Showing 39001 words to 42000 words out of 117786 words

Chapter 14 - Me Zanyi Da Ita Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

461

Amarya Shaheedah ta fito a cikin shigar laffaya sai zabga ‘kamshi take kai kace anyi ‘barin turare a jikinta,sanye take cikin pink d’in laffaya, ta dai rufe kanta amma idonta ko alamar kuka babu,
Burinta a yau ya cika na auran Imran, kamar yarda ta dad’e tana mafarki,yau dai ga ta a matsayin matarsa,don haka take jin kamar taje ta kai kanta ganin su masu kaiwar basa sauri sun tsaya sai zagaye suke da ita wajen ‘yan uwa.


Gida yayi kyau ya sha kayan alfarma na gani a fad’a,sai zabga ‘kamshi yake. Amarya tun daga haraba take sakin murmushi cikin laffaya.

Kowa ya yaba sannan masu kawota suka tattara suka tafi, ‘yan mata zuciyarsu cike da burin samun irin gidan ko makwafinsa.



Ango dai tunda abokansa suka fara siyan baki yake sakin tsaki,burinsa suyi su tattara su tafi,tunda ya dad’e yana jiran wannan ranar a matsayinsa na kamilin saurayi.

Abubuwan da suka faru a daren abubuwane da baza su manta su ba a kaf tarihin rayuwarsu,ango dai ya riski matarsa sabuwa dal a leda sai muce Allah ya kawo ‘kazantar d’aki.


*************


Tsaf tayi shirin makarantar ta ta fito, tana isa parlour taji ‘kamshin turarensa a parlourn, tayi mamakin ganinsa a yau d’in don rabonsa da zuwa gidan kwana hudu kenan cif tun bayan da amaryarsa ta tare. Yayi kyau sosai cikin black blue d’in yard d’inkinsa na kullum ne a jikinsa,gajeriyar riga mai gajeren hannu kan sa ba hula, hakan kuma sai yayi masa kyau. Har zata wuce da sauri Dada ta ‘kwalo mata kira “zo nan ‘yar nema baki ga mijin ki bane?” Bakin ta ta turo murya a cunkushe tace “Dada na makara fa.” Tsaki Dada ta ja cikin masifa tace “Allah dai wadaran naka ya lalace uwarki ce ta d’aure miki wani abu can, an ce wani sai kin yi tsinanniyar boko matar da za’a kai d’akin miji jibi ace tana yawo a gantale don wauta ko ‘yan magungunan gyara na daka ban ga ana baki ba,balle aje ga batun gyaran jiki,sai anje an cuce shi an kai masa ke salam kamar kazar da ba maggi ba gishiri,ko da yake ina ruwa na ke da uwarki ku zaku yi da na sani,ki wuce ki koma ciki yau ba zuwa wata makarnta idan kika tare idan ya zama dole kya je.” ‘Kwalla ce ta kawo idon ta,murya a cunkushe tace “Test ce fa dani zaki ce wani ba zan je school ba.”Mommah ran ta a ‘bace tace “Dada ki bar ta taje idan yaso goben sai ta ha’kura insha Allah ai kema dai zaki so ace ‘yar jikar ki ta zama likita.” Dada ta gyara zama cikin masifa tace”To kuwa idan har zata je makarantar nan sai dai wannan ‘katon banzan ya kaita ba Ammaru ba da kullum za’a dinga tashin sa da sassafe kai ta makaranta don an gan shi salihin bawa.” Ko kallon in da Dada take bai yi ba,ya mi’ke yana yiwa Shatu kallon sama da ‘kasa a
Zuciyarsa yace “Ai dama Ammar d’in aka aura wa ita.” “Ki nemi mai kai ki school ba abinda nazo yi ba kenan.” Cikin ‘bacin rai Mommah tace “Wuce kije ya kai ki idan yaso ya zubar da ke a titi,saboda ka ga na kyale ka? Kwanan ka nawa rabon ka da gidannan sai kace a kanka aka fara aure to kai zaka kai ta daga yau kuma kai zaka cigaba da kaita, wuce ku tafi Shatu kada kiyi late ai ha’kkin ta akan ka yake.” Dada tace “‘kwarai kuwa.” A ran sa yace yau zaku ga ha’k’ki wallahi sai nayi mata abinda ba zata sake shiga mota ta ba.


Tafiya suka yi sosai kafin su isa d’an ‘karamin building d’in mai tsananin kyau a ido,ginin kuma bungalow ne,gurin sam ba hayaniya. Da sauri Shatu ta kalleshi murya a cunkushe da tayi al’kawarin ba zata yi magana ba tunda taga ba hanyar makaranta yayi ba, ta san wata muguntar ya shirya mata saboda ance ya kaita makaranta.”please Yaya Imran ka mayar dani gida idan ma ba zaka kai ni school d’in ba.” Ko kallon inda take bai yi ba, ya zare seat belt d’insa yace “wuce muje malam ba dai sunce ha’k’kinki yana kai na ba,to yau zan sauke babban ha’k’kin kafin ‘kananan su biyo baya.”
Jikin Shatu ne ya d’au rawa don tun tana ‘kauyensu ta san menene aure tunda da friends d’inta da yawa da aka yiwa Aure. Ta kalleshi da sauri ta ga ya had’e rai, tuni idonta ya kawo ‘kwalla ta san matan. ‘Kauyensu suna bata labarin wahalar da suke sha har ruwan zafi ake saka su.”Don Allah Ya Imran kayi ha’kur.” Ba tare da ya kalleta ba yace “fita muje malama you are wasting my time,ai kin girma zaki iya d’aukan nauyin auratayya zaki kuma iya d’aukan duk wani abu da matan aure suke iya d’auka,tunda Babar ki ta aurar dake,ko baki san aure ba?” Da sauri ta girgiza kai “Ban sani ba Yaya Imran.” “To me yasa kika tsorata har da kuka? Kada kiyi min ‘karya fad’a min gaskiya kin san aure ne?wallahi kika yi min ‘karya kika bari na gane ‘karya kike min a yau zamu goge raini tsakanin ni dake don ba zan bar mana wajenan ba sai na mayar dake cikakkiyar mace mai amsa sunan matar aure,gaya min nace.” Da sauri ta fara wasa da hannunta jikin ta yayi sanyi sosai kamar ba Shatu Danger ba, ta sunkuyar da kai sosai hawaye sai zirara yake.
Shi kuwa dariya ce take son kama shi ganin tun ba aje ko ina ba ta razana alamar ta san duk abinda ake a aure,ya matse dariyar kafin yace “oya tell me ina jin ki mai ake a Aure?” “Iskanci” shatu ta fad’a murya na rawa sai kuma ta fashe da kuka “Don Allah kada kayi min kaji Yaya Imran wallahi Dijen gidan maigari tace da mijin ta yayi mata shine ta samu ciki.”
Still idon ta a ‘kasa take magana ta ma kasa kallonsa.shi kuwa dariya ce kawai take cin sa amma ya kasa yi,sai murmushi yake yana kallon yarda duk ta gigice. “Kin san meye iskancin Kenan?” Da sauri ta girgiza kai “Ban sani ba wallahi amma dai tace min cire kaya....” “yi min shiru fita muje ashe ma kin san komai yau kuwa zaki san menene iskanci,shashasha kuma Idan baka da aure idan kayi shine ake ce masa iskanci idan kuwa kana da aure raya sunna ake ce masa,Fita muje nace.” Ganin ba alamar wasa a fuskar sa yasa ta fita ‘kafarta na rawa al’amarin ya gigita ta sai kace ba Shatun Mommah danger ba. ‘kafar ta ta kasa d’aukanta a zafafe yace “ko sai nazo mun fara daga nan.” Da sauri tabi bayansa hankalinta a tashe,ta san yau kashin ta ya gama Yawo.”



Yana knocking Gate man ya bud’e gidan da sauri yana kai masa gaisuwa.gidansa ne da ya gina yake saukar guest d’insa turawa idan sun zo harkar business Nigeria. Ya tsaru iya tsaruwa yanayinsa tsarin turawa. Yayi kyau sosai parlor ne guda d’aya babba sai kitchen da toilet a parlourn sai 2 bedrooms.
Raku’bewa tayi a one seater tana chewing hand finger d’inta a tsorace take sosai tana kallo ya shiga bedroom ya fito daga shi sai singlet da gajeran wando da sauri ta runtse idon ta ganin ya nufo ta ta mi’ke a guje tayi hanyar bedroom.murmushi yayi yace “shikkenan kin hutar dani kin
Kai kan ki.” Tana shiga ta rufo ‘kofar sai dai abin takaici babu key a Jiki. Tana kallo ya shigo fuskarsa a had’e, ta dinga ja da baya tana ro'konsa "please Ya Imran!" "wuce toilet kiyi brush sosai malama." ta bud'e toilet d'in shima abin takaici babu key a jiki. Shatu ta zaro ido a hankali tace "Na shiga uku." Idanunta duk sun firgice, tana ji ya turo ‘kofar ya shigo idanun sa a kanta “Ba zaki yi sauri ba?” “Ni fa nayi brush d’ina a gida.” “Na sani ai wannan na musamman ne ba na son naje kissing d’inki naji bakinki ba daidai ba.” Ai da sauri ta zube a ‘kasa hawaye sha’be-sha’be.”Don daraja da girman iyayenkaw Ya Imran kayi ha’kuri.” “Idan na ha’kura za kiyi min abinda nake so?” Da sauri ta d’aga kai,murmushi yayi “okey taso ki fito mu d’aura al’kawari.” Da sauri ta mi’ke ta fito tana sakin ajiyar zuciya, sai kuma ta kalleshi tayi saurin d’auke kai “please amma ka fara mayar da kayan ka tukun.” Yayi mata wani kallo “Meye a jikin nawa? Ko naked kika ganni?” Da sauri ta girgiza kai “To kina feelinga sha’awa ta ne? In d’auke miki ita yanzun nan?” Da sauri nan ma ta girgiza kai ba tare da ta san menene ma sha’awar ba.
Ya ta’be baki “Oya zauna maza na fad’a miki sharad’ina.” Ta kuwa zauna ta ra’be a gefe kamar ace kyat ta gudu.”Zan kyale ki idan kin amince da sharad’ina,kije gida ki sawa Mommah rigima kice mata ba kya son auren idan kuma ta ‘ki kice mata ba kya son ki tare yanzu,kiyi ta kuka idan ba haka ba wallahi kika bari aka kawo ki gida na sai kin gaya wa aya za’kin ta zuwa zan miki abinda ake yiwa masu aure,kina ji na ko?” Ta d’aga kai da sauri. “Yauwa idan kika yi haka kin zama good girl kuma zaki yi karatu sosai,idan kuwa kika ‘ki ana kai ki zan miki ciki ki haihu kuma ba karatu kina jina?” Da sauri ta d’aga kai, yayi tsaki “Ba kai zaki d’aga min ba kice na amince da sharad’inka Ya Imran.” Da sauri tace “Na amince da sharad’inka Ya Imran.” Ya gyad’a kai yana mi’kewa had’e fad’in “Good Girl.”


‘Daya bedroom d’in ya shige yayi kwanciyrsa, don ba zai mayar da ita yanzu ba sai ya kad’a ‘yan hanjin Mommah tukunna. Murmushi yayi a zuciyarsa yana tunanin halin da Mommah zata shiga.

Mommah lokacin d’auko ta yana yi ta tura driver, sai dai me? Driver ya kira ta yace ai ance shatu ba ta zo makaranta ba.Mommah bata san san da ta zauna da’bas a kujera ‘kirjin ta yana bugu bata so ace hasashenta ya zama gaskiya ace Imran yaje ya aikatawa Shatu wani abun da kan ta ba zai iya d’auka ba. wayarsa ta dinga kira,kusan missed call biyar kafin ya d’aga murya a dashe tamkar yana cikin wani hali yace “Hello Mommah.” Bata san san da ta ‘kunduma zagi ba.”Gidan uban wa ka kai ta?” Dariya ta so kubce masa yace “Ba ko ina fa Mommah gamu nan muna tare.” Mommah ta saki salati “kuna tare a gidan uban wa?” “Haba Mommah ki kwantar da hankalinki ni fa mijinta ne ku da kanku ku ka fad’a to me ye na........” a zafafe ta katseshi “Wallahi Imran ka jini da kyau idan ka sake ka bud’ewa yarinyar nan sirrin da yake cikin aure zaka gamu dani nawa Shatun take?” Cikin dakiya yace “Amma ku kayi mata aure Mommah ku fa kuka ce duk hakkinta a wuya na yake..” “Uban ka nace Imran, kaci uban ka ka dawo min da yarinyar nan yanzunnan wallahi ko ranka ya ‘baci.” Ta kashe wayar tana jan salati “Na shige su nima wa ya aike ni?”

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-24


Elegant Online Writers..



Bai Tashi mayar da ita gida ba sai da yaga 3:00pm sharp, lokacin yunwa ta ci ta cinyeta. Ranta duk ya gama ‘baci da wannan mulkin mallakar,tana kallo ya fito fuskar sa fresh da alama wanka yayi ya fito. Ita d’in ma watsa mata kallo yayi “Tashi Malama kije kiyi wanka ban son ‘kazanta ba zaki shiga min mota ba sai kin yi wanka tun safe har 3:00pm.” Marauraice fuska tayi ,idanunta yana shirin kawo ‘kwalla tace “Don Allah Ya Imran ka bari idan naje gida zan yi.” Ya girgiza kai “Ba zan iya ba kusan 7 hours rabonki da wanka sannnan ki shigar min mota yi sauri I have something to do kina wasting time d’ina.” Mi’kewa tayi bisa tilas ta shige cikin d’akin don yin wankan.



Suna parking ya watso mata kallo “kada ki manta da al’kawarinmu,idan kuma kin ‘ki ki shirya kar’bar ha’k’kin ki na aure,don in dai na gan ki a gidana na san kin za’bi zama cikakkiyar House wife.” Ta d’aga kan ta kawai,ta fice daga motar cikin azama. Imran ya bita da murmushin mugunta, ko bakomai ya san yau ya kad’ar da hanjin Mommah.


Tana shiga gida ta tarar da su Hajja a main parlour na gidan, bisa tilas ta dur’kusa ta gaishesu, ko bakomai dole ne ta bi umarnin Mommah, sai dai ko kallo bata ishe su ba, har da masu harara da zabga tsaki, tana ji Hameedah tace “shegiya mai siffar jinnu.” Girgiza kai tayi a zuciyarta tace zamu had’u wallahi kafin ki tafi.


Ba kowa a parlourn Mommah, hakan yasa tayi saurin shigewa bedroom d’inta, sai dai tuni Mommah taji motsin ‘kofarta hakan yasa ta fito da sauri har tana yi kamar zata fad’i.
A bakin Gado ta tarar da shatu tana zaune ta zabga uban tagumi,idanunta ya d’an kad’a alamar yunwa da barci ne a cikinsu,sai dai ita Mommah tuni tayi wa hakan wata fassarar ta daban.
Da sauri ta dafa ta tana zama a gefenta tace “Shatu hope ba abinda yayi miki? Ko ya miki wani abin?” Girgiza kai tayi hawaye na zuba a idon ta, ta rungume Mommah,hankalin Mommah idan yayi dubu ya tashi,ta
dinga salati tana tafa hannu “Tashi mu gani muje toilet.” Shatu ta ri’ke hannunta tana girgiza kai “Mommah bakomai ni dai don Allah bana son auren yanzu bana son na tare please Mommah.” Kuka take sosai hankalin Mommah ya tashi,saboda bata ta’ba ganin shatu a wannan halin ba.

“Kin tabbatar ba abinda yayi miki?” Ta d’aga kai kawai,tana cigaba da share hawayen fuskarta.Mommah ta girgiza kai “To me yasa ba kya son ki tare?” Kuka ta sake saki kafin tace “Mommah bana son na haihu yanzu,ya ce kuma idan na bari na tare yanzu sai ya bud’e min duk da wani sirri na aure. Mommah ta saka salati kafin tace “Amma Imran ya iya tsiya, bai dai yi miki komai ba bayan hakan ko?” Shatu ta d’aga kai “Shikkenan ki bar ni dashi ai ba ke kad’ai zaki tare ba da Dada zan had’a ku,kuma d’aki d’aya zaku dinga kwana, ki rabu dashi tsokanarki yake ba abinda zai iya yi miki. Yanzu ki tashi kije ki ci abinci ko kin ci?” Tana share hawayenta tace “Ban ci ba tun breakfast” Momma ta mi’ke tana cewa “okey maza kije ki ci abinci,nima kasuwa zan je yanzu zan dawo.” Daga haka ta fice ita kuwa Shatu kwanciya tayi idanunta a lumshe tana tariyo moment d’in da ya gaba ta. Gaba d’aya jikinta ‘kamshin turarensa yake duk da tayi wanka. ‘kamshin da take masifar so,don haka ta kasa cire kayan.




Babu wani gyaran jiki da aka yi mata,duk da Dada tana ta maganar gyaran jikin, Mommah kuwa tace ba yanzu ba tunda yanzu ba zaman Aure za taje yi ba. Ita kuwa Dada da kanta ta bawa mai gadi kud’i yaje kasuwa ya siyo mata kayan magunguna tace suna tarewa zata fara banka mata.
Masifa take tana ‘karawa “Ni ban ga dalilin wannan tsiya ba ace wai Auren da aka yi ba yanzu miji zai tare da matarsa ba, to ba dani za’a yi wannan shirmen ba.”




Imran gani yayi kawai ana ta shiga da kaya na gani na fad’a, bugun turkey, ‘bangaren Amarya ya fara d’aukan harami kamar a ‘kasashen ‘ketare. Ransa ya gama ‘baci ya tabbatar shatu bata ji jan kunnen da yayi mata ba kenan. ‘Karshe don takaici ficewa yayi ya bar gidan zuciyarsa a hassale, musammman ganin yarda shaheedah ta hassala,sai kuka take masa.




Kashegarin Ranar Mommah ta shirya walima gagaruma, a kuma ranar aka yi kamun Amarya Shatu. An ci an sha an kuma yi wa’azi sannan Mommah tasa aka yi saukar Al’kur’ani, da niyyar Allah ya basu zaman lafiya ya sanya albarka a auren. Ango dai ko gidan bai zo ba.
Mutane da dama walimar ta burgesu, har suka gaza shiru suke fad’an dama haka aka dawo ake yi a kowane aure, aka rage bidi’a ko don samun albarka a Aure.

Tsirarun mutane ne suke fad’ar haka, yayinda majority abin bai burgesu ba, musamman dangin Dahda da suke ta’be baki suke fad’in Iyayi ne da son a sani, ta kuma nunawa mutane wai ita mai tsoron Allah ce. Bata ce komai ba duk da zancen yaje har kunnenta tace “Allah ne kad’ai ya san zuciyar bayin sa.” Don haka sam surutun jama’a baya damunta.


Rabuwar Mommah da Shatu, abu ne da girgiza zuciyarka in dai kana wajen, Shatu kuka take kamar ranta zai fita, musamman idan ta tuna al’kawarin Imran na aikata mata irin abinda aka yi wa ‘yar gidan maigari matu’kar bata saka Mommah ta janye auren ba,haka ne yake sake tunzura zuciyar Shatu take kuka kamar zata mutu.
Mommah ma kukan take, tana ji kamar ta saka Imran ya saki Shatu tausayinta yana sake tsirga mata.Ta rungumeta sosai a jikinta, tana rad’a mata kalamai masu dad’i, wanda duk uwa ta gari ya kamata ta gayawa d’iyarta,yayin sallamar Aure. Tabbas rabuwa da gida abu ne mai ciwo Shatu,sai dai fatan dacewa a gidan Aure.

Haka tana ji tana gani aka raba ta da jikin Mommah, su Anty Nahna suka jata jikinsu.

Kamar yarda ake a al’adance dole sai an kai ka wajen dangin miji, itama Shatu haka aka dangana ta da na ta dangin mijin. Sai dai ba wanda yayi musu kar’ba ta mutunci musamman Hajja da tace ba zata kar’bi amana ba,haka nan cikin yaranta bata amince wani ya kar’ba ba. Ta ‘kara da cewa “Ai ita ‘yar gata ce sai a mi’ka ta gurin uwar mijinta kuma uwar ri’konta mai zai dame ta?” Ba wanda ya tanka su kamar yarda Hajiya Mama ta ro’kesu, kada suyi abinda za’a tafi dasu a baki.




——————————————-
Gefe guda kuwa Imran yana can zaune a part d’insa, yana kallon Shaheeda da tabi ta nad’e masa a jiki,tana kukan shagwa’ba, zuciyarsa har ta fara tunzira da rashin ha’kurinta.
A zafafe ya janye jikinsa cikin kaurara murya yace “Wai Shaheedah ya kike so nayi ne? For Goodness sake, nace miki nima ba a son raina aka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login