Showing 51001 words to 54000 words out of 117786 words
shi fit daga ranta. Bata muradinsa a rayuwarta kamar yarda ya tozar ta ta iya tozarci.
Suna yin parking Nahna ta sake kallonta tace “ki tabbata al’kawarin da kika d’aukar min kin cika shi kada ki sanya Mommah ‘bacin rai.” Shatu ta d’aga kai, har a zuciyarta tana fatan ta iya danne ‘bacin ran ta amma gani take abin da kamar wuya. Kafad’ar Mommah nanne wajen da take sauke duk wani ‘bacin ranta burinta yanzu ta jita jikin Mommah tana sauke mata damiyoyinta. Ta kuma sanar da ita Imran ya ‘kwace mata budurcinta sannan ya dan’kara mata saki. Amma anya kuwa zata Iya? Zuciyarta ta tambayeta da sauri ta girgiza kai “No I can’t ai da kunya wallahi ba zan iya ba.”
Suna bud’e ‘kofar main parlourn, da Anty Amarya suka fara had’a ido tana zaune ta d’ora ‘kafa d’aya kan d’aya. Nahna ta ja hannun Shatu da take ‘k’karin gaishe ta suka wuce part d’in Mommah. Anty Amarya tsaki ta ja.
Sai dai tayi farin cikin ganin Shatun don ‘kila ha’karsu ce ta cimma ruwa kamar yarda suke fata.
A zaune suka samu Mommah ran ta duk a ‘bace tun ma ba ta ji maganar sakin ba, wannan ‘bacin ran na tafiyar da yayi ya barta ne ba ta da lafiya alhali sarai ya sani. Shatu na ganinta ta ji zuciyarta ta narke duk ‘ko’karin da take na son cikawa Anty Nahna al’kawarinta hakan ya gaza cimma faruwa, tuni ta fad’a jikin Mommahn ta saki kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro. Momma ranta a ‘bace ta shiga shafa bayanta. Cikin muryar lallashi ta fara mata magana “kiyi ha’kuri Shatu bai kyauta ba, kuma ni da ya sanar dani baki da lafiya da tuni ban tura an d’aukoki ba, tun da ni na damu dake.” Nahna ji tayi ita ma zuciyarta ta karye da sauri ta sunkuyar da kanta. Hawaye wani na bin Wani. Sai a lokacin Mommah ta lura da Nahna da take hawaye, tun kafin ta kai ga tambayarta menene? Gabanta ya yanke ya fad’i, dama dauriya take gaba d’aya ranar bata jin dad’in yanayin jikinta. Da sauri tace “Wai menene kun bar ni a cikin duhu.” Nahna a hankali ta mi’ke tare da mi’kawa Hafsa takardar, sam ba zata iya tsayawa ba, ba zata iya jure ganin Yanayin Mommah a lokacin da ta ankare da abinda yake cikin takardar ba. Tana mi’ka mata ta fice da Sauri. Hafsa ma gabanta ne ya fara dukan uku-uku hannunta na rawa ta fara ‘ko’karin mi’kawa Mommah takardar, sai dai cak da Mommah tayi bata kar’bi takardar ba yasa Hafsa kai idon ta kan Mommah, sai lokacin ta lura Mommahn a tsaye idanunta suke cak, yanayin da yake nuna ta shiga shock sosai. Da sauri Hafsa ta mi’ke tana girgizata, sai a Lokacin Mommah Ta saki ajiyar zuciya ta runtse idanunta kawai ba tare da ta ce komai ba, ko ba a fad’a ba ta san meye a cikin takardar ba ta bu’katar ‘karin bayani. Imran ya kasa bin umarninta ya saki Shatu. Ba tare da ta karanta takardar ba tace “Saki nawa ne?” Hafsa tace “‘Daya ne Mommah amma please kada ki d’aga hankalinki.” Ganin shirun da Mommah tayi yawa yasa Hafsa d’aukan wayar ta ta kira Dahda sannan ta kira Hajiya Mama duk ta sanar dasu halin da ake ciki. Hajiya Mama sakin ajiyar zuciya tayi kafin tace “Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, ina Addar ta ku?” Hafsa cikin sauri ta kama Mommah da take shirin zubewa ‘kasa, vedio call ta shiga ta kira Hajiya Mama. Hajiya Mamar tayi mata umarni ta saka wa Mommahn wayar a kunne. Da sauri ta kara mata. Muryarta cikin nutsuwa ta fara mata magana “Rashin yarda da ‘kaddara a lokacin da ta sameka alamune na tawayar wani sashe daga cikin imanin mutum, idan masifa ta sameka kuma cewa aka yi kace Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna. Don haka ina umaratar ki da ki fad’a yanzunnan.”cikin rawar murya alamar kuka yana son cin ‘karfinta ta furta Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna Hajiya Mama Imran ya cuc...” cikin daka tsawa Hajiya Mama tace “akul kada na soma ji kada na soma jin kin yi masa baki ko kin fad’i mummunar kalma a kansa, duk uwa ta gari bata furuci akan d’anta a lokacin da ranta yake ‘bace, an fiso kiyi shiru ko kiyi musu addu’ar shiriya idan Imran ya lalace sai kin fi kowa shiga tashin hankali a rayuwa don haka tsakaninki dashi addu’a. Aure dai Allah ne yake ‘kaddarashi haka nan saki shi yake zartar dashi da so ko ba so duk wannan a hannun rabbul izzati yake, babu wani mahaluki da zai aikata abu face dama yana rubuce a cikin Kundin ‘kaddararsa, don haka ki yawaita yi masa addu’a da fatan Allah yasa hakan ya zame musu alheri gaba d’ayansu dama Allah (s.w.a)ya fad’a zaka ga kana tsananin son abu a zuciyarka baka san sharri bane a wajenka, kamar yarda zaka ‘ki abu tsananin ‘kiyayya ba ka san alheri bane a wajenka shi yasa a koda yaushe ake son mi’ka lamari ga ubangiji fiye da za’bin rai ko son zuciya.” Zuciyar Mommah ta d’an huce daga kumburin fushin da take sai dai hakan bai hana ta furta “Hajiya Mama a karo na ba adadi mutanennan suna samun nasara a kaina wannan karan ma sune da nasara a kaina. Ni na tabbata ba haka suka bar Imran ba.” Cikin tsananin fushi Hajiya Mama tace “Baki yarda da abinda nace miki ba kenan? Baki yarda Allah ke hukuntawa ba saboda kin saka a ranki zasu iya yi miki abinda Allah bai miki ba, ki cire wannan tunanin a ranki ki kama Allah, duk abinda ya samu bawa ko zai sameshi daga gareshi yake, idan ma su d’inne to muje a cewar sun ci Nasara a duniya to ki kwana da sanin cewa fad’uwa da madawwamiyar asara ta tabbata a garesu ranar al’kiyama. Bana son ki sanya damuwa a ranki har tayi tasiri a lafiyarki. Kiyi ha’kuri mai ha’kuri yana tare da samu, ita kanta ‘yar taki idan ta ganki cikin damuwa zaki raunatar da zuciyarta, alhali ke ake so ki ‘karfafa mata gwiwa.”
Sosai zuciyar Mommah tayi sanyi daga tu’ku’kin ba’kin cikin da take, tabbas duk wanda ya rasa mahaifiya yayi kuka. Ta d’aga mata kai alamar ta aminta da duk abinda tace “Yauwa Allah yayi miki albarka ki tashi kiyi sallah kiyi addu’a Allah yasa mu dace. Su Nahna kuma suyi shirin tahowa don sun kusa komawa makaranta.” Mommah tace “To insha Allah.” Ta fad’a tana sakin ajiyar zuciya bayan ta kashe wayar, tabbas ta samu rangwame sosai kashi talatin cikin d’ari tuni ya zagwanye ta d’ora hannunta bayan Shatu da take kwance lamo a jikinta. Ta windownta ta ga alamar giftawar mutum ta tabbatar la’be aka yi mata. Ta saki murmushi a zuciyarta tace kuyi murna kuyi farin ciki a karo na barkatai burinku ya sake cika.
Kamar yarda tayi hasashe kuwa Zainab ce jikin windown ta kuma ji duk abinda yake wanka na, don tsananin farin ciki har rawa da juyi tayi a cikin parlournta burinta ya cika wannan karon ma suke da nasara. A fili ta furta haba Dijah muje zuwa ni daku d’an halak ka fasa in dai ina da Shuwa ai na tabbata bani ba kuka. Yarda na zauna da ba’kin cikin ki shekara da shekaru kema yanzu zaki fara d’and’ana nawa. Don Imran dai haihuwarsa kawai kika yi sai na dawo ni nake iko dashi kamar ra’kumi da akala.
Ta sake lalubar numberr Shuwa wannan karan ma dai switch off da alama har zuwa lokacin bata isa wajen mutumin ba. Tsaki ta ja labari take son bata amma ba dama. Ta juya akalar kirannata a layin Shaheedah ita ma still switch off. Kawai sai ta dangwarar da wayar tana sakin dariya.sai muce Allah ya shirya.
Dahda kuwa hankalinsa a tashe ya baro office ya taho gidan jin wannan tashin hankali, shi kansa ya tausayawa Dijah a yanayin da ya ganta. Sam Imran bai kyauta ba wallahi gashi yayi ta kiran wayarsa a kashe burinsa dama yaji idan da damar sulhuntawa a sulhunta tun kafin labari ya baza dangi. Shi kansa yaga wautar Imran da ya saki Shatu yarinya son kowa ‘kin wanda ya rasa. Rashin samun wayar yasa ya taho gidan jikinsa a salu’be.
A parlour ya tarar dasu kan kujera, har Shatu da take kwance kanta a saman cinyar Mommahn, ita kad’ai ta san azabar da take cinta a ‘kar’kashinta sai dai ba damar furtawa. Ina kunya ba zata barta furtawar ba don haka take ta nu’ku-nu’ku da abinta, su kuma zatonsu duk damuwar sakin da aka yi mata ce. Dahda yayi sallama ya shigo wanda ya sa Shatu saurin mi’kewa, Dahda ya kai dubansa kanta tausayinta gaba d’aya ya sake rufeshi. Ta gaida shi ya amsa cikin kulawa. Tare da shiga ciki yana duban Mommah “Muje ina son ganin Ki.” Mommah ta mi’ke ta bi bayansa bayan ya shige bedroom d’inta. Tana shiga ta saki ‘yan ragowar hawayen da take ta ‘ko’karin dannewa. “Kaji abinda d’anka yayi min ko?” Dahda ya saki d’an murmushin da bai kai zuci ba. “Shine abinda yasa kike ‘bata ranki a banza, shin sakin ba d’aya bane? Idan kuwa haka ne ai Kin ga za’a iya mayar da auren kafin ma wani yaji.” Wani kallo Mommah tayi masa kafin ta saki murmushi mai ciwo tace “Ai Dahda ko Imran ne autan maza a duniya Shatu ba zata sake komawa aurensa ba, anyi an gama kenan wallahi.” Dahda ya girgiza kai “kada kice haka Dija na ba’a yiwa aure wannan cin alwashin baki san abinda Allah zai zaratar ana gaba ba.” Ranta ne ya sake ‘baci “Don Allah Dahda mu bar wannan maganar ni ko zancen Imran ma a yanzu bana son ji, aure kuma tsakaninsa da Shatu ko bayan raina na haramta masa shi har abada kuwa, kuma daga yanzu na kulle wannan chapterr Shatu karatu zata cigaba da yi har zuwa sanda zata siyawa kanta ‘kima da mutunci a gurin kowa, a daina kallonta a matsayin fulanin daji bagidajiya har ayi mata sakin wula’kanci, farin ciki na d’aya da bai riga ya d’ebe mata albarkatun jiki ba, bai kuma kawar mata da budurci ba da ya cuce ni wallahi, saboda haka ni yanzu ba ya gaba na yaje ya cigaba da matar so har gaban abada.” Dahda ya saki ajiyar zuciya “A daiyi ha’kuri kada ayi masa baki idan rai ya ‘baci ba’a sob hankali ya gushe Dija na. Amma ya aka yi kika san bai kawar mata da budurci ba kin tambayeta ne?” Momma ta girgiza kai “kwananta nawa a gidan uku fa dama Dahda tace ko kallon arziki bai yi musu ba, yarda ya tsaneta bana jin zata tsole masa idon da har zai aikata wani abin da ita, ba ma zan tambayeta ba balle na sa ta jin kunya ‘karshenta ma bata san abinda zan tambaya d’in ba inje in bud’e mata wani sirrin da ya girmi kwanyar kanta in jefa mata tunani da ‘kananan shekarunta.” Dahda ya girgiza Kai “kafin yace Ai shikkenan zan dai cigaba da kiransa har zuwa sanda zan sameshi ban san inda ya tafi bane.” Momma ta ta’be baki kawai ba tace komai ba.
Dada tsohuwa tana fitowa daga d’akin da take taga Shatu zaune da su Hafsa. Baki ta kama tana taunar goro kafin tace “Muhammdu d’an Abdallah mai zan gani haka ke kuma wa yace ki fito wirjanjan haka ko yunwar ya sake barinki da ita?” “Cab Dada ai gwara yunwa akan abinda yayi mata sakinta fa yayi.” Momma ta fad’a tana fitowa daga bedroom d’inta. Sai gani su kayi Dada ta zauna da’bas akan kujera “menene saki? ko dad’in ji babu ke dai wallahi Dijah kiyi ta instingifari don bakinki ba ya fad’ar Alheri sai sharri, sharrin ma Ki rasa wa zaki yiwa sai d’anki Na cikinki auzubillahi wallahi uwarki bata yi sa’ar haihuwarki ba.” Mommah cikin takaici ta shige d’aki, tana ji Nahna na sake tabbatarwa da Dada sakin. Ji tayi ta saki kuka tana fad’in “Wallahi Dijah kin haifi tanbad’adde tunda muke a danginmu ba’a ta’ba bazawara ba sai yanzu...”.
Zainab Amarya da sauri ta sallame sallahr, ta d’au wayarta da take ta faman ringing, kamar yarda tayi hasashe kuwa Shuwa ce. Don haka cikin azama ta saka wayar a kunne tace “ke kuwa Shuwa ina kika shiga? Tun safe nake nemanki da daddad’an labari saki dai ya tabbata.” Shuwa tace “ Kai har naji dad’i, hankalina ya kwanta. Sai dai fa da wata a ‘kasa don kuwa yanzu daga wajen sa nake ya bani wani magani yace lallai a saka masa a abinci, shine ‘kiyayyarta zata dawwamawa zuciyarsa idan ba haka ba nan da lokaci kad’an komai zai iya canjawa kuma yauyau ake son a saka masa kafin wancan na jikinsa ya sake shi. Don haka ga maganin yanzu zan taho dashi.” Anty Amarya ta zaro ido “Yau kuma Shuwa ba sa fa gari, ya za’a yi yanzu?” Shuwa ta zaro ido “ki aika mata mana sai ta tura tasha a kar’ba” Zainab tace “kin san ina kuwa suka tafi? Turkey fa.” Wayar da take hannun Shuwa ce ta fad’i cikin tashin hankali tace “Wallahi to zainab akwai gagarumar matsala matu’kar wancan maganin ya sakeshi kiyi sauri ki kirata idan jirginsu bai d’aga ba ta san yarda tayi ta hana tafiyar a yau har sai ta amshi maganinnan..” zainab hannunta na rawa ta shiga danna kiran Shaheedah....
*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍
NAZEEFAH SABO NASHE
FREE📚
08033748387
-30
Elegant Online Writers......
Cikin hukuncin ubangiji bugu d’aya wayar ta shiga, Shaheeda tayi saurin picking call tamkar jira take dama a kira. Anty Amarya ta saki ajiyar zuciya. Shaheeda da hannunta yake sar’ke da na Imran taji Antynta tace “Hello Shaheedah ki san yarda kika yi kika ruguza tafiyar nan dan akwai babbar matsala, auren dai ya mutu amma komai zai iya faruwa Idan ba kiyi amfani da wannan maganin da Shuwa ta kawo yanzu ba.” Shaheedah da ta saki baki cikin tsananin razana tace “Ai muna cikin jirgi har mun d’aura belt, ina shirin switching wayar Off fa kika kira ni.” Zainab tace “shikkenan Shuwa kin ji sun tafi.” Shuwa ta dafe kai, sun jima zaune cikin hali na tashin hankali, kafin Shuwa ta saki ajiyar zuciya ta dubi Zainab tana mi’kewa “Shikkenan ni bari na wuce zama bai ganni ba, tunani na d’aya shiga kwazazzabonnan sam hanyar bata da kyau, shima nace masa yayi ‘ko’kari ya samu waya yace min wani baya bu’kata, yana da babbar hanyar sadarwa daga aljannu. Kema kiyi ‘ko’kari ki san hanya da kanki ki dinga zuwa kin bi kin li’ke a gida uwa a kanki aka fara aure, daga anyi magana kice kina shakkar mijinki tattabara uwar aure. Kin zauna kamar wata sokuwa har yau kin kasa kame miji.” Anty Amarya jiki a sanyaye tace “Ke dai kiyi ha’kuri Shuwa Manga waccar matar ta riga ta shanye zuciyarsa tsaf, wallahi duk asirina ta fini, don duk zaman da nayi a gidannan da asirce-asircen da nake baya tasiri a zuciyar manga, kallon arziki wannan ba yi min shi yake ba,a wajen danginmu kad’ai nake samun sau’ki don Hajja da kanta ma bani abu take tace na zuba masa a abinci, don mu had’u muyi maganin makira Dijah,amma wallahi kamar ‘kara masa ‘kaunarta ma nake yi.” Shuwa tayi tsaki “ Dai na ga ya min kayan haushi don Allah da kinje kin yiwa mutumin can bayani ai da ba haka ba, kin zauna kina jira na inyi hidimarki in yi Ta ‘yarki, shi yasa sam ni ban yarda da lamarin zaman aure ba a wani kulle ka a gida sai san da a kaso zaka fita. Idan zaki tashi tsaye ki tashi idan kuwa ba haka ba kina ji kina gani burinki zai bi iska.” Daga haka ta fice kamar guguwa ta tafi. Duk takaicin zainab na cika ta shi ys sam bata so tayi wannan auren na jaraba ba, da tun tana yarinya ta ‘kidirce sai ta auri Manga shi yasa ma ta taimaka mata, don sosai take ji da ita ta d’auketa tamkar uwa d’aya uba d’aya suke.
Ita kuwa Shaheedah tana cikin jirgi abin duniya ya isheta, tunaninta mai zaije ya dawo. Burinta na farko dai ya cika da taji an saki Shatu. Amma fargabar ta d’aya yarda lamarin zai juya, duk da ba ta haufi a al’amarin Shuwa ta san tabbas zata taimaka mata. Ta sake kwantar da kanta a kafad’ar Imran, da har I zuwa lokacin ya kasa walwala fuskar sa a had’e take kamar hadarin kaji. Ji yake kamar bai kyauta ba kamar Allah zai tambayeshi akan tsakaninsa da Mommah. Ya lumshe ido sakamakon wata ‘yar ‘kwalla da ta tarar masa. Yana ji jirgin ya lula dasu sararin samaniya alamar ya daidaita. Zuciyar Imran tayi nauyi, har wani bugu take na tashin hankali. Fatansa da burinsa Allah ya huci zuciyar Mommah, amma fa sam bai yi dana sanin sakin Shatu da yayi ba. Zuciyarsa ce ma take ‘karfafarsa akan hakan da yayi shine abinda ya dace.
—————————-
Shatu a kwance kan Gadon ta na ainahi na gidansu, idanunta kulle kamar mai barci sai dai ba barcin take ba, sa’banin haka tunani ne ya cika zuciyarta fal, tunanin Imran da moment d’in da suka yi spending a first Night d’insu na daren jiya, shine abinda ya hana ta sukuni, ya kuma yi tsaye a zuciyarta kamar me. Da zarar ta lumshe ido hakan take gani. Imran dai Imran dai, kunnuwanta kuwa sun kasa toshewa da jiyo tarin za’ka’kan kalaman da yake furta mata a kunnuwanta cikin zallar so da alfahari da kasancewarta matarsa. Ashe hakan duk sun wani salon yaudara ne na maza da suke aiwatar wa idan suna bu’katar matansu, tabbas Imran ya bar mata tabon da ba zai ta’ba gogewa ba, ya d’arsa mata ‘kaunarsa a zuciyarta ta yarda ko nan gaba bata jin zata samu wanda zai maye gurbin tarin ‘kaunarsa a cikin ran Ta. Ya cuce ta tun daga ran da ta samu kanta a matsayin matarsa take jin dad’i da farincikin samun miji kamar sa. Ashe lamarin zai zama