Showing 75001 words to 78000 words out of 117786 words
am going through amma insha Allah zanyi ta addu’a safe flight sai mun ha’du.” Jikin Hisham ne yayi sanyi yana jin kamar wani abu mai kama da tausayin Imran yana tsirga masa amma Ammar fa? Ya ri’ke kai Allah ya kiyaye samuwar tashin hankali a zuri’ar su.
Gefe ‘daya Imran da sauri ya isa ‘dakin Shaheedah, a gaban dressing mirror ya tarar da ita sai tsara kwalliya take tamkar zata shiga gasar sarauniyar kyau, sai dai maimakon ya ga kyan muninta ya gani saboda wasu ‘kasusuwa da suka bayyana a fuskarta, ya dai daure don tilas ya sakar mata murmushi “Kin yi kyau” ya furta a hankali wanda da Shaheeda da za ta tsaya ta kalleshi sosai zata tarar furucin iya bakinsa ne bai kai zuciyarsa ba, amma ina idanunta ya rufe wani farinciki ya baibayeta har bata san sanda ta taso da azama da rungumeshi ba hawayen farinciki na zurara a fuskarta “Nagode Habibi.” Tausayinta ne ya kama shi ya ‘dan bubbuga bayanta “Is Okey ki shirya maza zamu bi jirgin safe gobe, Dada is death.” Cikin tsananin farincikin zuwa Nigeria da bayyana a fuskarta ‘Baro-‘baro tace “Okey Habibi.” Ya tsaya sak yana kallonta ganin ko ka’dan mutuwar Dadan bata girgiza bata mamaki ya cika shi, sai kawai ya girgiza kai ya juya zai fita. Ji yayi da sauri tace “What should I cook for you?” Ransa a ‘bace yace “Nothing.” Jikinta ne yayi sanyi kuma ganin yarda yayin bai wani yi ‘dokin son kasancewa da ita ba balle yayi tunanin bata ha’k’kinta. Ta ta’be baki a zuciyarta tace “Mu je dai Nigeria ai matsalata ta kusa zuwa ‘Karshe sai ka zo kana bina, wallahi sai na mayar da kai abin kwatance mijin kafin tace ma ba tace ba.” ta tuge hular gashin da tasa ta cilla akan Gado.
—————-
‘Karfe 9:00 Na safiyar asabar aka sada Dada da makwancinta, ‘daruruwan mutane ne suka halarci jana’izar baiwar Allah Dada kuma kowa yazo fa’dar alhairinta yake musamman maigidanta Moddibo da shima yana nan tsoho mai ran ‘karfe, ‘ya’yanta su lami’do da su Alhaji Baba ba ‘karamin girgiza suma su ka yi da mutuwar ba, haka nan jikoki da ‘ya’yan jikoki su Shatu, tabbas Dada tayi tsahon rai ta kuma tara zuri’a mai amfani sai dai fatan saduwa da Rahmar Jalla.
Ta mutu daren juma’a an kuma birneta asabar Allah ya gafartawa iyayenmu. Duk inda Shatu tayi idanun mutane ne a kanta ganin yarda tayi wani irin kyau ta kuma cika ko ina mulmul da ita ta ko ina idan ka ganta ba zaka bata shekaru sha bakwai da rabi ba sai dai ka lulata ashirin saboda cikar da tayi, su Akram dama tuni ta yayesu, ba kuma a taho dasu ba suna can gidan Alhaji Baban da ya ‘kera anan liman katagum ‘din.
—————————
‘Karfe takwas jirginsu ya sauka a airport ‘din Nnamdi azikwe da ke Abuja. Mutanen turkey an bayyana a Nigeria bayan tsawon shekara ‘daya da rabi. Kasancewar ba su samu jirgi ba hakan yasa dole gidan Dahda suka nufa da niyyar gobe suyi asubanci su nufi garin Bauchi by flight.
Da murna Anty Amarya ta tare su kamar ta goya su, shi dai Imran sassan Mommah ya tafi da sauri ba tare da ya tsaya rawar jiki wajen Antyn ba. takaici ya kama ta sai dai bata nunaba burinta ya ci abincin da ta riga ta ba’deshi da sihirtaccen Maganin da Shuwa ta kawo mata.
Yana knocking Basirah da Yasirah da suke aiki a parlourn suka kalli juna, suna tunanin bu’dewa, ‘kara knocking ‘din da suka ji an ‘kara yi ne yasa su cewa waye? Ya amsa da “Bu’de” jin muryarsa yasa su bu’de ido, da sauri Basirah ta bu’de. Ya shiga cikin takunsa na ginshira idanunsa zube a kansu, yana amsa sannu da zuwan da suke masa, sai da ya zauna sannan yace musu “Ku nutsu tambaya zan muku,kuna ji na?” Gaba ‘daya suka nutsuwa suka dur’kushe idanunsu a ‘kasa “Tambayar ku zan yi Da gaske Shatu tayi Aure?” Da sauri suka zare ido suna kallon juna ga shi ba daman su yi masa ‘karya hakan ya sa suka sunkuyar da Kai...... ya buga table ‘din da ‘karfi yace “Ba kwa ji ne malamai?” Basirah ce Ta ‘dago idanunta a kansa tace..........
Saduwar alheri ina ji daku mutanena.
Me Zan Yi Da Ita?
41
“Eeh tayi aure...” Yasirah ta zuba mata ido da sauri kafin ta mayar da kallonta akan Imran da ya runtse idonsa gam yana furta “Oh shit!” Yana buga hannunsa a table, sai kuma ya mi’ke hannunsa saye cikin aljihu ya bu’de ainahin ‘dakin Shatu, fes dashi ‘dakin ga wani ‘kamshi da ya kamashi ram na ainahin turaren da take amfani dashi. Idanunsa ya sauka akan wangamemen pic ‘din twins suna babies, zuciyarsa na dukan Tara-tara ya ‘karasa gurin pic ‘din... cikin takaici yake shafa hoton kishi ya cika zuciyarsa fal. Ya shiga tunanin da tuni zuri’arsa ce wannan ‘din. Ji yayi har jiri na neman kada shi hakan yasa ya kwanta flat a saman gadon Shatun, tunaninta ya dinga bijiro masa a yanayin da ba zai fasaltu ba. Da sauri ya dinga jan istigfari tunawa da yayi a yanzu Shatun matar wani ce. Jikinsa a sanyaye ya bar bedroom ‘din nata bayan yaji a yanzu ba abinda yake bu’kata irin yara.
Ko da ya fito Anty Amarya ba yarda ba tayi dashi ba ya tsaya ya ci abinci amma ya girgiza kai “Alhamdulillah nagode” ya yi furucin yana ficewa da sauri. Motar Mommah ya hau ya bar gidan.
Takaici ya cika zuciyar Anty Amarya da Shaheedah da suke jin tamkar su saka kuka.
———————————
‘Karfe 9:00 dai-dai suka isa garin katagum. Gidan a cike yake dan’kam nan ido gaba ‘daya ya koma kan Shaheedah kowa mamakin ramarta yake yi. Wai don ma a haka Hijabi ta sako har ‘kafa.
Lokacin Mommah da Shatu basu iso ba suna gidan su Mommahn, Hajiya Mama ce kawai ta taho amma har su Hafsa da Nahna suna can Gidan ba su taho ba, haka nan Hisham da Ammar.
Dalilin hakan bayan ya gaida jama’ar da suke dam’kar a gidan ya fice da sauri burinsa yaga Mommah. Ita kuwa Shaheedah Hajiya Mama da farinciki ta tare ta, ta sa aka kawo mata kayan breakfast.
Drivern Alhaji Baban yana parking Imran ya fito, cikin takunsa na ginshira, kayan sun amsheshi sun masa kyau sosai ba’kin yard ne a jikinsa ‘dinkinsa na kullum gajeriyar riga da gajeran hannu, wannan karan dai anyi abin arziki ya saka hula a kansa, kuma hular ta amsheshi sosai da sai ‘kamshin turare yake yi.
Ya da’de yana Knocking kafin Shatu da take kitchen tayi saurin fitowa kanta ko ‘dankwali babu, Gashinta gaba ‘daya ya zuba har gadon bayanta. Doguwar riga ce a jikinta mai jikin robber da tabi ta kwanta a jikinta ta kuma lafe ta fidda duk surar jikinta. Fitowar Hisham da Ammar ce ya sata jin wata matsananciyar kunya tayi saurin bu’de ‘kofar kafin ta juya ta shige kitchen ya danno kai cikin parlourn ha’de da ‘kamshin turarensa da ya baibaiye parlourn, wani shock da bugawar zuciya ne ya samu Shatu a lokaci guda, haka nan Imran da Ammar da yake gefe. Da sauri ta juya ta shiga kitchen ba tare da tayi masa second look ba.
Ko a kitchen ‘din ma tsayawa tayi hannayenta dafe da ‘kirjinta tana saurarar yarda bugawar zuciyarta ke ‘karuwa, idanunta na sake hango mata fuskar Ammar da ya sake ‘kawata ta da kyakkyawan saje, yayi fresh sosai alamar Naira ta zauna masa. Wani danshi taji a saman fuskarta, da hakan ya sata saka hannayenta ta ji ko menene mamaki ya kamata da taji wai ashe hawaye ne yake zuba daga idaniyarta ta, hawayen da za ta kira na takaicin ganinsa, ba ta so ganinsa ba a lokacin da komai ya ‘kure. Mutumin da take kwana take tashi dashi, zuciyarta kullum bata fasa tunanoshi ba, in dai za tayi sallah sai ta Ro’ki ubangiji ya zare mata son shi daga zuciyarta, amma abin al’ajabi kullum soyayyar nan ninkuwa take, musamman idan tana ganin Akram da yake tsananin kama da shi. Idan tace bata son Imran ta yiwa kanta ‘karya shine first love ‘dinta da kuma shi ta so tayi rayuwar aure na dindindin, rayuwar da babu tasgaro a cikinta, sai dai tuni ‘kaddara ta riga fata a yanzu dai kam ba zata ta’ba iya kallon idon Ammar tace bata sonsa ba, ko ba zata iya aurensa ba ya riga yayi mata halarcin da bai kamata ta bar shi ba a cikin ko wane hali. Sai kuma ta tuna da jan kunnenta da Hisham yayi akan ko da Imran yazo ta gaya masa tayi aure ‘ya’yan bana sa bane, haka ma ya ro’ki Mommah, hakan ya sa ta sakin murmushi a zuciyarta tace “Za’a buga drammer domin a jikinta ta ji kallon da Imran yake jifanta dashi, ta shafa kanta da ko head tie babu, idanunta akan ‘kirjinta da hips ‘dinta da suka cika fam a cikin rigarta, wata kunya ta kamata ta san dole ko ba so duk namijin da ya ganta a wannan shigar ya baibayeta da kallo, wanda ba zai kasance na komai ba sai na zallar sha’awa. A hankali tace “Astagfirullah! Don kuwa sarai ta san ba muharramanta bane Hisham ne kawai muharrimanta. Ba tayi aune ba ta fara jiyo ‘kauri, da sauri ta kai dubanta ga naman da take tafasawa za tayi shawarma, tuni ta waro ido ganin naman yana shirin ‘konewa saboda tunanin da ya aureta na ba gaira ba dalili, tunda dai bata san da wacce Imran yazo ba. Duk da Uncle Hisham ya fara bata labari.
—————————-
Mommah da take shirya ‘yan jikallenta ta jiyo sallamarsa a bakin ‘kofa, sak tayi tana amsa sallamar cikin wata irin fa’duwar gaba da ita kanta bata san ta mececeba, ganinshi a gabanta ya sa zuciyarta ta karye, ‘kwalla ta baibaye idanunta, tsawon shekara ‘daya da rabi sai yanzu ya tuna da gida? Ta lumshe idanunta tana kallonsa ido cikin ido ‘kwalla ta shiga gangaro mata. Da azama Akram ya shiga share mata cikin salon maganarsu ta gwaranci yake fa’din “Sowi Mommah.” Ya kuma rungumeta, yana fasa kuka shima. Sosai memory ‘din da ya dawo mata yarda Imran ‘dinta yake mata a duk lokacin da ya ganta a
Damuwa, jikinsa kamar an zare laka haka ya shiga takowa inda take idanunsa akan Akram da tun bayan ganinsu yake jin wata fa’duwar gaba.
A gabanta ya dur’kushe ya kama duk hannayenta ya damtse su kamar yarda yake yi a lokutan baya idan yayi mata laifi ya rasa yarda zai yi ya nemi afuwa. Shiru tayi idanunsa cikin na ta kafin ta zare hannunta cikin dakiya da ‘karfin hali tace “Maraba lale da mutanen turkey dirar yaushe kuma?” ‘Ko’kari yayi sosai wajen mayar da dukkan damuwarsa ya saki murmushin ‘krfin hali kafin yace “Jiya muka iso muna Abuja, ya ha’kurin Dada?” Mommah ta gya’da kai kafin tace “Kun kyauta, Dada kuma anzo sa’i sai dai Allah ya gafarta mata yasa kuma can ta fi mata nan. Ina Hakimar take?” “Allah yaji ‘kanta ya bamu ha’kurin rashinta.”
Ya amsa mata yana bagarar da waccen tambayar ba don ya rasa amsarta ba, sai don ba ita bace a gabansa. Mommah ta bi shi da kallo tana kallon yarda yake kallon yaran ta san tambaya ce fal a bakinsa, amma ya rasa ta yarda zai fara, hakan yasa tace “Akram ku gaida uncle ‘din ku.” Yaran suka zuba masa ido kafin su fara gwarancinsu, yana murmushi yake amsa zuciyrsa fal da mamakin yarda Akram ‘din ya ‘dauko zahirin kamanninsa “Mommah yaran wanene?” “Na Shatu” Direct ta ba shi amsa tana mamakin tambayar tasa wato da gaskiyar Hisham da yace bai san an yi haihuwar ba, idan kuwa haka ne waye ya turo wannan message ‘din, akwai alamar tambaya akan hakan sai dai ba yanzu za tayi masa ba sai nan gaba. Ta mi’ke ta fice daga ‘dakin ba tare da ta sake waiwayarsa ba. Shi kuwa flat ya kwanta akan bed zuciyarsa cike da tunaninnika da dama Musamman Shatu yau da ya gani ta zama Hamsha’kiyar mace ta ko ina ta amsa sunanta na mai kyau.”
Mommah na shiga kitchen ta ga Shatu na aikin abincinta duk da ta kammala tana juye su a wammers, ga ikeey a gefenta da take ta kukan noodles zata ci. Mommah ta ja Ikeeyn tana rarrashi kafin ta kalli Shatu tace “Ko ka’dan kada ki bashi fuska ba ruwanki da shi, tunda dai kinga an riga an saka ranar ku da Ammar bana son wani abu yasa a fasa Ammar ne abin a tausayawa yanzu tunda shi ba shi da mata shi kuwa ya rasa ki yana da inda zai je yaji sanyi, yara kuma alamu sun nuna bai san da su ba, don haka kada ki nuna masa nasa ne. Ni da kaina idan ta tunkareni da zancenki zan sanar dashi Ammar zan bawa ke ko ma na riga bashi. Ki kula sosai bana son zubar da aji.” Shatu ta sunkuyar da kai a hankali tace “To Mommah.” “Yauwa ki kiyaye don yanzu haka ya zata kina da aure kamar yarda Hisham ya sanar masa, sai dai a yau idan na dawo a gaban Hajiya Mama zan sanar da shi yaransa ne, aure kuma ba ki dashi sai dai Ammar za ki aura kin ji me na gaya miki?” Shatu ta ‘daga kai kawai a zuciyarta tace ma “duk zancenku kuke ba ni bace a gabansa.”
A gurguje tayi wankan Ta ‘dauko set ‘din mayukanta na makari ta fura mutstsika wa a fatarta da take walainiya kamar ta tarwa’da, ko powder bata saka ba kasancewar gidan mutuwa za suje, ta zira tight trozer ‘din ta da half gown, sannan ta kawo after dress bugun Larabawan Oman ta saka sea blue mai touches ‘din maroum don haka ta yane kan ta da mayafi maroum. Sosai tayi kyau kamar ka sure ka gudu musamma da ta saka medical Glass ‘dinta fari tas da shi da zagayen ba’ki sai ta fito zam kamar Bahabashiya. Duk da ba wata kwalliya ta fesa ba illa lip gloss da ta goga a le’benta.
Takalmi flat ne a ‘kafarta amma yanayin yarda take tafiya sai ka zata hill shoe ne, taku take gaba ‘daya’kugunta da sassan jikinta na rausaya kamar ganyen bishiya. Yarda ya kafa mata ido har bai san san da ya kur’bi tea ya ‘kwareshi ba, hakan yasa duk gurin suka kai duba ga yarda yake kallo. Mommah ta’be baki tayi kawai ta cigaba da shan shayinta. Ita kuwa Shatu tana ‘karasowa ta ha’de rai shi sai ya ga ma kamar harararsa take, ganin yarda suka zuba masa ido sai abin ya bashi kunya da sauri ya mayar da idonsa kan tea cup ‘din da yake hannunsa, amma ‘kasa-‘kasa kallon fresh fingers ‘din Shatu yake yi da suka sha zanen lalle. Tunda yake bai ta’ba yarda lalle abin kwalliya bane sai yau da ya gan shi a hannun Shatu. Tamkar ya sa hannu ya dam’ko su yayi ta shafar su, gaba ‘daya yaji zaman cin abincin ya gundireshi da sauri ya mi’ke ya kai hannu zai zari tissue kamar ha’din baki ita ma Shatu ta kai hannu zata ‘dauka hannayensu suka ha’de just like magnet, wani yarr Shatu ta ji a jiknta tayi saurin ‘dauke nata hannun tana kallonsa, “Sowie” yace wanda muryar sa ba ta fito ba illa la’b’ban bakinsa da suka motsa. Shatu ta ‘dauke idonta tana sakin wata ajiyar zuciya.
Yana juya baya ya ji Akram yace “Mommah uncle waye wannan?” Ya fa’da cikin gwarin hausar sa, da sauri Mommah tace “Go and ask him.” Cikin takaicin wai bai san ‘ya’yansa ba. Yaron yana zuwa ya ‘daneshi, yana cewa “uncle wa?” Imran da sauri ya rungumeshi yana kallon cikin eyes ‘din yaron irinnasa sak ba banbanci, har zai wuce sai wani tunani ya shige shi da sauri ya koma dinning area ‘din idanunsa cikin na Mommah yace “Mommah idan dai har Shatu tayi aure to da cikina tayi aure saboda wannan yaron da ni yayi kama, don haka auren ta bai halarta ba ina da damar maka shi court ya sakar min matata!” Gaba ‘daya gurin suka zuba masa ido...
Kuyi manage da wannan ina gidan mai jego.
Me Zan yi da ita?
Wannan ne complete wancan mistake ne
42
Hafsa da Nahna dariya ta so ku’buce musu sai dai suka gimtse kawai. Yayin da Ammar gabansa ya shiga dukan uku-uku, yaji ganinsa na neman ‘daukewa, tashin hankalinsa ‘daya kada dai ace Imran kome ya zo yayi da Shatu, tabbas kuwa da zuciyarsa ta buga. Da kuma ya sanya hakan a mizani na rashin halarci matu’kar iyayensu za su sake yarda da Auren Imran da Shatu shi kuma ya tashi a tutar babu da ba’a yi masa adalci ba.
Mommah ta’be baki tayi a fusace tace “Sai ka ‘daura himma.” Ta mi’ke ma ta bar table ‘din gaba ‘daya tana ‘ko’karin yakice ‘bacin ran da ya taso mata, na abubuwan da duk suka faru a lokutan baya. Imran kuwa wucewa yayi da Akram aka fa’darsa zuciyarsa fes da samun mafita don ko ba’a yi DNA ba ya tabbatar wannan ‘dan nasa ne ko makaho ya shafa zai yarda da hakan.
A ranar su Hajja su kazo gaisuwa bisa tilastawar Kawu Sa’idu. Har da Zainab aka taho. Lokacin da su Mommah suka zo suka tarar dasu. Zuciyarsu gaba ‘daya sai da ta kusan bugawa da suka ga yarda Shatu da twins ‘dinta suka Koma. Yara kamar ‘diyoyin larabawa jajur dasu ga suma ba’ka si’dik kwantacciya a kansu ga shi jikinsu dumimi a murje gwanin sha’awa. Idanuwan kowa a kansu yake don ma Mommah tana tofe su da addu’oi kafin su shiga taro.
Gaba ‘dayansu da kyar suke amsa gaisuwar Shatu ita kuwa ba abinda ya dame ta bayan ta gaishe su mi’kewa tayi ta fice daga sashen gaba ‘daya tana mamakin yarda Shaheedah ta koma kamar mai cutar ‘kanjamau.” A gefe can daga tsakar gida suka zauna ita da Hafsa da Nahna sai suka zamo tamkar wasu fitulu masu haskawa.
Suna zaune su Imran suka shigo, Idanunsa suka fa’da cikin na Shatu tayi saurin ‘dauke nata ta mayar kan nasu Akram da suka mi’ke da guru, suka nufesu direct Akram wajen Babansa ya