Showing 6001 words to 9000 words out of 117786 words
yayi Kwafa. Dada ta gyara zama “ yo saboda Allah ai gaskiya bature ya fad’a nima fa mamaki nakeyi ace wannan bararojin jininmu ce to ka fad’a ace ina ka fito don dai mune masu kalan dangi sai kuma mu had’a jini da bararo “ mommah idan ranta yayi dubu ya ‘baci ta kalli dadan kafin taja’kafar shatu ta nunawa dadar “ duk wanda ya san yar uwata maryama ya san wannan copyn kafarta ne da hannunta dada ki daina daka ta imran da shegen halinsa dinnan na bin kwakwkwafi a ina yasan maryama balle ya tantance jininta maryama da ta bar gida yana shekara guda duk’kaunar da maryama ta nuna maka ban mance da ita ba.” Imran ya ta’be baki kawai ita kuwa shatu zaro hotuna tayi ta mikawa mommah da takardar da innaji ta bata tace ta basu. Mommah na gani ta mikawa lamid’o “ Baba kalla kaga wallahi rubutun maryama ne wannan tabbas “ lamid’o ya kar’ba ya kuma shaida tabbas rubutun d’iyarsa ne.
Sun ci sun sha akayiwa maryama addua sannan su lamid’o mazauna abuja suka fara haramar tafiya. Mama tace shatu tayi wanka ta canja kaya kafin su wuce shatu ta had’e rai sam bata san zancen wanka. Mommah ce tace” haba mama na zata zaki bar min ita mu koma kano tare musamman ganin bani da y’a mace ashe maryama ce zata haifa min” mama ta girgiza kai imran yana zaune a gefe yana adduar kada Allah yasa mama ta amine banda rigimar mommah ya zata kai musu bararo gida......😂😂😂😂 To fa!
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
ELEGANT ONLINE WRITERS......
-5....
Momma ta sake gyara murya cikin kwantar da kai ta furta “ Don Allah mama ki bar min ita kinga ke kina da wasu y’an matan ga hafsa ga nahnah ni kuwa Allah bai bani haihuwar d’iya mace haihuwar ma daga ‘ya’ya biyun ba saketa nayi ba.” Mama ta girgiza kai “ Gaskiyar magana addarsu ba zan iya ba su wadancan da kike magana ina na gansu kun kwashe kun kai can uwa duniyar turkey karatu, yanzu kuwa ita zan dinga gani kamar maryama da na rasa “. Dada taja tsaki “ kaji min wani zancen shirme Idan da wanda ya dace ya ri’ke wannan ‘ya ai dijama ce yo fisabilillahi tana da wata uwar ne bayan ita a duniya ai itace take da iko da yarinyar nan ba ke ba daga kawai kin haifi uwarta, don haka na zartar da hukunci dijama ki tafi da ita ke kad’ai zaki iya da wannan bararojin mai ido a tsakar ka ko samarinki sa ladabtar da ita musamman wancan miskilin kafi mahaukaci ban haushi da idanunsa kad’ai sun isa hukunta ‘yar banza idan ta’kamarta ido ai gidan ta tarar.” Wani kallo shatu ta watsa mata a zuciyarta tace “ sai nayi maganin wannan tsohuwar kafin ta sheka barzahu “. Liman da lamid’o murmushi kawai suke ganin yarda mama ta had’a rai alamar sam hukuncin dada baiyi mata ba sai dai ba yarda za tayi da ita. Momma kuwa sai murmushi take tana sake jan shatu a jikinta. Daga gefe kuwa imran ne yake ta watso mata harara kamar ya sha’keta ta mutu tabbas banda an kusa bikinsa zai bar ‘kasar da amaryarsa ‘yar abuja zubin london inji dada da barin’kasar zaiyi kafin a sake ganinsa kuwa sai an yara. Ya kalli agogo yana mi’kewa “Momma ya kamata muyi haramar komawa saboda akwai abinda dada ya sani a company ban kai ga hattamawa ba kuma kinga mota muka biyo “ Duk wannan dogon zancen yayi shine saboda baya so dada tace kwana za suyi yamma tayi. Dada ta zabga masa harara da ficificin idonta na tsoffi “ Ma’karyacin banza Ka dai ce ba zaka iya kwana anan ba saboda shegen gwalangwasonka kada kayi ubanka’karya salihin bawa dashi ko da yake shima ya zama d’an banza watansa nawa bai zo ya dubani ba ko don bani na haifo wanda ya haifi ubansa ba amma ko bakomai ai ubannasa aminin lamid’o ne, shikkenan dai Allah raka taki gona ban kuma ce Ka gaya masa ba bare kasa ya daina min aiken wata da ya saba ko bakomai ai d’an albarka ne tsiyarsa ta rashin zuriya ta bishi sahura dai taga takaici da jikanta baya son ziyara”. Gaba d’aya gurin ba wanda baiyi dariya ba har shatu idan Ka d’auke imran da ya sake kicin-kicin da fuska ya d’aureta tamau ya mayar da kud’in da yayi niyyar bawa mutanenta da ita kanta aljihu, yasa kai ya fice bayan yayiwa liman da lamid’o sallama. Dadah ta gyad’a kai “jarababbe umma ta gaida aisa gayyar na ayya ke dai dijama kin haifi ala’ka’kai.” Murmushi kawai tayi ta mi’ke tana ri’ke da hannun shatu ta furta “Allah dai ya shirya mana zuri’a bari mu wuce kada dare yayi don ma mugun gudu yake a motar “. “ wani irin gudu ki gaya masa ya tafi a hankali bana son shashanci “ lamid’o ya fada yana kallon babbar d’iyar tasa cike da kulawa ya san sosai take jin zafin rad’ad’in mutuwar nan “ kuma ki cire damuwa a ranki kada kije kiyi tunani har ciwonki ya tashi maryama addua take bu’kata yanzu, ita ta dace ko bakomai tayi mutuwar shahada tsakaninmu da ita addu’a dafatan muma mu cika da imani “ lamid’o ya sake fad’a yana kallon’yar tasa ba tare da dubi da hararar da dada take watsa masa ba “ Ba shakka zamani wato lamid’o a gabana kake lallashin ‘yarka ta fari kai Allah da ya tsinewa nasara da ya kawo boka har tayi sanadin rusa al’adarmu da dane ko inuwa d’aya ba zaka had’a da dan fari ba balle har zance ya shiga tsakaninku tur da wannan wayewa, ko da yake har gwara kai ba gani ba na tsaya ina magana da kai da iyayenan zasu dawo da sunyi tur da haihuwata kai ku tashi ku tafi kada wanda ya sake dawo min nan balle ku sake sakani rashin kunya wai da bakina nake kiran sunan lamid’o waliyazubillah duk da dai na uku ne kai amma wa ya san na farko da na biyun Allah na tuba tun kan ayi suna suka mutu ai dai kai ne dai na farkon....” gaba d’aya gurin dariya ake suka fice suna mata sallama Momma tace “ Danger number one “
Ta mudubin motar ya hango fitowarsu da sauri ya waro sexy eyes ganin da yarinyar aka fito mai hakan yake nufi wai wannan’yar dajin motarsa zata shiga kai ina impossible ai da sake.
Ya fito daga motar daidai lokacin’karasowarsu mommah tace “bud’e motar mana imran, yamma fa tayi “ ya ‘bata fuska sosai “ Momma yamma fa tayi kuma gaskiya gudu zanyi sosai why not ku kwana anan idan yaso gobe nayi muku booking flight ku taho.” Momma ta watsa masa wani kallo ta san sarai nufinsa Aysha ce baya son ta shiga motar bai kuwa isa ba zata nuna masa ita ta haifeshi “ sannu ubana to yau d’in za mu tafi idan yaso’karewar gudu ka mayar da motar taka jirgi bud’e mana malam “ fuska a d’aure tamau tayi maganar tana mamakin halayen imran da sam bata san inda ya kwaso su ba. Jiki a salu’be ya bud’e motar had’e da mi’kawa Ammar key d’in “ kuje I will manage ko a hotel ne by morning insha Allah zan bi flight na taho and make sure kuna zuwa ka kira car wash su d’au motar nan every thing na cikinta ya zama clean.” Ammar ya kar’bi key had’e da bud’e driver seat momma ta waro ido tace “ yana ina shi “ Ammar yaja numfashi don yasan fad’an momma shi kuma yana son d’an uwansa baya son’bacin ransa “ Momma zai zo ya tuna akwai yana da abinda zaiyi a bauchi “. Gani yayi kawai momman ta fita ware ido tayi tana kallon imran jingine jikin bishiyar’kofar gidan kallo da take masa ne yasa shi rusinar da idanunsa baya jurewa sun saba tun suna yara da idon take hukunta su, hanya kawai ta
nuna masa ta shige. Ransa a ‘bace ya bita tabbas ya san dai kafin ya isa gida wani ciwon sai ya kamashi.
Shima Ammar d’in kallo d’aya tayi masa ya fito ya koma d’aya seat d’in zuciyarsa fal da tausayin d’an uwansa don ya san kam yau sai ta Allah.
A salu’be ya tada motar bayan yayi adduar tafiya الحمدلله الذي سخر لنا... zuwa Karshe ya kuma ware a .c don ya kore masa warin jikinta da dum da motar tayi har da su fess turaruka. Momma tana kallonsa tana’bata rai cikin’kyamar banzar d’abi’arsa. Shatu kuwa kwafa tayi don sarai ta san ma’anarsa ta hakan wato kyamarta ma yake yi ai kuwa za tayi maganinsa kafin ta bar motar, ba mamaki ma bayan fitsari har kashi sai tayi a motar....😂😂.
Wani irin gudu yake shararawa duk a tsorace suke a motar ganin yarda yake mommah kuwa ta’ki magana sai addu’a da take a zuciyarta. Shatu kwance take luf a cinyar mommah wani barci ne yake fusgarta, cikin hukuncin ubangiji kuwa cikinta ya fara murd’awa ta daddage ta saki wata tusa da ta d’umame motar gaba d’aya Allah ne ya kiyaye saura’kiris ya saki sitiyarin motar yaja wani wawan burki, ammar ya dinga’kok’arin’kinshe dariyar da ke cikinsa amma ina sai da ta bayyana a guje ya fice tuni ya fara kwara amai, Ammar ya fito masa da ruwa yana aikin jera masa sannu. Momma kuwa duk da tausayinsa ya shigeta haka ta gintse. Shatu sai dariya take yi tana’karawa momma tace “ wallahi shatu idan ya kamaki ba ruwana “ “ yo mommah ba k’yamata yake ba saura gudawa ma “ Mommah ta waro ido “ kada ki fara shatu idan ba so kike ya kashemu a titi ba kina ganin wawan burkin da ya sha Ba don Allah ya kiyaye Ba kowa a bayanmu ba da tuni mun mutu.” Shatu ta zaro ido “ momma mutuwa kuma a yanzun da zan fara jin dad’in rayuwa aradu ma ki daina wagga zance yo tunda nake ban ta’ba tunanin zan shiga wannan abin ba ban Ta’ ba ganinsa ba sai yau amalanke muke shiga garinmu da zanzo nan kuwa motar kayan miya Na shigo aradu dana shiga nan na zata aljannah nake “ mommah ta girgiza kai “To kada ki sake abinda zai zubar damu a titi motoci su take mu mutu.” Ta d’aga kai. Ya huta sosai kafin yace “ Ammar jeka Kai bud’e glasses d’in motar ventilation ya shiga ka fesa air freshners tabbas Ba mamaki mommah ta d’auko ajalina “ Ammar ya d’an shafa bayansa “ bros ba zaka mutu ba just because of her sai kwananka ya ‘kare Ka dinga daurewa pls mommah bata jin dad’i the way she looked at you ka dinga controlling temper Dinka” hannu ya d’aga masa “ jeka kayi abinda nace maka kawai ni Na san abinda zanyi muna zuwa gida I will pack everything nawa na tare “ Ammar ya zaro ido “ saura fa 4 months bikin ya zaka tare yanzu “ Imran tsaki yayi idan ban tare ba so kake na mutu ko?” Ammar ya juya yana’kunshe dariyarsa ya gama duk abinda ya sashi sannan ya dawo yana kallon yarda yake mayar da numfashi alamar ya galabaita a aman “ Bros mu tafi kada dare yayi “ mikewa kawai yayi ya mi’ka masa key d’in “ muje kayi driving I can’t do it “
Ta mudubin motar yake watsa mata harara ta saki baki sai barci take har da munshari ya sauke duk glasses d’in iska Na shiga motar a zuciyarsa yace “ Gwara a tafi haka “ momma dake kallonsa ta ta’be baki “ zan baka mamaki imran kada Ka shiga hankalinka “.
Idan ba’a commnts zan dakatar da book d’innan.....
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-6
ELEGANT ONLINE WRITERS ******
Ammar cikin nutsuwa yake driving har suka isa cikin garin kano’karfe 8:00 dai-dai, shatu lokacin har fitsari ta janga’ba a kujerar ba tare da sanin mommah ba.
A unguwar railway su kayi parking bakin wani tangamemen gida gari guda, da tafkeken gate, gani tayi kawai gate din ya zuge ba tare da tasan wanda ya zugeshi ba.Automatic gate ne. Ammar yayi packing a packing space. Momma ta bud’e ‘kofar had’e da jan hannun shatu a hankali ta waro ido ganin gurin da lema murya ‘kasa-k’asa tace “ shatu fitsari kika yi?” Shatu ta d’an ta’be baki “ To mommah fitsarin ne ai ya matseni kuma ina cewa zanyi zai fara masifa “. Momma tayi saurin rufe mata baki don kada imran da ya fice da sauri yaji “Muje kafin ya ankare “ da sauri shatu ta fita daga motar ammar yayi dariya yana tunanin yarda za’ayi da cakwakiyar’yar mommah da yayansa, yasan dai kwarai za’a buga show.
Suna shiga tangamemen falon kamshi ya doki hancin shatu ga sanyin A.c ta lumshe ido had’e da runtse ido tana bud’ewa tabbas dai da a mafarki taga wannan gidan to tabbas zata ce aljanna tayi mafarki da ita. Momma ta ri’ke mata hannunta ta kaita’kofar wani sashe suna shiga ta kaita wani d’aki kusa da nata “ daga yau ga d’akin Ayshata muje in nuna miki komai a toilet kiyi wanka ko da yake wannan wankan na yau yafi ‘karfinki da kaina zan miki da nace ma in kaiki saloon to bana so su fara ganin wannan daud’ar kannaki jira ni anan am coming.” Da sauri ta fita daga d’akin shatu ta sake ware ido tana kallon gadon yanzu wannan d’akina ne gado na da sauri tayi tsalle a gadon tana tintsira dariya “ ahe dai ina da gata muke zaune can a dajin Allah aradu innaji ta kwari kanta cabd’i”
Shigowar mommah yasa tayi shiru momma ta shige toilet ta zube kayan da yake hannunta duk mayukan wanke kaine da combs dama toilet din akwai dryer. Shatu ta fara’bata rai sam bata son a ta’ba mata kai da dai mommah zata gane da ta kyaleta. Momma ta zare du’kun’kunennan mayafin nata ta zaunar da ita bakin jaucuzi ta fara kunce tufkekken gashin kanta mommah tayi mamakin ganin tumulin gashin ta ji’kashi ta saka shampoo ta barshi for a minutes sannan ta fara had’a ruwan da zata dirje daud’ar Jikinta.
Sosai ta wanke kan sai sheki yake wajen wanka ne shatu Ta fara’boye-‘boyen jiki mommah Ta harareta “ zaki tsaya ko sai na ‘bata miki rai ke da ko irgar dangi baki fara ba to koma kin fara ni ba uwarki bace “. Shatu Ta d’an sunkiyar da kai mommah Ta saki murmushi “ Ashe kina da kunya.” Tas shatu Ta fito duk da dai sai a hankali zata baje amma ko bakomai anfi baya.
Fitowarta ne yasa momma ta tsaya domin ba kayan da zata bata tasa tsaki tayi tace “zauna nan ina zuwa bari na aika ammar ya siyo miki ready made kafin da safe mu shiga kasuwa “.
Tana fitowa babban falo ba taga ammar ba sai imran da yake zaune yayi wanka da fara jallabiya tas a jikinta mai gajeran hannu a jikinsa yayi kyau sosai kana ganinsa kaga mutum mai mutu’kar tsafta. Sai baza’kamshin turare yake yunwa ce take cinsa ya aika ammar yayi musu take away don baiga alamar masu aikin sunyi girki ba, may be basu zata zasu dawo ba.” ina Ammar?” Momma Ta fad’a tana tsatstsare sa da ido , Imran murya can’kasa yace “ Na aike shi eatery samo abinci.” “ sai ka tashi kai na aikeka samowa Aysha kayan sawa ba tazo da kaya ba “ ta fad’a tana juyawa ba tare da Ta lura da waro idon da yayi ba yana ji kamar ya rusa ihu ganin zata shige yace “ kud’in fa?” Ba tare da Ta juyo ba tace “ ka siya da naka “ dunkule hannu yayi ya daki d’aya cikin d’aya kamar ya tashi sama kuma ya juya da sauri ya fice daga cikin gida.
Da yaje ma rasa mai zai d’auka yayi ya d’auko mata riga da wando Na maza kawai bayan ya kintata tsahonta yaga ba zata zarta hakan ba. yunwa yake ji sosai amma mommah Ta sashi zuwa siyawa wannan bararojin kaya.
A falo ya ajiye kayan ya nunawa Ammar “ mikawa mommah “ ya zauna a dinning ya fara cin abincin” mintuna kad’an mommah da ‘yarta suka fito Ta saka riga da wando duk da Na maza ne sai sukayi mata kyau, mommah Ta gyara mata kai an tsaga an raba biyu, jelar gashin Ta sauka har dantsen hannunta gashi mai yawa masha Allah sai ‘kamshi take kallo d’aya yayi mata ya d’auke kai ya cigaba da cin abincinsa momma taja kujera tace “zauna “ Ta zauna tana hararar naman da yake ci tsoronta Allah kada ya cinye naman hakan yasa ta shiga tunanin yarda zata koreshi daga wajen ta kuwa daddage ta saki attishawa sai kuwa ga majina ta biyo hancinta da sauri ya furzo abincin dake bakinsa ya mi’ke da sauri ya bar wajen. Zuciyarsa na tunzirashi yayi mata dan banzan duka kawai. Ita kuwa dariya Ta fara babbakawa “ Nagode Allah yo mommah da fa cinye naman zaiyi kaf da banyi haka ba “ mommah duk da dariyar da take cinta ta gintse tace “ baki kyauta ba kings yanzu kin hanashi cin abincin Ba kyau kada ki sake Ammar bishi da abincin d’aki”. Ammar ya mi’ke yana murmushi sosai yarinyar take burgeshi shi kam sam bata damuwa sha’aninta take zubawa.
A parlornsu ya ganshi a zaune ya dafe kansa sosai tausayinsa ya kamashi ya ‘karasa da abincin yana dafa bayansa Bros sorry don Allah ga abincin momma tace a kawo maka “ zubawa plate din ido yayi yana saurin ja baya gani yake zai hango majinar a cikin abincin murya can ‘kasa yace “ ‘dauki Ka tafi dashi ba zan ci ba ta had’a Ta cinye kana tunanin yau zan iya cin wani abin ko mai na kai bakina sai na tuna ‘kazamar yarinyar nan bitch “ ya mi’ke ya shige bed room