Showing 63001 words to 66000 words out of 117786 words
ba da ya bawa ‘dan uwanki mata wance, a wannan zamaninfa ba dama aga mace tana zama da mijinta lafiya sai ace ai ta mallakeshi ta asirceshi alhalin ba a san mizanin ha’kurinta akan shi mijin ba, ya kamata mutene su farka a daina jayayya da hukuncin ubangiji. Sannan kayi ha’kuri Manga an zo ga’bar da ya kamata ‘yan uwanka su san Dijah tana da gata, sannan karamci da kawaici na mahaifiyarta yasa nake ‘dauke kai nake ha’kura kamar yarda taso idan banda haka da tuni na nunawa danginka ina son yarinyata, don duk cikin ‘ya’yana ba na biyunta a biyayya, zan ‘dauke Dijah zuwa gida na har sai ta samu lafiya sannan kuma sai maza daga zuri’arku sun zo an zauna, don bana fata na wayi gari ace zuciyar Dijah ta buga dalilin kyara da tsangwamar danginka. Ba kuma don komai zanyi haka ba sai don kanku kai da Dijan su sakar muku mara su barku ku sha’kata ina dalili shekara da shekaru ayi tayin abu kamar cin ‘kwan makauniya.” Manga shiru yayi ba don zuciyarsa ta amince a tafi masa da Dijah ba sai don
Baya son jayayya da surikinsa dattijon arziki, da duk abinda ake bai ta’ba magana ba sai yanzu da tura ta kai bango. Alhaji Baba ya dafa shi yana murmushi yace “kada ka damu ba rabaka zanyi da Dijah ba, asali ma sashe guda zan baku a gidana kafin mu ga abinda hali zaiyi. Sannan kuma ka gayawa su Imran bata da lafiya?” Dahda ya girgiza kai, Alhaji Baba yace “Hakan bai dace ba kayi ‘ko’karin sanar dasu su zo su dubata, ko bakomai uwa-uwa ce, kuma ita kanta zata so ta gansu yanzu. Allah yayi muku albarka gaba ‘daya.” Ameen manga yace, hankalinsa ko yanzu ya kwanta jin sashe guda zai basu da Dijah.
Basu bar gurin ba sai da kuwa Dahda ya kira Ammar ya sanar dashi, cikin tashin hankali Ammar yace yana nan tafe ko zuwa dare idan ya samu jirgi. Ya kira Imran ya gaya masa Imran sak yayi zuciyarsa Na bugu yace “Please don’t hide the truth ka gaya min idan Mommah mutuwa Tayi? Na shiga uku ya zanyi...” cikin tsawa Dahda yace “idan mutuwar ma tayi kai kana da asara ne ba dai ka za’bi farincikin wasu ba fiye da Na mahaifiyarka. To Na baka 24hours duk abinda kake kazo ka ganta ba ta da lafiya kuma umarni Na Baka.” Daga haka ya yanke kiran ya bar Imran da waya a hannu hawaye Na bin ‘kuncinsa zuciyarsa Na wani irin bugu da ‘karfin gaske tamkar Zara bud’e ‘kirjin ta fito. Da azama ya mi’ke yana kallon Shaheedah da take kwance a gadon asibiti ya ‘dau car key ‘dinsa tare da furta “Nigeria is calling......! Shaheeda ta waro ido tana kallonsa.
(Ku fito mu tattauna, shin me yake kawo ‘kiyayyar dangin miji da matar ‘dan uwansu? Me yake kawo rashin jituwa tsakanin uwar miji da surikarta? Kowa dai ya san abubuwan da suke yawan faruwa kenan a duniyar mu ta yanzu. Mecece Mafita? Sannan laifin wanene?”)
Jikar Nashe ‘yar mutan makwarari mai ta’kama da ikon Rabbi. Sai naji daga gareku!
Me Zanyi Da ita?
35
Cikin ‘bacin rai ta kamo hannunsa, idanunta cikin nasa kafin ta furta “Haba Habibi yanzu Nigeria zaka tafi? Ka bari na samu sau’ki mana sai mu tafi tare, wai shin mai ma ake yi a Nigerian?” Zame hannunsa yayi kafin yace “Zuwa ta Nigeria ba shi zai hanaki samun lafiya ba, Mommah ce ba lafiya kuma Dahda yayi min umarnin lallai na tafi. Ko da ma baiyi min ba ya zama tilas naje na ga jikin Mommah.” Har ya kai ‘kofa ya jiyo yace “zan sanar da grace tazo ta zauna dake.” Yana fita ta saki ajiyar zuciya, ‘kirjinta yana matu’kar suya da saboda tsananin ‘bacin rai. Da sauri ta lalibi numberr Anty Amarya ta shiga danna mata kira ba ji ba gani.
‘Daga wayar ke da wuya, Shaheeeda ta sa mata kuka “Ki taimakeni Anty, wallahi kamar komai ya warware ina hango tsanata a idanun Imran, duk da bai furta ba ina jin tsoro Anty. Yanzu ma fa Nigeria zai taho wai Mommah ba lafiya.” Anty ya ri’ke kanta, ga shi time ‘din tana cikin dangin su, ana ta sha’anin biki ba damar tayi wani abin. “Kiyi ha’kuri, zan san abin yi, ba dai Nigeria zai zo ba Allah ya kawo shi lafiya.” Shaheedah ta kashe wayar ranta a ‘bace don ba haka Ta so ta ji ba, so tayi Antyn ta san yarda aka yi ta hanashi zuwa Nigerian gaba ‘daya.
—————-
Bayan fitar Dahda daga hospital ‘din direct Family House ‘dinsu ya tafi ransa a ‘bace matu’ka, dama rashin mai zama da Mommah ya hana shi zuwa yayi musu maganar.
Tun daga corridor ‘din sashen Hajiya yake jiyo ihunsu da shewarsu, yana jiyo Anty Amarya tana cewa “Ai cewa yayi bata da lafiya, shi yasa bai zo ba tun jiya.”
Hameedah tayi zumbur tace “Shegiya ina ma mutuwa tayi muka huta da gayyar tsiya.” Hajja tace “Wallahi kuwa, wannan masifa har ina? Ni na rasa yarda zanyi na datse wannan auren, amma kam na tsani yarinyar nan.” Zuciyarsa ce ta sake dugunzuma kamar mai? A zafafe ya danna ‘kofar ‘dakin da ‘karfin gaske,da yasa su saurin ‘dagowa suna kallonsa. Gaba ‘daya suka firgita har Hajja, musamman ganin yarda idanunsa suka ka’da su kayi jazur, ya kalli Zainab sai kuma ya mayar da kallonsa kan ‘yan uwansa mata, “Duk abinda kuke fa’da ina jinku, a yau kuma na sake tabbatar da al’amarin tsanarku da Dijah mai girma ne, ba tare da sanin wani laifin Dijah tayi muku ba, laifinta ‘daya da ta aureni take tattalina da nuna min soyayya, ku kuma abinda ba kwa so kenan kun fi son ku ganni da macen da zata dinga ‘daga min hankali, don haka ayau ba sai gobe ba zan tabbatar muku mahaifiyata kawai nake shakka, kuma ita ka’daice wacce ba zan iya rabuwa da ita ba, kun saka mata a gaba gata can a gadon asibiti zuciya ta cunkushe da ‘bacin rai, ku ko kunyar yaranta ba kwa ji? To daga yau na yanke ala’kata daku matu’kar ba zaku zauna da matata ‘kalau ba, ke kuma zainab kije na sakeki saki ‘daya.” Gaba ‘daya wajen ihu aka saka da salati, Zainab kuwa cikin tashin hankali take kallon Hajja tace.” Hajja please kice wani abu mana, kina ji yace ya sake ni.” Cikin takaici Hajja tace “Ince mai Zainab? Ina da mutunci ne a idonsa? Kina jin irin maganganun da yake fa’da a gaba na saboda baya gani na da mutunci, zuciyar Manga gaba ‘daya an canja ta, ni kuma yarda ya rabu da ‘yan uwansa akan Dijah ya kuma sake ki, ina tabbatar masa nima na zare hannuna daga lamarinsa, yaje dangin Dijah su zame masa uwa da uba. Na sallama musu shi wallahi.” Hawaye ne taf a Idonta, don lamarin Manga ya kere tunaninta. Cikin wata irin karayar zuciya Manga ya zube idanunsa cikin na Hajja ji yake tamkar yasa hannu aka yayi ta ihu, ba tare da yayi magana ba ya juya ya fice, da sauri tamkar tashin iska.
———————
A ranar aka sallami Mommah, cikin hukuncin ubangiji jikinnata da sau’ki sosai. Fargabar ta ‘daya komawa Abuja da aka ce zata yi bata so ta koma saboda bata son a san Shatunta na da juna biyu.
A ranar kuwa suka bi Flight zuwa Abuja, bayan Hajja ta sanar da ita ba matsala, suna da c.c.t.v camera yanzu a gidan, suna ganin mai shiga da fita a gidan duk wanda yazo zata saka Shatun Ta shige bedroom. Hakanne ya kwantar da hankalin Mommah, ita ma kam wannan ciwon ya razana ta kuma yanzu tana bu’katar a kar’bar mata ha’kkinta bata son ta rasa rayuwarta a garin kawaicin ta na banza.
Tun safe Shatu ta shiga gyaran gidan, bayan Hajiya Mama ta sanar da ita da Mommah za’a taho, tsananin murna yasa ta fara shiryawa Mommahn girkuna masu da’di burinta Mommahnta ta san a yanzu itama ta fara zama ‘kwararriya a ‘bangaren Girki-Girke na mu na gargajiya da na ‘kasashen ‘ketare. Mandi Rice tayi mata, sai chines Rice aka kuma Gasa mata kaji Gashin larabawan Oman, sannan aka yi mata Gizdodo, da kunun aya da Dinger drink sun kuwa yi da’di sosai, ‘bangaren snacks kuwa had’addiyar pizza tayi mata da fish roll don ta san tana matu’kar sonsu sosai. Ta gyare mata ‘daki tsaf, inda ta saba sauka sam Shatu yau ko nauyin cikinta bata ji burinta ta kyautatawa Mommahnta.
——————————
‘Karfe 6:00 jirginsu yayi landing, a Nnamdi azikwe International airport, kamar ha’din baki dai-dai lokacin da jirgin su Imran yayi landing kenan, tsakaninsu mintuna ‘kalilan ne. Sai dai basu had’u ba don su Mommah sun riga shi fita saboda nasu jirgin na gida ne.
Wayar Dahda ya shiga kira don ya gaya masa isowarsa Abuja da safe kuma zai biyo jirgin Kano. Dahdan ya sanar dashi Suna Abuja suma a yanzu hakan gidan su Mommahn. Gaban Imran ya fa’di, addu’a ya dinga yi Allah kada ya tabbatar da Hasashensa ace Mommah mutuwa tayi, idan banda haka mai zai dawo da ita Abuja.
Gwiwoyinsa a salu’be ya samu taxi don tafiya gidansu Mommahn da yake unguwar Gwarinfa. Zuciyarsa cike da fargaba.
—————
Tunda su Mommah suka isa take bin Shatu da kallo, ganin yarda take ta hidima da ita ko nauyin jikinta bata ji, ga cikin yayi mata wani turtsetse, sai jansa take yi, kuma Shatun tayi duhu ka’dan ta kuma kumbura ka’dan. Sai da ta gaji da zirga-zirgar sannan ta zauna a hankali tana furta wash. Mommah ta jata jikinta tana matsa mata yatsun hannunta, murya a ‘kasa alamar ta marasa lafiya tace “Shatu haka kika canja? Mai Hajiya Mama take baki? Naga cikin yayi girma sosai kamar ya wuce watanninsa.” Murmushi Shatu tayi tana duban Hajiya Mama da take cewa “Yo wannan uban ci da Shatun taki take yi ai dole kiga Haka, ban da likita yace is better ayi mata aiki ai da ta gane kurenta wajen haihuwa yarinya kullum hannu a Kwano.” Basirah da take gefe ta tuntsire da dariya, Shatu ta hurgeta da pillow tana ‘dora kan ta a cinyar Mommah tace “Mommah kin ganta ko? Zata fara zolaya ta.” Mommah ta harari Basirah tace “Allah ya ha’daku zaku fara ko? To ki bari ta haihu sai ku cigaba don yanzu ba ita ka’dai bace.” Kamar ance Hajiya Mama ta ‘daga kanta ta hango Imran yana shigowa ta jikin t.v ‘din dake hasko camerar gidan. Da sauri tace Shatu ta shige ‘dakinta don basa son Imran ya ganta.
Ba’a fi mintuna biyar ba kuwa suka ji knocking ‘dinsa a bakin parlourn. Basirah ce ta bu’de masa ‘kofar, ‘kamshin turarensa tuni ta baza parlourn, jikinsa a sanyaye hannunsa janye da ‘Yar ‘karamar trolley da ba zata gaza ‘daukan kayan da suka fi 2set ba. idanunsa ya sauka cikin na Mommah, ya saki wata ‘kakkarfar ajiyar zuciya, ‘kirjinsa ya samu salama don bai ta’ba zaton zai zo ya risketa da rai ba, ya ‘dauka gawarta zaiyi arba da ita kamar yarda yake ta hasashe a cikin jirgi. Mommah idanunsa a cikin nata, duk da tana fushi dashi tayi farin cikin ganinsa cikin ‘koshin lafiya ta tabbatar yana cikin kwanciyar hankali tunda gashi har ‘yar ‘kiba yayi, ya kuma ‘kara haske akan nasa Na da duk da haskennasa disashshen haske ne, ba mai irin fau ‘dinnan bane.
Hawaye ya fara ‘kokarin kwaranyo masa a idonsa, da sassarfa ya ‘karasa wajen su ya dur’kushe a gabanta cikin wani yanayi ya dam’ki hannayenta yasa fuskarsa a ciki, sai a lokacin ya samu sukunin kwararrar da hawayensa, wanda yake nuni da zallar farin cikinsa Na riskar Mommah cikin ‘koshin lafiya. Hannayenta kawai akan bayansa ba tare da furta komai ba. zuciyarta a cunkushe tana tunano mata girman laififfukan da ya aikata mata musamman sakin Shatu da yafi tsaya mata a rai. Hajiya Mama sa’ke tayi tana kallonsu zuciyarta cike da tausayinsu duka tana addu’ar Allah ubangiji ya daidaita lamarinsu ya kawar da dukkan lamarin da yake lullu’be.
Kamar ‘kiftawar ido suka ga Mommah ta mi’ke a zafafe ta shige ‘daki ta kullo ha’de da murza key, sai sannan kukan yazo mata duk ‘kokarin da tayi Na danneshi. Imran da sauri ya bi bayanta sai dai kafin isarsa ya tarar ta datse da key. Jikinsa a salu’be ya dawo gaban Hajiya Mama ya zauna idanunusa kawai ya ke aikin murzawa. Yana duban Hajiya Maman kafin ya saki wani huci da zallar tururi ya fito daga bakinsa, ya gaishe da Hajiya Maman. Ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa tace “Ai ta samu sau’ki sosai ma kuwa,kwana uku da suka shige tuni muka cire rai da ita, duk da Allah yace Latakna’du min rahmatillah.” Imran yace “Alhamdulillah,amma Hajiya Mama menene musabbabin ciwon?” “Musabbabin ciwo Imran ya wuceka? Kai da dangin mahaifinka da ka biyewa kuke ‘ko’karin kai mahaifiyarka ‘kasa, saboda baka san ciwon kanka ba, Idan ta mutu wallahi kune kuke da asara ba ruwan danginka, in Banda sakarci ya za’ayi ka saki Shatu kasan ‘yar uwarka ce kuma itace za’bin Ta, amma ka zubawa idonka toka ka saketa ka bamu mamaki wallahi, kuma Alhaji Baba ma yana nan yana jiranka.” Shiru Imran yayi yana jin tsanar Shatu tana sake hauhawa a zuciyarsa, sa’banin da yake turkey da kullum yake kwana da tunaninta har yayi Al’kawarin duk ran da yazo Nigeria zai saka a mayar da aurensu, amma yanzu duk wannan soyayyar da begen ya kau, gani yake duk itace musabbabin sake samun sa’bani tsakaninsa da mahaifiyarsa, ban da haka kafin zuwan ta ‘kalau suke zaune. Ransa a ‘bace ya mi’ke yayi hanyar waje bayan ya amshi key ‘din part ‘din Hisham a wajen Hajiya Mama.
Hajiya Mama kuwa binsa tayi da kallo zuciyarta Na sake girmama ‘kiyayyar da Imran yake yiwa Shatu da ko sunanta baya son a ambata, tabbas al’amarin sai ta tashi tsaye da addu’a don alamar sihiri maigirma a tare dashi.
Mi’kewa tayi ta isa bedroom ‘din Mommah bayan tasa Yaseerah ta kai masa abinci, duk da ta san bai ci zaiyi ba.
bugu ‘daya tayi tace da Mommah “Bu’de, nice nan Addarsu.” Da sauri Mommah ta bu’de Hajiya Mama ta mayar da ‘kofar ta rufe.
A gefen Gado ta zauna, Idanunta akan Mommah da yayi jazur dashi. “Sau nawa zan gaya miki ki daina wannan fushin akan Imran? Addu’a ta kamaceshi don na gano tabbas akwai sihiri a tare dashi.” Murmushi Mommah tayi tace “Mai kika gani Hajiya Mama? Kada ki sawa kanki wannan tunanin, ke fa kike cewa mu daina beleiving da asiri.” Hajiya Mama ta girgiza Kai “Tabbas da asiri a jikin Imran, saboda yau zancen Shatu kawai nayi masa amma kamar na sanar dashi ranar mutuwarsa, ban ta’ba yarda a zuciyata Imran Zai yiwa Shatu wannan ‘kiyayyar da ba gaira ba sabab ba.” Mommah ta saki murmushi” “Hajiya Mama baki san Imran bane, tun a farkon fari ya tsani Shatu shine ma dalilin da yasa na ha’dasu aure, amma ya nuna min ban isa ba saboda yana tunanin ya fi ‘karfin Shatu da tazo daga Daji yana yi mata kallon bata waye ba. don haka ki cirewa zuciyarki wannan tunanin, ni yanzu ko Shatun ma bana son ya ha’du da ita wallahi.” Hajiya Mam cewa tayi “Allah ya kyauta” ba tare da ta amince da maganar Addarsu ba.
———————————
Ran kawu sa’idu a ‘bace yake kallon Alhaji Babba yace “lamarin mutane ya zama abin tsoro, duk jan kunnen da nayi mata sai da aka sake kwantantawa shikkenan ka barni dasu Insha Allah Na san maganinsu.” Alhaji Babba yayi masa sallama suka rabu cikin farin ciki da fahimtar Juna.
——————-
Da safe Imran ya shiga gidan, Hajiya Mama na ganinsa ta fara addu’oi a cikin ranta, Mommah kuwa fuskarta ta ha’de tana godiya ga Allah da baiga Shatu ba. Ha’kuri ya shiga bata ta ta’be baki kafin tace “Bakomai ni mai kayi min? Aure ai a hannunka yake tun da ka riga ka saketa kuma ai shikkenan Allah yasa hakan shi yafi alheri.” Jikinsa a sanyaye ya mi’ke Hajiya Mama tace “Ina zaka? Ba zaka tsaya ka karya ba?” Lumshe idanunsa yayi yace a kawo min garden can zanje...” ya nufi garden ‘din da sassarfa, gaban Mommah ya fa’di sanin Shatu a can take lesson kafin tayi ‘ko’karin hanashi har ya Tura ‘kofar da zata sada shi da Garden ‘din........ Mommah ta ware ido ita kanta Hajiya Maman bata son had’uwar Shatu da Imran a yanzu sai dai kana taka Allah Na tasa, Zahiran kuma ta Allah ce Gaskiya.....
Me Zan yi da ita?
36
Kiran da Alhaji Baba yayi masa ne yasa sh jiyowa, hakan yasa shi fasa shiga garden ‘din. Alhaji Baba ya yafito shi da hannu alamar yazo. Hakan ya saka shi nufar kakannasa.
A parlourn sa ya zaunar dashi, yana dubansa zuciyarsa cike da begen jikannasa. “Ka shigo jiya bamu ha’du ba? Ko da yake ni na hana Hajiya taso ka, Na san baka samu isashsshen barci ba anyi tafiyar da ba shiri, ya iyalinna ka?”
“Suna lafiya” “Masha Allah” nan ya zaunar dashi suka karya, yana ta tambayarsa cigaban da ake samu a business ‘dinsa.
Mommah da Hajiya Mama suka saki ajiyar zuciya a kusan tare, ganin Imran bai shiga ba. Mommah tace “Alhamdulillah, ke basirah maza kije kice ta koma sitroom da karatun nan.” Basira ta mi’ke ta fita isar da sa’ko, ita kanta mamakin yarda taga Shatu da ciki take yi.
——————————
Cikin masifa Kawu Sa’idu ya kalli Hajja, sannan ya dubi Manga “Tunda ya sake ta ba mahalu’kin da ya isa yasa ya dawo da ita, ai ni tun farko ban san da wata manufa kika ha’dashi aure da zainabun ba da ba zan amince ba wallahi, kuma yafiya dole ki yafe masa matu’kar ba kina so nima na janye hannuna a kanki ba, ban ta’ba ganin shashanci da zubar da mutunci ba irin naki, amma an zo ‘karshe tun da gashi iyayenta sun ‘dauketa, to ina dalili yarinya da gatan ta da komai ku saka ta a gaba har ciwon zuciya na neman hallakata, magana ta ta ‘karshe kenan tsakani na dake ki bar Manga da Iyalinsa su huta, kafin ubangiji ya nuna miki Ishara, kuma ya zama dole ki