Showing 15001 words to 18000 words out of 117786 words
Shatu dake zaune a main parlour tana jiyo duk abinda yake wakana tayi al’kawarin yau tsohuwar nan ba zata kwana da lafiya ba. Ta shige d’akinta tana’kissama irin abinda za tayi mata. Da sauri ta shiga tanadin kayan duk da zata yi amfani dasu. Cikin dare ta nufi d’akin da aka sauke hajja, a hankali ta murd’a’kofar Ta shiga, Hajja ta tarar ta saki baki tana barci taci sa’a kuwa hajjan ita kad’aice a d’akin tabbas shirinta zai tafi yarda take so, Ta sake kallon shigar da tayi a mudubi’kusumbi tayi sosai a bayanta ga gashinta da ta saka ya rufe mata fuska gaba d’aya sai wani farin hjibin momma da ta sin’kife jikinta dashi, ba’a ganin fuskrta Sam, Ta dur’kushe sosai kamar wada tana lan’kwashe ‘kafarta kamar a shanye take. Tsaye tayi gefen gadon hajjan kafin tasa sandar hannunta ta zunguri ‘kafar Hajjan “ Ke tashi ajalinki yau yazo tsohuwar banza mai takurawa jama’a....... A razane Hajja ta rusa wani ihu fad’i take “ ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba innahu ala raja’ihi la’kadir......
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-10
Sosai Hajja ta sake razana ganin shatu tana nufota, fad’i take “ Don Allah kada ku cutar dani ku fad’i mai kuke so nayi? Ni baiwar Allah ce ba ruwa na da kowa a duniya.” Shatu ta ‘kya’kyata wata mahaukaciyar dariya “ so muke kada ki sake cutar da hadizatu idan kuma kin’ki zaki ga sakamakon taurin kai kina ji?.” Da sauri hajja ta d’aga kai “ Na bi Allah na biku insha Allah ba zan sake komai ba” shatu ta sake kecewa da dariya bayan jin abinda tace cikin daka tsawa tace “ To rufe idonki kuma kada ki sake ki bud’e sai nayi nisa da tashi sama.” Da sauri hajja ta rintse idonta gam, shatu da sauri ta fice daga d’akin ta shige d’akinta. Ai cikin azama hajja tana bud’e idonta tayi saurin mi’kewa ta fice daga d’akin jikinta har makyarkyata yake, A tsakiyar falon ta tsaya ta dinga kwalawa mutanen gidan kira. Yarda muryar tata ta karad’e gidanne yasa d’aukacin mutanen gidan fitowa, suka tarar da ita a dur’kushe hankali tashe suke dubanta. Dahda ne yayi’karfin halin cewa “lafiya hajja?” Hajja ta zuba masa wani irin kallo “ ina kuwa lafiya ko da yake yanzu ba zan yi magana ba sai da safe kai ni falonka a can zan kwana kuma kana zaune daga gefe na Yau gamo nayi da aljannu a gidannan.” Dariya ce taso kama Ammar ganin yarda ta ha’ki’kiance take’buya a bayan dahda. Momma kuwa baki ta ta’be ta juya ta koma ciki bayan tayi wa amaryar mijinta kallo d’aya. Ita kuwa amaryar bin bayan mijinta tayi tana tsinewa hajja a zuciyrta yarda zata’bata mata daren amarci duk da tanadin da ta shirya masa ga turarukan tsubbace tsubbace da ta ambula a jikinta banda wanda ta turara sai da ta kusa samo kan mai gidan sannan wannan tsohuwar zata rusa mata shirinta.
‘Karfe bakwai nayi Hajja ta fito babban falon gidan bayan ta tasa ‘keyar dahda a gaba “ Muje ka had’o min kaf kan ahalin gidannan ina da magana dasu “ cikin tausasa murya yace” Hajja da kin bari gari ya ‘kara wayewa ....” “ Na’ki Na bari garin ya waye ahmadu nace na’ki Na bari manga uba na, saboda ba kai kayi gamo da abinda Na gani ba ko.” Tayi saurin tare shi da sababin fad’a. Shiru kawai yayi yabi bayanta zuciyarsa fal ‘bacin rai don dai uwa uwa ce da ba wanda ya isa yazo gidansa ya aikata masa haka.
A tsaye suka tarar da momma tana sake gyara cushions d’in main parlour d’in tas ta gyara gidan sai’kamshin turaren wuta gidan yake. Dahda ya bita da kallo ganin yarda tayi kyau sosai cikin wani pink lace duk da fuskarta ba fara’a amma dai bata fasa gaisheshi ba, sannan ta’karasa gefen hajja da take zaune saman kujera ‘kafa d’aya kan d’aya tana girgiza jiki fuska cike da masifa, muryar mommah a cunkushe itama tace “ Hajja barka da safiya an tashi lafiya?” Sai da Ta ‘kare mata kallo sama da ‘kasa cikin masifa tace “ ‘kalau sumul na tashi duk da ba haka kika so ba, cikin kiyayewar ubangiji na tashi lafiya, saboda kin san tsaye nake akan ‘kafafuna wajen ibada, wai ke deejah har tsubbun taki ta kai ki fara turawa mutum aljannu ? Saboda Na saka d’ana yayi aure, to albishirinki wannan auren mutu ka raba kuma idan kin tashi yau da daddare ki turo min sarkin rauhanai ma ba aljannu ba , Aljannun naki mai suka isa suyi min sunzo sun baki labarin yarda Na fatattakesu da ayar Allah.” Shatu da sauri ta juya Ta shige kitchen saboda dariyar da Ta ciyota. Hajja Ta cigaba “ kuma ni da gidan d’ana ba inda zani zama daram.” Mommah shiru tayi tana al’ajabin hajja yau kuma gingimemen sharrin da za tayi mata kenan lallai tsanarta da hajja ta girmama. Hajja ta juya gun Dahda “ kai kuma manga kana tsaye baka tambayeni ba’asi ba, yo ai dai kace hajja mai ya faru kike wannan fad’a da safiya haka tunda kai haka Allah yayi ka kamar d’an fari, to ko Mahmud da yake d’an farin baya abin da kake. Wato kana ji cikin dare matarka tayi min turen jinnu wai suna gargad’i na na rabu da hadizatu kaji fa wai dijah yanzu har tayi shaharar turo min Jinny?” Dahda ya girgiza kai saboda ‘bacin rai ma kasa magana yayi ya zuba mata ido kawai. Ammar ne cikin d’aure fuska yace “ ko dai mafarki kika yi hajja ina mommah taga aljannun da zata turo miki? Mu tunda muke gidannan ba wasu aljannu.” Girgiza kai hajja tayi sai kuma tace “ Ba shakka, ‘karya nayi maka kenan? To manga ubanka da yake zaune shine ma’karyaci ba ni ba. Ra’ayal aini yarda nake ganinka haka naga aljannu ina tofa musu addu’a suna ihu da tumami suna fad’in deejah ce ta aiko su, haka Na ‘konesu ‘kurmus ba mamaki idan kuka je d’akin ma kuka ga haya’kin da tokarsu, yo ni za’a kawowa zancen banza aljannun me Allah na tuba”. Ba wanda ya sake mata magana haka ta mi’ke ta koma d’akinta tana sake bambamin tijara. Shatu da take la’be a bayan ‘kofar kitchen ta girgiza kai had’e da yin ‘kwafa ta juya ta shige d’akinta .
‘Karfe biyu daidai ba’kin Abuja suka sauka. ‘Kannen mommah ne hisham da hafsa sai nahnah. Kyawawa dasu farare tas kamar su innaji da mommah. Shatu tana zaune tana lesson driver ya dawo daga’daukosu d’aya bayan d’aya suke bin ta da kallo ita ma tana kallonsu, Hisham ne ya bud’e mata alamar ta taho ya dube ta kafin yace If I guessed It right you’re shatu ?na canka shatu ce ko?” Da sauri ta d’aga kai hisham da su nahna suka rungumeta da ihu cikin tsananin farin ciki suna murnar ganinta hakanne Yasa Ammar da mommah da imran saurin fitowa suna murnar ganinsu , kasancewar sun dad’e basu zo hutu ba nahna da hafsa suna turkey, shi kuwa hisham mate d’in Ammar ne tare suka gama makaranta a egypt, Imran ne yayi oxford university england. Murna da hayaniyar da suke ce a main parlour ta fito da mutanen gidan har Hajja da ta fito tana dogara sandarta da yake tana da ‘kiba ciwon’kafa ya sata a gaba.
‘Daya bayan’daya take hurga musu kallo tana amsa gaisuwarsu a gatsine “ Ba shakka dijah kin ci gida kin mallake manga kin mallake dukiyarsa ga ‘yan uwanki ma sun zo sun taru a gida, kai Allah wadaran naka ya lalace su kuma wad’annan gand’an-gand’an ‘yan matan daga ina?” Nahna fuska a d’aure za tayi magana mommah ta girgiza mata kai “ Don’t say any word here ku shiga part d’ina am coming.” Kasancewar akwai tarbiyya hakan yasa basu shiga ba suka ja hannun shatu su kayi gaba su imran ma suka bi bayansu. Mommah ba tace da hajja komai ba ta mi’ke zata wuce. Cikin masifa Hajja tace “ la shakka ga ‘yar iska wato kin bawa banza ajiyata nayi tayi ko? To kinyi da gyatumarki mai kama da sadakar yallar nan kuma da ni kike zancen yau yau zasu juya su koma, kuma kaf jakunkunansu sai nazo Na caje don yanzu haka wani tsubbun suka kawo miki an ji anyi miki kishiya azo a koreta ko? Kuma idan zasu tafi ki tattara har bararojinnan su tafi da ita shaid’anun banza kawai.” Momma wani abu Ta had’iya kawai ta juya ta shige part d’inta zuciyarta na tafarfasa, itama fa mutum ce ba dutse ba dole zuciyarta zata dinga zafi da irin cin kashin da hajja take mata amma ya zata yi dole ta girmamata tunda d’anta take aure. Sai da Ta share hawayen fuskarta sannan ta’ka’kalo fara’ar dole ta bud’e’kofar falonta.
A zazzaune ta samesu tuni sun watsar da lamarin hajja sun saka shatu a tsakiya, sai fito mata da tsarabar kayayyaki suke wanda suka siyo mata a turkey da wanda kakanninta suka bata, sai nuna mata tsananin soyayya suke, hakan yasa fara’ar fuskar shatu ta kasa ‘boyuwa kowa nuna mata ‘kauna yake ashe ba zata yi maraiciba bayan mutuwar innaji, ashe yanzu ne zata fara fuskantar farin ciki a rayuwa. Ta lura kowa sonta yake idan ka d'auke Imran da yake gefe yana harararta ‘kasa-‘kasa. Hisham ya dubi Mommah kafin yace “ Hope dai by now an yi mata register a school ?“ Momma ta girgiza kai “ so muke brain d’inta ya da’n bud’e before taking her to school insha Allah” Imran ya ta’be baki cikin takaici yace “ Allah wahala kawai kuke wannan yarinyar she will never be socialized kamar yarda kuke so , rayuwar daji fa tayi ai sai a slow kawai dama kun daina wahalar da kud’inku kawai don wasting time dinku zaku yi ji fa wasu tarkace a hannunta “ ya fad’a yana nuna hannunnata, gaba d’aya gurin shiru kawai su kayi zuciyarsu kowa da mamakin imran. Hisham ne ya katse shirun yana dafa Imran yace “ Amma son banyi expecting hakan daga wajenka ko bakomai she is your bloody sister da nake fatan mu nuna mata soyayya mu kuma bata jin dad’in da ta rasa.” Tsaki yayi Hasfa ganin yarda mommah ta damu sai ta sako wasa cikin zancen “ Rabu dashi Yaya hisham bayan ma bai san yarda rana zata fad’i ba “ da sauri ya zaro ido “ wa? God forbid wallahi insha Allah rana a gabas zata fad’i ko don ba kiga babban kamun da nayi ba classy baby ga good hygiene ga kyau ga ladabi.” Tsakin da mommah ta zabga ne yasa yin shiru duk gurin kuma aka saka dariya ban da shatu da imran ya riga ya ‘bata mata rai. Mi’kewa tayi zata shige ciki taji Nahna tana cewa “ Mhmn Allah ya kaimu lokacin da zaka zo kana’yar murya “ ya mi’ke yana fad’in “ ai ko a ‘kafa aka d’aura min wallahi sai na cire na yar “ Mommah kwafa tayi tana nuna musu dinning “ Hisham close the chapter kuyi taking shower ku ci abinci duk da dai tafiyar dad’i kuka yi tafiya a jirgi” Nahna tace “ Yo wa zai zo kano from Abuja a mota.”
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-11
ELEGANT ONLINE WRITERS.....
Da yammacin ranar kuwa ‘yan matan mommahn gaba d’aya suke a kitchen suna tayata d’ora sanwar dare, shatu na gefen Nahna tana tayata had’a salad. Ta dubi antynnata kafin tace “ Anty Nahna ku nawa ne’yan uwan innaji?” Nahna murmushi tayi tana dafa gashin kan shatu data gyara mata shi ya sauka har tsakiyar gadon bayanta. “ Mu biyar ne Mommah ce babba sai adda maryamu sai hamma hisham sai ni sai kuma hafsa shekara d’aya ne tsakaninmu da hafsa. Mu kad’ai ne a gidanmu babanmu bai kara aure ba shi yasa sam ba abinda yake d’aga mana hankali bamu da yawan da za’a samu sa’bani a cikinmu muna son junanmu kamar mu had’iye kanmu, shi yasa sam ba muyi Farin ciki da auren da ammar zaiyi ba, mun so ya auri jininmu ta yarda zamu sake tashi tsintsiya mad’aurinki d’aya, amma hakan bai yiwuba kana tasa Allah na tasa amma Allah’s plan is better than ours right?”murmushi shatu tayi ‘kaunar dangin innajinta yana sake ratsa ta musamman ganin yarda suke nan nan da ita. Sai kuma ta kama hannun nahna race “me kika fad’a daga ‘Karshennan ina so in iya irin maganar nan” Nahna ta sake sakin murmushi kasancewarta ma’abociyar murmushi, tana jan hancin shatu tace “ kin san turanci?” Shatu Ta d’aga kai “ Na sani innarmu idan tana koya min karatu tana yawan ce min sai na iya abcd sannan zan iya turanci “ Nahna tace “ To wannan maganar da nayi shine turanci kice kin iya abcd?” Shatu cikin dariya tace “ kai na iya fa har’karshe kuma har rubutu na iya da karatun hausa Na abcd kuma na iya su boy girl, man da woman kai har su cup fa na iya.” Da sauri hafsa da mommah suka juyo nahna kuwa murmushi tayi kice “ yarinyar tawa kanta na ja ba zama kiyi wuyar shiga school ba.” Momma farin ciki ya cikata “ai kuwa gobe za’a miki register a school ko primary 4 su kaiki shekara nawa kika ji innajinki na fad’ar shekarunki?” Shiru tayi tana lissafi sai tace “ haka dai da zata mutu ina shekara sha uku “. Hafsa tace nawa kenan a karatun book?” Wani kallo tayi mata tace “ kai mhmn thirteen d’inne ban sani ba aradu har dubu munje da innaji tace min thousand sunansa “ gaba d’aya suka hau tafa mata. Momma cikin farin ciki ta jata ta rungumeta tace “lalle maryama tayi ‘ko’kari am so proud of her .”
Shigowar amaryar dahda ce ya dakatar dasu daga hirar da suke, ko magana bata yi musu ba ta bud’e fridge tana wani gatsine sai kuma Ta d’aga waya murya cikin kissa take fad’in “ Am coming dear naje samo maka drink d’in da kace ne.” Tana fad’a tana kallon mommah da take murmushi ‘kasa-‘kasa, “0key dear yanzu zan dawo kada ka damu zan maka abinda yafi kis.......” wani kallo mommah tayi mata da yasa ta gintse abinda tayi niyyar fad’a ta juya har ta kai ‘kofa momma tace “ kice masa har ya dawo daga kadunan da ya tafine? Kuma yaushe ya fara shan drinks na general kitchen..” wata kunya ce ta kama amarya ta juya da sauri ta fice, gaba d’aya suka saka dariya a kitchen d’in mommah tace “ kaji min shashasha right now fa na gama receiving call d’in and he told me yana kaduna amma kaji makira “. Suka sake she’kewa da dariya. Nahnah tayi tsaki “ Ni ba’kin cikina d’aya mommah da kuka amincewa imran ya auri ‘yarta ba kiyi masa jan ido ba, don sun ga d’anki ya taso da nasibi ga arziki ta ko ina ‘karuwar masa yake, kuma sun lura da matsanancin son da yake miki shi yasa fa suka shiga jikinsa idan ban da haka ina imran ina wannan yarinyar tana tafiya kamar bulala, ji fa ranar da muka had’u da ita a mall wallahi nunawa tayi bata son mu ba.” cikin takaici momma ta girgiza kai “ ki rabu da imran taurin kai gareshi kamar mutanen farko sau nawa na nuna masa bana so sau nawa na hanashi, amma ya’ki jin zancena amma lokacine zan nuna masa bashi da wayo daga shi har dangin ubannasa, muje dai zuwa a kuma juri zuwa rafi....”
Ita kuwa amarya tana fita d’akin hajja ta shiga ta zauna ta gaya mata’karya da gaskiya hajja ta hau kai ta zauna. “ kika ce sun zageki zainabu?” Amarya Ta d’aga kai hajja ta kuwa mi’ke zaune “ Ai kuwa tunda suka zageki ba ke suka zaga ba ni suka so zaga aka fake dake, to kuwa ba zai yiwu ba uwarki ni na sha mama na bar mata ban ga d’an abu ta kazar uban da zai zagar mana mahaifiya na ‘kyaleshi ba ke ko da kuwa sadakar yallar uwarsu ce muje madafar “ Amarya farin ciki fal ranta ta mi’ke ta bi hajja kitchen.
Tsaye hajja tayi ri’ke da ‘kugu tana musu kallon sama da ‘kasa “ Eeh lallai kuwa ba shakka na ta’kar’kare na d’au cikin manga, Na sha ba’kar wuya a haihuwarsa ashe dai ku na haifawa, an shigo cikin daula a dafa wannan a sauke wannan,A samu na banza aci ai nak, bama wannan ba uban me zainabu tayi muku kuka zageta? Ko kuwa sa’kon zagin kuka bata taje ta isar min hamsha’kai ?” Shatu ta zaro ido tana kallon amarya murya ‘kasa-‘kasa tace “ Allah ya shirya babba da ‘karya cab” gaba d’aya kitchen d’in ba wanda bai ji maganarta ba har hajja. Amarya ta zaro ido “ ke don ubanki ni nake miki ‘karya ko hajja?” Shatu Ta sake gyara zama tace “ duk wanda yayi ‘karyar ai addu’a nayi “ a sukwane ba suyi auneba suka ga ta zuba wa shatu mari hannu bibbiyu a zafafe hafsa ta janye ta tana mata wani banzan kallo “ kada ki sake ki sake dukanta me tayi miki? “ momma ta nuna musu hanyar ‘kofa “ ku fita “ ta’kofar baya suka fice sannan ta kalli hajja “ kiyi ha’kuri ba wanda ya zageta amma tunda ta fad’a miki kin yarda Allah ya baki ha’kuri” daga haka Ta fice bayan ta watsa wa amarya kallon banza.
Hajja bata shiga d’aki ba anan main parlour ta dinga zazzaga tijara zagi ta uwa ta uba ta dinga aikawa su mommah bayan amarya ta zauna ta sake fonfata wai har taji sanda suke cewa so suke ta mutu su sake mallake manga gaba d’aya har dukiyrsa hakan yasa ta sake sauke kwandon tijara zagi ta uwa ta uba. Ran shatu ya’baci musamman ganin yarda su nahna suka fara had’a kaya wai tafiya