Showing 81001 words to 84000 words out of 117786 words
amince ta aura.” Daga Alhaji Baban har Hajiya Maman shiru suka yi sun ma rasa tudun dafawa.
Shatu kuwa tana shiga ‘daki ta sulale akan gado, tausayin Imran ne gaba ‘daya ya cika zuciyarta duk da ba tana nufin ta komawa aurensa bane, amma bata son Mommah ta cigaba da zafafa masa. Turowar ‘kofar da aka yi ne da ‘karfi ya sata ‘dagowa. Anty Nahna ta gani sam fuskarta ba rahma, ta ‘karaso a ‘dakin a zafafe tace “Mi’ke zaune Shatu.” A sanyaye ta mi’ke tana goge 'kwallar da ta kwanta mata cikin idonta.
“Kada kice min kukan rasa Imran kike? Ko kuma kukan mutuncinki da Mommah ta kare? Cab da kuwa kin bani kunya na zata da ke za’a zage a ‘kwaci martabarki da mutuncinki, shine kika zauna kina kuka? Ba dai zuciyarki har yanzu tana son mutumin da ya gallaza miki a rayuwa ba? Da nace kuwa zuciyarki ba tayi miki halacci ba da kuma na kira ki da wacce ta rako mata duniya. Ki bu’de kunnenki ki ji abinda zan gaya miki da kyau, a yanzu ne zaki nuna wa Imran kuskurensa, a yanzu ne zaki ‘dandana masa guba irin wacce ya cusa miki, ki shayar dashi mamaki ki nuna masa kema mace ce Hamsha’kiya yanzu da ko ya sameki zai san mutuncinki da darajarki ba zai ce ya sameki a ‘bagas ba. ki nuna masa kin cika kin ri’ka kin tumbasa samun ki sai wanda ya shiryi. A zahirance ki nuna masa Ammar ne za’binki ko da a ba’dinance ba hakan bane. Kiyi gogayya da shi ki jashi a ‘kasa kada kuma ki sake ki bujirewa umarnin Mommah duk da ‘ko’karin kare martabarki da tayi, kiyi watsi da Imran ki kama Ammar shine ya dace dake. Kin ji mai na gaya Miki?” Shatu Ta ‘daga kai tana jin duk abinda Anty Nahna ta gaya mata shine gaskiya dole ta yakice soyayyar Imran ta yi wulli da ita matu’kar tana son siyawa kanta mutunci. Ta rungume Antyn ta Nahna tana sakin hawaye Na zallar samun nutsuwa.
Ammar kuwa tun da ya shige ‘daki ya kulle kansa ya da’de zaune dafe da kansa, yana jin zuciyarsa na suya, ina ma zai iya da ya sahalewa Imran matarsa, amma ina zuciyarsa ta kasa yi masa lamini soyayyar Shatu sake gauraye duk ilahirin sassan jikin sa take, baya jin zai iya rayuwa idan ba Shatu a tare dashi.
————
Lamarin Imran kuwa babu da’din ji, domin ya rasa mafita ya kuma rasa waye ya turo wannan sa’kon, zuciyarsa sunan Shaheedah ta ke Ta nana ta masa, hakan yasa a zafafe ya mi’ke. Dole ne ya nemo Shaheedah duk da sun koma barci amma asubanci zaiyi yaje ya tambayeta dalilin da yasa ta aikata haka.
Jirin da yaji yana ‘dibansa ne yasa ya tuna rabonsa da abinci tun tea ‘din da ya sha da safe, don haka ya mi’ke a hankali cike da ‘karfin hali ya nufi hanyar fita daga bedroom ‘din.
A kitchen ‘din take a tsaye tana ‘ko’karin dafawa Akram noodles da ya dameta da kuka. Jikinta sanye da Hijabin da tayi sallah da shi, fuskarta fayau ko powder babu, hakan ya saka idanunta fita dar dasu, dama ita tafi kyau ba makeup.
Jin ‘kamshin turarensa ya tabbatar mata shine ya shigo kitchen ‘din, don haka ta aro fuskar jarumta ta saka akan fuskarta, domin kuwa kicin-kicin tayi da fuska, tana zubawa Akram da ya isa wajensa harara tare da jawo shi da ‘karfi “Don gidanku matsa daga jikinsa saninka ma yayi da kake ‘ko’karin li’ke masa shashashan yaro kawai.” Kuka Akram ya fara yi yana ‘ko’karin ‘kwace hannunsa daga jikinta. Shi kuwa Imran sak yayi yana kallonta, yana son yi mata masifa amma yana shakkar kada ya sake cusa tsanarsa a zuciyarta. “Kiyi ha’kuri sabida ya zo wajena kika masa wannan fa’dan?” Wani tsaki taja kafin ta harareshi tace “Anyi masa ‘din ko kai ka haifa min shi?” Jikinta ya matsa sosai tamkar za su ha’de yana jifanta da wani irin kallo mai narka zuciya, cikin wata iriyar murya da tasa gaba ‘daya tsigar jikinta tashi yace “Idan ba ni na haifa miki shi ba amma ni na yi miki cikinsa, kuma cikin son ran ki da shau’ki.” Ta ja baya ha’de da ‘bata rai tace “Sai me don kai ka yi min cikinsa? Ai abu ne mai sau’ki kuma ko yanzu na yi aure wani ma zai min ciki na haihu.” Bai san lokacin da ya dam’ko ta ba cikin ‘bacin rai yana kallon cikin ‘kwayar idon ta da tayi saurin rintsesu saboda bata son idaninsa su yi mata tasirin da za ta kasa yi masa rashin kunya. “Ka cika ni.” Ta fa’da tana kicinyar ‘kwacewa saboda gaba ‘daya yayi kusa da ita tamkar ma rungumeta yayi “An ‘ki a cika kin sai kin sake fa’dar abinda kika ce yanzu, say it again.” Shiru tayi masa, hakan yasa ya samu wannan damar ya cugaba da magana cikin husky voice ‘dinsa. “Ba zaki Ta’ba auren wanda ya jiyar dake da’din da Na jiyar dake ba a first night ‘din mu, kada ki mance zafafan kiss da kika dinga aika min kamar dama ma jira kike Na zo, twins ka’dai sun isa ki shaida cewa ni ‘din gwarzon namiji ne, don haka ki taimaki kan ki kije ki sanar da Mommah ‘dakin mijinki zaki Koma, ni kuma in cigaba da jiyar dake da’di fiye da na wancan daren da ya gabata, Ayshatu na wallahi ina son ki, son da ni kaina bana yiwa kaina shi.” Tsaki ta ja duk da yanayin da ta tsinci kanta bai hanata yin furuci a zafafe ba “Kana so na? Yanzu da Na tashi daga fulanin daji Na tashi daga ‘kazama mai wari, wacce kake ‘kyama har kake gudun a kai ta gidanku, yaushe ka fara so na yanzu da Na zama educated da zaka iya shiga taro dani ba kuma zaka ji kunyar nunawa kowa ni ba a matsayin matarka, yaushe ka fara so na? Yaushe ka daina tunanin me zaka yi da ni? Lokacin da ka ‘dan’dani zumata ka gauraya da ni’imar da Allah yayi min shine kake ba’kin cikin Ammar shima ya ‘dan’dana ya ji ni’imata, ya samu tarin nutsuwa da baiwowin da Allah yayi min...” Da sauri ya sa tafin hannunsa ya rufe bakinta ruf cikin tsananin kishi yake furta “Ki fa’da min komai zaki fa’da amma please kada ki sake danganta kan ki da wani please Ayshatu forgive and Forget wallahi ina matu’kar son ki sai yanzu na fahimci dalilina na takura miki.” Hawaye ne kawai yake sauka daga idanunta, dalilin tuno wa’dannan abubuwan ashe Allah zai amshi addu’oin da take yi akan Imran? Dama bata haufi Ta san ubangiji mujibuddu’ai ne, amma yanzu lokaci ya ‘kure Mommah ta riga ta gindaya katanga mai ‘karfi tsakaninsu. Hannayensa masu tsananin taushi kawai ta ji a fuskarta suna goge mata hawaye, wani sanyi da nutsuwa suka zo mata ta lumshe ido, kafin a zafafe ta bu’de su ta kuma janye fuskarta, dole ta cusawa Imran tsanarta matu’kar tana so ya rabu da mahaifiyarsa lafiya tunda dai tace ko bayan ran ta bata amince su yi aure ba, cikin zafin rai ta shiga furta masa maganganu “Na tsaneka Imran, har abada kuma ba zan sake son ka ba ka riga ka cusa min tsanarka a zuciyata, ka fita a rayuwa ta Ammar nake so shi nake muradin Aure.” Sam bai san sanda ya jata jikinsa ba kamar magnet Lokaci ‘daya ya saki ajiyar zuciya yana furta “Ni kuma ina tsananin son ki ba mamaki son ki shine Ajalina I love you Ayshatu na and I really mean it...”
Turo ‘kofar kitchen ‘din da akayi ne yasa Shatu saurin zame jikinta, sai dai tuni idanunta suka sauka cikin na Ammar bata haufi ya riga ya gansu. A hankali ta furta ya salam!
Saduwar alheri.
Kamar yarda wasu daga cikinku suka bu’kaci a bu’de vip group, Alhamdulillah ‘korafinku ya kar’bu na bu’deshi akan farashin ku’di mafi ‘karanci daga 500 to above. Zaku dinga samun posting 2 times a day. Normal group kuma posting ba kullum ba. nagode da ha’din kan da kuka bani.
Da bazarku muke taka rawa!
Me Zan yi da ita?
43
Tun bayan shigarsa bedroom ‘din ya zauna gefen gado hannayensa ri’ke da kansa da yake matu’kar sara masa, yana fata abinda yaji ya kasance mafarki ne, ba zahiri ba. Ammar ne ya auri matar da ya saki? Kafin yayi aune ya ji zubar hawaye akan fuskarsa, da gaske zuciyarsa ‘kuna take tamkar ta fito daga ‘kirjinsa don tsananin bugu, lokaci guda zuciyarsa Ta dinga hasasho masa rashin adalcin da aka yi masa. Gaba ‘daya wutar tsanar Ammar ta bijirowa zuciyarsa.
Kamar an mintsineshi ya mi’ke da sauri hannunsa ri’ke da takardar gwajin ‘kwayar halitta da aka yi masa, zuciyarsa na sake ‘karfafa masa gwiwar hasashensa gaskiya ne ko da ace Ammar ne mijinta to tabbas wannan yaron nasa ne hakan yana nuni da cikinsa Shatu ta auri Ammar. Tashin hankali! Ya fa’da a fili. Da sauri ya fita parlourn.
Ya kuwa ci sa’a har a lokacin ba su gama cin abincin ba. Ganinsa kawai suka yi ya shigo da hanzarinsa tamkar zai kifa ya kalli Ammar a zafafe yace “Duk wanda ya ‘daura maka aure da ita ka sanar dashi ya aikata haramun domin da ciki na ka aureta, kuma wannan yaron tun ‘dazu na kaishi hospital aka tabbatar min ‘kwayoyin halittarsa irin nawa ne.” Alhaji Baba sak yayi cikin mamakin furucinsa kafin yace. “Waye ya sanar da kai an yi masa aure da ita? ba ayi auren ba amma ana shirin yi nan kusa.” Wani abu ne ya fa’da masa wanda da ya tokare zuciyarsa, har sakin ajiyar zuciya yayi kafin cikin sanyin jiki ya dur’kushe murya a raunane yace “To don girman zatin ubangiji ku yi ha’kuri ku yafe min abinda na aikata na sakin da nayi mata wallahi sharrin shai’dan ne da na zuciya.. kuyi ha’kuri ku mayar min da matata.” Wani kallo Mommah ta watsa masa wanda ya ka’da ‘yan hanjinsa. Cikin matu’kar ‘bacin rai tace “Wallahi idan kaga Shatu ta komawa aurenka sai dai idan bana raye.” Wata irin razana da fa’duwar gaba Ta riske shi ya runtse idonsa gam, yana sake jiyo amon sautin Mommah, da ta cigaba da magana a zafafe “Shatun da ka wula’kanta ka tozarta, ka tsallake ka barta cikin ra’da’di da zafin rashin budurcinta, a ranar da ka hai’ke mata ka saketa sakin tozarci, ka ‘dauke matar so kuka shilla uwa duniya, Bayan ta haihu Hajiya Mama da kanta ta kira ka a waya ta sanar da kai haihuwar amma saboda kai isashshe ne ko magana ba ka yiwa Hajiya Maman ba sai message ‘din banza da ka turo..” Imran da sauri yace “Ni Mommah!” “Kai ‘din fa, ko ‘karya zan maka? Dama saboda irin wannan na ajiye evidence.” Ta ‘dauko wayarta ta bu’de message ‘din a ma’adanar ta ta sirri da ta ajiye shi. “Ko ba kai bane? sannan saboda ma kada a dameka sai ka kama duk numbobinmu kayi blocking, shima ba kai bane?” Wata irin zufa ce ta fara zubo masa bayan ya karanta message ‘din hawaye kuwa tuni ya fara tsere a fuskarsa, tunani yake yi ko dai an zuba masa wani abu ya sha da har ya yi wannan rubutun don dai wallahi ba shi bane itama Mommah da za tayi masa adalci ta san ba zai aikata ba. Amma zai tsaurara bincike akan hakan matu’kar kuwa ya samu Shaheedah ce da aikata irin wannan abun wallahi shi ka’dai ya san hukuncin da zai yi mata. Mommah ta cigaba da magana a zafafe “Saboda haka in dai ni na haifi Shatu na haramta maka aurenta, kuma don in ‘kunsa maka takaicin da ka ‘kunsa mana,Ammar zan aurawa ita.” Wannan karan ba Imran kawai ba har ta Shatu ‘kirjinta dakan uku-uku yake yi.
Idanunsa sun ka’da sun yi ja sosai ya ‘dago ya kalli Alhaji Baba murya a raunane yace “Don Allah ka bata ha’kuri na rantse da girman Allah ban san wa ya aikata haka ba, kuma wallahi ban san Shatu ta haihuba, kuma ba ni nayi blocking ‘din numbers ‘dinku ba hasalima nima ina yawan kira bana samunku.” Mommah tace “Ai na gama magana, su da kan su sun san nayi ha’kuri da abubuwan da ka dinga yi min, wanda har hawan jini suka saka ni, na san kuma iyayena masu adalci ne wannan abinda kayi ba zai sa su su sani janye furucina ba, ko bayan raina Shatu Ammar na yarda ta aura. Don haka ga sadakinsa.” Ta bu’de jaka ta ciro dubu maitan ta ajiye gaban Alhaji Baba. Cikin tu’ku’kin zuciya Imran ya mi’ke ko ganin gabansa baya yi. Ita kanta Shatu ‘ko’kari take sosai wajen danne damuwarta da tuni ta saka kuka gani take kamar abin yayi masa yawa. Kuma ta amince da gaske Imran bai san da haihuwar nan ba. Jikinta a salu’be ita ma ta mi’ke ta shige bedroom, Mommah ta bita da kallon mamaki.
Alhaji Baba ya saki ajiyar zuciya shi kansa yana cikin wani hali da bai san yarda zai warware cukurku’dewar al’amurannan ba, ya zubawa sadakin da Mommah ta ajiye idanu, a fili ya furta “Tir’kashi! Amma Dijah da zaki fahaimceni da kin bari anyi abubuwannan a hankali.” Da sauri ya kalleta ganin ta saka masa kuka “Don Allah kada ku goyi bayansa, alhali yayi abinda bai kamata a goyi bayannasa ba, sai yanzu da yaga matarsa ta kwara’be ita kuma wannan ya ga ta goge sannan zai lalla’bo yace yana sonta, ni na tabbatar son sha’awa yake mata Ammar ne yake mata zahirin so, please ko bayan raina Ammar na amince ta aura.” Daga Alhaji Baban har Hajiya Maman shiru suka yi sun ma rasa tudun dafawa.
Shatu kuwa tana shiga ‘daki ta sulale akan gado, tausayin Imran ne gaba ‘daya ya cika zuciyarta duk da ba tana nufin ta komawa aurensa bane, amma bata son Mommah ta cigaba da zafafa masa. Turowar ‘kofar da aka yi ne da ‘karfi ya sata ‘dagowa. Anty Nahna ta gani sam fuskarta ba rahma, ta ‘karaso a ‘dakin a zafafe tace “Mi’ke zaune Shatu.” A sanyaye ta mi’ke tana goge 'kwallar da ta kwanta mata cikin idonta.
“Kada kice min kukan rasa Imran kike? Ko kuma kukan mutuncinki da Mommah ta kare? Cab da kuwa kin bani kunya na zata da ke za’a zage a ‘kwaci martabarki da mutuncinki, shine kika zauna kina kuka? Ba dai zuciyarki har yanzu tana son mutumin da ya gallaza miki a rayuwa ba? Da nace kuwa zuciyarki ba tayi miki halacci ba da kuma na kira ki da wacce ta rako mata duniya. Ki bu’de kunnenki ki ji abinda zan gaya miki da kyau, a yanzu ne zaki nuna wa Imran kuskurensa, a yanzu ne zaki ‘dandana masa guba irin wacce ya cusa miki, ki shayar dashi mamaki ki nuna masa kema mace ce Hamsha’kiya yanzu da ko ya sameki zai san mutuncinki da darajarki ba zai ce ya sameki a ‘bagas ba. ki nuna masa kin cika kin ri’ka kin tumbasa samun ki sai wanda ya shiryi. A zahirance ki nuna masa Ammar ne za’binki ko da a ba’dinance ba hakan bane. Kiyi gogayya da shi ki jashi a ‘kasa kada kuma ki sake ki bujirewa umarnin Mommah duk da ‘ko’karin kare martabarki da tayi, kiyi watsi da Imran ki kama Ammar shine ya dace dake. Kin ji mai na gaya Miki?” Shatu Ta ‘daga kai tana jin duk abinda Anty Nahna ta gaya mata shine gaskiya dole ta yakice soyayyar Imran ta yi wulli da ita matu’kar tana son siyawa kanta mutunci. Ta rungume Antyn ta Nahna tana sakin hawaye Na zallar samun nutsuwa.
Ammar kuwa tun da ya shige ‘daki ya kulle kansa ya da’de zaune dafe da kansa, yana jin zuciyarsa na suya, ina ma zai iya da ya sahalewa Imran matarsa, amma ina zuciyarsa ta kasa yi masa lamini soyayyar Shatu sake gauraye duk ilahirin sassan jikin sa take, baya jin zai iya rayuwa idan ba Shatu a tare dashi.
————
Lamarin Imran kuwa babu da’din ji, domin ya rasa mafita ya kuma rasa waye ya turo wannan sa’kon, zuciyarsa sunan Shaheedah ta ke Ta nana ta masa, hakan yasa a zafafe ya mi’ke. Dole ne ya nemo Shaheedah duk da sun koma barci amma asubanci zaiyi yaje ya tambayeta dalilin da yasa ta aikata haka.
Jirin da yaji yana ‘dibansa ne yasa ya tuna rabonsa da abinci tun tea ‘din da ya sha da safe, don haka ya mi’ke a hankali cike da ‘karfin hali ya nufi hanyar fita daga bedroom ‘din.
A kitchen ‘din take a tsaye tana ‘ko’karin dafawa Akram noodles da ya dameta da kuka. Jikinta sanye da Hijabin da tayi sallah da shi, fuskarta fayau ko powder babu, hakan ya saka idanunta fita dar dasu, dama ita tafi kyau ba makeup.
Jin ‘kamshin turarensa ya tabbatar mata shine ya shigo kitchen ‘din, don haka ta aro fuskar jarumta ta saka akan fuskarta, domin kuwa kicin-kicin tayi da fuska, tana zubawa Akram da ya isa wajensa harara tare da jawo shi da ‘karfi “Don gidanku matsa daga jikinsa saninka ma yayi da kake ‘ko’karin li’ke masa shashashan yaro kawai.” Kuka Akram ya fara yi yana ‘ko’karin ‘kwace hannunsa daga jikinta. Shi kuwa Imran sak yayi yana kallonta, yana son yi mata masifa amma yana shakkar kada ya sake cusa tsanarsa a zuciyarta. “Kiyi ha’kuri sabida ya zo wajena kika masa wannan fa’dan?” Wani tsaki taja kafin ta harareshi tace “Anyi masa ‘din ko kai ka haifa min shi?” Jikinta ya matsa sosai tamkar za su ha’de yana jifanta da wani irin kallo mai narka zuciya, cikin wata iriyar murya da tasa gaba ‘daya tsigar jikinta tashi yace “Idan ba ni na haifa miki shi ba amma ni na yi miki cikinsa, kuma cikin son ran ki da shau’ki.” Ta ja baya ha’de da ‘bata rai tace “Sai me don kai ka yi min cikinsa? Ai abu ne mai sau’ki kuma ko yanzu na yi aure wani ma zai min ciki na haihu.” Bai san lokacin da ya dam’ko ta ba cikin ‘bacin rai yana kallon cikin ‘kwayar idon ta da tayi saurin