Showing 108001 words to 111000 words out of 117786 words

Chapter 37 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

473

zai basu mafiyinsu idan ta koma gidan Imran.

Imran dai da Shatu suna zaune sun zuba musu ido suna mamakin k’arfin hali irinnasu.

Shaheedah ta mik’e cike da confidence ta yi hanyar ‘dakin Imran, da sauri ya ce mata “Hey where are you go?” Idanunta da suka rine suka yi jajur ta zuba masa kafin ta ce “Zan tattaro kayana da suke bedroom ‘dinka ko ka kwashe ne?” Shatu ta zabura hankalinta a tashe zuciyarta tana bugun kishi, da gaske kayanta na bedroom d’in Imran da su ya ke rayuwa wa ya sani ma ko tsawon lokaci sai ya gansu ya shinshina su ya ke jin da’di in banda haka me yasa bai fito dasu ba?

Ta ja hannunsa suka bi Shaheedahn da sauri cikin ‘dakin saboda ba ta so ta saka mata wani abinda ‘dakin.

Tsaye Shatu ta yi cak tana kallon ta tana packing kayanta da suke daga gefe ‘d’ayansu wardrobe ‘din Imran da take a kulle ya ce bai ga key ‘dinta ba sai ga shi ita ya ciro key ‘din ya bata.
Kamar ta fice amma kishi na cinta ba zata iya fita ta bar Shaheedah da Imran ka’dai a bedroom ‘dinta ba don ba ta gama yarda da ita ba.

Shaheedah tana kuka ta kwashe kayan tas har trolleys guda biyu, ta fice tana waige bedroom ‘din ta cije baki. Akwai abubuwa da tayi targeting sosai a zuciyarta.




Gaba ‘daya suka mi’ke suka fice daga gidan cike da sagaggiyar gwiwar rashin cikar burinsu.



Tun a cab d’in da zata kaisu hotel ‘din da zasu sauka suke kitsa wacce za su fishshesu, Shuwa cikin zafin rai da takaicin dukiyar da ta ‘batar ta ce “Wannan Imran an yi tabbataccen ‘dan iska, amma akwai shawara ta ‘karshe wadda zaki zage ki yita idan kuma kin ‘ki wallahi zan tattara lamarinki na watsar abu ‘daya nake so dole na mayar da dukiyoyina da na yi asara ko ku’din zuwa nan nawa ne?” Ta fa’da tana cizon yatsa. “Shawara ta ‘karshe dole mu samu duk yarda za’a yi mu jawo Imran hotel ‘dinnan ko magani na bugarwa mu zuba masa ya yi having sex dake, wanda zamu ‘dau hotonsa mu kuma tabbatar masa idan har bai mayar da ke ba zamu baza hoton a duniya, mu kuma cire fuskarki mu saka ta wata na san wannan shawarar za ta yi aiki.”
Zainab ta saki ajiyar zuciya kafin ta girgiza kai ta ce “Tabbas sai dai yarda zamu jawo shi zuwa Hotel ‘dinne aiki.” Shuwa tana girgiza kai ta ce “Babu wata wuya numberr wayarsa zamu samu, sai mu yi ‘karyar Shaheedah ta mutu, na san dole ya zo daga nan sai mu san abin yi ko likita mu kira yayi masa allurar futar hankali ko da Ta ‘karfi ne kuwa.”
Shaheedah ta yi murmushi tana tantamar lamarin tunda ta san ba Nigeria bane hakan ba mafita bace” ta sanar da su tana girgiza kai, ku dai kira shi d’in idan yaso ni na san yarda zai yaudare shi dole ya kusanceni.




Shatu kuwa suna fita daga gidan ta ja fuska ta tsuke da gaske lamarin ya bata haushi, fuskarsa da murmushi ya ke dubanta kafin ya kai hannu ya sakar mata cakulkuli da dole ta dur’kushe tana dariya cikin dariyar ta ce masa “Wallahi naji haushi, shine har da hanani key kace baka ganshi ba, ashe kaya mai amfani ka saka a ciki kayan Lovy d’inka.”

Kyakkyawar sumbata ya kai mata bakinta hakan yasa ta yi shiru, yana murmushi ya janye jikinta a kunnenta ya rad’a mata “Shatu Danger!” Ya lumshe ido bayan ya hura mata wata iska a kunne....

Nazeefah Nashe


Shikkenan Shatu tayi shiru da zancen, kafin ta janye jikinta ta mi’ke direct kitchen ta shige Imran murmushi yayi a zuciyrsa ya ce sai kace iya girkin ta yi, saboda tun ranar da tayi ‘kwa’ba ya hanata yin girkin ya zata da gasken bata iya ba.


Nutsuwa tayi sosai ta fara shirin girkin da zata yi Mandi Rice sai patoosh salad da steam bread tayi sai kuma ta had’a shredded chicken, tuni gidan ya bad’e da wani daddad’an ‘kamshi da ya farkar da Imran daga barcin da yake akan three sitter a parlour d’in.

Mamaki ya kamashi jin yanayin ‘kamshin tamkar a restaurant wato da gaske dai Shatun girki take, shi tsoron shiga kirchen d’in yake shi yasa bai shiga ya hanata ba ko kuma ta saka masa rigima.


Yana zaune ta fito ta fara arranging abincin a dinning ta gama komai sannan ta shiga wanka.


Tsaf ta fito cikin wani sassau’kan lace mara nauyi ta kashe d’aurin ta kana ganinta kaga cikakkiyar bahaushiya don yau kam har da sar’ka da d’ankunne aka saka ga bakin nan ya ji red lipstick duk da shi kad’ai ta saka a fuskarta ba ‘karamin kyau ta yi ba.


Tunda ta fito Imran ya kasa janye idonta daga kansa ba ‘karamin kyau tayi masa ba na fitar hankali, ya dinga godiya ga rabbil izzati da ya bashi kyakkyawar mata. Tana zuwa ta bushe fuskar sa da iskar bakinta, da sauri ya lumshe ido yana sha’kar hucin daddad’an mouthwash d’inta. Ri’ko hannunta ya yi da sauri ta zame “Please ‘kalbeey kada ka ‘bata min makeup after all ma ni yunwa nake ji.” “Mai zaki ci?” Ta guntse dariya tace “Jagwalgwalon abincina mana na gaji da cin abincin garinnan ni baya min test, kai kuma kace ban iya girki ba, amma kuma yau dole kaci abincina.” Gabansa ya fad’i sosai yake tsoron cin abincin saboda bai san mai zai tarar ba. Yana kallonta tana zuba masa abincin a ido dai tamkar zai yi dad’i bai san a bakin ba.

Ta saka spoon d’aya a plate idanunta cikin nasa ta bud’e abincin a spoon tace “Ha” ya runtse idanunsa kafin ya bud’e bakin saboda bai san mai zai tarar ba tsami ko gishiri ko yaji? Sai dai ga mamakinsa wani daddad’an test ne ya gauraye bakinsa har bai san sanda ya bud’e ido ba yana tauna abincin ya had’iye cikin tsananin mamaki ya ce “Dama kin iya girki har haka?” Dariya ce taso ku’buce mata tace “Dama gwada ka nayi naga zaka iya zama dani ban iya abinci ba? Alhamdulillah kaci jarabawa, dole nagode wa Mommah da Maman tayseer da ta koya min abincin ‘kasashen waje.” Hannunta ya kamo ya ‘kwace spoon d’in ya dambazo abincin ya fara ci cikin nishad’in don ya dad’e bai ci abinci mai dad’insa ba. Ya cika abincin a bakinsa yace “wacece Maman tayseer d’in?” Tana murmushi tace mai eatery d’in MHD fa? Wato Mara Hamisu Dankaka ba abinda ba tayi har abincin gidan biki, snacks da cakes Na birthday ta ‘kware a kowane fanni.” Imran ya girgiza kai yace “Tabbas ni shaida ne tunda ga matata ta ‘kware ita ma.” Shatu ta dubeshi yarda yake cin abincin ba wasa abin har mamaki ya bata. Ta ce “Yanzu ace na yi maka abinda nayi maka kwanakin baya ina yarinya zaka cigaba da cin abincin?” “Menene abinda kika yi min kwanakin baya?” Dariya tayi sosai ta ce “Lokacin da ka tsaneni na ji haushi na zuba maka yawu da ruwan hammata a tea.” Yana murmushi ya kamo hannunta “Ban da tona abinda ya wuce Hayateey ai yanzu ko hammatar ina lashe ta tas yawu kuwa nawa nasha? Ko mai na jikinki yanzu bana ‘kyamarsa ji nake kamar daga jikina suka fito.” Shatu murmushi kawai tayi ba don ta yarda ba ta zuba ruwan tatacciyar pineapple da ta had’a masa sannan ta tara yawu a bakinta ta zuba sosai a ciki ta mi’ka masa. Yana murmushi ya had’a da hannunta ya shanye abinsa tas cikin dad’in rai ya kai mata peck a lips d’inta “Yanzu kin tabbatar?” Shatu cikin farin ciki ta fad’a jikinsa kawai tana tsananin murna. Sai da suka nutsu da kansa ya zuba abincin ya dinga bata har sai da tace ta ‘koshi, sosai yake mamakin yawan cin abincinta gashi ta ‘kara murjewa duka wasu halittun jikinta sun sake cika sun tumbatsa kamar ana hura musu iska.





———————————

Hameedah ta dur’kushe gaban Mommah tana hawaye sosai ta ce “Please Anty Dijah ki yafe min wallahi ina jin ha’k’kinki ne yake d’awainiya da ni, gaba d’aya Habib ya juya min baya tunda na dawo gida bai nemeni ba ko a waya Shuwa ta riga tada gama dashi da asirinta.”
Mommah tana murmushi ta kamata tausayinta sosai ya ratsa zuciyarta, dama ita bata ri’kesu da komai ba tuni ta yafe mata, kuma kullum ta yi sallah sai ta ro’ki ubangiji ya daidaita tsakanin Hameedah da mijinta, idan ma asirin ne a jikinsa Allah ya ruguza kaidinsu saboda ko bakomai ‘kanwar mijinta masoyinta ce, wanda in dai Hameedah na cikin rashin nutsuwar zuciya ta tabbatar itama na ta mijin zuciyar tasa ba zata nutsu ba ko da kuwa ya nuna mata bakomai, ta san zance kawai ya ke. Musamman Hajja da shekarun girma suka kamata yau lafiya gobe cuta, wannan nema dalilin da yasa tasa Manga yada dawo da Hajjan kusa da ita, ita ke kula da Hajja da abincinta da magungunanta na hawan jini da ciwon sugar. Sosai ta d’au Hajja matsayin uwa ba suruka ba, yarda zata kula da babarta ba tantama haka zata kula da mahaifiyar mijinta domin itama uwa ce.

“Kiyi shiru Hameedah insha Allah zaku daidaita tsakaninki da mijinki, zan baki wasu addu’oi matu’kar kika lazimci yinsu ina tabbatar miki Habib da kansa zai kawo ‘kafarsa neman biko in dai asiri ne insha Allah kamar ya karye ya gama, burina d’aya ki yarda da Allah shine mai yi ba boka ko malam ba, idan har kin ri’ke haka kin rabauta duka daga fitintunan duniya, wallahi Hameedah boka ko malam basu isa su baki abinda ba ya cikin littafin kundin ‘kaddararki ba, ba abinda suke sakawa sai dai su dulmiyar da mutane a turbar ‘bata, kuma bahaushe yana cewa ‘karshen tuka tuki tik, duka aikin nasu akwai ‘kayyadadden lokacinsa, Allah cewa ya yi Ud’uni Astajib lakum ku ro’keni da kanku zan amsa muku, ba fa cewa ya yi dole sai kaje wajen malami ka gaya masa bu’katarka ba sannan zai amsa maka, direct ya ce ke da kanki ki ro’keshi ki kuma saka ya’kini a zuciyarki Allahnnan dai shine mai yi, sai kiga Allah ya amsa miki Allah yasa mu dace. Yanzu ki tura masa text na bada ha’kuri kada kuma kiyi jayayya da mijinki idan yace zai auri Shuwa, ki amince masa tsuntsun da yaja ruwa ai shi ruwa kan doka, ki ja gefe ki yi kallo ke dai kiyi tada addu’a Allah ya kiyayesu daga sharrinsu da duk wani asirce-asircensu idan su nayi d’in kenan Allah ya shiryesu mu kuma da ba mu fad’a ba ba wayon mu ko dabarar mu bace Allah ya kiyayemu ya sake tsare imaninmu.” Hameedah ta rungume Mommah tana kuka tare da jin haushin kanta da tunanin tun farko me yasa ta tsani Mommahn menene dalili tunda ta tabbatar da ba abinda ta tsare musu ba tama fiye shiga shirginsu ba. Mommah ta dafa kanta ta ce “Ki je, Allah ya shige mana gaba.”




———————————-


Cikin kwana biyu suka gama duk wani shirinsu da ‘kulle-‘kullensu, sun tanadi wani ruwa mai yau’ki da zasu zuba masa a ‘kofar d’akin da zarar ya shigo sai ya zame wannan zamewar ita zata sa su d’auko ruwan da suka zuba ruwan maganin bugarwa su ba shi ya sha daga haka kuma labarin sai ya canja. With full confidence suka had’a hannu suka tafa suna dariya sosai gani suke tamkar Imran yazo hannu ya gama.




——————-

Cikin dare Shatu ta tashi da matsananciyar yunwa da sauri ta zame jikinta daga na Imran zata sauka daga gadon ya ri’ko hannunta, da muryar barci ya ce “Hayateey sleep mana ina zaki?” Jikinta na rawa tace “Imran yunwa na keji ji nake kamar na fad’i.” Ya bud’e idonsa yana mi’kewa zaune ya ce “Muje amma wani irin ci ne wannan kullum ke kenan cin abinci kada fa ki zama ‘katuwa.” Da muryar shagwa’ba tana bubbuga ‘kafa ta ce “Ni yunwa na ke ji wallahi”
Da sauri ya ja hannunta suka fita, cikin sauri ya had’a mata tea mai kauri ta shanye amma still wai yunwar bata tafi ba hakan yasa ya dafa mata noodles ai kuwa da zafinta ta dinga turata. Imran tsayawa kawai ya yi yana kallon ikon Allah da tunanin tabbas ba lafiya ba dole gobe suje suga doctor, don abin har tsoro yake bashi. Sai da ta cinye tas ta kora drink mai sanyi sannan ta yi gyatsa ta ce “Alhamdulillah” Imran ya girgiza kai ya ce “Ta’b” wai ‘kalau kike kuwa? Ni fa cinnnan ya fara bani tsoro.” Bakinta ta turo tace baka so nayi ‘kiba ko?” Da sauri ya girgiza kai “Ni fa ko buhu kika zama ina sonki haka.” Ta yi murmushi tana d’ane bayansa “Tohm goya ni mu tafi.” Caf Imran ya cafe ta a bayansa suka koma bedroom.



Da safe ta yi wanka, amma duk kayan da ta saka sai taga sun ‘ki shiga, a gefen bed ta zauna ta zubawa kayan ido tana saka kuka, tabbas ba mamaki ciki ne da ita don idan bata manta ba cikin su Akram ma haka tayi. Ta zaro ido ta ce caf yanzu haka zanzo na ‘kara zama ba’ka hancina ya zama ‘kato kamar cikin su Akram, ta tura bakinta tana sake hararar kayan da suke zube a gado a fili ta ce “Ni gwara ma nazo na fara shirin komawa Nigeria tunda mun kusa resuming school.”


Yana fitowa daga wankan don yau da rigima ta tashi ta’ki yarda ma suyi wankan tare ko da yake idan tana period dama bata amincewa su yi wanka tare. Ya zuba mata ido yana kallon hawaye sha’be-sha’be a fuskarta, ga uban kaya ta barbaza a gabanta kuma bata saka ko d’aya ba sai ‘bingilin towel a jikinta.

Ya ‘karasa wajen yana murmushi “Ya dai madam? Ko tsokana kike ji kika zauna min daga ke sai towel don kin san a off kike, haka ba zai hana ni zuwa ba wallahi.” Bakinta ta turo tace “Ni Nigeria zan tafi, ji fa kaya na duk sun min kad’an bani da kayan sawa, Mommah tace an had’a min lefe na daka tura kud’i, ni kawai ka barni na koma na gaji da zaman nan garin.
Murmushi ya saki ya fad’a gadon daga shi sai towel ya ce “Wallahi kin jawowa kanki kin san sarai wannan shagwa’bar hana ni sukuni take.” “Period fa nake.” Ta fad’a da sauri cikin wata irin murya shima ya ce “Period d’in ai ba a haramta min kusantarki ba, bance miki zan wuce gona da iri ba.” Daga nan labari ya sha banban.



————-
2:00 pm sharp tayi musu a gaban doctor d’in bayan aune-aune da gwaje-gwaje, ya tabbatar musu da wanzuwar ciki a jikin Shatu na wata uku da kwanaki. Farin ciki sosai Imran d’in ya nuna tun a gaban likitan ya rungumeta tsam a jikinsa a kunne ya rad’a mata “Kin amince ni sharp shooter ne wannan karan triple nake so ba twins ba.” Murmushi kawai ta saki.


Sai da ya biya ta mall ya sake siya mata kaya wanda zasu mata dad’in sawa da kayan ciye ciye iri-iri musamman pringles da ta mayar da shi kamar wajibi ne kullum sai ta cishi. Tun a hanya ya ri’ke hannunta gam yana murzarshi yana driving zuciyarsa fal annashuwa “Yaushe zamu koma Nigeria sabida karatu na.” Yana murza hannunta ya ce “Dropping semesterr za kiyi sai kin haihu kya cigaba yanzu dai kam ba zan iya barinki yawo da cikina ba,
Sai nan da 4 months zamu koma Nigeria.” Ta turo baki alamar ba haka ta so ba, bai kulata ba ya cigaba da murzar hannunta yana driving yana bin wa’kar westlife a cikin motar. Dai-dai lokacin da yayi U turn zai shiga gida wayarsa ta yi ringing, ganin ba’kuwar number kuma ta garin yasa shi d’auka, gani Shatu kawai tayi ya zare ido ya ce “What? Gani nan gani nan.” Ya katse wayar yana kallon Shatu ya ce “Shaheedah ta mutu bari nayi dropping d’inki a gida naje.....

Me ya zan yi da ita?



A razane Shatu take kallonsa ta ce “Kamar ya ta mutu?” Da sauri ya yi parking a gefen gidansu ya ce “Haka suka ce min, ki shiga gida bari naje na yi confirming.” Shatu ta yi shiru tana nazarin abin tabbas a matsayin karatunta yaci ace ta fahimci shiri ne, don haka ta ri’ke hannunsa “Ba zaka je ba, idan kuma zaka je ba dai kai kad’ai ba, muje tare a nemi police su shiga lamarin, idan yaso ni da police d’in mu tsaya daga waje sai kai ka shiga ciki.” Shiru ya yi yana nazarin maganarta kafin ya girgiza kai “Hakan ya yi muje.” Kafin suje kuwa sun kira yafi sau nawa. Basu yi wuyar samun police ba bayan sun yi musu bayanin issue d’in,
Aka basu police uku ciki har da mace suka kuma tafi da motar police d’in.



A harabar fundu’k d’in suka yi packing ya ciro waya ya yi dialling numberr da aka kira shi, ba ‘bata lokaci aka d’aga Shuwa a gigice kamar gaske ta sanar da shi numberr d’akin da suke. Imran ya shige ciki ya bar su Shatu a reception bayan ya sanar da su room number d’in da yarjejeniyar idan suka ji shiru after just like ten minutes kawai su biyoshi.


Shatu tana kallo ya shige lifter d’in kawai sai hankalinta ya kasa kwanciya zuciyarta ta dinga bugu.


A bud’e ya tarar da room d’in kasancewar apartment ne suka kama mai room and parlour. Shuwa da zainab suna zaune a parlourn da alamun tashin hankali a fuskokinsu, suna ganinsa suka mi’ke a kid’ime Shuwa tana sake matsar hawayen ‘karya ta ce “Shiga tana ciki Imran Shaheedah tazo sa’i da ambaton sunanka ta cika.” Imran gaba d’aya ya gigice ko bakomai akwai dangantaka da ya zama dole ya damu da mutuwarta, da sauri ya danna kansa cikin d’akin dai-dai lokacin da ya su’bale ji kake tim ya fad’i a ‘kasa cikin azama Shaheedah da ta riga ta gama shirinta ta yo kansa da ruwan maganin a cup ta saka masa a bakinsa azaba ta saka shi kur’be ruwan da aka zuba maganin bugarwar a ciki, yana ware ido alamar mamakin ganin Shaheedah da ranta, mintuna biyu sunyi yawa maganin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login