itama ta kasa ta tsare, amma ina zainab tuni ta furta abin da ya ri’ke mata ma’kogaro “Hajja da gaske ne? Da gaske ne Imran mata biyu aka aura masa da wata wai Aysha wacece ita?” Gaba d’aya gurin zaro ido su kayi, musamman Hajja da maganar tayi mata dirar mikiya, da sauri ta girgiza kai “wannan ba gaskiya bane ba yarda za’ayi manga ya zartar da wannan hukuncin bai gaya min ba sharri ne da surutu irin na d’an Adam” zainab ta girgiza kai “Hajja babu fa batun sharri a wannan zancen it’s true naji a bakunan da ba zasu min ‘karya ba kuma sun halarci d’aurin auren ga shaheedah canma ance ta sume daga kin zancen.” Hajja ta ja ta zauna ja’bar a kujera “To wacece yarinyar aka ce miki idan kuwa zancennan ya tabbata tabbas manga zai ga ‘bacin raina kuma Imran dole ya saketa koma wacece zancen banza zancen wofi kenan, ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa.” Mommah dake zaune murmushi kawai take zubawa ta tabbata yau gidannan akwai show idan har suka san wacece amaryar.tana kallonsu suka shige d’aki bayan hameedah ta tunatar dasu zancen a sirri ya kamata ayi shi.Mommah ta ta’be baki a zuciyarta tace “oho dai burina ya gama cika.”
Kowa burinsa Dahda ya dawo yaji ya gaskiyar lamarin yake.ko su Hajiya Mama mommah bata gayawaba ta ja bakinta tayi shiru tana jiran kowa yaji labarin kamar dirar mikiya tunda ta lura har yanzu basu san da shatunta aka d’aura aure ba.
Shi kuwa Imran yana can asibiti ya tasa shaheedah gaba da kallo da take ta kuka bayan farkowarta,ta kuma tabbatar da lamarin gaskiya ne.sai ga Imran ya ‘bige da jinya madadin hotunan d’aurin aure da suka ci burin aiwatarwa,irin dai wanda ake yayi a social media d’innan.
Kukan take sosai da har ya ‘karawa Imran zazzafan ciwon kai,ya kama kannasa ya ri’ke tun yana rarrashin ta da yi mata rantsuwar ta kwantar da hankalinta koma wacece idan ya tabbatar da auren sakinta zai yi kuma da gaske yake.amma ina shaheeda bata ji shi ba,hakan yasa kawai ya kama hannunta yana murzawa alamar rarrashi idanunsa a lumshe. Haushi ma lamarin ya bawa abokansa yanda take kuka kamar a kanta aka fara kishiya.Tsawon lokaci sannan aka sallamesu bayan ta gama shan drip.ana komawa gida Abbanta yace ta bari ta warware a kaita. Suna ke’bewa da Imran tace yace kawai a kaita please Imran anty na nake son gani kawai ko zuciyata tayi sanyi.” Tausayinta yasa Imran gayawa wata ‘kanwar babanta cewar a kaita kawai ta ‘karasa warwarewa a gidanta.
Haka kuwa aka yi babu ‘bata lokaci aka tafi airport dama sun yi booking jirgi.amarya dai ta tafi fuska ‘kozai-‘kozai fuska ko kwalliya babu duk da burin da aka ci na budiri a wannan ranar.
Ana kaita ko ta kan mommah da danginta ba abi ba duk da tunasarwar da dangin ubanta suke musu amma Hajja ‘kememe ta’ki yarda tace “ku shige da ita d’akinta mai aka yi aka yi wata dijah balle danginta wa ya san surkullen da suka yiwa manga ya d’aura masa aure da wata yarinyar.ku kaita gurin uwarta ni ina nan ina jiran shigowar manga tunda ya’ki d’aga waya ta.”hakan yasa ba wanda ya sake bi ta kan uwar miji duk da al’ada ta shar’anta a bata damarta a kai mata matar d’anta. Hakan sam bai damu mommah ba tunda burinta ya cika.
Shi kuwa ango Imran yana cikin d’akinsa zuciyarsa sai suya ta keyi shi mamakinsa d’aya dama ana yiwa namiji auren dole? Yana jiyo abokansa suna ta dariyar shegantkarsu.
SHIGOWAR DAHDA**************
Yana dawowa ya tarar Hajja da jama’arta baje a parlourn,gefe d’aya ga Dada da tata jama’ar,zancen dai ya san ake hakan yasa bai san lokacin da murmushi ya ku’buce masa ba ya san sarai za’a rina,Dijah ta jawo masa rigima yau,da bai san yarda zaiyi solving d’inta ba. ya dur’kusa ya gaida su Dada sannan ya ‘karasa gefen hajja ya zauna, Da kyar take amsa gaisuwar da yake mata tana gama amsa gaisuwar ta d’ora da “meye gaskiyar labarin da naji game da aure biyu da akace an d’aurawa Imrana,wacece yarinyar da har ni ban isa kayi shawara dani ba?” Manga waigawa Yayi yaga Dijah bata wajen don haka ya ciro wayarsa ya kira ta yana kallon hararar da Hajja take masa ya cigaba da kiran Imran shima a waya,so yake su hallara duk ayi komai a gabansu. Tsawon mintuna mommah ta shigo da su Hajiya mama, sai ga Imran shima ya shigo jikinsa a sanyaye, ya zauna a gefen mommah, haka nan zainab da su shaheedah su hameedah suma duk suka bayyana.
Sannan manga ya gyara zama ya fara da “kamar yarda kuka saka Imran da shaheedah soyayya har suka amince da junansu suka ‘kaunar junansu haka ita ma Dijah mahaifiyarsa ta bu’kaci son a had’a Auren Imran da shatu yarinyar wajenta.........
Idanu waje kowa yake kallonsa cikin tsananin mamaki.Imran kuwa zama yayi kamar statue yayi masa ‘kuri da ido kawai yana tunani shatu shi aka aura ma Shatu,shatun dai da ya sani ‘kazama shi kuwa mai zai yi da ita a yanzu ba sai anjima ba zai saketa wallahi yaushe zai iya wannan abin kunyar mai zai cewa mutanen da yake cikawa baki yana fad’in mai zai yi da ita? Ita kuwa shaheeda tuni ta zube a jikin hameedah ta ma kasa kuka sai sakin ajiyar zuciya take.
Imran murya na rawa ya fara ro’kon Dahda “please dahda wallahi bana sonta ko kad’an kada kuyi min haka zaku sa min attack wallahi don Allah ka amince Na sake ta.” “Wallahi Imran ka sake Na saki shatu sai dai ka sake uwa don wallahi sai na zare ka daga cikin ‘ya’yana Na gaya maka kada ma ka fara attempting zancen saki idan kuwa haka ta faru zan nuna wa kowa bad side d’ina wallahi an kaini ‘karshe” sosai kuwa yake kallonta saboda yarda take maganar da gaske take daga ‘kasan zuciyarta take fitowa, ranta a ‘bace idanunta kuwa yayi jajir.
Sai ji su kayi Hajja ta saki dariya muryarta a sama tace “Ai kuwa ba ki isa ba dijah ni kuma zan nuna miki nice uwar manga ko ki amince ya sake ta ko kuma ni na saka manga ya sake ki.......
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-20
ELEGANT ONLINE WRITERS.....
“Babu wanda aurensa zai mutu saboda son zuciyarki,ashe abinda kike aikatawa kenan a gidan d’anki Hindatu duk abinda kike ciki labari yana zuwar min,kamar na san hakan zata faru nace a kawo ni nan d’in kafin na wuce gida na, gaskiya Hindatu kin bani mamaki kuma sam ba jinin y’ar uwata ce a jikinkiba ita d’in macece mai kara mai mutunci mai yakana da alkunya idan Banda ma zamani mai ya kawoki gidan d’anki saboda abin kunya kuma kizo ki saka matarsa a gaba da rashin mutunci saboda siyawa kai raini,to bakin ki ya mutu anan wajen,aure dai ya d’auru kuma ba mai warwareshi manga ya sanar dani komai,don mai ita ba zata yi iko da d’anta ba alhali kema da naki d’an kike iko babu wacce zaka saki a cikinsu duka matanka ne kuma ban amince da saki ba zancen banza zancen wofi wa yace maka ana sakin mace haka kawai,to kada in sake jin makamancin wannan zancen, duk abinda kuke ina zaune ina jinku dama don inga kamun ludayin kowa shi yasa nayi bakam a waje na zauna, to hindatu naji duk tijararki.”sai a sannan dattijon arzikin yaja ajiyar numfashi ransa a matu’kar ‘bace yana kallon hindatu (Hajja yau dai munji sunan hajja na gaskiya a bakin kawunta kawu sa’idu)Hajja tana shakkarsa sosai don duk dangi yanzu shine babba shine kuma mai fad’a aji, gashi dama mafad’aci ne ba’a kuma isa yace ga abinda za’ayi ba a canja ba, kaifi d’aya ne kuma wargi yake dai-dai ‘kugun ko wani ja’iri. Parlourn shiru yayi kowa yana jin kawu yana ta fad’a Hajja zuciyarta sai tafasa take, tabbas kawu ya kawo mata cikas kuma sai taci uban manga da yaje ya sanar dashi. Kawu yayi fad’ansa son ransa sannan ya kalli Imran “Na jiyo gareka ko gaba naji magana makamancin ta rabuwa da za’bin uwarka sai naci mutuncinka,wa ya gaya maka ana jayayya da maganar uwa? Kada in sake jin haka ba and mamaki abinda ta hango kai baka hangoshi ba.” Haka ya gama fad’ansa ya kuma ce gobe ana gama biki Hajja ta had’a karonta ta tafi kada kuma ya sake ganin ‘kafarta a gidan d’anta ba da wani muhimmin daliliba.
Shatu kuwa tana can d’aki bata san budirin da ake ba, tana kwance saman bed d’in mommah da wayar mommah a hannunta tana buga game. Har sai da anty nahna ta shigo murmushi fal fuskarta ta dafa shatun “Amaryar Imran.” Shatu ta mi’ke zaune hankalinta na kan game tace “mai tayi amaryar tasa? Nahna tsaki tayi tace “akwai wata amaryar bayan ke.” Sam bata d’au zancen serious ba don ko a mafarki bata ta’ba sawa zuciyarta Imran ba balle har tayi tunanin zama amaryarsa tsokana ce dai irin ta Anty Nahna ina ita ina Imran da ko inuwa guda basa had’awa. Shigowar mommah da fad’a da mitar Hajiya mama ne yasa su kayi shiru da zancen fad’a take tana ‘karawa “Haba addarsu ai wallahi kin yi wauta ta ina aka ta’ba wasa da aure anyi magana kince wai nuna musu iko za kiyi to ikon me ki jefa yara cikin matsala, yaushe shatu ta isa aure fisabilillahi nawa shatun take? Ai shirme dai kinyi shi wallahi kuma ina jiye miki fad’an Babanku kin saka yrinya a matsala ke baki fita daga ciki ba kin jefa y’arki a ciki wannan dangin mijinnaki da ba kirki bane dasu.” Shatu dai mi’kewa tayi daga kwancen da take tana kallonsu d’aya bayan d’aya wai mai take ji ne? Ita dai shatu aka d’aurawa aure da Imran da take ji duk duniya ba wanda ya kaishi tsanar ta ina ita ina Imran d’an gayu mai ji da kansa? Muryar Dada ce ta dawo da shatu duniyar su mommah tana jin Dada ta fara masifa “Ah to ni ban ga laifin dijah ba ai maganin shege d’an banza yanzu Na san ashe Dijah jini na ta d’auko, ba naki ba solo’biyo da abinda kika sani sai ha’kuri,yo akan me? Wani shegen yayi mata na’kudar d’an sun d’auki wata ‘kanjamammiyar mata sun bashi, bayan a haka an zauna ana yi mata isa da iko da fankamar banza sai kace a kansu aka fara arziki ko da yake ba’ko a arziki shi yake nuna shi wani ne. Yanzu kuwa da tayi musu haka ai sa san annabi ya faku, to ina dalili idan ban da tsiya ma ace ‘yar kishiyarka d’anka zai aura ban ta’ba ganin wannan iskancin ba sai a dangin mijin dijah.ai gasu can dai wancan jarababben kawunnasu ya kashe bakin tsanya yayi min dai-dai wallahi.” Hajiya mama shiru kawai tayi tana jin fad’an Dada.ita kuwa shatu tayi zugum ba tare da ta san mai ‘kwa’kwalwarta zata tuna ba.wai ita shatu ‘yar ‘karamar nan aka yiwa aure? Lura da haka da mommah tayi yasa ta isa bakin gadon ta kamata,rungumeta tayi a jikinta tana shafa bayanta “kwantar da hankalinki daughter na ba yanzu zaki tare ba sai kin girma kin gama karatu sannan zaki tare kin ga ko ai da dad’ewa.” Sai sannan shatu ta saki ajiyar zuciya tana dariya ta rungume mommah. Gaba d’aya d’akin murmushi su kayi banda Dada da ta ‘bata fuska cikin masifa tace “zancen wofi kenan kaji shashancin banza shikkenan ita kuma sai ta ‘kare a gantale a titi to ba zai yiwuba yanzun zata tare mu da akayi mana aure yaushe muka kaita yarinya ta fara ‘kirgar dangi sannan ace wani sai ta girma yo girma na me? Kin san da hakan kika d’aura mata aure, to ban amince ba a sada ta da d’akin mijin ta cikin mutunci da kima wallahi kafin ayi abin kunya yayi mata ciki a gadonki.” Gaba d’aya d’akin kunya ce ta kama su wannan sakin baki na Dada, murya can ‘kasa mommah tace “To shikkenan zata tare amma ai sai an gama shirya mata abinda za’a kaita d’aki dashi ko?” Dada ta mi’ke tana fad’in “To shine zance amma kya ajiye budurwa zangangan a gaba kice wani sai ta girma,girmo nace ba girma ba.” ficewa tayi tana ‘kananun mita. Hajiya mama fuska ba walwala tace “Ba dai maganar Dada zaki bi ba na tariya ban amince da wannan shashancin ba ki bari ta girma ta san ciwon kanta tukunna.” Mommah d’aga mata kai tayi kafin tace “ko d’aya Na dai amsa mata ne don mu huta da mita kafin ta tara mana gayyar jama’a ba wani tarewa da zata yi sai ta gama makaranta tsaf tukun.” Hafsa tace “wannan shine dai-dai wallahi Addarmu gwara ma da kika yi maganin mutanen can haba ikon yayi yawa.”haka dai aka yi ta tattauna zancen har Ammar da Hisham suka shigo hundred percent sun goyi bayan mommah.
Shi kuwa ango yana can zuciyarsa tamkar ta fashe bak’in ciki ya gama cika shi.yana ji abokansa suna ta tambayarsa wacece Amaryarsa ta biyu amma ya kasa basu amsa,sun lura ransa a matu’kar ‘bace yake don haka suka kyaleshi suna cigaba da shirin dinner shi kuwa ko kallonsu bai yi ba balle ya nuna alamar shirin.
A can ‘bangaren Amarya an sha ba’kin gumurzu kafin ta ha’kura ta saduda bayan mahaifiyarta ta tabbatar mata ko za tayi yawo tsirara sai ta raba auren Imran da wannan mai kama da bararojin.hakan yasa ta share hawayenta ta fara shirin dinner don mai kwalliya Nashe glam wato khadija Nashe tazo za tayi mata, kafin a fara kuwa tace bari ta je ta ga angon.
Cikin part d’insu ta shiga duk da abokansa da suke zaune dam’kar a parlourn bai hana ta kutsa kai ba, ba tare da wani shakka ba tace musu “sannunku” Gaba d’aya suka amsa ta dubi Ali da shi suka fi d’an sabawa tace Imran fa?nuna mata cikin bedroom yayi yana sakin murmushi a zuciyarsa yake tunanin ko mai Imran zai yi da wannan ai shi cetonsa aka yi da aka bashi wata duk da waccen d’in ma basu san wacece ba. Suna kallo ta shige uwar d’aka ba tare da shakka ko kunya ba Amarya ta kawo kanta kenan sabon salo abdul ya fad’a yana dariyar sha’kiyanci.
Tana shiga ta tarar dashi kwance a rigingine saman carpet idonsa a lumshe da alama dai ba barci yake ba,zama tayi a gefensa tana jan yatsun hannunsa, a hankali ya bud’e idonsa